Chapter 20



"Lallai Mukhtar ya cika butulu wanda ba dan halak ba,shiyasa akace idan kaga mutum to ka barshi inda yake koda kuwa dan'uwankane ki duba kiga yanda nayiwa mukhtar halacci a rayuwa amma shine ze rasa wanda ze yiwa butulci seni?ajiyar zuciya mum tayi sannan ta kalli dad da yake ta masifa tace alhaji amma da mun bi komai a hankali zamu gane gaskiyar alamarin tunda kaga bai kamata daga ganin abu bamu tsaya munyi tambayaba mu sawa ranmu anyi mana butulci tunda iya sanina mukhtar da matarsa mutanen kirkine kuma yanda yake nuna kulawarsa shima akan aneesa ina ganin bazeyi mata wani abu ba tare da daliliba,a fusace yace ya isa malama har akwai wani abin da zaa fadamin in yarda bacin wanda idona ya gani?da idona naga matarsa ta mari aneesa kuma yana tsaye babu wani alamar ze hanata,shiru tayi sannan tace duk da haka alhaji ayi hakuri mu bi komai a hankali sannan kaga yarinyar nan meenal karatunta ya fara nisa bai kamata ace ta tsaya da karatuntaba,tsaki yayi yace tashi ki bani waje kafin ranki ya baci na fara ganin alama kamar bakya kishin aneesa ko kadan,mikewa tai ta shiga daki ganin yanda ransa ya baci,itama aneesa wucewa bedroom dinta tayi ta kwanta ji take gaba daya duniyar ma ya isheta yanzu shikenan umma da abba sun gane menene tsakaninta da khushi,shikenan yanzu rabasu za,ayi?wayartace ta fara kara sai data dade tana kallon screen din kafin ta daga,ta daya bangaren aketa magana sai bayan ya gama maganane ta zaro ido kamar yana ganinta tace how did he escape?taya zan saku aiki sannan kuzo kucemin wai ya gudu?bata jira me aka sake cewa ba tayi tsaki ta kashe wayan ta jefar dashi akan gadon....dora hannu tayi akan gashinta tace god something is wrong,gaba daya kantane yake yin ciwo ji take kamar ta mutu ta huta,sai kiran wayan khushi takeyi amma amsa daya ake bata wayar a kashe yake,wani irin ciwo kanta yakeyi kamar zai fashe bayan wani zazzafan tears ya zubo mata daga idonta tace i don't want to loose you khushi i cant live without you rayuwana saboda ke aka yishi wlhy bazan iya rayuwa babu keba khushi,maganganu takeyi kamar wata zararriya gaba daya wunin ranar batayi bacciba duk bayan mintuna sai ta kira number khushi amma amsa daya ake bata cewar wayar is switched off

"Itama bangaren khushi tun bayan abinda ya faru gaba daya ta kasa samun sukuni gashi an kwace mata wayarta gashi sam bata da wani sukuni a cikin gidan kullum fada ne da hantara tsakaninta da umma kwata-kwata ta dena kulata sedai zagi da kallon banza gashi an tsawaita bincike akanta duk inda ta motsa sai umma ta kalleta kamar wata barauniya ko marar gaskiya bata barinta fita ko ina,ita kanta batasan ta damu da anee kamar yanda take jinta a cikin ranta bazata taba iya rayuwa ba tare da aneesa ba cikin 2 days dinda tayi duk ta rame sosai tayi duhu,ganin umma na aiki a kitchen yasa khushi karasawa duk da tasan ba lallai umma ta sauraretaba tace umma kawo na karasa girkin,kallon banza umma tayiwa khushi tace banaso fice ki bani guri,kamar zatayi kuka tace umma don Allah kiyi hakuri mana yanzu bakya barina inayi miki komai kiyi hakuri umma,tsaki umma tai tace wlhy in baki fice min daga kitchen ba zan tsitsinka miki mari sallamar wani yarone ya katse musu sainsar da sukeyi a tare suka amsa sallamar yaron inda meenal tayi saurin fitowa tace kamal menene?wata takarda ya miko mata ba tare da yace komaiba ya kifta mata ido ya fita jikinta sanyaye ta bude takardar,bristol palace hotel room 9 vip section,sai karshen takardar aka rubuta anee,da sauri ta ninke takardar ta boye a hannunta ta shige daki,umma ce ta bude labulen dakin daga tsaye tace me kamal din ya kawo miki?kika shigo daki saboda kin zama munafuka ko?sunkuyar da kanta tayi sannan ta dago tace a,a umma yazo ne ya fadamin basma bata da lafiya tun wancan satin ashe har aiki akayi mata duk bansaniba,cikin sanyin jiki umma tace Allah sarki basma yarinya me mutunci ai bamu saniba wlhy da ni kaina senaje na dubo ta,ajiyar zuciya khushi tayi jin karyarta ta samu shiga tace nima banji dadiba umma ai yanzun nan zan shirya inje in dubota,jirani in gama girki sai muje tare umma ta fada a takaice,gabantane yayi mugun faduwa jin umma tace suje tare toh ita da tayi karyar rashin lafiya don taje taga anee yanzu in sukaje umma taga basma lafiya lau ya kenan?au na tuna hajiya saudat tace zatazo anjima kawai ki shirya ki tafi in yaso gobe sai naje ni umma ta fada tana kallon agogo,wani irin dadi khushi taji kamar zatayi tsalle saboda murna tace toh,umma na fita khushi tayi tsalle akan gado cikin farin ciki tace i love you anee i cant wait to see you,sauri tayi ta shiga bathroom tayi wanka bayan ta fito tayi sallar la,asar ta shafa lotion tasa powder da lip balm,wannan karon ta tsaya tayi kwalliya sosai,black turkish abaya tasa wacce take da kyau sosai sannan ta feshe jikinta da perfume dinta ta dauko jakarta ta fito,a palour ta tarar da umma tana kallo duk da hankalinta baya wajen kallon yana chan wajen tunanin yarinyar tata,cikin sanyin murya tace umma na fito,kare mata kallo tayi daga sama har kasa sannan tace a dawo lafiya kuma karki dade,toh kawai tace sannan ta fita zuciyarta cike da farinciki,tana kokarin saka takalmi paper dake jakarta ta fado ba tare data saniba,sai da umma ta bari khushi ta fita tukunna ta taso ta dauki takardar ta bude ganin bristol palace hotel room 9 ya sata rikicewa da sauri ta fara salati cike da tashin hankali,wannan wacce irin masiface meenal tasa kanta ciki?wannan wanne irin tashin hankali ne haka?yanzu iskancin meenal har yakai ga ana turo mata invitation zuwa hotel don lalacewa?jin kafarta ta kasa daukanta yasata samun guri ta zauna tana jujjuya takardar a hannunta

"Bayan ta shiga napep ta fara duba takardar sedai kwata-kwata ta kasa ganinta,bata damuba saboda ta haddace no dakin da anee ta rubuta,bayan ta isa reception ne aka karasa da ita dakin,knocking 1 tayi anee tayi saurin bude mata dakin muryarta kamar me shirin kuka tace anee......hugging dinta tayi very tightly tace i miss you darling

Thank you for reading my story!!!
My heart is melting for khushi like seriously

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top