Chapter 19




"Jikinta sanyaye ta mike ta kalli aneesa dake zaune a kasa tace kin gani ko?kinga abinda kike shirin jawo mana ko?janyo hannunta tayi tace khushi try to understand ba lefina bane kuma ki kwantar da hankalinki umma bazatace komaiba tunda batasan menene tsakaninmu ba kinji,daga kai khushi tai alamar ta yarda da maganar anee sedai a zuciyarta tasan ba gaskiya bane,khushi ki saki ranki mana please banaso kije gaban umma a wannan mood din ta karasa magana tana tabe baki kamar me shirin kuka,okay kawai khushi ta fada sannan tayi murmushi ta nufi hanyar fita,gabanta na faduwa ta shiga dakin ta tarar da umma zaune a gefen gado da alama khushi din take jira fuskarta cike da damuwa ta kalli khushi,zama tayi a gefen da umman ke zaune tace gani gabanta naci gaba da faduwa,kallonta umma tayi cike da tuhuma tace menene tsakaninki da aneesa?inaso yanzunan ki fadamin abinda yake tsakaninki da ita kafin na sauke miki tafin hannuna a fuskarki,cikin sanyin murya khushi tace Allah umma bakomai,cikin tsawa tace saurara meenal tunda kika taso da hankalinki baki taba yimin karyaba kuma nasan karya ba halinki bace saboda haka kar kice zaki fara yimin karya yanzu saboda idona ya gane min abunda na dade ina zargi,gaban khushi ne ya sake faduwa da sauri ta dago ido suka kalli juna da umma tabbas maganar umma gaskiya ne tunda take tare dasu bata taba yi musu karyaba kuma umma macece mai nuna kulawa akan tarbiya da rayuwar yarta koda bata fadawa umma gaskiyar zance ba tasan cewa ta gane duk abinda yake faruwa tsakaninsu,hawayene ya gangaro daga fuskar khushi bakinta yayi mata nauyi ta kasa cewa komai,itama umma wani irin bakin ciki da takaicine a zuciyarta da sauri tace kina nufin abinda nake tunani gaskiyane meenal?kin cucemu kuma kin yaudaremu kin bata tarbiyar da tun kafin a haifeki muke miki tanadinta,ganin yanda umma ke zubar da hawaye tana magana yasa khushi sake firgita tace umma don Allah kiyi hakuri ba lefina bane don Allah umma ki tsaya ki fahimceni,saukar marin da tajine ya hanata karasa magana inda umma ta mike tsaye tace ficemin daga daki bana bukatar ganin ko inuwarki a gabana meenal,ganin yanda umma ta shiga rudani da rikicewa yasa khushi saurin fita daga dakin wani irin jiri yana dibanta,cin karo tayi da abba a kofar dakin cikin mamaki yace meenal lafiya?umma ce ta amsa mishi cike da takaici tace dole meenal taki amincewa da auren najeeb ashe bin mata takeyi gaba daya aneesa ta lalata mata rayuwarta shiyasa tun farko naki amincewa da zaman meenal a wannan gidan sam ba gidan tarbiya bane,cikin mamaki abban khushi ke kallonsu su duka Innalillahi wa inna ilaihir raj,un shine abinda yake fada cikin zuciyarsa sannan ya kalli khushi dake faman kuka cikin tashin hankali yace meenal abinda nakeji akanki gaskiya ne?sake fashewa tayi da kuka ganin yanda hankalin iyayenta yai matukar tashi cike da nadama tace abba don Allah kayi hakuri wallahi ba lefina bane,hannu ya sauke mata a fuskarta kafin yaci gaba da dukanta kamar Allah ya aikoshi,ganin yanda gidan ya rikice da hayaniya yasa aneesa karasowa palour din don ganin menene yake faruwa,cak ta tsaya ganin abba yana dukan meenal a zafafe,da gudu ta karaso gurin cikin tashin hankali da rikicewa take kokarin rike hannun abba sedai kafin ta kai hannunta umma ta dakatar da ita cike da masifa tace dakata aneesa babu abinda zakice mana kuma babu abinda zamuce miki sai Allah ya isa bamu yafeba,na dade ina ganin take takenki tun zuwanki gidannan na farko haka nayi kokari na bawa zuciyata hakuri saboda zargi haramunne amma yau na sake tabbatarwa saboda haka kiyi gaggawar fita daga sabgar ahalin gidannan bana sonki bana kaunarki ki bacewa ganina tun kafin ranki yayi mummunan baci umma ta karasa magana tana nunawa aneesa hanyar fita daga palour din,babu alamar nadama ko dana sani a fuskar aneesa sai sake hade rai da tayi tace umma ki dena tunanin abinda ba gaskiya bane akaina da meenal kawai zuciyarki ke saka miki wani abu amma,sauke mata mari tayi tace saurara min aneesa idan bamuda arziki toh munada tarbiya saboda haka baze yiwu ki tsaya gabana kina karyatani akan abinda na gani zahiri ba,a tsorace abba ya juyo ganin umma ta mari aneesa itama khushi zaro ido tayi tasa hannu ta rufe bakinta ganin tunda take a gidansu aneesa babu wanda ya taba yi mata kallon banza balle ya mareta,hannu aneesa tasa ta dafe kumatunta cikin tashin hankali tace what?umma marina fa kika yi,cikin tsawa tace na mareki marar mutuncin banza da wofi na mareki din marar tarbiya kawai Allah wadarai da mummunan halin son zuciya irin naki amma ba lefinki bane lefin iyayenkine da suka kasa baki tarbiya,cikin kuka aneesa tace ki fadamin duk abinda zaki fadamin umma zan jure amma tabbas kika sake ambato iyayena kika zaga nima zan rama,marinta ta sakeyi a karo na 2 hakan yayi daidai da yaye labulen dakin mum ce da dad tsaye fuskokinsu cike da tashin hankali dad yace subhanallahi menene haka?da gudu aneesa ta karasa jikin mum ta fashe da kuka cikin tashin hankali dukansu suka tsaya babu wanda yake iya yin kwakkwaran numfashi cikinsu,kallon umma dad yayi yace me aneesa tayi miki kika mareta?sannan ya kalli abba yace amma ka bani mamaki yanda na daukeka ba haka ka daukeniba a gabanka matarka zata dauki hannu ta mari aneesa tare da jifanta da kalmomi marasa dadi?meyasa zakamun haka na baka yarda da amana ashe yaudarata zakayi ka cuceni wallahi na tsaneka na tsani ahalinka na tsani duk wani abu da zai fito ta dalilinka bana sonshi,cikin sanyin jiki abba yace haba yaya ka tsaya ka fuskanci komai mana,dakatar dashi yayi yace bana bukatar jin maganarka daga rana irinta yau har Allah ya dauki raina,kallonsu aneesa da mum yayi yace ku wuce mu tafi,juyawa yayi suka bi bayansa cike da damuwa saboda duk abinda akayi mum tana matukar kewar khushi saboda yarinyar ta shiga ranta yanayin tarbiyarta da nutsuwarta,ganin driver na shirin jan mota yasa mum kallon dad tace Alhaji da mun tsaya meenal din ta fito sai mu tafi saboda karatunta,kallon banza yayiwa mum yace ke wacce irin shashashar macece marar kishin kanta bakya ganin abinda sukayi mana yanzu,toh indai nine mahaifin aneesa daga yau na yanke duk wata alaka da take tsakanina da dan'uwana da duk iyalansa sannan ya kalli driver yace juya ka mayar damu airport

"Bayan Abba ya karbe wayar khushi inda ya sake cin karo da love messages dinda suke exchanging da anee yasa kanshi mugun sarawa,tare da tabbatar da abinda aka fada masa gaskiya ne aneesa da khushi soyayya sukeyi,duk wata hanya da aneesa da khushi zasuyi magana ko haduwa sai da abba yai kokari ya tosheta,bayan su anee sun karasa gidane mum da dad ke tambayarta sedai amsa daya kawai take basu ita sam batasan metayi musu ba kawai suka kama marinta da zage-zage

Thank you for reading my story!!!

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top