Chapter 12



"Cikin tashin hankali hamida ta dora hannunta a kumatunta sannan taci gaba da kallon aneesa cikin mamaki,muryar khushi na rawa tace anee,kallon khushi hamida tayi cike da tambayoyi a bakinta tace kin santane?ganin khushi bata da niyyar bata amsa yasa hamida kallon aneesa tace me nai miki?hannu tasa ta zare sun glass din dake idonta sannan ta gyara tsayuwarta a wulakance tace idan har kazamin hannunki zai ci gaba da taba jikin khushi toh lallai hakan yana nufin yanzu kika fara jero min kalar wannan tambayoyin saboda duk sanda kika sake taba ta sena zartar miki da hukunci,tuni students sama da 20 suka zagaye su aneesa suna tambayar me yake faruwa,dariya hamida tayi jin abinda aneesa ta fada sannan tace amma wlhy a tarihin jahilan mutane ban taba ganin wacce ta fiki jahilci ba kuma babu abinda zai hanani rama marin da kika yimin,hannu ta kai zata mari aneesa sedai kafin hannunta ya karasa khushi tai saurin rikewa tace don't try it hamida please kiyi hakuri,cikin mamaki gaba dayansu suka kalli khushi ganin yanda kiri kiri zata hana a mari aneesa bacin ita ta fara marin hamida,daya daga cikin students din dake tsaye ne yace amma yau nake ganin rainin hankali wato ita da aka mara ba mutum bace kenan ko?daya guy din dake gefensa ne yayi murmushi yace haba abokina ai ya kamata ka dau haske wannan ai kana ganinsu kaga yan lesbian in banda yan lesbian wacce macece zata mari macce akan kawai ta dafota suna tafiya,a tare suka kwashe da dariya daga nan kowa ya watse yana cewa Allah ya shiryesu,ganin an barsu su 2 tsaye yasa khushi kallon aneesa cike da takaici jikinta sanyaye tace kinga abinda kika ja mana ko?tsaki tayi fuskarta babu alamar damuwa tace i don't have a damn!!!kuma dama tuntuni na fada miki i can do anything for you,tana gama fadan haka ta shige mota tai tafiyarta ta bar khushi tsaye gabanta naci gaba da faduwa,jikinta sanyaye ta koma class gaba daya idon kowa ya koma kanta anata gulmarta....

"Ranta a bace tayi parking din mota ko key din bata cireba ta shiga gida da sauri,kan gadonta kawai ta fada wasu zafafan hawaye suka fara biyo kumatunta,sosai take regretting abinda tayi a school dinsu khushi yau amma ya zama dole tayi haka saboda duk duniya ta tsani duk wanda zai zama so close da khushi,sai data dauki kusan 30 minutes tana kuka,mum ce ta tura kofar ta shiga cikin tashin hankali tace aneesa,aneesa meya sameki kike kuka?girgiza kai tayi tace mum ba komai,zama tai a gefen gadon jikinta na rawa tace ya zaki cemin babu komai bacin yanzu atine me aiki tace taga kin shigo gidannan a fusace ko key din motarki baki cireba haka nan kika shigo,meyake faruwane?ganin yanda mum ta damu yasa dole anee tace bata da lafiyane amma tasha magani hutu kawai take bukata,a dole mumcy ta fita daga dakin saboda anee ta huta.....

"Hannun hamida taja suka matsa chan gefe jikinta sanyaye tace hamida don Allah kiyi hakuri da abinda ya faru dazu,wlhy ba,ason raina hakan ta faruba kuma bansan anee zatazoba wlhy,kallon khushi tayi cike da tuhuma tace khushi inaso ki fadamin wacece aneesa,sannan inaso ki fadamin meyasa aneesa ta mareni kuma meyasa aneesa ta damu da duk wani abu da zai shiga rayuwarki?shiru tayi kadan sannan tace hamida wannan tambayoyin ai sunyi yawa kuma yanzu kinga driver chan yazo yana jirana sedai kiyi hakuri zuwa gobe zan amsa miki tambayoyinki amma kafin goben ina sake baki hakuri akan abinda ya faru dazu,murmushi hamida tayi tace babu damuwa insha Allah komai ya wuce,bayan sunyi sallamane khushi ta shiga mota ta wuce gida

"Jikinta sanyaye ta fito daga motar,palour din mummy ta wuce duk da faduwar da gabanta keyi be hanata yin murmushi ba tace mum na dawo,dariya mumcy tayi tace lallai khushi yan jami,a to ya makarantar?lafiya lau mum ashe haka university take da dadi?a tare sukayi dariya tace eh mana yanzu dai kafin ki fara zuba min surutu kije kiyi wanka kici abinci,toh kawai tace har ta juya zata fita mumcy tace au  khushi zonan,gabantane ya fadi da sauri ta kalli mumcy tace gani,yawwa dauki abincin nan ki kaiwa aneesa dakinta tun dazu ta fita ta dawo tana ta kuka na tambayeta meya sameta tace bata da lafiya ne amma nafi tunanin akwai abinda yake damunta,toh kawai khushi ta fada sannan ta dauki abincin kanta na tsananin sarawa ta nufi apartment din anee,a kwance ta tarar da ita sedai yanxu wayace a hannunta da alama charting takeyi,tray din ta ajiye a kasa ta bude fridge ta dauko parfait ta ajiye a kasa da ruwa sannan ta juya zata fita,jin anee ta kira sunanta yasa ta saurin juyowa tace naam,have a seat ta fada a hankali sannan ta dauki parfait din ta fara sha duk da ba wani dadinsa take jiba,sai data shanye parfait din duka sannan ta ajiye cup din ta fuskanci khushi tace inajin kin manta maganar da mukayi dake kwanaki ta cewar indai zaki mu'amala dani ya zama dole ki rabu da kowa ki soni ni kadai ko?idan kuwa baki amince da wannan tsarin ba toh tabbas ina tabbatar miki da cewa yau itace ranar da duk duniya zatasan cewa ni aneesa na fada tarkon son yar uwata mace,da sauri khushi ta kalli anee ganin fuskarta babu alamar wasa yasa gabanta sake faduwa tace anee are you serious?hannu tasa ta bude bottle din ruwa tasha kadan sannan ta ajiye glass cup din tace yap ban taba wasa da soyayyar abinda nakesoba kuma bazan faraba akankiba saboda duk kin fisu mahimmaci,a yau naga abinda ze hanani bacci na tsawon ranaku dayawa wanda bana fatan haka ya sake faruwa,wannan karon ran khushi ya fara baci matuka akan anee cikin fada khushi ta kalli aneesa tace anee meyasa kike son kanki dayawa?bakya ganin batamin sunan da kikayi a school yau?bakisan abinda kikayi min yau ze iya batamin future dinaba gaba daya?ni gaskiya abinda kika yiwa hamida yau be birgeniba ko kadan kuma baki kyautaminb........da sauri anee ta katse khushi cikin mamaki take bin ta da kallo khushi just because i love you shine har kike fadamin irin wannan harsh words din?khushi saboda nace ina sonki zaki tsaya kina kallon idona kina fadamin maganar da kikaga dama?don nayi abinda zai zamo mafita ga zuciyata shine kike cewa banyi dai-daiba so kike na bar soyayyarki ta kasheni kenan?girgiza kai  khushi tayi alamar a,a gabanta naci gaba da faduwa ganin yanda yanayin anee ya sanja lokaci daya,khushi get out from my room ta fada a fusace ganin khushi bata da niyar fita yasa anisa buga hannunta jikin mirror da karfin gaske tace i said get out from my room i don't need you anymore,da sauri khushi ta kalli mudubin jin yayi tsawa ya fashe ga kuma hannun anee yana zubar da jini,da gudu khushi ta rike hannun anee muryarta na rawa tace anee your hand is bleeding,tureta tayi har tana bigewa da jikin bangon dakin tace don't you dare touch me again karki sake interfering kanki dani i don't need you anymore just get out,cikin kuka khushi ta sake rike hannun anee a karo na 2 tace I'm so sorry anee hannu ta kara sawa ta tureta a zafafe tace just leave me alone i don't want you again.....just get out...i said fuck off from here seriously ta karasa maganar tana zare ido hannunta na pointing kofa,jikin  khushi na rawa tai saurin fita daga dakin,a bakin kofa taci karo da mumcy hannunta rike da jug zata shiga apartment din anee,ganin khushi na kuka yasa mumcy karasowa da sauri tace lafiya meenal?menene yake faruwa?cikin kuka khushi ta nuna dakin aneesa tace anee,zaro ido mumcy tai tace meya faru da aneesan?na shiga 3 kalli jikinki jini meenal me kika yiwa aneesan kasheta kikayi?ganin babu amsa ko daya yasa mumcy jefar da kunun madaran a kasa ta shiga dakin da gudu,a tsaye ta tarar da aneesa tana goge hannunta da cotton ganin yanda mirror ya farfashe a dakin yasa mum dora hannu akanta tace na shiga 3 aneesa meya sameki?lumshe ido tai ta bude tace mum karki damu ba wani abu bane it just happened accidentally bansan hannuna zai iya fasa mirror ba,cikin rikicewa mum ta kira dr samar yazo yayiwa anee dressing a hannunta tare da bata wasu magungunan....

"Juyi khushi take akan gado gaba daya bacci ya fita daga idonta tunanin anee kawai takeyi ganin yanda ta shiga wani yanayi wanda bata taba ganinta cikin irinshiba,yanda anee ke riritata amma yau gaba daya ta nuna ko kallonta bata sonyi,jikinta sanyaye ta nufi dakin anee gabanta na faduwa,ganin kofar rufe ya sata knocking muryarta kasa kasa tace who's that?itama muryarta sanyaye tace nice tsaki anee tai tace don't disturb me,duk da knocking din da khushi taci gaba dayi besa anee ta bude dakinba a dole ta hakura ta koma dakinta ba don ranta yaso ba

Ayi manage da wannan zan sake wani posting din daga nan zuwa 12am insha Allah👍🏻thanks for the love and support that you shown toward this book

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top