SAKO...
Yau ta ga ta kanta Mama ta ji abin da ta fadawa Abdul-Aali, dolenta ya sa ta sa mayafinta ta bi bayansa. Ya sa hannu zai bude kofar motar ne, ya ganta, tuni Sulaiman yana zaune a mazaunin direba. "Lafiya dai? Ko kin canza ra'ayin ki ne?"
"Babu, ka yi hakuri, raina ne yake bace. Allah ya kiyaye hanya".
Murmushi ya yi sannan ya-ce. "Ameen, na gode Jidda". Za ta koma ne, ya-ce "Me ya bata miki rai?"
"Ka bar shi kawai, za mu yi maganar daga baya".
"To shi kenan, sai kin kira, sau dayan nan dai a daure a kirani ni ma".
Kanta na kasa ta gyada masa shi, ta wuce cikin gida, bai san sallamar ma albarkacin Mama ya sameta ba. Ita wataran tana ganin karfin halin sa ma, duk abin da take mashin nan, ya kasa hakura da ita. Tana komawa cikin gida ta samu Mama a daki, nan take ce mata.
"Nan gaba ki daina haka, wa ya-ce miki ana wasa da al'amarin miji, ko ba tafiya zai yi ba, idan ma cikin gari zai fita, ki nuna kulawarki gare shi. Bare kuma sha'anin hanya, ai bai dace ku rabu da mutum cikin fushi ba."
Mai-jidda kuka take yi, wanda ita kanta ba ta san dalili daya na yinsa ba, shin don Mama tana mata magana tamkar Ummanta ne, ko kuwa don tana tuna irin zaman da suka yi da ita lokacin da Dokta ke da rai ne? "Assha meye kuma na kuka? Haka za ki zauna da mijinki, kullum cikin kunci?"
"Mama ban san yadda zan yi ba, marigayi na raina har yau, ba zan iya manta shi ba".
"Hauwa, ba wanda ya-ce ki manta shi, asali ma yana da kyau ki rinka masa addu'a, amma kuma hakan ba shi zai hanaki rayuwa ba."
Mama ta mike ta bude wardrobe dinta, dake jikin bango, can ta dawo da wata takarda a hannunta, ta mikawa Mai-jidda, ita kuwa ta dubi Mama cikin alamar tambaya. "Mene ne wannan Mama?"
"Takarda ce." Idanun Mama suka ciko da hawaye sannan ta-ce. "Daga wurinsa."
Mai-jidda ta firgita, tamkar wacce ta ga 'yan fashi "Meye?"
"Shi ya rubuta watanni uku kafin rasuwarsa, yana so a ba ki idan lokaci ya yi." Mama ta dan yi shiru sannan ta-ce. "Kuma ina ga wannan lokacin ya zo, shi ya sa na ba ki".
"Meye..." Mai-jidda ta kasa fito da sautin da ya taso a makogwaronta. "Me ya rubuta?"
Mama ta yi murmushi, ta mika mata takardar. "Ki karanta mana."
Mai-jidda ta sa hannu ta karbi wasikar, tana kallo. Mama za ta tashi ne. Mai-jidda ta yi saurin rike mata hannu, saboda ba ta tsammanin ta shirya fuskantar koma meye yake cikin wasikar nan, ita kadai.
Tana bude wasikar, ta ga rubutun Dokta, wanda ya fara birkicewa a lokacin saboda ciwon ya fara kwace masa ikon yin rubutunsa.
Hauwa!
"Lokacina yana karatowa. Dukkan mu mun sani, duk da ba mu barin haka ya bayyana ko kuwa mu yi magana akai, raina a hannun Allah yake, shi kadai ya san lokacin da zai karbe ni.
Muhammad yana hannun ki, na san za ki kula da shi, saboda ki na daya daga cikin matan da na sani masu juriya, don haka na san ba zai samu matsala ba.
Ke kuma fa? Shin wa zai kula da ke? Na san za ki ci gaba da rayuwa, saboda Muhammad, amma kuma ina son ki kasance cikin farin-ciki.
wannan ya sa na ke rubuta wannan wasikar.
Idan Mama ta ba ki wannan wasikar, to zai kasance saboda alaqa ta shiga tsakaninki da Abdul-Aali ne, na san zai zo dominki. Na sani, na san Abdul-Aali sosai ciki da bai.
Da ba yadda za ayi na kasa gane cewa yana sonki. Ba zai iya kiyaye kallon da yake miki ba, tunda ni kaina ina sonki na fahimci ko menene ma'anar kallonsa gareki. Na fahimci alamomin..."
"Ya Allah!" Mai-jidda ta fashe da kuka.
Mama ta yi saurin shafa bayanta. "Yi shiru, ba komai ci-gaba da karantawa".
Mai-jidda ta share hawayenta ta ci-gaba.
"...Ga abinda zance. Hauwa kar ki damu, ba komai, kar ki ji tsarguwa ko kuwa bakin-ciki a tare dake. Ki kasance cikin farin-ciki. Idan Abdul-Aali ya saki farin-ciki, ki kasance tare da shi, idan baya sonki, ki rabu da shi.
Ki samu wanda zai sa ki murmushi. Ko ba za ki yi don kanki ba, ki yi domina, kin ji? Ba na son rayuwarki ta kare, don kawai tawa ta kare.
Mijinki mai kaunar ki.
Dr. Rayyaan S.
A hankali takardar ta sulale daga hannun Mai-jidda, da ya rasa karfin sa zuwa kasa. Cikin tunanin Dokta ta sa fuskarta a hannunta tana kuka mai tsuma rai, cikin kunci da son da take yiwa mijinta Marigayi hade da wani abu da ya shige ta, wanda ba ta san menene ba.
"Hauwa na dauke ki tamkar yadda na dauki Suwaiba. Abdul-Aali Dana ne kuma na san yana sonki, idan har ke ba za ki iya mayar masa da makamancin son da yake miki ba, ko kasa da haka, to ina ga kawai ki rabu da shi, ki samu wanda zai sa ki farin-ciki."
Mai-jidda ta samu kanta da matukar jin nauyin Mama, duk yadda take da ita, ko take sonta, ta san ita-ce ta haifi Abdul-Aali, ko da kuwa don Danta Rayyaan take kin Abdul-Aali, amma hakan yana mata zafi.
Sai bayan azahar. Sulaiman ya kai ta gida, don dauko abubuwan da za ta bukata, jikinta duk ba kwari. Yanzu daman tun Rayyaan na da rai. Abdul-Aali yake sonta? Yaya za ayi ya so matar Dan-uwansa? Abin yana daure mata kai ainun!
Tana kwance a daki banda tunani ba abin da take yi, wajen karfe hudu na yamma, ta kira lambar Abdul-Aali a karo na farko da ta kira, ba cikin fushi ba kenan, ta kira don ta ji isarsa, kamar yadda ya bukata.
"Hello". Muryar Hamama ta ji, nan take ta ji kamar ta ajiye wayar, saboda ba ta san me za ta-ce ba, cewa za ta yi ta bawa mijinta waya ko me?
"Hello, ina wuni?"
"Mtsss! Ke yanzu ko kunya ba kya ji, bayan kin ji muryata ma, hakan bai sa ki ajiye wayar ba, to bari na fada miki, don kin auri mijina, ba shi zai ba ki damar ki shige mana rayuwa ba. Sai ki jira, idan yana tare dake, ki yi masa magana ko kuwa idan ya fita ya kiraki, amma ba a gidana ba".
Ran Mai-jidda ya baci, me ya sa Hamamatu za ta fadi irin wannan maganar? Duk da Abdul-Aali baya gabanta, ai shi mijinta ne, kuma tana da damar kiransa a duk lokacin da ta so, sai dai idan shi yayi mata iyaka.
"Allah ya ba ki hakuri, daman na kira na ji isarsa ne, amma tunda kin amsa. Hakan ma ya wadatar, ki gaida 'yar..."
Kafin ta karasa magana. Hamama ta tsinke wayar. Mai-jidda ta kufula, zuciyarta ta kawo, don me ya sa za a wulakanta ta, akan abin da ba ma so take yi ba, in dai miji ne, ta je ta bar mata.
******
Da dare bayan sun gama hira da su Mama da su Kasim a falo, kowa ya watse. Mai-jidda tana daki, sai ga Abdul-Aali na kiranta a waya, tana gani har wayar ta tsinke ba ta dauka ba, sai da ya sake kira, sannan ta dauka.
"Shi ne har yanzu ban ji wayarki ba?"
"Hmm! Idan ka san za ka sa mutum ya yi maka waya, sannan ka na da doka akan yin hakan, ina ga tun farko gwamma ka ce kar na kira, sai lokacin da ka ke da sararin yin hakan, kai ka nemeni".
"Ban gane ba, doka kamar Yaya?'
"Ban san idan ka na cikin gidan ka, bai dace na kira wayarka ba, amma tunda yanzu na sani, gaba zan kiyaye."
Ta fada ranta na kuna.
"I'm sorry about that. Amma ban sa wata doka ba. Duk lokacin da wani abu ya taso za ki iya kirana, lokutan da ba na son amsa waya, za ki samu wayar a kashe, amma ki tura Message."
"Sai ka fadawa matarka, don fahimtar ta daban da taka."
Abdul-Aali ya yi shiru, wato Hamama ce ta amsa wayar Mai-jidda. No wonder take ta hada rai, tun da yamma.
"Ki yi hakuri, mu bar wannan maganar, hakan ba zai sake faruwa ba Insha-Allahu. Kin koma gidan Abban ne, ko ki na gida?"
"Na dawo tun da rana."
"To ya yi kyau, akwai isassun kudi a hannunki ko? Idan babu akwai a daki na a durowa, duk sanda ki ke da bukatar su, za ki iya zuwa ki dauka".
"Na gode. Amma ba na bukatar komai".
"To shi kenan." Bayan ya dan yi shiru ne, ya-ce mata. "Yanzu za ki iya fada min abin da ya bata miki rai dazu?"
"A'a, sai dai wani lokacin, don ya wuce. Besides ka bawa Madam time, kafin a kara dora min laifin rike miji."
Murmushi ya yi mai wannan sautin dake tayar mata da tsikar jiki, sannan ya-ce. "Jidda kenan, to shi kenan. Mun yi magana da Abbakar ya-ce, idan zai shigo Kano, zai taho miki da kayanki."
"To, na gode".
"Sai da safe". Ya fada a takaice.
"Allah ya tashe mu lafiya."
Ta kashe wayar a sanyaye, haka kawai ta rasa abin da yake mata dadi. A bangare guda ba abin da ta fi so, irin ta ji ta tsani Abdul-Aali. A bangare guda kuma al'amarin sa na ba ta al'ajabi, jira take yi sai randa ya zo tukun, tayi masa duk tambayoyin da suke ranta.
Haka sati biyu suka yi, suka wuce ba ta gan shi ba, abin dai yana damunta, amma kuma ba damar tayi masa magana a waya. Kullum da dare, sai ya kirata sun gaisa koda na minti daya ne. Wataran ta kan ji kamar ta tambaye shi lokacin zuwan sa.
Amma kuma sai ta fasa, saboda kar ma ya yi tunanin ko son ganin sa take yi. Ita akwai abin da ba ta so su yi magana ne akai a waya, don haka ta yi shiru.
Ran Asabar ta je gidan Yaya Maryam, nan take ba ta labarin wasikar da Dokta ya bari. Yaya Maryam ba ta ce komai ba, sai kallon Mai-jidda take yi.
"Don Allah ki ce wani abu, na rasa me zan yi, kaina ya kulle".
"Mai-jidda kenan, lamarinki akwai abin ban dariya, meye kuma abin kulle kai a nan? Ina ce don Rayyaan ki ke kin Abdul-Aali? To ya bar miki wasiyya, ki manta da shi, ki kuma so Dan-uwansa, idan yana sa ki farin-ciki, dadin karawa, shi da kansa ya-ce kar ki ji guilt na son Abdul-Aali, don haka ya gama cewa komai saura ya rage naki."
"Yaya Maryam ba za ki gane bane, ban san yadda aka yi Dokta yake tunanin so-na Abdul-Aali yake yi ba, ya iya mugunta da gangan yake yi, ya tsane ni. Ki na ga tun da ya tafi yau fiye da sati uku kenan, amma ko maganar zuwa baya yi?"
"Ki na so ya zo kenan?"
Mai-jidda ta gyara zamanta kan gadon, tana wasa da yatsun hannunta. "Zaman wa na ke yi, ni ba na son ganin sa. Amma dai ya kamata ya san ya ajiye mutum a nan, ni ya hana ni aiki na, sannan kuma ya bar ni ba abin yi, ya koma wajen iyalin sa."
"Mai-jidda sha'aninki da Abdul-Aali sai idanu, ba abin cewa, ni dai ina nan dake har zuwa lokacin da zai bude miki idanu, ki san me ki ke ciki, wai a tunaninki duk wannan meye idan ba so ba? Ki na son Abdul-Aali Mai-jidda".
Mai-jidda ta dubi Yaya Maryam a razane. Yaya za ayi ta so mutane biyu a tare? Kai Yaya Maryam ba ta gane ba dai, ba yadda za ayi ta ma so Abdul-Aali fa? Ina! "Ni kuma na so Abdul-Aali. Hmm! Lallai ranar jaki zai fidda kaho. Allah ya sawwaka, na gama soyayya a duniya, sai dai zaman aure."
"To Allah ya bada sa'a."
Ko da ta zo tafiya, sai da ta bi gidanta tukun, ta duba komai lafiya. Ta dan yi share-share, a karo na farko ta shiga sashen Mai-gidan. Babban falo ne mai dauke da (Dining Area) da dakinsa a ciki, sai madaidaicin bandaki daga ciki.
Komai gwanin sha'awa, nan ta shiga ta wanke (Toilet) din, ta duba ma'ajiyin komai a dakin, tana taba kayayyakin tana tunanin, hala Hamamatu ce ta shirya masa su.
Shirmammiya, wa zai shirya masa da to. Ta fada wa kanta. Dakinta ta koma ta dauko turaren wuta ta kunna a dakin. Sai wajen karfe biyar, ta gama kimtsa ko ina, sannan ta kulle ta fito.
A wannan daren zama ta yi kusa da wayarta, amma shiru Abdul-Aali bai kira ba, hakan ya ba ta mamaki kwarai, ganin tun aurensu kullum sai yayi mata waya a wannan lokacin, sai dai idan yana gari. Tun tana jira wayar, ta yi kara har dai ta hakura. Barci ya dauketa.
Sai washegari da safe ta samu wayarsa, ita ma haka ta bari ta yi ta ringing, sannan ta daga. "Ina ki ka shiga haka, tun dazu na ke neman ki a waya".
Mai-jidda ta-ce. "Ba na kusa ne. Ina su Mimie?"
Nan ya-ce. "Bari na ba su ku gaisa". Mai-jidda ta hadiyi wani abu, saboda tsoron abin da zai biyo baya idan Hamama ta san ta yi waya da yaranta, sai dai hakan bai hana ta yi magana da su ba daya bayan daya. Sai murna suke yi sun ji muryar Anty Hauwa.
Baban su ya karbi wayar yana dariya ya-ce. "Kin ji yara ma suna marmarin jin muryarki."
"Hmm! Hakan ya sa na ga jiya ba ka kira ba."
Ya karanci fushi a cikin muryarta. "Da ki ka ji shiru, ke me ya hana ki kira?"
"Ban san dalilin rashin kiran ba, wannan ya sa na ga zan saurara zuwa yau, idan na ji shiru, sai na nemeka."
"Uhmm! Wallahi aiki ne ya min yawa jiya har yamma ina ofis, duk da kasancewar Asabar ce. Ina sallar issha, barci ya daukeni, da na farka kuwa dare ya yi sosai, shi ya sa na kyale ki."
"Yau na je gidan Yaya Maryam, ta can na duba gida."
Ji ta yi ya yi shiru kafin ya-ce. "Haka aka ce miki ake fita ba tambayar izini?"
"Na fada maka, ni ba zan kira wayarka ba, kuma ba ka kira ba, ni kuma ban ga abin kin zuwa ba a duka inda na je ba, shi ya sa na yi tafiyata".
"Gaba nan ko gidan Umma za ki je, sai kin fada min, saboda ba amfanin fita haka ba izini, ki na ji na ko?"
Ta hada rai, yanzu zai fara nuna mata isarsa na shi Mai-gida. "To."
"Sannan ran Alhamis ki shirya, ki koma gida. Insha-Allahu muna tahowa."
Muna tahowa? Abin da ta fi dauka daga zancen sa kenan, wannan yana nufin da su Hamama zai zo, tun da aka yi biki, ba su hada idanu ba, yanzu ga shi za su taho, ko da wane idanu za ta dubeta? Oho.
"To, Allah ya kawo ku lafiya. Makarantar su Mimie fa?"
"Ai za ayi (Public holiday), wannan ya sa za mu taho gaba daya. Sannan akwai Sister din Hamama da ta haihu, duk dai za mu hada tafiyar."
"Allah ya kai mu, sai kun zo".
"Ana maraba da ni kenan."
"Kai ma dai ka fiye rudan kanka wasu lokutan, sai anjima".
Yana dariya ya-ce. "Mu jima da yawa."
Tana kashe wayar, ta shiga tunanin yadda za ta kasance tsakaninta da Hamama, tunda ta san yadda ta dauki zafin abin kawai za ta bi-ta a hankali ne, har ta sauko.
Don batun gaskiya, ko ita-ce hakan ya faru da ita, to ba za ta dau abin da sauki ba. To ma me zai daga mata hankali?
Tun ran laraba ta koma gidanta, ta kara kimtsa ko ina, kasuwa ta shiga ta sayi abubuwan da za ta bukata na aiki. Tun safe ta fara rage ayyuka, saboda ya zamana daidai isowarsu, ta kammala ta kimtsa.
Sai dai har ta ji shigowar mota cikin gate, zuciyarta bai bar bugun uku-uku ba. Dogon numfashi ta ja ta sauke, sannan ta dan samu natsuwa.
Gefenta ta bude, suka fara shiga, don Mai-jidda ta ji hayaniyar yaran. Falon Abdul-Aali ta shirya masu komai daman, tana daki ne, ya shigo. Ta dago fuskarta suka hada idanu. "Sannun ku da isowa".
"Yauwa, sannunki da gida." Shiru ta yi saboda ta rasa abin cewa. "Yaya ki ka zauna a ciki, kun gaisa da Hamama ne?"
"Ina jira tukun, sai sun dan kimtsa, zan shiga mu gaisa."
"To ba laifi." Mai-jidda ta mike ta-ce. "Na ajiye abinci a falonka, akwai drinks kuma a fridge. Idan da wani abu, ina nan".
Kallo ya bi-ta da shi. "Don Hamamatu ta zo, shi ne za ki kunshe kanki a daki?" Kanta na kasa, ba ta amsa masa ba. "Ki fito mu ci abincin tare".
Za ta yi magana ne ya-ce. "Bari na yi sallah kafin nan."
Ba daman ta musa, don bai ba ta filin yin hakan ba. Shigowarsu da kusan minti talatin. Sannan Mai-jidda ta yi sallama a sashin Hamamatu, su Mimie ta samu a falo, nan suka yi kanta a guje, suna murna. Musamman Mimie da ta fi wayo. "A'a Mimie, kin zo ne? Lallai sannunki da zuwa. Me ki ka kawo min?"
"Anty Hauwa, me zan kawo miki?"
"Ina tsaraba ta?"
"Ni ban san inda ake sayarwa ba, sai dai ki tambayi Mami na."
Dariya Mai-jidda ta yi ta-ce. "To lallai, ni kuma ga shi na ajiye maku wani abin dadi, ina Mamin naku?"
"Tana daki, ina abin dadin nawa?"
"Zan ba ki anjima, je ki mata magana, ki ce Anty Hauwa ta zo su gaisa."
Sai dai kafin Mimie ta shiga daki, sai ga Hamamatu ta fito daga ciki. "Mimie ke da wa na ke jinki?"
"Anty Hauwa ce ta zo gaisheki. Mami kin san ta ajiye min abin dadi?"
Hamamatu ta kufula, ita ba ta son rainin hankali, wane gaisheta za ta zo yi, neman gindin zama ko?.
"Sannun ku da hanya." Mai-jidda ta fada ganin fitowarta.
"Meye haka za ki shigo wa mutum ba notice, ba na son wannan kinibibin, bayan abin da ki ka yi, har za ki iya nuna min fuskarki?"
Mai-jidda ta dubi yaran da suke zaune suna kallon Maminsu. "Ba abinda ya yi zafi Mamin Mimie, ki yi hakuri."
"Ko ba ki fada ba kam, hakuri ya zama min dole, tunda kin samu abinda ki ke so, sannan magana ta karshe, ba ruwanki da shiga jikin yarana. Ba ke ki ka haifar min su ba bare ki yi Pretending ki na sonsu, kowa ya yi sabgar gaban sa, tun farko. Ba na son Munafurci, ehe!"
Maganar ta bawa Mai-jidda mamaki, don ita ba ta zaci abin ya yi zafi haka ba. Ba ta kara tankawa ba, ta fita a sashin.
Ko da Abdul-Aali ya nemeta cin abinci, sai ta ji kamar kar ta je, sai dai kuma ba ta son yawan yi masa gardama, hakan ya sa, ta dauki mayafin da ya shiga da atamfarta ta sa a jikinta, sannan ta yi sallama (Side) dinsa. Ya amsa mata fuska a cike da fara'a.
Ita ko kallon sa ma ba ta yi sosai ba, hankalinta duk yana kan maganar Hamama, ai kuwa idan za su yi zaman tare, ba yadda za ayi ta-ce ba za ta kula yara ba, tunda dai 'ya'yan mijinta ne, randa ta haihu a gidan, idan ba ta kula su.
Yaya za ayi su shaku da kannensu, su so juna? Sai a lokacin ta tsaya ta daga ido, ta dubi Abdul-Aali. Subhaanallah! Me ya kai ni tunanin haihuwa da Abdul-Aali?
"Lafiya, Jidda? Me ya faru?'
Ta tabbata razanar fuskarta ya gani a dalilin tunanin da ke ranta. "Babu komai".
Nan suka jira sai da yaran suka shigo, sannan ta zuba masu abincin, ta fiddo Jugs na abin sha kala-kala daga fridge, wanda duk ta hada da kanta. (Mango juice) ne da su zobo.
Ta gama zubawa ne. Hamamatu ta shigo falon, ba abinda take ji, sai kuna, musamman da ta samu Mai-jidda tana zubawa Abdul-Aali drink a kofinsa. Haka dai ta daure ta zauna. Mai-jidda ta mika mata (Serving spoon), saboda ta sa abin da take so.
Haka aka yi zaman cin abincin cikin shiru, sai yaran da suke hira da Baban su. Tana gamawa, ta mike ta bar falon. Abdul-Aali yana ganin yadda suka yi, ya san ya samu babban matsala a hannu, idan bai dau mataki ba.
*****
Ufff don't let me forget, get ready for the next chapter. It's going to be interesting. Reaaally interesting 😀😀😉☺️☺️
Drop lots of votes and comments.
Thank you
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top