RIKITACCIYAR ALAKA

Mai-jidda ta ajiye numfashi, ta kasa yarda wai Abdul-Aali take mayarwa amsa, kuma yana zaune yana saurarenta ba tare da ya yayyankata ba, don ta san tsanarsa ta kai haka.

"Ni zan koma nan da Three weeks Insha-Allahu, idan har kin canza ra'ayinki, ki na son ki saurareni, sai na zo mu yi magana a tsanake kafin nan."

*****

Ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, nan take wani bakin ciki ya damketa, yau Dokta baya nan, wai har shi ne zai sa mutumin da ya fi kowa tsanarta a duniya ya zo ya-ce zai aureta, sannan ma kanin Dokta? Bayan ma haka yana mata tamkar dole ne ta amince.

"Yanzu har za ka iya daga idanu ka dubi kanka a madubi, bayan abinda ka furta?"

Abdul-Aali ya tsaya yana duban Mai-jidda. "Duk duniya ba wanda Rayyan yake so kamar ka, babu wanda ya amincewa ya fi kauna kamar kai, amma yau a rashin sa kana nema ka auri matar da ya mutu ya bari.

Bayan a lokacin da yake da rai ba ka da makiyar da ta fita? Don me ya sa zan saurare ka, don me ya sa zan yi tunanin akan wannan gurbataccen al'amarin? Duk yadda Dokta ya so mu daina kyarar juna, na san ba zai amince ka auri matarsa ba, koda kuwa bayan ransa ne."

"So ki ke yi na bari wani ya auri matarsa? Yaya za ayi na barki da Danki ku shiga wani hannu da ban san rikon da za ayi maku ba. Bayan ku na matsayin amana a gare ni?"

"Muna matsayin amana a gareka ka, iya tafiya har na shekara guda ba tare da sanin halin da muke ciki ba, mun mutu ko mun rayu? Rashin ka bai rage mu da komai ba, saboda haka idan amana ka ke son rikewa.

Ka rike na wanda ya zamo maka lallai, shine Muhammad, shi ne maraya, shine mai bukatar kula, amma ni kam, ina tsammanin na wuce nan." Ta fada tare da goge hawayen ta, sannan ta-ce "Allah ya kiyaye hanya."

Muhammad ne ya koma cikin gida da gudu ya-ce. "Umma Mamana tana kuka". Daidai lokacin ta fito daga falon ta samu Umma akan baranda tana zaune kan tabarma.

Ba ta san lokacin da ta zube jikinta ba, ta rushe da kuka mai taba zuciya. Tabbas yau ta san Dokta yayi mata nisa. Allah ya masa rahama.

Amma yanzu kwata-kwata ma ji ta yi auren ya fita a ranta. Umma ta-ce "Mai-jidda, lafiya ki ke kuwa, me ya faru haka?" Ba tare da ta bawa Umma amsa ba, ta tuna ranar da ta san cewa lokaci kawai suke jira...

Idanunsa a rufe suke, amma ba barci yake yi ba, yayin da numfashinsa yake fita da kyar, nan ma da taimakon roba mai bada iskar Oxygen.

Bakin sa ya bushe, ba abin da za ka ji a dakin, sai karar na'ura kawai, a cikin shekaru biyu da suka shude, anyi masa aiki sun yi uku.

Sannan kusan gabaki daya shekarun a asibiti suka shudesu, randa ya yi lafiya a sallame su. Amma a wannan lokacin an daina maida shi gida ma, saboda wahalar da yake samu a dalilin hakan.

Tun aikin da akai masa na karshe. Dokta ya bukaci a maida shi Najeriya ya yi jinyarsa a can, ko ya raka ganin 'yan-uwansa duka da Dansa kullum a gefensa. "Hauwa na fi son idan lokaci ya yi, na kasance cikin 'yan uwana, cikin gatana."

Hannu ta sa ta toshe bakin sa. "Muna nan a tare da kai har zuwa lokacin da za ka warke, kowa yana jiranka, kar ka cire rai, do not lose hope."

Murmushi ya yi cikin rashin karfin jiki da sarkafewar murya ya-ce. "Hauwa, kin tuna lokacin da ki ka ce kar na sake boye miki komai ko?"

Ta gyada masa kai. "To wannan karon ba zan boye miki ba, amma ni na san lokacina ya kusa, gaskiyar maganar, ita-ce ba zan..."

Tari ne ya sarke shi kafin nan ya ci-gaba "...Tashi ba. Na gode sosai da juriyarki da kokarin da ki ka yi a kai na. Allah ya saka miki da aljannar firdausi..."

Cikin kuka ta fada jikinsa, rigar sa a cikin hannunta take wasu maganganun da ita kanta ba ta san meye take fadi ba. Abdul-Aali ne ya shigo dakin ya tarar da su a haka, ya sa kai zai juya ne. Rayyan ya yunkura ya kira shi da hannunsa.

Mai-jidda ta tashi ta zauna, idanunta sun yi luhu-luhu da kuka. "Abdul-Aali, Hauwa da Muhammad amanata ce a wurinka, koda wani zai tozarta su, kar ka bari su wulaqanta. Allah shi ne gatansu, na bar maka su amana."

Abdul-Aali ya kawar da kansa gefe, yana share kwalla, daga bisani ya rungumi Dan -uwansa "Insha-Allahu ba abin da zai faru."

Rayyan ya kada kai ya-ce. "Da ni da kai mun sani..." Numfashin sa ne ya soma yin sama-sama, cikin sauri Abdul-Aali ya kai hannu kan robar hancin sa da ya cire na Oxygen, daidai lokacin Mai-jidda ta kai hanunta, don ita ma ta mayar masa. Da sauri ta cire hannunta ta matsa da baya.

"Yana bukatar hutu, ki daina zuwa ki na tayar masa da hankali da koke- koke." Ba ta yi mamakin kalamansa ba. Mamakin da ta ji shi ne na inda ya furta kalaman nasa. Dokta Allah ne kadai gatan mu, amma wanda ka barwa amanarmu, tunda ranka ma yana kyarar mu.

Bayan Umma ta gama sauraren Mai-jidda ne ta-ce. "Lallai wannan abu da daure kai, ke dai ki yi ta addu'a. Allah ya yi miki zabi na-gari".

"Umma ba ma yadda zan sa Abdul-Aali a addu'ata, saboda ba mai yiwuwa bane ma, ba na fatan ko a mafarki ne hakan ta faru bare a zahiri.

Don haka zan rabu da shi ne har ya gaji ya bari." Umma ta jinjina kai, don ita ma kanta tana tunanin yiwuwar wannan al'amari.

Ransa na kuna ya bar Dutse, ba haka ya so ya baro can ba, ya so ya kawar da wani tunani a tare da Jidda. Amma kuma ya kula da abu guda, har yanzu ba ta manta da mijinta ba.

Lokaci take bukata, wanda shi kuma bayida shi. Yana isa gidan Abba ya wuce, ya san a can zai samu su Hamama, sai da ya ci abinci.

Sannan ya bada motar Mukhtar wa kaninsa Kasim ya-ce ya kai masa ita. Nan ya biyewa su Mimie, don su kawar masa da damuwar da ke ransa, har bayan issha, sannan ya-cewa Mama. "Yau kam mun gaisheki, sai an kwana biyu kuma".

"Wannan wace irin gaisuwa ce? Ni ku bar min Ramlatu anan za ta kwana".

Mimie ta juya ta-ce. "Daddy ka yarda mu kwana?"

Abdul-Aali ya yi dariya ya-ce. "Idan ku na da kaya anan, ba sai ku kwana ba." Mimie ta juya ta dubi Mamin ta. "Mami mu kwana?"

Dole dai haka suka baro yaran a gidan Abba, sannan suka kama hanyar gida, ta kula da yadda ya yi shiru da yawa, saboda haka da farko ta yi tunanin ta rabu da shi, don ba yau ya fara ba. Amma daga baya ta canza ra'ayinta.

"Sweety, yau kam zan iya sanin dalilin da ya sa ka ke janyewa walwala a wasu lokuta?" Sai da ya yi firgigit! Ya gane magana take masa.

"Great! Ina maka magana ma ba ka san ina yi ba, wane irin abu ne yake dauke maka hankali haka?"

Abdul-Aali ya yi ajiyar zuciya a ransa ya-ce. Da kin san abin da yake dauke min hankali da kuma irin wahalar da take ba ni, watakila ki tausaya min, ki tayani rokonta. Amma shi ma ya san kuskure ne furta hakan, don wannan sai ya-ce mata.

"Wani abu ne na ke matukar so, kuma yana ba ni wahalar samuwa. Don haka ki tayani addu'a. Allah ya zabar min da abin da ya fi alkhairi. Idan kuma alkharin ne, Allah ya ba ni ikon cimma sa cikin gaggawa."

Hamamatu ta yi shiru, tana duban Abdul-Aali, ta san shi da abubuwa da dama, amma a cikin su banda damuwa da abin duniya. Wannan ya sa ta tunanin ko me yake so har haka da zai iya dauke masa hankali?

*************

Cikin dare ta samu kanta da gwada wayar Dan Kano da zummar ba shi labarin abin da take ciki, ta san zai ba ta shawara, sai dai kash!

Shi ma ta tuna rabuwar da suka yi ta baram-baram!

Mai-jidda na zaune a ofis dinsu, banda damuwa ba abin da take ciki. Walida ta shigo ta dubeta, sannan ta-ce. "Alhaji Yusuf ya zo yana ofis din Manaja."

Mai-jidda ta sauke taguminta ta-ce. "Yau na ga ikon Allah, wasa ki ke yi dai ko? Mutumin da muka yi da shi sai a Weekend zai zo gida, ba ranar aiki ba ma, shi ne zai ce na same shi a ofis din Manaja?"

"To ni dai sako aka ba ni, idan ba ki je ba, ki na ji, ki na gani zai shigo har nan ya same ki, don kin san zai iya aikatawa, in dai a kanki ne."

Mai-jidda ta ja tsaki hade da buga wani sabon tagumi. Tana zaune har sai da Walida ta sake mata magana tukun, sannan ta mike zuwa ofis din Manajan.

Ga mamakinta shi kadai ne a ofis din, da alama ya yi aron ofis din ne, don su gana, to meye ne mai muhimmanci da ba zai jira sai ya zo gida ba, ko kuwa ya fada mata a waya, har sai ya sameta a wurin aiki?

A tsume ta zauna, wanda aka yi fushin domin sa kuwa ya kula da hakan. murmushi ya yi ya-ce. "Haba Hauwa Kulun Majada, duk wannan fushin wa Yusuf shi kadai ake yiwa?"

Dole ta sa ta dan saki fuska kadan. "Yallabai, a tunanina mun gama magana kan cewa koda maganar mu za ta dore ba za mu hadu a ofis ba".

"Na ji, ina kuma neman afuwa, saboda saba yarjejeniyarmu, amma wani albishir na zo miki da shi, wanda ba zai iya jira har karshen mako ba." Ya fada yana kallonta. A hankali ta-ce. "Albishir kuma?"

"Eh, na gama shawara kuma ina son bada dadewa ba na tura gidanku, domin ayi min tambayar aurenki."

Wani sauti Mai-jidda ta saki, shi ba dariya ba, shi ba kuka ba, har ma sai an yi wata shawara a kanta.

A bangare guda an maida ita abin gado a wani bangaren kuma ana shawara kafin a mallaketa, tamkar kaya. Wayyo duniyar maza! Ita Hauwa'u ko yaushe za su gama dawainiya da ita a cikin ta oho.

"To, lalle magana ta girmama, amma dai ina tsammanin wannan shawara ba da Yayata aka yi ta ba ko?"

Alhaji Yusuf ya yi murmushi, yana sosa habarsa ya-ce. "Yayarki kam ai sai lallaba, ke dai mu yi fatan samun alkhairi cikin wannan al'amari".

Ta auna amsar ta sa, sannan ta-ce "Ameen."

"Wannan ya sa na kira ki, don na ji wani lokaci ki ka ga ya fi dacewa su je?"

"To ba damuwa, zan dan bukaci lokaci, domin na isar da maganar ga Baba duk lokacin da ya bayar, za ka ji daga gareni Insha-Allahu".

"To, Allah dai ya sa bada jimawa ba, don ba ni da burin ya wuce na gan ki a gidana."

Murmushi Mai-jidda ta yi. Duk da ba wani dadewa ta yi da Alhaji Yusuf ba, amma ko wani lokaci sai ya nuna mata tana da muhimmanci. Har tana shirin mikewa ne, ta zauna ta-ce.

"Yallabai, ina ga ka manta wayata na aiki, wannan albishir din ai ko ta waya ka isar, yanzu idan aka ga karamar ma'aikaciya irina ta fito daga ofis tare da mai kamfanin gaba daya, ka ga ai kowa da abin da zai raya a ransa".

Alhaji Yusuf ya-ce. "Ko ba komai na ga sanyin idaniyata, maganar abin da ma'aikata za su ce kuma, su fadi abin da suke so, saboda kwanan nan za su ga katin gayyata Insha-Allah, kin ga zargi ya kare kenan".

"Ka san sha'anin aiki, kar su dauka ina samun wata kulawa ta musamman daga kamfanin, tunda ina samun bakunta daga mai shi."

"Hauwa kar ki damu. Insha-Allah, na gane na yi kuskure, nan gaba idan na tashi zan yi amfani da waya shi kenan?"

Murmushi ta yi sannan, ta-ce "A gaida Yayata".

"Za ta ji."

Ita ta fara fita zuwa ofis din su, nan ta samu Walida na jiran kwakkwafi. "Ke da ki ke cewa ba za ki je ba, shi ne daga zuwa har da shan zaman ki ko?"

"Hmm! Ke dai bar ni da Alhaji Yusuf, wai nan zuwa ya yi ya fada min zai tura ayi tambaya, yana bukatar na ba shi lokaci."

"Ke da zafi-zafin sa ashe, to me ki ka ce masa?"

Nan ta fada mata yadda suka yi. Walida ta-ce. "Ke sha'aninki sai ke Mai-jidda, me ki ke jira kuma? Alhaji Yusuf mutumin kwarai ne, kowa ya san halayensa, sannan ya gwada miki so a zahiri, ya nuna kaunarsa gareki da Danki, me kuma ki ke nema?"

"Hmm! Walida ba na miki fata, amma ki na fadan haka ne kawai, don ba ki san mutuwar miji ba. Har yanzu Dokta na raina."

Walida ta zauna a kujerar dake fuskantar ta Mai-jidda.

"Duk da ban san mutuwar miji ba, amma na san abu guda, shin rashin mancewa da shi zai dawo da shi, ko kuwa haka za ki rayu cikin tunaninsa iya ranakun rayuwarki, dole ki ci-gaba da rayuwa. You have to move on.

Ko shi ba zai so ya gan ki cikin kunci ba. Rayyan wani bangare ne na rayuwarki da ya wuce addu'a ce tsakanin ki da shi, ki kuma tarbiyyantar da Dansa zuwa hanya na kwarai, ki gwada masa son mahaifinsa. Amma ke kuma fa, za ki kasa rayuwa ne saboda rashinsa?"

Mai-jidda ta nisa tare da jinjina zancen Walida. Tabbas! Gaskiya ta fada mata, kuma ita ma tunanin da ta yi kenan, wanda har ya sa ta samu karfin gwiwar bawa Alhaji Yusuf dama.

Amma tambayar aure yanzu, kamar ya yi sauri, ta fi son ta san mu'amalarsa da matarsa kafin ta shiga, don zai iya yiwuwa yadda yake a waje, gidan sa ba haka yake ciki ba, shi ya sa za ta bi a hankali tukun, kafin abubuwa su yi nisa. Kada ta dau kara da kiyashi....!

*****

"Mabruka kenan, ni dai nace masa zuwa karshen wata mai kamawa, kafin nan mun kara fahimtar juna".

"To Allah ya tabbatar da alheri, na yi murna kwarai, lallai Alhaji Yusuf ya taka rawar gani, tunda ya rusa wannan katangar. Allah ya nuna mana lafiya".

"Hmm! Ina Farida da Babanta?"

"Lafiyarsu kalau! Farida ta kusa shiga makaranta".

"Wai sai yaushe za ku zo mana ne, kun je kun makale a Ibadan, kamar an shuka ku".

Mabruka ta yi dariya. "Lallai akwai gagarumin abu, yau ni kuma ai dole na tattara na taho. Dole nace Hafiz ya tattara aiki ya ajiye kawata ta yi miji, za mu taho biki"

"Ke dai zolayarki ta yi yawa, ki gayar min da 'yata sai kun zo." Kamar ta ba ta labarin wainar da Abdul-Aali yake toyawa, amma ta yi shiru, saboda ko maganar ba ta son tunawa, bare maimaitawa.

Suna gama waya da Mabruka, ta shiga taya Umma ayyukan gidan, suna cikin aiki ne, sai ga Anty Fauziyya ta shigo.

Nan Mai-jidda ta mai da hankalinta kanta, suka koma dakin Umma. "Kawai ranar sai ga Abdul-Aali har gida, har da shiga dawainiya. Don Allah ki min godiya idan kun yi waya".

Mai-jidda ta zaro idanu, yanzu kuma Abdul-Aali sayan danginta yake tunanin yi ko meye "Yaushe ya je gidanki?"

"Last week, ke kuma ashe ya dade da dawowa, shi ne ko ki fada, sai da ya zo yake fadawa Yayanki".

"Hmm! Ki rabu da shi kawai, duk wani dadin bakin da zai maku, kar ku ma saurare shi."

Fauziyya tayi mata kallon mamaki, "Abdul-Aali fa nace, ko kin dauka wani na fada?"

"Shi din na ke nufi. Anty Fauziyya ke ba ki san me ya zo min da shi ba, yana neman rikito min wani rikincin da ya fi karfina ne, na daukar dala ba gammo."

Nan Mai-jidda ta fadawa Anty Fauziyya duk yadda suka yi da Abdul-Aali.

"To, ni ban ga laifi ba anan, don ya-ce yana son auren ki, meye laifinsa? Ai ni ina ga ya kyauta ne ma da yake so ya rike ki da Danki".

"Idan ya yi niyyar kyautatawa, ai hanyoyin yinsu da yawa, me ya sa zai ce zai aureni? Ni fa na san shi, baya kaunata ko ta kwayar zarra."

"Ke ki na kaunar Alhaji Yusuf ne, da ki ke shirin auren sa?"

Mai-jidda ta dubi Anty Fauziyya, sannan ta-ce. "Ba anan maganar take ba, ni na san tafiyar mu za ta zo daidai da Alhaji Yusuf, kuma baida wani hali da ya yi kama da na Abdul-Aali. Sannan ina son yanayin komai nasa, domin mutum ne mai kamala."

"To ashe za ki iya auren wanda ba kya kauna kenan, shin da bakinsa ya shaida miki baya kaunarki, ko ya tsaneki? Kai idan baya sonki, me zai sa ya-ce zai aureki? Bayan ba iyali ya rasa ba, ba komai ba, sannan shi ba karamin yaro bane, bare ya yi maku wasa da hankali."

Ajiyar zuciya Mai-jidda ta sake kawai, ta san Anty Fauziyya ba za ta fahimci daga inda take tunani ba, don haka ta-ce.

"Shi kenan, tunda sun yi haka, amma ai ni ban ce ina kaunarsa ba, kuma nace ya kyale ni, ashe ba sai ya kyaleni ba? Ko an taba auren dole?"

"Ba a taba ba, amma dai ni shawarata shi ne ki ba shi dama, ki gane hakikanin manufarsa, ya fi ai, kin san sai an gwada, akan san na kwarai. Kuma magani sai da gwaji"

Mai-jidda ta yi kwafa. Allah ya sawwaka ta neme shi, tana da zuwa Kano. Kai Muhammad ganin su Mama, amma haka ta hakura har zuwa lokacin da ya dace Abdul-Aali ya tafi, kamar yadda ya fada mata, sannan za ta tafi. Ai sai dai ya samu labarin aurenta, amma ba dai da shi ba kam. Bindin rakumi ta yi nesa da kasa.

*******

Hankalinta a kwance, ta manta da wata sabga ta Abdul-Aali. Ranar Juma'a ta shirya Muhammad don ta kai shi wurin su Mama a Kano. Yaya Abbakar ne zai kai su.

"Ki gaishe da su Hajiya Zainab din".

"To Umma za su ji Insha-Allahu, gidan Yaya Maryam zan kwana, ina ga sai lahadi Insha-Allahu zan juyo".

"To ba damuwa, kin yi sallama da Baban ku ne?"

"Eh, tun kafin ya fita ma."

Umma ta jawo Muhammad jikinta ta-ce. "To, banda kiriniya Babana. Yaushe za ka dawo?"

"Ni kam a can zan zauna."

Umma ta yi dariya ta-ce. "Shi kenan, idan ka zauna a can, na fasa auren."

"Shi kenan Mama za ta aure ni ai."

Suka yi dariya, sannan suka fita, inda Yaya Abbakar ke jiran su. Mama ta yi murnar ganinsu sosai, da gudu Muhammad ya shiga falon Abba, yana cewa yau kam ya dawo kuma sai an masa aure da Mama ya koma.

Mai-jidda na zaune a dakin Mama, ta shigo dakin, haka kawai ta samu kanta da faduwar gaba da kuma jin wani iri, musamman da ta gan shi ya shigo rike da Ramla a hannunsa, tana murmushi ta-ce. "Mamin Mimie, ku na nan ashe ba ku koma ba."

"Kai Anty Hauwa, har na ji kunya, ba ki ganmu ba, duk ga shi nan Sweety ne ya yi ta wasa da hankalinmu".

"Ba komai ai, komai lokaci ne, shi kam ai muna ganin shi ko bai fada miki ba?"

Nan take hankalin Abdul-Aali ya tashi, ya dubi Mai-jidda da sauri ya kada mata kai hade da cewa. "Rabu da ita Jidda, tun zuwansu in banda yawo, ba abinda suke yi".

Mai-jidda ta yi murmushi ta san Hamama ba ta da labarin abin da yake da shirin yi, don haka ta san maganin sa.

"Mamin Mimie ku wane irin aiki ku ke yi ne? Kun kwashe wata guda ba ku wurin aikin ku."

"Ai sai wata mai kamawa ne zai koma bakin aikin na sa."

Mai-jidda ta karbi Ramla, tana mata wasa. "Ina Muhammad din yake?"

"Muna shigowa, ya yi falon Abba yana can yanzu haka ya cika shi da surutu."

Tana sane da Abdul-Aali dake zaune kan kujera bai fita ba, don haka gaba daya ta kasa sakewa. Hamamatu ta-ce. "Ki na nan ne ko kuwa yau za ki koma?"

"Zuwa Sunday dai Insha-Allahu, zan duba su Yaya Maryam".

"Allah Sarki, ya kwana biyu ba mu hadu da ita ba Sweety, yaushe za mu je na gaishe ta?"

Abdul-Aali ya kalli yadda Mai-jidda ta hada rai, sai ya-ce. "Tunda ita ma za ta je, ba sai ki jira, idan ta zo tafiya, sai na kai ku ba?"

"A'a kar mu bata maka lokaci, ka bar ta kawai, za mu yi tafiyar mu." Mai-jidda ta fada da sauri.

"Ke ma dai kya fada masa Anty Hauwa, bini-bini ko ina, sai ya-ce shi zai kai mutum, ba dama nace ya ba mu, ko danin motarsa mu zagaya son ran mu, sai ranar ne ya ba mu sau daya."

Mai-jidda dai ba abinda yake damunta, irin yadda Abdul-Aali yake mata wani irin kallo a gaban matarsa, duk sai wani iri take ji. Ga shi ya samu wuri ya zauna baida niyyar fita, sai canza tasha yake yi a T.V.

Amma tana sane hankalinsa ba a kan T.V din yake ba. Don sau biyu suna hada idanu, idan ta kai masa harara.

*********

hahahhaa😜

Abdul Ali na da guts, what do you think? 😂

So barka da sallah, kuma ina naman Sallah na?

A miko tare da himilin votes da comments.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top