RIKITACCEN SAKO


I know you like me😉

Okay here is a double update for today.

Because...

Because KNKS is at number 7 today in Romance

Awesome, yaaron. I love you to bits and pieces keep voting and showering this with lots of comments, share and add to your reading list in fact recommend to all your zuri'a.😜

Huge twist coming up

And I'm afraid we are two more updates away from ending KNKS.

Write your thoughts.

If you've not been commenting please do so, we want KNKS at number 1 someday😉

******

Abdul-Aali baya samun matsalar zuwa Weekend, wani lokaci sai bayan sati biyu yake zuwa. Yara suna hutu, ya karbi nasa hutun gaba daya suka antayo. Muhammad kuwa tamkar jira yake yi, yana ganin 'Yan-uwan sai murna.

Suna isa Mimie ta-ce. "Mami, zan je gun Anty Hauwa mu yi wasa da Muhammad".

Hamama ta zare mata idanu ta-ce. "Wasa? Bayan dazu ku ka shigo? Ku zauna ku huta, ba na son kaudi."

Mimie ta bata fuska, tana buga kafa. "Mami, ki yi hakuri kin ji? Ba za mu dade ba a falon Anty Hauwa ne fa".

"Nace miki babu inda za ku je, ku zauna. Ga Cartoon nan na kunna maku, ko kuma ki yi wasan da Ramla, amma daga yau idan na kara ganin ki a falon Anty Hauwa, sai nayi miki bulala."

Abin ka da yaro, sai Mimie ta sa kuka da bori, a haka har barci ya dauketa. Da yamma ya shigo ya sameta a kwance. "Yaya, yau kuma Mimie da barcin yamma, sai ta tashi ta yi ta rikici ko?"

Hamama ta kalle shi, ba ta ce komai ba, idan ya tashi tamkar shi kadai ne mai 'ya'yan.

"Ki daina bari tana irin wannan barcin." Ya fada yana gyara mata kwanciya. Sannan ya-ce. "Ba abinda zan samu ne a kicin dinki?"

"Kwadayin ya motsa kenan, me ka ke so?" ta fada murya kasa-kasa.

"Koma meye dai, amma marar nauyi."

Nan ta koma kicin ta samo masa wani abin, sannan suka zauna suna hira, yana ci. Ba abin da ya fi mata haka dadi, suna zaman zaman su, ya kama ya bata masu rayuwa da wani aure na fama.

****

Mai-jidda dai ba abin da yake damunta irin yau kwana uku kenan, ba ta ganin yaran a Side dinta, sai sun tashi cin abinci, duk da haka dai ba ta yi magana ba.

A kwana na hudun ne. Abdul-Aali ya-ce. "Mimie, je ki falon Anty Hauwa ki kira Muhammad ku zo mu tafi yawo."

Har ta tashi za ta tafi ta dawo ta-ce. "Dadi, Mamina fa ta-ce na daina shiga falon Anty Hauwa ko kuma ta min bulala."

Abdul ya sunkuyo daidai tsawon yarinyar ya-ce. "Mamin ki ta-ce ki daina shiga? Kin yi tsokana ne ko barna?"

"A'a wasa ne fa za mu yi da Yaya Muhammad, shi ne ta-ce kar na je. Har na yi kuka, amma ta ki ta barni na je."

Ya dago kansa cikin al'ajabi ya-ce. "Kar ki damu ko? Ku rinka zuwa ku na wasan ku Anty Hauwa ma Maminku ce, kin ji?"

Ta daga kai tana murna, da sauri ta bude kofar Side din Mai-jidda. Abdul Ali bai nemi magana da Hamamatu ba, har suka tafi unguwarsu suka dawo. Sai washegari a gabansa, ya ga tana zarewa Mimie ido, don ta ambaci shiga Side din Mai-jidda.

"Mimie kama hannun Ramla, ku je ku yi wasan ku." Suna fita ya-ce. "Hamama, abin da ki ke koyawa yaran nan ya dace kenan a ganin ki?"

Cikin rashin kulawa ta-ce. "Me kenan?"

"Ina sane da cewa kin hana yaran nan zuwa sashen Jidda. Akan wane dalili za ki hanasu mu'amala?"

"Oh, akan wannan ne, shi ne za ka wani tada jijiyoyi? Ni haka kawai ba na so."

"Kin yi adalci kenan, idan kin yi haka? Yin hakan da ki ka yi, zai sa su dauketa a matsayin uwa ko kuwa wani abin ki ke nema ki cusa a cikin zukatan yara kanana da ba su san komai ba, na sha fada miki, duk wani abu da za ki yi, kar ki kuskura ki jawo yara a ciki.

Don ranki ba zai yi dadi ba. Jidda matata ce, kuma ya zama lallai su yi mu'amala da yarana, idan kuma ki na da matsala, sai ki fada min tun yanzu na sani."

Shiru ta yi, tana diri ita kadai, akan me ya sa zai nuna mata iko kan 'ya'yan da ita ta haifa. Haka kawai ayi ta yin munafunci kamar ana son yaranta, alhali ba haka bane.

"Na ji abinda ka ce, tunda kuwa ka na da iko da yaranka, haka ni ma na ke da iko da su, kai idanunka sun rufe kan Hauwa, ba ka ganin komai. To ni gaskiya ba za a munafunceni, sannan a kaleleyeni da zance ba, tunda ai mai hali, baya fasawa."

"Ki fada min wani abu? Kin taba gani ta cutar da su, ko kuwa radin kanki ne kawai, ki tarwatsa min zaman lafiyan gida?"

"Mai hali yana fasa halinsa ne?"

Mamaki ya kama Abdul-Aali ya-ce. "Shi kenan, ki bi a hankali, don kuwa akan wannan maganar, ba za mu shirya da ke ba." Ya mike ya bar falon.

"Tabdi! Ai Wallahi ba za ta yiwu ba, haka kawai a cuci mutum." Haka suka shafe kwana uku, kwata-kwata, ya fita sabgarta, saboda ya gwada mata kuskurenta. Ranar na ukun ne ta tafi gidansu, saboda haka nan akan gaskiyarta, ba zai daure mata fuska ba, ya fita sha'aninta.

"Hajiya kin ji yadda muka yi da shi, abu kadan yake jira, idan dai ya shafi Hauwa, sai ki ga ya tattara, duk wani laifi ya dora min."

"Yanzu fita sha'anin ki ya yi, don kawai ba ki son huldarta da yaranki?"

Tana share hawaye ta-ce. "Eh Hajiya, kuma Wallahi kiriniya Danta ya ke koya masu, da ba su iya wasu wasannin ba, amma yanzu rashin ji ba iyaka. Akan me zan yi shiru?"

"Kar ki damu, ni zan yi magana da Alhaji, ya same shi yayi masa magana, amma ai ba zai yi fushi ba, bayan bai san hujjarki ba."

Ita ba wanda take so irin Hajiyarta, saboda ba ta kasa da gwiwa wajen tsayawa ta ga ta samowa mutum 'yanci, shi ya sa ma ta taho, ta san za ta sa Abdul-Aali ya zo tayi masa magana.

Sai dai maimakon haka. Alhaji na jin maganar ransa ya baci, ya-ce a kira masa Hamama.

Tana zaune a babban falon Alhajin, ya dubeta daga karatun da yake yi, na wani littafi, "Gani Alhaji, ance ka na son ganina."

Shiru ya yi, sai da ya kare mata kallo, sannan ya-ce. "Hamama, da dai ban san ki da wannan tsirface-tsirfacen ba, ko me ya sa ki ke so ki canza dabi'unki? Yaya za ki sa kafa ki taho gida, kan abin da bai taka kara ya karya ba?

A kanki aka fara yin kishiya? Don me ya sa ki ke daga hankalin mijinki, ki fada min, tunda ki ke zaune da ita, kin taba ganin wani mummunan abu da ta yi miki, ko yiwa 'ya'yanki, da har za ki ce don sun shiga sashenta, za ki tada hankalinki har da yin yaji." Ya yi shiru, sannan ya-ce. "Ke na ke saurare, ki fada min."

"Alhaji babu."

"To, akan babu za ki fitini kanki, ki hana kanki zaman lafiya? Don ke ki na jin dadin rayuwa, ba ki san me matsalar rayuwa ba ko? Komai kin samu ana yi miki shi, mijinki yana biye miki, shi ne za ki samu Hajiya da wani zance na rashin hankali. Kin dauka zaman gidan za ki ji dadin sa ne yanzu? Idan kuma shi ki ka fi so, shi kenan, sai ki tsaya kishin hauka ya kashe miki auren ki zo ki samu a gaba, ki yi ta kallo."

"Alhaji ka yi hakuri, ba zan sake ba".

"Ki kwantar da hankalinki Hamama, ina son fa ki san cewa wannan auren da mijinki ya yi, kaddara ce, kuma koda duka duniya za su taru, su hana shi, ba zai hanu ba, saboda Allah ya riga ya sa a cikin kaddararsa, sai ya auri wata macen bayan ke. Don haka ki zauna da su tsakani da Allah.

Kar ki zauna da mugunta a cikin ranki ko wata manufa ta sharri, zai yiwu ba ta da sharri a zuciyarta game da ke, kin ga kuwa idan ki kayi mata sharri, alhakinta zai iya kamaki, sannan ga zunubin zargi da ki ka mata.

Sannan idan ki ka faye yawan fitina, to za ki gunduri mijinki, maimakon ki yi aikin ibada, sai ya zama kwasan zunubi ki ke yi. Don haka ki kiyaye, ki zauna tsakaninki da Allah.

Duk abinda mijinki ya ke so, to ke ma ki taya shi son abin, idan kuwa ya ki abin, to maza ki guje shi, sai ki ga kun zauna lafiya matukar bai sabawa Allah ba. Sannan daga yau kar ki kara zuwa gidan nan da sunan yaji. Ina fatan kin ji?"

Tana kuka ta yi masa godiya, sannan ta-ce za ta koma gidanta. Tunda ta fito ta fadawa Hajiya abinda Alhajinsu ya ce, sai Hajiya ta saduda ta-ce. "To shi kenan. Allah ya baku zaman lafiya."

Tana komawa gida, sai ta ji wani iri, yaran da take ta fadan kar kishiyarta ta raba su, can ta same su suna karatu da ita da kuma Dan cikinta, tana jansu a jiki, tamkar ita ta haifa, sannan Ramlah na zaune kan cinyarta, tana taya su jagwalgwale, sai ta ji jikinta ya mutu. Ta dan sassauto kan maganar yaran.

*******

Ranar Alhamis ne ya ce, masu zai je Dutse gaisuwa, bayan tafiyarsa ne Mai-jidda ta kwanta a falo, saboda kanta dake sara mata, ga shi tana dauke da azumi a bakinta, shigowar sa ta ji, ya sa ta mike. "Lafiya ka dawo?"

"Mantuwa na yi." Nan ya shiga bude drawer ya dauki abin da ya dawo dashi. Ya zo fita ne ya ankara da yanayinta. "Lafiya na gan ki haka?"

"Wallahi gajiya-ce, kawai kaina ke min ciwo."

"To ki sha magani mana, sai ki kwanta ki huta?"

Yamutsa fuska ta yi sannan ta-ce. "Ina azumi ai, ba yadda za ayi na sha magani".

Abdul-Aali ya dube ta kamar wacce ta-ce wani abin tsoro. "Az... Azumi ki ke yi?"

Kai ta daga masa. "Zan iya sanin wanda ya ba ki izinin ki yi azumi, ba tare da sanina ba?"

Mai-jidda tayi masa duban mamaki, yau ta ga ikon Allah, ina ruwan sa da azuminta? Ta ga dai yanzu ta yi karfi, bare ya-ce kar baby ya wahala, don yanzu ya shiga wata hudu da 'yan kai, laulayin ma ta rage yinsa, sai dan abinda ba a rasa ba. "Na ga ba girki na bane, shi ya sa ban fada maka ba."

"Saboda ba girkin ki bane, shi ya sa ba ki fada ba? Don ba girkin ki bane, hakan yana nufin ke ba mata ta bace yau ko me?"

"A'a ba haka bane, ka yi hakuri." Ta fada cikinta na wani kara saboda kallon da taga yake mata.

Kai kawai ya gyada ya yi tafiyarsa.

Da yamma ta kammala aikin abinci, kasancewar Mamin Mimie ta mika mata girki, daman ita tarkacen kayan buda baki, ba wai sun dameta bane, don haka abin da ta yi na gida , shi za ta yi buda bakinta da shi, sai kayan marmari da ta yanka.

Tana zaune da su Ramla a daki suna ta wasan su, yayin da ita kam a kwance take akan gado tana azkar, don azumin ya riga ya shige ta. Wanka ta yi ko za ta dan ji karfin jikinta.

Ta zo ta mike, nan ne su Mimie suka shigo, wai ta goya masu 'yar bebinsu. Ramla kuma wai ayi wa nata kitso, irin wanda tayi mata ranan. Abdul-Aali ya yi sallama, ya shigo, ta dube shi, tayi masa sannu da zuwa, cikin fara'a.

"Yauwwa". Ya amsa yana ganin yadda ta dawo. "Hmm! Yau azumi yana kwada wata kenan." Kafin ta amsa, ya dubi Mimie da ta kawo masa 'yar bebinta na dora ya-ce. "Je ku kai wa Mamin ku ta gyara maku goyon."

Nan da nan yaran suka fita, suna fita Abdul-Aali ya sa key a kofar dakin Mai-jidda. Ita dai kallon sa kawai take yi. "Lafiya?"

Hannunta ya rike ya-ce. "Zo ki ga wani abu". Nan ya ja ta gaban madubi ya-ce. "Kin gama aikin ki ne?"

"Eh na gama." Ganin yadda yake kallonta, ta gano ko meye a ransa, musamman yadda ta ga ya fara shisshige mata. "Meye ne Abdul-Aali? Ta fada tana kokarin janye jikinta.

"hmm... Babu, me ki ka gani?"

"Ka bari mana". Ta fada tana zulmiyewa.

"Uhm-uhm! Ina tsammanin dai yanzu ke ce da girki?"

Nan gabanta ya yanke ya fadi. "Saboda haka ba laifi bane, ko kuwa?"

"Ina azumi fa?" Ta fada tana rarraba idanu, ya juyo da ita yana kallonta. "Nan gaba za ki sake azumin nafila ba izini?"

Da sauri ta kada masa kanta ya-ce. "Good! Saboda (I'am about to teach you a lesson)."

Nan kuwa ya shiga sarrafata, tana rokon sa da ya kyaleta, amma ina, ya riga ya yi nisa, sai da ya karya mata azuminta rugu-rugu!

Haka ta zauna a bakin gado, ta sha kukanta, sai da ya yi wanka ya fito ne ya-ce. "Gobe ko a kasar Sin na ke, ba girkin wata ba, za ki fada min kan ki dau azumin nafila.

Sai ka ce wata abin nan, wai 'ba girkina bane'". Haka kawai ya karya mata azuminta don mugunta, kuma sai da ya jira ta gama galabaita, sannan ya hanata karasa azuminta.

"Yanzu kukan meye ki ke yi bayan kuma..."

Ta watsa masa wani kallo tukun ta-ce. "Bayan ka hanani ladan azumina?"

"Ai ke ce da riba biyu, kin ga kin samu ladan niyya, kin kuma samu ladan shimfida. Don haka ki daina fushi. Ko ba komai, na san ranki fes! Ba wanda ya kai ki jin dadi."

Yana dariya ya dauki kankana a cikin Plate din Fruits da ta ajiye a dakin, don buda bakinta, ya kai baki. Ranar kwana ta yi tana fushi da Abdul-Aali, amma shi ya san yadda yake sauko da fushinta, cikin lokaci kalilan.

Ganin ta bata rai da safe shi kuwa ya-ce "Hamamatu miko min ruwa a fridge"

Yana sane sarai da cewa Mai-jidda ce ta sa abinci, hakan ya bata mata rai, amma ta danne. Ita kuwa Hamamatu tana jin haka, ta mike ta yi yadda ya-ce, ko da ta ga hirarsa da Hamama ya fi karkata.

Sai ta daina sa baki a maganar. Sai da suka gama karyawa ta same shi a daki ta-ce. "Don Allah ina son zuwa gidan Yaya Maryam anjima".

"Ga shi zan yi amfani da motar, ki shirya sai na ajiyeki."

A tsume ta bar dakin, ta gama shirinta ta fito, ta same shi, za ta shiga mota ne, ta ji karar (Text) a wayarta. Sai da ta sa Muhammad da Mimie a mota tukun, don Hamama ta-ce ta bar Ramla, za su zauna a gida, sannan ta shiga ta bude sakon.

Abdul-Aali ya tada motar, daidai da faduwar gaban Mai-jidda. "I miss you, Hauwa" Ta ga sakon da aka turo mata, nan ta shiga karanto "Inna-Lillahi'wa-Inna-Ilaihir- Raji'un!

Abdul-Aali ya-ce. "Lafiya?" Fuskarsa cike da mamakin ganin yanayin ta.

Wasu lokutan ta kan ji kamar ta fadawa Abdul-Aali maganar Dan Kano da matsa mata da yake yi yanzu, don abin nasa ya soma wuce tunaninta.

"Babu, mu je kawai".

"Ba dai wani abu ke miki ciwo ba?"

Kai ta girgiza masa, sannan ta rubuta reply wa Dan Kano. "Ko ma wanene kai, don Allah, ka barni saboda ka fi-ni sanin rashin dacewar hakan a matsayinka na mai mata. Shin za ka so idan wani yayi ta matsawa matarka haka?"

Nan take ta tura sakon. Abdul-Aali yana lura da yanayin Mai-jidda, har suka isa gidan Yaya Maryam. Nan ya bar su akan idan ya gama abubuwan da yake yi, zai zo ya dauke su. Gaba daya ba ta ji dadin wunin ba, tsabar fargaban al'amarin Dan Kano. Dole ta san abin yi.

*****

Huge twist coming up

Brace your minds and eyes

Big revelation ahead...

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top