MAFARKI

Sorry for the delay Network issues

Enjoy!

****

Ta dai ci-gaba da zuwa aiki sai dai ko da Alhaji Yusuf ya zo Dutse bai neme ta a ofis ba, hakan ya sa ta san har yanzu dai fushin yake yi.

Don haka bayan ta tashi a wajen aiki ranar laraba ta nemi wayarsa. Yana dauka ta-ce "Yallabai, kaina bisa wuya ina neman afuwa, wani laifi na yi haka har za ka shigo ka wuce ba tare da neman ganina ba?"

Alhaji Yusuf ya saki ajiyar zuciya sannan ya-ce "Hauwa ke kadai kin iya dagawa mutum hankali ki kuma kwantar masa, yanzu wace rigima ki ke nema za ki ce baki san laifinki ba?"

"Yallabai, kai dai ka sa lokaci kawai ka zo gida sai mu tattauna"

"To shi kenan, ina fata dai ba zan tarar da wannan Dan zafin kan naki ba?"

Dariya Mai-jidda ta yi ta-ce. "Wannan kuma tsohon zance kenan, ai madar ka ce, sai yadda ka yi."

Alhaji Yusuf ya yi murmushi ya-ce. "To ranki shi dade, sai kin ganni da daren, don gobe zan koma Kano Insha-Allahu".

"Ba laifi, sai na ganka."

Tana kashe wayar, ta kalli agogon bangon da ke manne a dakinta, karfe shida ne, yanzu ba da dadewa ba za a kira sallar magariba.

Don haka ta mike, ta dan shiryawa Alhaji Yusuf abin tarba. Sannan ta yi sallah. Zuwa issha ta shirya tsab! Don haka Alhaji Yusuf take jira, domin su gyaro ta.

******

"Na san na yi kuskuren rashin fada maka ko ma menene manufar Abdul-Aali tun farko, amma ba na so ka bari ya zame mana matsala a tsakani."

"Hauwa, ai ba sai kin fada ba, tun farkon haduwata da shi, na so na gane hakan, amma kuma idan har zai rinka yin haka, wataran zai kureni, in dai a kanki ne."

"Ba ma fatan ma ya kai ga haka, yanzu dai mu bar wannan maganar, tunda ya wuce. Yaya hidima da fama da mu?"

"In dai da irinki zan yi ta fama Hauwa, to lallai da na ji dadina."

Mai-jidda ta yi murmushi cikin sunne kai. "Yanzu dai mu bar wancan maganar, hankali na ya kara kwanciya."

"Na ji dadin hakan".

"Yanzu na kara jin karfin gwiwar turo magabata."

"Wai, ai Yallabai ba abin da zai girgiza ka." Murmushi ya yi, ya ci-gaba da kara gwada mata matsayinta a rayuwarsa. Hankali kwance ranar suka kwashi hirar su, ba wani wanda ya daga masu hankula. Da ya tashi tafiya ne, ya dauki wata 'yar jaka ya ba ta.

Ta yi masa godiya, kasancewar Baba yana kwance a kofar gida akan taburma, ba tayi masa rakiya har waje ba. Nan ta juyo muryarsu sama-sama suna gaisawa da Baban.

Turare ne mai dan karen kyau, ya kawo mata, sai kudi a rafarsu 'yan dari bibbiyu. Ta ji dadin turaren, kasancewarsa marar karfi sosai, sannan yana da dadi tamkar kamshin fure.

Bayan Alhaji Yusuf ya tafi ne. Ta yi shiru tana kwance a dakinta, haka nan ta tsinci kanta cikin kadaici da rashin sanin madafa, wani sayau! Take jin ta tamkar fanko.

Ba dai wannan bane karo na farko da Muhammad ya tafi Kano hutu don haka ta san ba kewarsa ke damunta ba, sannan ta dade da daina kuka cikin dare idan ta tuna Dakta.

Ga shi kuma ta shirya da Alhaji Yusuf har ya jaddada mata batun tambayarsa, karshen wata, ta rasa me yake sanyata jin abubuwan da take ji a lokacin.

Nan tunaninta ya fado kan Abdul-Aali, komai a tare da shi da abinda ya shafe shi, damuwa ce da rikicewa a tare da ita, wannan ya sa ko sa shi a tunaninta ba ta cika son yi ba.

Amma kuma don radin kansa, tunanin ke kai mata ziyara, musamman kan maganar da ya fada mata a dakin Mama. "Shin dama Abdul-Aali na so-na ne?

Amma wane irin so ne ake nuna shi ta hanyar kiyayya? Oh Yaya za ayi ma na rinka tunaninsa?"

Nan ta ji wani mutuwar jiki ya sauka mata. Ta dai hana kanta tunanin Abdul-Aali a zahiri. Amma sai da ya addabeta cikin barci, don kuwa ranar mafarkin sa ta rinka yi.

********

Wani irin kuna ta ji da tashin hankalin da ba ta taba samun kanta a ciki ba iyaka rayuwarta, idan mafarki ne, ba abinda take so, ta gani illa farkawarta.

Kallon sa take yi kamar ya rikide ya zama wata halitta daban, ko kuwa yana rike da makamin katse mata rayuwa. Ya fara damuwa da shirunta, don haka ya-ce. "Ba ki ce komai ba Hamamatu."

Wai ance shiru ma amsa ne, haka dai take zaune tana kallonsa, tsawon minti biyar, ba ta furta komai ba, ganin haka. Abdul-Aali ya sa hannu ya riko tafin hannunta, wanda bai yi nasarar zama a ma'ajiyinsa ba.

Hamama ta-ce "Why, me ya sa za kai min haka Abdul-Aali? Ka san muhimmancin da ka ke da shi a gareni kuwa? Ka san yadda na dauke ka, za kai min haka. Anya ka min adalci kenan?

Na sallame komai na, saboda kai, ba ni da kamarka, shi ne za ka saka min da haka? Me ya sa ba ka bar mu a Kano ba, ka yi tahowarka kai kadai? Or better yet ka taho da amaryarka?

Na kasa yarda da abin da ka ke fada min, aure fa ka ce za ka yi. Wai me na rage ka da shi Sweety? Iyaka kokarina ina yi maka a gidan nan, idan akwai abinda ka ke so na gyara, sai ka fada min, amma aure?"

Nan ta fashe masa da kuka, ina ma da zai iya mata bayanin dalilin da ya sa zai yi wannan auren? Amma ba za ta so ji ba. Ta dago ta-ce.

"Wato shi ne abin da ka ke so, kasa na ke maka addu'a akai ko? Har da wani dauko gyara, ni ina murna za ka sabunta mana wuri da yara a sake, ashe kudurinka kenan, lalle na miji sai dai a bar shi. Allah ya baka sa'a."

Ta mike ta wuce dakinta hade da bugo kofa. Abdul-Aali yana zaune a falon kansa a cikin tafukan hannunsa.

Kansa ya kulle gaba daya, amma ko ba komai ya sauke abin da yake damunsa, don tun ba yau ba yake son ya fadawa Hamamatu ya na so ya kara aure, amma ya rasa ta inda zai fuskanceta, dadin karawa, bai samu hadin kan Jidda ba.

Haka ya kwana biyu bai gane kan Hamamatu ba, daidai da abincinsa a gidan idan ya tambaya, sai ta-ce. "Ka jira amaryar ka idan ta zo, sai ta dafa ta ba ka. That is, idan ba ta cika maka ciki da soyayya ba."

Murmushi ya yi, ya fita ya nemi abinda zai ci, idan ya samu wata walwala a gidan, to daga wurin yaransa ne, yana dawowa za su makale shi suna ba shi labarai.

Shi kuwa yana biye masu. Amma hanklinsa na kan Hamama, yadda ranta ke kuna, har wasu lokutan ta sauke fushinta kan yaran, ba gaira ba dalili ta fadasu da fada ko ta bugesu. Ranar Mimie ta kaiwa mari a gaban sa, ya fusata.

"Lafiyarki Hamamatu? Yaya za ki mata irin wannan bugun? Akan me za ki sauke fushinki a kanta? Idan ki na fushi da ni, to ki sauke a kaina, amma kar ki kara sa yaran nan a gaba".

"Yau kam ka gwada min ba ni da matsayi a rayuwarka da yaranka da matar da za ka aura sun shige maka gaban komai, wai ma na tambaye ka, a dan dawowarmun nan ne har ka ganta ku ka daidaita, ko kuwa dama tun can ni ka rufa da maganar?"

"Hamama ki bar maganar nan haka, na ga dacewar na sanar dake ne, saboda na fita hakkin ki, amma ba na so ki daga hankalinki akan wannan maganar har ya bata zamantakewar mu.

Idan kin bada kofa, hakan na iya sawa ki ga bambanci a tare da ni, amma idan ki ka kwantar da hankalinki, ba abinda zai canza, wannan auren da zan yi, ba yana nufin na daina sonki bane, ko kina da wani aibu a tare da ke, ki dauke shi a matsayin kaddarata da ta ki ne."

"Wace ce za ka aura?" Ta tambaya a dakile.

Nan ne ya sa hannun sa ya riko kafadunta a hankali ya-ce. "Zan fada miki wannan, amma ba yanzu ba. Saboda haka ki natsu ki kwantar da hankalinki.

Ni Abdul-Aalin ki ne har yanzu, kar ki yi tunanin ko auren da zan yi wata za ta kwace miki wani abu daga gareni. Ba abinda za a gwadawa Hamamatuna".

Ya fada yana mata wani murmushi, mai kashe jiki, ita kuwa duk da hakan yayi mata tasiri, tsumewa ta yi ta-ce. "Ina ce dai mace za ka auro, ko ma me za ka fada, sai ka fada, amma ba za ka fahimci me yake gudana a cikin zuciyata ba."

Ya dai samu ta kwantar da hankalinta, duk randa abubuwan suka motsa kuwa sai ta hau binciken wayarsa, da gangan yake bari wataran, saboda ya san ba abinda za ta gani, burinta shi ne ta ga wa zai aura, waye ta dauke mata hankalin Sweety dinta.

*******

Tana kallo har ya ja zip din jakarsa, ba ta ce masa komai ba, kasancewar ba wai tana goyon bayan wannan tafiyar bane. Asali ma shi ya shirya kayansa ma, don duk wani abin da ya shafe shi, ta sauke daga kanta, saboda haushinsa da take ji.

Mamaki kawai yake ba ta, yadda ta ga ya rikide, tamkar ita ba komai bace, ita dai za ta so ta ga koma wace ce ta daukewa mijinta hankali haka, yake wannan bare-baren, don abin ya wuce gaban komai.

Wataran tana masa magana ma kamar hanakalinsa baya wajen, sai tana nata, sai ya ba ta amsa. Ta yi wa kanta fada ma ta daina like masa, tunda yayi mata maganar aurensa, don ta san ita za ta sha wuya.

"Yaushe za ka dawo?" A sanyaye ta tambaya.

"Sai kun ganni."

Wata irin dariya Hamamatu ta saki. "Ya Allah, Oh ni yau Abdul ina ka samu wannan yarinyar ne? Anya ko ba gamo ka yi ba?"

Kallon da yayi mata ne, ya sa ta shiga taitayinta ta bar dariyar. "Seriously, na kasa fahimtar yadda son mutum zai shigeka farat daya, ya kidima ka yadda ka ke a yanzun nan".

Murmushi ya yi ya-ce. "Wannan na daban ne shi ya sa, idan kuma ki na da lokaci sai ki zauna nayi miki shi filla-filla.

Wanda na san yayi miki nauyi da yawa ba za ki iya dauka ba, so ki kula da gida da yara, kafin na dawo, Sweety". Da wannan murmushin a fuskarsa, ya sumbace ta. Sannan ya fita a dakin.

Sulalewa ta yi kasan kafet din dakin, ta fashe da kuka, ta san ita da Abdul-Aali kam shi kenan, ba ta yafewa duk wacce ta shiga tsakaninsu ba.

*************

Ta dawo daga ofis ne ranar Juma'a ta samu motar Mukhtaar a kofar gidansu, ba ta yi mamaki ba, kasancewar ya kan zo ya gaishesu, za ta shiga cikin gida ne ta kofar zaure, ta ga ya fito daga kofar falon Baba, don haka ta tsaya suka gaisa. "Yaya su Mama?"

"Lafiyarsu kalau, suna gaisheku. Har kin taso daga ofis kenan?"

"Wallahi, ka san yau (Short day). Na ga kamar ba kai kadai bane?"

Mukhtaar ya sosa kai, ya-ce. "Eh, da Kawu Garba muka zo."

Mai-jidda ta dube shi a ranta tana nanata Kawu Garba? Kanin Abba da yake Zariya kenan fa, shi yake shige masu gaba idan al'amuran auren gidan ya tashi.

Me ya kawo shi wajen Baba? Nan da nan ta fahimci ko me yake faruwa, ta zare idanu. "Mukhtaar, Abdul-Aali ya zo Kano ne?"

"Anty Hauwa..."

Ba ta jira ta ji me Mukhtaar zai ce ba, ta wuce cikin gida a fusace. Khimar dinta ta cire kawai ta dau wayarta, ta nemi sunan Abdul-Aali ta danna masa kira.

Yana ganin wayarta, ya yi mamaki kwarai, don wannan ne karo na biyu da ta kira shi a wayarsa. "Me ka ke tunanin ka ke yi? Ka na tsammanin za ka sani na aure ka dole ne, ba na son alaqar dake tsakanin Baba da Abba ya baci, don haka tun wuri ka san yadda aka yi ka janye maganar nan, tun kafin su Kawu Garba su tafi".

"Shi kenan damuwarki?"

"Eh, idan kuma ba ka janye ba, zan fadawa Hamama duk abin da ake ciki."

Ta ba shi dariya. "Sai dai kamar kin makara, don ta riga ta sani, saboda haka ki sake lalubo abinda za ki min barazana da shi, don na fada miki wannan karon ba ja da baya."

"Hmmm! Ban san me zance maka ba, amma mu zuba ni da kai."

Ta kashe wayar cikin fushi ta zauna a daki ranar ba ta ko ci abinci ba. Muhammad ma wajen Umma ya gama sintirin sa.

Ba ta dai ji kiran Baba ba a wannan ranar, amma hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba.

********

Hakan ya sa tana shiga falon inda aka ce yana jiranta, ta yi zamanta ba ta ce masa komai ba.

Da yayi mata magana ne ta-ce. "Hankalinka ya kwanta, ka samu abinda ka ke so ai, sai ka sakar min mara, za ka iya komawa Portharcourt hankalin ka kwance, tunda ka yi yadda ka ke so, ba mai sace maka ni".

Baya gajiya da kallonta har ta gama, hannunsa daya yana tallafe da bakinsa, "Ameen da addu'arki. Allah ya ba ni abin da na ke so. Allah ya ba ni ke.

Amma zan fi farin-ciki idan ki ka kwantar da hankalinki, ki ka tayani son ki, saboda kar ki hadu da wata cutar.

Ji yadda ki ke tada hankalinki. Abdul-Aali ne ya-ce yana son ki ba wani abin tsoro ba. A iya sanina kuwa, ba wanda ya taba ce min ni abin tsoro ne."

Ta rasa yadda za ta yi da wannan mutumin, idan banda munafurci, wai shi ne mai sonta, cikin tausayin kanta fuska a narke, ta durkusa har kasa. Yana ganin haka ya mike ya-ce. "Jidda meye haka?"

Ba ta kula shi ba, ta-ce. "Don Allah Abdul-Aali, ka rabu da ni, ka koma rayuwarka da ka saba, ba tare da ni a ciki ba, ko Turai ne ka koma, amma don Allah ka bar ni, kar ka sake tunani na, ka yi hakuri ka cireni a ranka.

Don ba zan iya auren ka ba, za ka cutar da ni, idan har ka aureni, saboda ba zan iya zama da kai ba alhalin ka na matsayin kanin Dakta, ba zan iya sonka ba, ban san me ya sa ka ke cewa ka na so-na ba, Alhali da ni da kai mun san ba haka bane."

Kallonta yake yi, a ransa kuwa tamkar ana kara rura masa wutan sonta ne, duk lokacin da ya kalleta, musamman a irin wannan yanayi da take kuka, ga kuma tausayinta da yake lullube shi, wanda idan zai iya tunawa ya fi ganinta a wannan yanayin.

Ji yake yi kamar ya daga ta daga durkusonta, ya zaunar da ita yayi mata alqawura masu dama wadanda za su sa ta fita daga kunci. "Ki na nufin idan na zo da wata siffa, ba ta kanin Yaya Rayyan ba, za ki iya so na Jidda?"

Mai-jidda ta tsayar da kukanta, ta dube shi, yayin da zuciyarta ke bugawa fiye da tunaninta har take tsoron kar ya fashe a kirjinta.

"Abdul-Aali ba zan taba iya son wani ba kamar yadda na so Dakta, wannan ita ce gaskiyar magana, kuma the earlier you know the better." Ta mike ta zauna a kujerarta a takure.

"Shi kenan, tunda haka ne, amma za ki iya auren wani koda ba ki son shi kenan?"

"Me ya sa za ka ce haka, bayan ka san amsar?"

"Saboda za ki auri Alhaji Yusuf, kuma bayan kin san ba kya son sa, shin kin masa adalci? Kin san abin da ya fuskanta, kafin ya zo miki da maganar aure ko kuwa bayan ya zo miki da ita? Kin san tashin hankalin da ki ka jefa matarsa da shi kansa, duk don yana so ya kawo ki gidansa.

A tunaninsa za ki mayar masa da wannan soyayyar, ki haifa masa kyawawan yara kamar ki? Kin san me zai fuskanta idan ya kasance ya auri matar da har yanzu take soyayya da wanin sa?"

Idanunta a rufe ta-ce. "Ka daina shiga rayuwata Abdul-Aali, ka daina dagula min lissafi, ka daina damuna, a farke ko a mafarki, ba na son ganinka, ba na son jin muryarka."

Kallonta yake yi a nishadance, tamkar ya samu wani majigi na fim. (Oh! how he loved her), yana son Jidda da yawa.

"Na barki Lafiya Jidda, kin bawa kanki amsa, ina kuma fatan ki gane shi, tun kan lokaci ya kure miki."

Idanunta sun yi jawur! Haka ta bi-shi da kallo har ya bar falon. Anan ta zauna tana kuka, har Baba ya shigo, ta goge hawayenta tana shirin fita ne ya-ce. "Hauwa dawo nan."

Ta riga ta san me zai ce mata, don haka kawai zama ta yi tana sauraren sa. "Lafiya ki ke wannan irin kuka? Kullum ina fada miki, duk abin da ya shige miki duhu, to addu'a ce maganinsa.

Saboda bakin-ciki da abinda Allah ya turo mana, tamkar rashin yarda da qaddara ce, wanda ko mai kyau ko marar kyau, imanin mu ya rataya ne a amincewa da wannan qaddarar."

Ta daga kai alamar amsawa, ta goge hawayen nata, sannan Baba ya-ce. "Akwai wasu takardu da Kawun marigayi suka kawo jiya, wasu filayensa ne suka fito, to an raba su, shi ne aka kawo miki takardar na wurin Muhammad, saboda haka sai ki adana shi."

Ta yi shiru tana jiran Baba ya dago mata maganar Abdul-Aali, amma shiru bai ce komai ba. Yana miko mata ta-ce masa. "Na gode, shi kenan Baba?"

Ya dubi kumburarren fuskarta ya-ce. "Eh shi kenan, idan kin shiga, ki yiwa Laraba magana."

Ta fita jiki ba kwari, dama takardun fili ne suka kawo su Kawu Garba, shi ne ta tada hankalinta har da kiran Abdul-Aali, wato shi kuma sai ya biye mata, nan take haushin kanta ya kamata, ta rasa me yake mata dadi.

Da dare ta daga wayarta ya yi sau biyar tana son ta kira ta bawa Abdul-Aali hakuri. Amma ta rasa da me za ta fara? Da kyar ta danna lambar, ya yi ta Ringing. Kafin nan ya daga, kamar ta ajiye.

Nan kuma ta rasa me za ta ce da ta ji muryarsa. "Uhmm... Dama na kira ne... Ka yi hakuri, na yi maka wata irin fahimta.

Baba ya ban sakon da ya kawo su Kawu Garba, to amma me ya hana kayi min bayani, ka bari na yi ta fada maka son raina?" Ta fada cikin jin kunyar kanta.

Ya gyara hannunsa, ya rike wayar sosai, sannan ya-ce. "Well! Ko ba komai na san ina damunki ko a mafarki, don haka za mu iya cewa mun yi daidai kenan ko? We are even."

Wata kunyar ta sake kamata "Ni yaushe nace maka..."

"Kar ki musa, dazu da kike ta kuka, ki na magana, kin dauka ba na jin me ki ke fada ne? Ai idan Abdul-Aali zai auri Jiddansa, sai duniya duka sun sani.

Saboda haka ba zancen boye miki komai, ki dai zauna cikin shiri, don jiki na ya ban nan ba da jimawa bane".

Matsalarta da shi kenan, shi ya sa ta sake tamke fuska. "Hmm! A mafarki kenan."

"Jidda a zahiri, kuma ke da kanki za ki shaida hakan."

"Dama abin da ya sa na kira kenan, don na ba ka hakuri. Amma kar hakan ya sa ka yi tunanin, idan ka yi da gaske, za ka share".

"Na ji ranki shi dade, mu kwana lafiya. Idan na dameki a mafarki kuma. You can always call, mu yi magana."

"Allah ya sawwaka." Ta fada hade da kashe wayar. Sannan ta samu kanta da murmushi, tana juya wayar a hannunta. Muhammad ta gani a kwance a gefenta, ta fita daga dan guntun duniyar da ta fada.

Ta shafa kan yaron, sannan tayi masu addu'a ta kwanta.

Ba kalmar da ya zo mata a rai, tana farkawa washegari, sai. "Maye". Ta ja tsaki, domin yau ma dai sai da aka kuma, mafarki dai kamar wani hadin baki.

********

Walida ta kasa daina dariya, tunda Mai-jidda ta ba ta labarin abinda ya faru. "Don Allah ki daina, kar su F and A su ji ki, ni dai dole wannan satin na yi magana da Alhaji Yusuf.

Idan ya shirya kawai, su iso gida, don ina tabbatar miki yadda take-taken Abdul-Aali take, zai iya saceni ya kai ni gidansa."

"Ya isa? Da sauran sa, ai Jiddan mu me tsada ce".

"Kar ki sake kirana Jidda, wani wai 'Jidda' yadda ki ka san sunan yanka na kenan. Abin da ya fi ba ni mamaki wai har ya fadawa matarsa tsabar azarbabi.

Bayan ko karbuwa bai samu ba, ni ce ita na shirga masa wulaqanci kala-kala, shi ba anan ba, shi ba a can ba, mu ga ta tsiyar".

"Yanzu kam maganar Abdul-Aali ta fara zama gaskiya, na fara yarda ke ce ki ka tsane shi, shi bai tsaneki ba."

Wata sabuwa, tana samun Alhaji Yusuf da maganar zuwa tambaya sai ya-ce. "Kar ki damu, ina bukatar lokaci tukun, saboda wasu dalilan da suka taso".

Mai-jidda ta yi masa wani irin duba. "Kamar dai musamman ka taho min da albishir, idan zan iya tunawa a dokance ka ke lokacin, me ya faru yanzu kuma?"

"Hauwa, Yayar ki ce Wallahi ta samu Mum dina da maganar. Allah kadai ya san me ta fada mata, yanzu haka ta-ce ita ba ta san wannan zancen ba, amma dai ina kan lallaba ta. Insha-Allahu komai zai daidaita, kin san sha'anin iyaye."

Kan Mai-jidda a kasa ta-ce. "Haka ne kam, to Allah ya shige mana gaba." Jikinta a sanyaye suka rabu ranar. A ce mutum kamar Alhaji Yusuf, sai abinda matar sa take so, zai yi, ai an samu matsala.

Daga nan ta fara tunanin anya ba kuskure za ta yi ba kuwa, idan ta karfafa batun sa? Sai dai za ta ba shi lokacin kamar yadda ya bukata.

********

Dariya yake yi, jin bayanin Mai-jidda. "Hauwa, easy slow down, ban gane ba."

"Hmm! Ni ma kaina ban gane ba Yayana, a bangare guda Alhaji Yusuf, wanda matarsa ta san hanyar da za ta bi ta sa shi yin son ranta.

Ka ga baida iko akan gidan sa, a bangare guda kuwa Abdul-Aali, na fada maka irin nuna isarsa.

Da ganin kamar ya fi kowa sanin komai, kuma sai abinda yake so za a yi. It's like dole ne na aure shi, tunda ya-ce min yana bukatar hakan."

Ta nisa sannan ta-ce. "Kaina ya daure, ban san abin yi ba, wasu lokatan ji na ke yi kamar da na yi zamana haka, ban sake dago maganar aure ba."

"Hmm! Na ji damuwarki, kwarai ki na cikin matsala sosai. Abu mai sauki, shi ne na zo mu ga juna, idan muni na bai miki yawa ba, sai mu yi auren mu hankali a kwance, tunda ni dai ba ki da matsala da ni".

Dariya ta yi ta-ce. "Ka bar wannan maganar don Allah. Ina bukatar addu'a, don ita-ce kawai mafitar".

"Kar ki damu, kullum ina miki addu'a. Batun zuwa na kuma da gaske na ke miki, kwanan nan za ki ganni Insha-Allahu, don yanzu na kusa na samu zama.

Ki duba ki gani fa shekara nawa, muna magana, duk da on and off ne, ai lokaci ya yi da za mu hadu. Ko ba haka ba?"

"To shi kenan, sai na ganka, amma dai Allah ya sa kar ka zo min da wani abin kwaba lissafin, don hannu na cike yake da matsaloli."

"Kar ki damu, sai dai na tayaki rage miki su."

"Na gode kwarai, da kasancewarka a rayuwata."

A lokacin ji ya yi da za ta manta da kowa, ta amince da shi ya shiga rayuwarta da kyau da ya huta radadin da yake kwana da shi a rai.

"Ran yaushe zan zo?"

"Duk randa yayi maka, ba laifi."

"Sai kin ganni. Insha-Allahu." Ta kashe wayar cikin jin dadi.

*************

Okayyyy Dan Kano wants to meet. 😱

What do you expect?

And Abdul-Ali he's soooo ... I don't know I just love him.😘

Jidda baiwar Allah ki tayamu son Abdul-Ali.

Alhaji Yusuf seriously? 🙄

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top