LAIFIN WA?

Abin da Mai-jidda ta kula da shi. Shi ne, Abdul-Aali mutum ne da sam baya wasa da lamarin abincinsa, sannan yana da matukar jan yaran a jikinsa, don kullum bayan Magariba shi da kansa yake masu karatu. Hakan ya bawa Mai-jidda sha'awa sosai.

Tun zuwansu, ya fi so su hadu, ayi hira kafin lokacin shiga, amma Hamama sai ta fara dauke wuta, ko kuwa ta yi ta masa hirar da ta san ya fi rinjaya a kanta.

Ganin haka Mai-jidda ta fara bada excuse, ko ta-ce ta gaji za ta shiga da wuri ko kuwa kanta na mata ciwo. A haka dai har ta daina zaman wannan hirar.

Hakan kuwa ya fi yiwa Hamama dadi. Duk randa dayansu ba ta da girki, to tana fama da al'amarin yara, har su yi barci, ita ma ta shiga.

********

Suna zaune a falon Abdul-Aali ne a Weekend. Sai ga Sam yaron gidan yana knocking wai oga ya yi baki. Mai-jidda ta yi mamaki kasancewar bai sanar da su da zauwan baki ba.

Har ta mike za ta bar falon, ganin Abdul-Aali ya fita wurin bakin, sai kuma ta hango bakin ta window, wannan wasu irin baki ne? Mata a gidan Abdul-Aali, ta juya ta ga Hamama na zaune, ba ta ce komai ba, don haka ta-ce hala ta san su ne.

Da yamma suna zaune a falon. Hamama na yanke farce, yayin da Mai-jidda take duba wani littafi, rufewa ta yi ta-ce. "Mamin Mimie, ni kuwa ban gane bakin Dadin Mimie da suka zo da safe ba?.

"Oh, Francisca ce, daga ofis din su suke."

Mai-jidda kanta ya daure. "Me zai kawo 'yan ofis gida kuma, duk wani aiki ba zai kare ba, har sai Weekend sun biyo shi gida?"

"Wani lokacin wasu al'amuransu suke nema na taimako, kin san sweety kuma, nan da nan zai sa a masu."

Tabdi! Wannan wace irin rayuwa ce? Ita Hamamatu ta fi ba ta mamaki ma da ta ga ko a jikinta, bayan ta san har gida ake zuwa a kira mijinta, sannan ya fita gun 'yan matan ofis. Lallai ita kam ba za ta yarda da wannan shirmen ba. Haka kawai! Ta ci-gaba da aikinta ba tare da ta ce komai ba.

Ranar litinin da safe ta tashi da wuri, ta kammala aikin Breakfast ta shiga daki ta hau shiri. Abdul-Aali ya shigo ya ganta cikin shirin fita. "Ah, Jidda yaya na gan ki haka?"

Ta juyo ta dube shi cikin murmushi ta-ce. "Wa, ni ce? Kar ka damu, ofis zan je".

Ya bude idanu. "Ofis kuma?"

"Eh wurin aikinka, ka ga ba mu samun isasshen time da kai a Weekend ba, hakan ya sa na yi tunanin may be, idan muka fita tare, zan karasa fahimtar ko kai waye ne, saboda zamantakewar mu ta dore". Ta fada hade da daura agogon hannunta.

"Na yaba da gesture dinki na son gyara zamantakewarki da ni, amma ofis kam, ai wurin aiki ne. Yaya za ayi..."

Pin din shaylarta ta makala "Right, haka gida ma wurin iyali ne, me ya sa za ka kawo 'yan ofis gida, su cinye mana lokacin mu?" ta karasa tana masa kallon tuhuma.

"Ok, in na fahimceki, kin gwada manufarki, ba kya so a zo wurina daga ofis, ko kuwa dai don mata ki ka gani shi ya sa?"

"Ko ma wa na gani, ai gida ba wurin aikin bane, idan ka tafi, ka yi yadda ka ke so, amma haka kawai wasu mata masu dangalallun siket su kama hanya su wani biyoka har gida, wai lamarin aiki? Ba maza ne a ofis din?"

Tana fada a tsume. Abdul-Aali kuwa ya sa dariya ya-ce. "Wallahi duk kishin Hamama, kin damata, kin shanye, ba ta taba cewa komai ba, amma ke... Sai a hankali."

"Ai laifinta na gani, da ta yi magana tun farko da ba a biyoka har gida ba. Don haka ni ma yau ofis zan je."

Ta fita daga dakin da jakarta, ya bi-ta da kallo. Lamarin Jidda baya daina ba shi mamaki. Tana wargaza masa kwakwalwa, nan ya fito ya sameta a falon ta gama dakewa. Hamama ta dubesu da neman karin bayani. Mai-jidda ta-ce. "Dadin Mimie ba ka fadawa Mamin Mimie za mu fita ba? Mamin Mimie rabu da shi, ya manta."

"Uhmm! Za mu je da Mai-jidda, ta ga wurin aikina, direban ofis zai kawo ta gida." ya fada tamkar dole yayi bayani.

Hamama ta 'kula akan me ya sa za a kai ta yawon ofis? Ita yaushe ya taba kai ta ofis dinsa?

"Amma Sweety..." Maijida ba ta jira, ta ji me za ta fada ba ma, ta yi waje abin ta, ita mata na ba ta mamaki. Yaya za ayi wai ba za ki yi kishin mijinki a waje ba, sai ya auro wata, ki zage wai ke ga mai kishi? A mota ta yi zamanta, yana fitowa, ya shiga mota.

"Jidda, ke 'yar rigima ce Wallahi."

"Don Allah tsakanin ka da Allah. Yaya za ayi na ga ana sintiri wurin mijina, hankali na ya kwanta? Idan Mamin Mimie tayi maka koma meye ne, ni ba zan damu ba, saboda matarka ce, amma haka kawai ka hau washe baki, don wai wasu kattin mata?"

"Ke ba ki dariya da wani ne, sai ni?"

"Kai ma ka san an wuce nan, wanda ya kama ayi shi daidai gwargwado, ana yi, amma kai fa, tamkar daya mai blun kayan nan, za ta shige jikin ka take yi."

Wani dadi ya ji a ransa, ya kai mata sumba. "Ina sonki da yawa Jidda, na ji dadi na, ashe ke ma haka ki ke so-na?"

"Don kawai, ina kishinka, ai ba shi bane so."

"Hmm! Na ji." Sai da suka je ofis din, ta ga har inda yake aiki tukun, sannan hankalinta ya kwanta ta-ce. "Zan koma na bar ka ka yi aiki, kuma Wallahi ko kallon wata ka yi, ni da kai yau."

"To ranki shi dade." Ya fada yana dariya. Nan ya hadata da mai mayar da ita gida. Tana tafe dadi fal! A ranta da ta dau mataki, gobe ba mai kara zuwan masu gida.

Wuraren azahar ya kirata, wai yana jin yin hira. "Ka fasa aikin yau din kenan."

"Babu, aikin da tun tafiyarki, kin tafi da concentration dina, banda ke ba abin da na ke son gani."

"Dadin Mimie kenan, kar ka wani dora min laifi. Idan za ka yi aikin ka, ka yi."

"Ke ba kya son na dawo gida yanzu?"

"Ni aiki na ke yi a kicin yanzu, idan na gama kuma za mu yi karatu da yara, idan mun gama kuma zan yi barci. Idan na tashi kuma na mikawa Maman Mimie ragamar gidan. Which includes you, saboda haka ka yi zaman ka a ofis."

"Ni dai ba ni da gata, haka kawai ayi ta wahalar da ni, ba a sani a lissafi".

Kashe wayar ta yi tana dariya, don ta kula yau a cikin (Mood) yanayin wasa yake. Tana kashewa ta hau tunanin yadda a hankali Abdul-Aali ya rikide kamar ba shi ba. Bayan sakin fuska da walwala da son yara da son kyautatawa, sai take mamakin yadda da duk ba ta ganin wannan a tare da shi.

A yanzu kuwa ba ta ma son tuno iya soyayyarsa, saboda tsikar jikinta tashi yake yi. Ashe za ta iya son Abdul-Aali? Ashe gaskiya su Yaya Maryam suke fada mata tana son shi tuntuni?

To amma kuma kusan hakan take ji game da Dan Kano a baya, an taba son mutum biyu lokaci guda? Me ya kai ta tunanin Dan Kano? Haka nan ta ji tsigar jikinta ta tashi, a daidai lokacin da (Pressure Cooker), ya saki kara.

Can falo ta jiyo fada. Da sauri ta fita don rabiya, don baya wuce Muhammad da Mimie, ga son wasa, amma da zaran an hadu, to sai an taba.

Bayan ta kammala ayyukanta ne. Ta kira su Mama suka gaisa, haka nan ta kira Umma. Zaman su dai ba laifi tsakaninta da Hamama, kasancewar ba mai shiga sabgar wani, randa rikicinta ya tashi kuwa.

Ta fi sauke fushinta kan Mai-gidan. Abu guda da ya fi damun Mai-jidda. Shi ne yadda sam ta ki ta sake da Muhammad, komai ya yi a gidan. Sai ta yi magana.

Hakan ya sa sai su zauna ko a falo, ko kuwa ta sa shi ya huta a daki. Abdul-Aali kuwa da ya kula da rashin sakewar da Muhammad ke yi, sai ya ja shi jiki, su fita tare su yi sallah tare.

Wannan ya kara sawa Mai-jidda ganin kimarsa da darajarsa, don haka ba ta wasa da duk wasu al'amuransa.

Ana shirin komawa makaranta ne, ta samu Abdul-Aali da batun makarantar Muhammad. Shi ya gwada mata yana so su zauna anan da su Mimie.

Saboda su shaku ne, ita kuma ta-ce ta fi son su koma Kano. Ganin ta dage kan maganar, ransa ya dan sosu, ya kyaleta ba tare da ya-ce komai ba.

Ran Juma'a ya-ce, su shirya zai maida su Kano, ta ji dadi. Amma ganin yadda ya bata rai, ta san ya yi ne kawai, don abin da take so kenan, ba wai hakan ya kwanta masa a rai ba. Ita dai kam haka kawai ba za a takurawa Danta ba, idan gidan Dadinsu Mimie ne, shi kuma Baffansa ne.

Ba bare ba, don haka ta danne zuciyarta, gwamma ta yi zamanta a Kano ta kula da yaronta, tana bangarenta duk lokacin da suka zo su zo a marmarce, kafin lokacin barin su PH din ya yi gaba daya.

************

Yana ajiye su. Kwanan sa biyu, ya gaida iyayensa, ya yi wasu harkokinsa, sannan ya koma. Gaba daya sai ta samu kanta da jin wani iri da rashin walwalarsa.

Ta yiwa Muhammad rajista a wata makarantar dake kusa da su, ta kudi ce mai kyau, kullum ita take kai shi, ta kuma dauko shi idan an tashi.

Hankalinsu kwance. Idan Weekend ya yi ta kai shi wurin su Mama, yayi masu Weekend, a haka ta sa shi a Islamiyya.

Ranar laraba da yamma Mukhtar ya kawo matarsa. Mai-jidda ta-ce. "Ai Mukhtaar na fara tunanin anya kuwa? Har zan sa ka a kwandon shara, ka ci albarkacin Kamila."

"Hmm! Anty Hauwa ba za ki gane bane, sai dai a hankali ke kam, kin san tana Service dinta a Damaturu so, zaman nata on and off, sai yanzu na samu aka dawo da ita nan, ni kaina ban ganta sosai ba."

"Hmm! To ya yi kyau. Kamila kin ji mijinki ya yi kwas a iya bada Excuse."

Kamila ta yi murmushi. Nan Mai-jidda ta cika masu gabansu da kayan cima iri-iri. Ita dai Kamila faram-faram din Mai-jidda kawai ke burgeta, tana da son mutane.

"Da Yaya Abdul-Aali ya ce, duk kun koma PH".

"Kai ka rabu da ni, na dawo nan ka ji mutane su yi ta zaman keji? Ka ga nan na sakata na ga 'Yan-uwa son raina. Ga shi yanzu na ga Kamila".

"Kin yiwa Anty Hamama wayo kenan."

"Suna can da yara ko da muka yi waya da su Mimie, su ma wai ba su jin dadi."

"Hakan ya fi, ko ba komai za mu rinka ganin Yaya Abdul akai-akai, tunda an ajiye gimbiya a nan."

Mai-jidda ta yi murmushi. Mukhtaar bai san darun da ake tabkawa bane, tun da ya ajiye su bai zo ba, sannan waya idan ya bugo to bukatunsu kawai yake tambaya ko kuwa ya ji lafiyarsu, babu wata doguwar zance.

Ita ma ba ta damu ba, duk da tun tahowarta ta fahimci, kamar tana dauke da ciki, don ba ta ga al'adarta ba, ga wani barci da take yawan yi na safe.

Ba ta fada masa ba, duk randa ya zo, sai ta fada masa. Wani ikon Allah, ba ta tashi fara laulayi ba, sai da ta yi PT, ta tabbatar da shigar ciki. Shi kenan zazzabi ya-ce salamu-alaikum, ga amai kamar me. Makaranta ma Kasim ne ke kai Muhammad.

Tana kwance lamo a falo, sai ga su Mama sun yi sallama, ta gyara jikinta, sannan ta bude kofa, ta yi farin cikin ganin su kwarai.

Bayan sun gaisa Abba ya-ce. "Hauwa yaya ki na kwance ba lafiya, ba za ki sanar da mu ba?"

"Abba, na ga da sauki shi ya sa."

"A'a an taba wasa da lafiyar jiki ne? Sai da Kasim yake fada mana wai ai kwana biyu shi yake zuwa ya kai Muhammad makaranta, saboda ki na kwance."

Nan Mama ta karbe. "To kin je asibiti ne?"

Kanta na kasa ba ta-ce komai ba, nan ne Mama ta fahimci ko menene, sa ta tayi a gaba ta-ce "Ki shirya gobe sai ku koma gida Insha-Allahu. Amma mutum ya kwanta ciwo shi kadai a gida?"

Ita duk ciwonta bai dameta ba, irin yadda Abdul-Aali ya yi banza da ita, ita ba kiran wayarsa take yi ba, bare ta kira ta ji dalili, shi kuma ya dau zafi ya sa ta a gefe, tunda ba ta damu da shi ba.

A wurin Mama ya samu labarin ciwon nata, sai ga wayarsa da dare ta daga suka gaisa. "Yaya jikin naki? Mama ta-ce ba ki ji dadi ba."

"Eh, da sauki Alhamdulillahi! Ina gidan Abba ma".

"Uhmm! Allah ya kara lafiya".

Kawai ya ce, ya kashe wayar Mai-jidda, ba ta san sanda ta sa kuka ba, ace wai ba ta da lafiya iya kulawar da Abdul-Aali zai nuna a gareta kenan?

Gwamma da ta taho Kano ya nuna mata halinsa na gaskiya, wato mugunta, da tana can ai ba za ta gane hakan ba. Ita kuma ta ki ta fada masa ciki ne da ita, ta san Mama ma ba ta fada ba.

*******

Washegari ta fito wanka kenan da yamma, sai ganin sa ta yi a dakin, ya ba ta mamaki kwarai, don ba ta yi tsammani ba.

"Dadin Mimie!"

"Jiddah. Yaya na ga kin tsaya ko zuwan ma kar nayi, tunda kin zabi ki gujeni?"

Murmushi ta fara yi ba ta san yaushe hawaye ya tabo gefen idanunta ba, don haka ta dan share da bakin Towel din da yake kafadarta. "Ni ban guje ka ba. Allah ma ya gani."

"Mikewa ya yi ya riko hannunta, ya zaunar da ita a bakin gado. "Yaya jikin naki? Kin ga yadda ki ka yi haske kuwa?

Ki na da jini a jikinki? Kin je asibiti kuwa? Me Likita ya-ce? Ni fa ba na son wasa da lafiya. Yaya za ki zauna har sai su Mama sun ce ki taho nan, alhali ki na fama da ciwo?"

Kallon sa kawai take yi, idanunta cike da hawaye, can kuma ta-ce. "Ina da jini na a jiki na, ban je asibiti ba da farko.

Saboda ba na zuwa asibiti bane, sannan wa zan fadawa damuwata bayan ka share ni, ka daina damuwa da ni ko waya, sai a tsume ka ke min?"

Shiru yayi sannan ya nisa. "Ki yi hakuri raina ne ya baci, na sha fada miki ba na son taurin kai. Kuma ba abinda na ke so irin ki kasance a tare da ni... Amma tsaya tukun, wane irin ciwo ne, ba na zuwa asibiti ba?"

Idanu ta bude masa tana murmushi, nan take ya dago zancen, da sauri ya kai mata sumba cikin jin dadi. "Da gaske ki ke yi Jidda?"

"Eh, bayan na dawo nan na je asibiti, sun sake tabbatar min, wata biyu kenan."

Wani farin ciki ne ya rufe shi, har ya kasa ce mata wani abu. Ta cire hannunta a nasa ta-ce. "Bari na shirya, har kasa jiki na ya bushe, ban shafa mai ba."

Kallonta yake yi cike da abubuwa a idanunsa. "Ki shirya ki zo mu tafi yawo."

"Yawo kuma ni da ba ni da lafiya, Ina za mu je?"

"Ke dai ki shirya ki fito, idan kuma so ki ke yi mu zauna anan, shi kenan sai na sa key a kofa."

Nan take ta dago manufarsa, yau ta shige su. Abdul-Aali zai jawo mata magana, yanzu ta shirya ta bi-shi, sannan su dawo bayan kuma Mama za ta gane?

To amma idan ya kulle kofa, kuma shi kenan ta tabbata a daki babu fita. Tana gama kimtsawa ta-ce. "Yaya ka ke son na yi? Mama ta san ba na jin karfin jiki na, wane unguwa za ka ce za mu je?"

"Idan ba ki fito ba, na rantse zan sa key, don ba zan iya hakuri ba."

Haka ta sungumi mayafi tana ji, ya kerawa Mama karya wai zai kai ta asibiti a sake duba ta, don ya ga kamar ba ta da jini sosai.

Mama ko ba ta ce komai ba, baya ga a dawo lafiya.

"Idan ba ta sani ba, kai za ka zo ka koma ka bar ni, ni na ke zaune da ita ka sani jin kunya kawai."

"Laifin waye? Wa ya-ce ki gudu ki bar ni, bayan kin san yadda na ke jinki a raina."

*********

Za ta mike ya kara janyota jikinsa. "Wa ya-ce miki ki tashi?"

"Yanzu kam idan muka yi dare, ce mata za ka yi PH ka kai ni asibitin ko meye?"

"Wa ya-ce miki za ki koma? Ai ta riga ta sani, saboda haka kawai ki yi zamanki da tushe, sai gobe zan mai dake."

Sai ga Mai-jidda har da kuka tana rokon Abdul-Aali ya maidata gidan Abba, amma haka ya share ta ya more abinsa.

A tsume ta zauna, a falo ta-ce. "Yanzu kam sai dai ka kwaso min kayana, ka ce na warke, don ni kam ba zan koma ba da wane ido zan kalli Mama Fisabilillahi?"

"Ki tashi na mai dake, anan din da wa za ki zauna, ki na ganin yadda ba ki iya yin komai."

"Na kusa na warke ai."

Ajiyar zuciya ya yi, ya zauna kusa da ita. "Ke da mijinki, koma ina ki ka je, ba mai miki magana, don haka ki kwantar da hankalinki, ki zo mu tafi, ni kin ga tafiya zan yi na fi son, kuma na san cewa na bar ki cikin kulawa.

Idan da son samu ne, ni da kaina na zo na kula dake, amma kin ga hakan ba zai yiwu ba for now. Amma na kusa daukar hutu Insha-Allahu, kafin nan ki daure, ki zauna da su Maman, ok, kin ji?"

"Idan za ka zo nan gaba, ka fada min, sai na taho kafin isowarka, ba wai ka saceni ka mayar da ni ba."

"Na ji Gimbiya, za mu tafi ko kuma da saura? Don ni kam zan iya."

Ta buge shi a kafadarsa, sannan ta mike suka tafi. Ranta dadi fal! Saboda Abdul-Aali ya bar fushi, daga ranar kuwa ya makalewa waya, idan suna hira kamar ya tsago ta cikin wayar haka yake ji, haka ita ma Jidda ba ta gajiya da jin muryarsa. Tunda ta samu karfin jikinta, suka tattara suka koma gidanta. Sai ta dauki A'ishan Yaya Maryam, don ta tayata zama a gidanta.

*****

Like this chappy?

I'ts short but it's also cave-man Abdul-Aali 😂😍

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top