KE NAKE SO

A wannan shekarar ne Abdul-Aali ya samu karin girma a wurin aiki, kwarai sun yi farin cikin wannan canji da aka samu.

Mai-jidda tana ta shirye-shiryen tafiya umrah da Mai-gidan, kasancewar wancan shekarar tana da tsohon ciki da Hamamatu ya je, don haka ya-ce wannan karon da ita zai je. Komai da komai ya fito, don haka ranar tafiya kawai suke jira, don har Abdul-Aali ya taho da su Hamama Kano.

Ana saura kwana biyu tafiyarsu ne, har ta je Dutse ta yi sallama Abdul-Aali, ya-ce mata. "Jidda."

Yadda ya fadi sunanta, ta san magana yake son su yi, don haka ta tattara hankalinta ta ba shi. "Daman ina son na fada miki fa tafiyar mu tare za mu yi da Hamama kasancewar Alhajinsu baida lafiya, an kwantar da shi, kuma a asibitin Jedda, za ta dubo shi, sannan mu yi Umrar. Already na gama sama mata visar ta da ticket."

"Oh, Allah ya kara masa lafiya." Ranta ya baci, don haka ba ta boye ba ta-ce. "Amma sai yanzu za ka fada min hakan, Dadin mimie?"

"Saboda ga yadda yanayin tafiyar ta kasance ne ai".

"Amma ai ka samu damar yi mata Visa, ba komai, ku je kawai. Allah ya bawa Alhajin lafiya."

"Yaya za ki ce haka? Tun farko ba da ke aka shirya tafiyar ba? Ba na son abu da rashin hankali, ko don Hamama za ta je, shi kenan sai ke ba za ki tafi ba? Ko ba jikin mahaifinta za ta je dubawa ba?"

"A'a Allah ya ba ka hakuri, ni ba nufi na ba kenan, kawai ku je tare, wata shekarar, sai ni na je, idan Allah ya bar mana rai da lafiya."

Zai yi magana, ba ta saurare shi ba, ta wuce bandaki. Ai daman Hamama ta san da rashin lafiyar, me ya sa ba ta tafi ba, sai lokacin tafiyarsu, sannan za ta wani ce za ta je dubo Alhaji.

Sai su tafi har gaba da Jedda ma, idan ana zuwa. Haka ta fara shirin kwanciyarta, bayan ta duba Muhammad da Ummita a dakin da take amfani da shi. Ba ta gama hucewa ba, ya bugo wayarta, ya shaida mata. "Ke na ke jira fa."

Duk da ranta a bace yake, ta dauki turare ta kara fesawa, sannan ta nufi sashinsa. Kallon ta yake yi, yadda ta hada rai, shigowarta don haka ya sake nasa fuskar. "Sarauniyar rigima, har yanzu maganar ce ba ta wuce ba?"

"A'a na nawa kuma? Ai ni kam ya wuce, sai dai wata kuma." Dadin sa da Jidda komin fadan da za su yi, ba ta taba kauracewa kiransa, sannan muddin ta fito.

Ta fadi ra'ayinta game da abu, to ya wuce kenan a wurinta, ga ta da dan karen kishi. Don haka ya faye kiyayewa da lallaba ta, don kar ta faye tunzura.

Cikin rarrashi ya lallaba ta, ta amince za su tafi tare, yaran duk gidan Mama suka tafi, da Ummita kawai ta tafi. Ta so ace tafiyar su biyu suka yi ta, ta gwadawa Abdul-Aali irin kulawarta, amma kuma hakan ma bai baci ba.

Abdul-Aali yana ganin ikon Allah, don ba daman ya rike jakar wata, dole haka ya bar su da kayansu, ko kallo yayi wa daya, sai daya ta daure fuska, sai suka koma ba shi dariya. Baya dai yi a gabansu, asali nunawa ma ya yi bai san suna yi ba.

*************

Madina suka fara zuwa. Mai-jidda kuwa ranta fes! Musamman idan tana cikin masallaci, ba ta jin komai sai nutsuwa, ibada ta sa a gaba sosai, ganin haka ya sa Hamama ta rage yawon saye-saye.

Ita ma ta na dan daure zuwa masallacin. Duk lokacin cin abinci. Abdul-Aali ya kan zo ya same su su tafi tare, hakan ya sa suka dan saki jiki da juna kadan. Kwanansu uku a Madina, sannan suka wuce Makkah, suna sauke Umra, suka dunguma Jidda saboda dubo jikin Alhaji.

Gaskiya yana jin jiki. Mai-jidda ta tausayawa Hamama da ta ga ta sa kuka da ta ga mahaifinta, wannan ya sa ta fita daga dakin don ta ba su wuri.

Can sai ga shi sun fito da Abdul-Aali yana rarrashinta. Sun gaisa da Hajiyarta, ita kam nan ta-ce za ta zauna, sai ta ga jikin Alhajin, sannan ta same su a Makka.

Tunda suka koma, muddin suka yi dawafi, sai sun sa mahaifinta a addu'a. Kwananta uku a Jidda ta dawo, ta ce jikin dai da sauki. Sun yi aikin su cikin kwanciyar hankali.

Kwanan su goma sha biyu, suka dawo gida. Mai-jidda dai ta kara godewa Allah, da fushi bai hanata tafiya ba, don ta samu sa'ida, a ibadar da ta yiwo.

Dawowarsu da kwana biyu aka sanar da su Allah ya yiwa Alhaji rasuwa. Wannan ba karamin girgiza su ya yi ba duka. Anyi jana'izar sa, acan, sannan Hajiyarta da yayinta maza suka dawo gida.

Duk wani kulawa da support Mai-jidda ta gwadawa Hamama a wannan lokacin, haka take kula da yaran kaf! Idan tana gidan su.

Su Baba da Umma duk sun taho gaisuwar. Tabbas Hamama ta ji mutuwar mahaifinta, kasancewar ta shaku da shi sosai. Wannan ya sa Abdul-Aali ya tsaya mata sosai, saboda ta farfado daga wannan rashin da ta yi.

Ko da aka watse, daga taron gaisuwar, gaba daya jikinta ya mutu, ba ta tsammanin za ta sake koda dariya ba, saboda wannan rashin, amma cikin ikon Allah sai radadin abin yake raguwa a zuciyarta da shudewar ko wane lokaci.

Rasuwar Alhaji ya sa kwarai ta wa'aztu da al'amarin duniya, wannan ya sa kwata-kwata ta rage duk wani kyashin da take nunawa Mai-jidda, baran ma da ya kasance ita ke da mijin, yawancin lokuta sai hakan bai dameta ba.

Ta sabarwa kanta duk da duk wani lokacin da Abdul Aali zai je Kano, sai take jin zafi a ranta, ta daina daga masa hankali, ba kamar da ba.

************

Tana ta shirye-shiryen isowar Mai-gidan tun safe ba ta ga ta zama ba, ta gyare gidan tsab! Ko ina sai kamshi yake yi, yaranta duk a tsabta ce, ko wanne tayi masu kwalliyansu gwanin ban sha'awa.

Girke-girke kuwa ta yi su masu kayatarwa. Dan daidai yadda ba zai barnatu ba. Ka na ganinta, ka san hankalinta a kwance yake, ba ta da damuwa, sai ko wanda ba za a rasa ba, saboda yanayin rayuwa. Misalin karfe hudu mai gidan ya shigo.

Mai-jiddah tana jin shigowarsa, ta mike ta bude kofar falon, daidai lokacin da zai shigo ciki, ba ta jira komai ba, tai masa kyakkyawar tarba. Ajiyar zuciya ya yi ya-ce. "Kai My Jidda, wataran za ki tsayar min da zuciya fa, wannan irin kyau haka? iye, menene sirrin ne?"

Murmushi ta yi hade da sadda kai sannan ta-ce. "Hmm! Dadin Mimie, ba ka rabo da zolaya, wai ma tukun, ina ka baro min yarana?"

Komawa ya yi da baya, ya kallo fuskarta. "Oh ke kam ta yaran ki ma ki ke ko?"

"Afuwan, to sannu da isowa. Shigo tukun na dai ka huta da kyau, amma dole ka fiddo min yara an taba haka ne?"

Murmushi ya yi. Jidda ko ta riko hannunsa zuwa daki yayin da 'yar jakarsa ta matafiya take daya hannun nata.

Kamshin da ya ji a dakinsa ne, ya haddasa masa son ya kwanta ya huta a cikin wannan ni'iman, amma kuma wasu ni'imomin suna jiran sa, domin kuwa cewa ya yi "Ban ga yarana ba Jidda, ina ki ka boye min su?"

"Kai ma ka san da sun ji shigowarka, ba sai ka gayyace su ba. Amma ina zuwa, ni ma na ji shirun ya yi yawa, idan ka ji haka, tabbas suna wani abin ne."

Ta mike za ta nemo su Muhammad, amma sai ta ji ya jawo hannunta, ya maidoda ita jikinsa, fuskarta na dab nasa, ya sa hannu ya shafo fuskarta. "Ok, yara za su iya jira kafin nan, saurara ki ji yadda ki ka dimautani."

Ai ko tabbas bugun zuciyarsa da karfi yake fita. Mai-jidda ko ta sunne kanta cikin kirjinsa, cikin jin kunya. Yana kokarin lalumo bakinta ne, suka ji motsin taba kofa, da sauri ta mike daga jikinsa ta-ce. "Young soldiers".

Dariya ya yi ya-ce "Oya, tafi daga nan, ni ma bari na karasa shiryawa na zo."

Cikin yanga da yaukin da ta san yana tabo zuciyar Mai-gidan ta fice, tana sane sarai idanunsa na kanta. A bakin kofa ta tadda M.R (Karamin Danta mai sunan marigayi). Ya dage sai dagelgel yake yi, yana so ya bude kofa. Dariya ta yi ta daga shi, sannan ta-ce. "Zo mu je mu ga me su Yaya suke yi. Uhm!

Ai kuwa tana shiga dakinta, ta sa salati. "Muhammad lafiyanka, me na ke gani haka?"

Dariya ya yi ya-ce. "Mama, Ummita ce ta-ce nai mata irin kwalliyarki, ita ma tana son ta yi kyau kamar ke."

Mai-jidda ta juya ta dubi fuskar Ummita, yadda akai mata dumu-dumu da shi, da kalolin jambaki da su eye shadow.

"Huh! Muhammad, ina ka taba ganin namiji ya yi wa mace kwalliya?" Tissue ta zara ta fara rage mata maikon fuskar. "Ummita na, ke ma ki na da kyau yadda ki ke kin ji?

Ke Beatiuful Princess ce, kuma Princesses, suna da kyau din su, ba sai sun yi kwalliya ba, sai idan sun kara girma sosai-sosai, sannan sai su yi kin ji ko?"

"Mama sai na yi girma, na yi dogon tsawo irin naki, sai ni ma na yiwa Dadin Mimie na kwalliya?"

Mai-jidda kam kunya duk ya bi ya kamata, ko a ina yarinyar nan take jin wannan. Sai Allah "Eh sai kin girma, sai ki yiwa Prince dinki kwalliya. Mu je (Toilet), na wanke miki wannan yanzu." Da aka wanko ta, sai da aka canza kaya, sannan ta-ce. "Mu tafi falo Dadi ya dawo." Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya shigo har dakin ya samesu.

Da gudu suka je suka kankame shi, suna murna.

Ya daga su duka. "Wai-wai, wani yana cin tuwo da yawa. Ai Dadi ba zai iya daga ka ba Muhammad, ka zama soldier."

Ummita ce ta shiga yi masa dariya. M.R kuma sai tafa masu yake yi, shi ma a dole ya gane ana dariya da wasa. "Me Mama ta tsaya baku, ku ka makale a daki?"

Ummita ta-ce "Dadi, ka san na yi kwalliya ta goge min, wai sai na girma na yiwa Prince dina, kamar yadda take yi maka kai ma?"

Abdul-Aali ya kallo Mai-jidda, suka hada idanu ta daga kafada ta fiddo idanu hade da daga gira. "What are you telling these kids? (Me ki ke fadawa yaran nan ne?)"

Ya tambaya cikin harshen turanci, saboda kar su ji, ai ko Muhammad ya yi caraf! Ya-ce. "She tells us nothing." Ai gaba daya suka sa dariya.

Abdul-Aali ya rike baki cikin Mamaki. "Yi hakuri na manta ashe muna da bature a gidan, Dokta Muhammad Rayyaan ko?"

"Yawwa Dadi ashe ka gane." Nan yaron ya mika masa hannu, suka tafa. Daga bisani suka koma falo aka zauna cin abinci. Sai da suka gama ne, ya fitowa kowa da tsarabarsa.

Mai-jidda ta-ce. "Nuna bambanci, ni ina tsaraba ta, wato yaranka ka sani ko?" Ta fada tana masa kallon tuhuma.

"Me ki ke sauri? Tsaraba kam naki ya fi na kowa yawa, ki jira kawai ki gani." Murmushi ta yi. Da dare suka je gidan Abba suka gaishe su. Sai da yaran suka soma hamma, sannan suka koma gida kan a isa kam M.R da Ummita sun lula.

Su ta fara kwantarwa, sannan ta shiga wanka kafin ta fito ta samu Muhammad din ma ya sa kayan barcinsa, ya bi sahunsu. Murmushi ta yi ta gyara masu kwanciyarsu ko wanne a gadon sa.

Dan siriri na yara, yayin da M.R ke cikin mai zurfi (crib). Duk ta tofe su da addu'o'i, sannan ta koma dakinta ta shirya. Tana shirin fita ne, ta ga ya shigo ya tura kofar. "Kawai kuma sai ki makale haka ake yi ne?"

"Sorry, hidindimun da yawa, da fatan dai ba wani abin ka ke bukata ba?"

Wani kallo yayi mata ya-ce. "Wace irin tambaya ce wannan?"

"A'a to wai na ga ka shigo ne kuma..."

"Ba dama na shigo dakin matata, sai da dalili? To barci na zo yi, ko ba za a ba ni wuri ba?"

Dariya ta yi game da rufe bakinta da siraran yatsunta. "Yi hakuri, ai da dakin da mai dakin duk mallakinka ne, sai yadda ka yi da su." Hannunsa ya sa ya zagaye ta game da rikota jikinsa yana shakar kamshinta. "Hmm! Na yi kewarki sosai."

Da sauri ta juyo ta-ce "Dadin Mimie, ina tsaraba ta, kar ka zaci na manta".

Ai ko ta samu kyakkyawar tsaraba. Sumbbatarta yayi da kyau sai da taji tamkar tana narkewa. "Ga tsarabar ki, ko ki na son kari, don ina da shi buhu buhu."

"Ah, wannan coge ne."

"Wannan din bai miki bane ko me? Ji ta dai tana wani abin nan..."

Hannu ta sa ta dan ture kafadansa "Ni ba na so". Ta fada a shagwabe.

"Na fada miki, ki daina min karya, ni na san komai, idan za ki ware, ki ware ehem."

Girgiza kai ta yi sannan, ta-ce. "Shi kenan tunda ka ce haka, na bada gari."

Dariya ya yi ya ja ta jikinsa. "Ehem ko ke fa."

***********

So how was the reveal?

What's your opinion about the book as a whole?

Brace yourself KNS is at #5 in romance today 😱

Alhamdulillah,

Allah knows you have a niche deep down in z bottom of my heart

Thanks for all the love.😘

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top