IKIRARI


Assalamu alaikum

I'm soooo thirlled that i want to share this good news with you.

With just five updates and your lots of love KE NAKE SO is now number 28 in romance. So thanks for voting and commenting please keep them rolling in.

I'm grinning like ear too ear, please share, vote and comment

Like bring your friends over, recommend and bring your whole zuri'a, clan and 'yan garinku over to read Ke Nake So, except for the kids of course. 🙈🙊

😌 May be I should start writing something for the kids, in prints of course no dilly dallying around the net😎

Okay ga ci gaban labarin.

******

Shigowar Mama ne ya ceci Mai-jidda. "Hamamatu ku je falo. Yahanasu ta kai maku abinci".

"To Mama mun gode."

Suna cin abinci ne. Wayar Mai-jidda ta yi kara. Mamaki ne ya kamata, da ta ga sunan da ke kan (Screen) dinta. Dan Kano? Mikewa ta yi ta-cewa Hamamatu tana zuwa, gefe can ta matsa ta amsa cikin murya kasa-kasa. "Assalamu-Alaikum."

"Wa'alaikumus-Salam." Ya fada cikinnatsuwa.

Ajiyar zuciya ta yi boyayyiya, sannan ta-ce. "Ba dai wani laifin na yi ba aka kira a tuhumeni da ranar Allah?"

"A'a, koda kin yi, ai ke kam dole a dauke idanu."

"Hmm! Yayana ke nan, Yaya iyali. Yaya kwana biyu?"

"Lafiya lau! Alhamdulillahi."

"Yau kuma me ya faru aka tuno da ni? Kwanaki wayarka ba ta shiga".

"Eh na dan yi tafiya ne, lafiya lau. Na ji shiru ne nace bari na bugo na ji ko har an shafa Fatiha ne ba mu da labari? Ko dai abin da ki ke nemana, ki fada min kenan?"

"A'a haba, ayi haka? Wannan karon dai ba za ka tsallake ba, sai ka halarci daurin aure."

"To, tunda za a ba ni wannan damar, ni ma kuma ba abin da zai hana ni zuwa da yardar Allah. Yaya Dutse?"

"Lafiya lau, yau kam gani a garinku. Tunda kai ka ki zuwa".

"Wai lallai muna da manyan baki ashe, sai dai mun yi sabani, na je wani daurin aure a Kaduna".

"Ka dai gama doje-dojen ka. Wataran dole ka nuna kanka."

Dariya ya yi cikin kasaita, sannan ya-ce. "Kar ki damu, ba ni da niyyar boye miki kaina har abada, bari na bar ki yanzu, daga baya zan kira, sai na ji dalilin nemana da ki ke yi".

"To shi kenan, na gode a gaida Madam".

Ta kashe wayar, yayin da abubuwa da dama suka motsa a cikin kirjinta. Ta zauna kenan za ta ci-gaba da cin abinci, sai ga wata wayar, ta duba ta ga Alhaji Yusuf ne.

A hankali ta amsa cikin murya mai taushi take magana. "Mun iso lafiya... Eh... anjima dai zan koma gidan Yaya Maryam". Murmushi ta yi, sannan ta-ce. "To shi kenan Allah ya kai mu." Sannan ta kashe wayar.

"Kai Anty Hauwa, wanann irin murmushi haka, kin zama Hot-Line fa, wannan na ajiyewa, wannan ke bugowa. Da gani dai, wani ya taki sa'a kenan."

"Kai Maman Mimie ke dai ayi sha'ani, wai an cuci na daji. Amma dai ana ta addu'a".

"To Allah ya tabbatar da alkhairi, yanzu za ki yi mana nisa kenan."

"A'a wane nisa kuma, ai ana tare. Bare ma fa da saura tukuna, ana dai kan fahimtar juna".

"Dama da haka ne ai, sannu a hankali har Allah ya sa a dace, ko kuma dai da wani ne daban?"

Nan take gaban Mai-jidda ya yanke ya fadi, ta daga idanu ta dube shi a bakin kofa, ba ta amsa ba, ta ji ya-ce. "Idan kun gama, sai ku kirani a waya, ni zan fita".

Matarsa ce ta amsa masa tare da mikewa ta isa wurin sa. Mai-jidda dai kanta na kasa ba ta ji me Hamamatu ta-ce ba, bare ta ga me ta yi. Sha'anin Hamama da Abdul-Aali sai su, don ko a gaban waye Sweety take ce masa.

Haka shi ma baya boye son da yake mata a gaban kowa. Sai dai yau hankalinsa na kan Mai-jidda da yadda ya ga kanta a kasa, saboda haka bai wani bawa Hamama Attention sosai ba.

Ya wuce. Ko da ya dawo, da yaran duka suka fita. Yaya Maryam ta yi murnar ganin su, ba su dade ba su Hamama suka koma nan suka bar Mai-jidda.

Yaya Maryam ta dubi Mai-jidda tana dariya Mai-jidda ta-ce "Meye?"

"A'a ni kin ji nace wani abu ne?"

"Su yi mana, haka kawai za ki fara dariya ne?"

"Na ga har kin shirya da mutumin ki, tunda ga shi har kun fara zagaye 'yan-uwa".

"Tab! Yaya Maryam dole ne ya sa ki ka ga haka, ni meye gami na da shi?" Mai-jidda ta fada hade da dauke Tray din kofuna zuwa kicin, da ta dawo ne. Yaya Maryam ta-ce "Umma dai ta fada min duk abin da yake faruwa".

"Na san kuma ta fada miki, yadda ban amince ba, da yadda kuma na gama magana da Alhaji Yusuf, har ma zai turo ayi masa tambaya."

"Duk na fahimci komai, sai dai ba na tsammanin Abdul-Aali yana da shirin barin ki nan kusa, bare ma har ya ga wani ya aure ki".

"Ni ban san me yai maku ba, duk ku ke biye masa, akwai rashin dacewa kwarai a wannan al'amari, amma sam ba ku gani, ki na ganin dai yadda na ke da matarsa.

Amma ko kunya baya ji a gaban matarsa, sai kin ga wani mayataccen kallon da yake min. Kai wasu mazan ma dai sai a hankali Wallahi".

Yaya Maryam ta yi dariya iya isarta, sannan ta-ce. "Allah ya gyara al'amarinki Mai-jidda, na ga dai haka aka yi kafin Dokta ya zo, kuma daga karshe kin bada kai, bori ya hau, yanzun ma ina ga hakan za a kuma maimaitawa. Tarihi zai maimaita kansa kenan".

"Don maza sun kare, sai na tabbata a auren 'yan gidan?" Yaya Maryam ba ta ba ta amsa ba. Can barci ya dauke ta, ba ta farka ba, sai la'asar ta tashi, jikinta ba dadi.

Don haka ta watsa ruwa, sannan ta nemi magani ta sha. Tana karatun Al-Qur'ani ne A'isha ta shigo ta-ce. "Anty Mai-jidda wai ki zo falon Baba. Uncle Abdul zai yi magana dake".

Mai-jidda kanta ta girgiza, yau kam za ta fadawa Sarkin nacin nan magana ta karshe, idan kuwa ya nemi ya matsa mata, ta san matakin da za ta dauka, don makaho bai san ana kallonsa ba, sai an taka shi.

Abdul-Aali na zaune a falon yana jiran fitowar Jidda, ya yanke shawarar bi da ita a hankali, har sai ta fahimci inda ya dosa, sannan ya kara dago mata maganar aure, tunda yin hakan da ya yi tun daga farko ne ya tsorata ta.

Tana zama a falon, ba tare da ta sake gaishe shi ba ta-ce. "Ban san wane irin zuciya ka ke da ita ba da ba ta fahimtar kalmar a'a. Ina tsammanin lokaci ya yi da za ka daina yaudarar kanka, domin ba abin da zai yiwu tsakanin mu."

Murmushi ya yi ya-ce. "Jidda kenan, ni ba maganar da ta kawoni ba kenan, ki maida wukar. Ni na kasa fahimtar wa ya tsani wani a tsakanin ni dake ne, ganin tun dawowata ke ce ki ke fada min kalamai marasa dadi."

Mai-jidda ta sassauta fushinta, don sai ta samu kanta da rashin jin dadin yadda ya dauki batunta, ta-ce.

"To idan ba abin da ya kawo ka ba kenan, me za ka fada min wanda ba za ka iya fada ba a gaban matarka dazu?"

"Na zauna na yi nazari, akan abin da na zo miki da shi, kuma na sa kaina a matsayin da ki ke ciki, na san na yi kuskuren zuwa miki da wannan maganar.

Wanda na san da wuya ki dauke ta da sauki, kasancewar ga yadda abubuwa suke. Wannan ya sa na ke so na ba ki hakuri kan duk wani abin da ki ka fuskanta a dalilina a baya."

Wani dadi ne ya ratsa zuciyar Mai-jidda, ta dago idanunta ta dube shi. "Na ji dadi da ka fahimci me na ke nufi, kuma ba komai. Komai ya wuce. Kuma ba a kara tuna komai."

"Da fatan kuma ba za ki fadawa kowa a kan na tsaneki ba, ko kuma batun da na zo miki da shi. Ni kuma zan taya ki addu'a. Allah ya zabar miki da abinda ya fi alkhairi".

"Ameen, na gode."

Ya mike tare da cewa shi zai wuce.

"Ba ka sha ruwa ba, ka jira don Allah na kawo ma".

Haka ta sa ya zauna ta kawo masa zobo mai sanyi da ruwa. Ta tsiyaya masa a (Glass Cup), sai da ya sha ne, sannan ta taka masa zuwa motarsa. "Ku, ku na nan har nan da kwana biyu ko?"

"Eh, ku yaushe za ku wuce?"

"Kin san abinka da Dan kwadago, lokacin komawata aiki ya yi, so zuwa ran litinin Insha-Allahu za mu koma. Idan ba so na ke su koreni ba."

Mai-jidda ta yi dariya har sai da ya yi dan sauti kadan. Kyawawan hakoranta suka bayyana, ya tsaya yana kallonta da gaske ita ta dauka ya hakura ne.

Shi ya sa ta saki jikinta da shi, bude masa kofar motar ta yi, sannan ta-ce. "To mun gode Abdul-Aali, ayi kwadago da kyau. Allah ya kiyaye hanya".

Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Alhaji Yusuf "Hauwa!" Da sauri ta matsa da baya, saboda yanayin fushin da ta gani a tare da shi, ta kuma rasa me za ta ce masa, don a hakikanin gaskiya, duk wanda ya ganta da Abdul-Aali a wannan lokacin, zai dauka da wani abin.

"Ka yi hakuri Yallabai ba abinda ka ke tunani ba..."

A take anan Abdul-Aali ya yi tunani, to hell with, sannu a hankali ya rufe marfin motar ya-ce da Alhaji Yusuf.

"Kwarai abin da ka ke tunani ne." Ya raba ganinsa tsakanin Alhaji Yusuf da Mai-jidda, wanda bakin su ya kusa taba kasa, don tsabar mamaki.

"Babu tantama kan tunaninka, ka yi hakuri, na san kai mutumin kirki ne kuma na yaba kwarai da yadda ka ke nuna kulawarka ga Jidda.

Sai dai ina son ka sani (I'm Wild) akan Jidda, kuma idan akwai yadda zan yi, to daga yau ba za ka sake ganinta ba, ko a gida ko a ofis".

Wannan bayanin nasa ya sa Alhaji Yusuf da Mai-jidda suka kasa furta komai, tsantsar mamaki, da ya tabbatar ya samu hankalin Mai-jidda, ya yi mata wani murmushi hade da kashe mata ido daya.

Sai da ta ji wani abu ya yi tsalle a cikin ta, yayin da da kyar ta hana kanta daga hannunta a wannan lokacin, tsabar bakin cikin da take ji tare da wani abu da ba ta san meye fassarar sa ba.

"Ina dawowa saboda ke Jidda." Ya zauna cikin motarsa, sannan ya rage glass ya-ce "Gobe Insha-Allahu".

Kafin ta-ce wani abu. Alhaji Yusuf ya koma motarsa, ya ja a fusace, jikinta a mace ta koma cikin gida.

Tana yanka ganye, tana ta fada. "Idan an ce maku baya son farin ciki na, ku bi ku rinka kare shi, idan ban da mugu, waye zai zo bayan ba aurenka zai yi ba, ya rinka korar maka masoyanka na asali.

Ni ban san inda zan je da ba zai bi-ni ba, ba na son na kara ganin ko fuskarsa, kin san wani nishadin da yake samu kansa a ciki, ganin bacin raina? Mugu kawai. Allah sai ya saka min."

Yaya Maryam ta rike hannunta ta-ce. "Hankali Mai-jidda za ki ji ciwo, kin gama yanka ganyen." Mai-jidda ta kalli (Chopping board) din taga yadda ta yi fici-fici da alayyahon.

Ta shafa goshinta cikin damuwa, game da sauke ajiyar zuciya. Yaya Maryam ta-ce. "Anya Mai-jidda ba ki dau maganar nan da zafi ba kuwa?"

Hawaye na bin fuskar Mai-jidda ta-ce. "Ina zaman zamana, ina lallaba rayuwata. Mugu ya shigo ya wargaza min komai, sai na yi sa'a na samu Alhaji Yusuf ya saurareni kuma, batun aiki na kam na san ina komawa Dutse, zan samu takardar sallama."

"Ba ki yarda da son da Alhaji Yusuf yake miki ba kenan?"

"Ba zancen haka bane, ba ki san yadda Abdul-Aali ya kure shi bane, sai kin ga yadda ya bar gidan nan."

"Abu mai sauki, idan ba kya so ki rasa shi, sai ki kira shi daga baya ki ba shi hakuri, kafin nan ya huce. Ai fushin masoyi, hutu ne."

Gaba daya sai Mai-jidda ta ji ba anan hankalin ta yake ba, damuwarta ta fi yawa akan fushin da take yi da Abdul-Aali.

Randa za ta koma ne ta daure ta je gidan Abba, saboda tayi masu sallama, koda kuwa tana shakkun haduwarta da Abdul-Aali, a halin da take ciki.

Ai kuwa suna gaisawa da Mama, sai ga shi ya shigo kamar wanda yake jiran zuwanta gidan, dauke kanta ta yi, ba ta damu da ta gaishe shi ba, koda kuwa a gaban Mama ne, don ya kai ta makura.

Sai ga Muhammad ya shigo fuskarsa duk kunu. Yana nuna wa Mama wai yau ya sha dadi. Mama ta kama shi ta-ce. "Mu je na wanke ma, haka Yahanasun ta bari, ka yi da jikinka?"

"Mama ki kara min masa tukun".

"Ka koshi haka nan, sai anjima kuma mu je na dauraye ka."

Mama tana fita a dakin. Abdul-Aali ya zauna a bakin gado kusa da kujerar da Mai-jidda take zaune ya-ce. "Jidda..."

Kallon shi ta yi a fusace, sannan ta mike za ta fita daga dakin da sauri ya bi bayanta, ya tura kofar. A razane Mai-jidda ta zaro idanunta ta-ce. "Ka bude min kofa, ba na bukatar jin komai daga gareka".

"Zan bude, amma ki zauna mu yi magana tukun".

"Dole ne magana da kai? Ka bude min kofa, tun kafin Mama ta san me ake ciki, me ka ke tsammanin za ta yi tunani, idan ta ga ka kulle kofa, bayan ina cikin dakin? Ko dama manufarka kenan?"

Ya yi ajiyar zuciya, sannan ya bude kofar. "Jidda, ki yi hakuri ki ba ni minti biyar, mu yi magana ta fahimta."

"Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar".

"Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi.

Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa.

Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya.

"Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?"

"Wace irin tambaya ce wannan?"

Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba.

"Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi?

Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?"

Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?"

This is the limit. Abdul-Aali ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wanann a tare da ni?"

"Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare.

"Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!

"Ki fada ko za ki ji dadi a ranki, amma dake da ni mun sani." Kan Mai-jidda ya kulle, mutumin da ya fi kowa tsanarta. Yaya za ayi ya maida hankali kan abin da ya shafe ta.

Har ya san su tamkar tafin hannunsa. "Yaya aka yi ka san duk wannan, bayan ka-fi kowa tsanata?"

Hannu ya sa ya shafo sumarsa, ya gaji da jin wannan kalmar a bakinta. "Jidda ki na son ki san hakikanin yadda na ke ji game da ke? Jidda duk duniya ba abinda na ke so kamarki, idan ki ka dauke Mama da Abba." Dubansa ta yi, yayin da amsarsa ta haddasa mata wani saran kai .

Mai-jidda ta bude baki, tana kallon ikon Allah, yau kuma ga wata sabuwa inji 'yan caca. Cikin kifkifta idanu ta-ce. "Engr. Abdul-Aali Sani, ba ka san me ka ke fada ba. Ina ga minti biyar dinka ya yi, za ka iya fita.

Koda yake dakin mahaifiyarka ne, ba ni da damar korar ka, ni ya kamata na tashi na tafi." Ta fada hade da mikewa za ta fita, hannu ya sa ya riko bakin mayafinta, don ya tsaida ta, amma kallon da ta masa, ya sa ya sake ta ba shiri.

"Kar ka sake kuskuren yin haka, don ka san wasu abubuwa game da rayuwata, ba shi bane zai ba ka dama ka kafa hakkin mallakarka a kaina, sannan ko da wa na ke tare, kar ka sake yi masa magana.

Bare har ka nemi korarsa ta hanyar karfi ko dabara, saboda ba ni, ba kai. Idan ko ka yi kuskuren sake tunkarata.

To Hamamatu za ta san sirrinka, don haka ka san yadda aka yi ka cire 'so na' a zuciyarka, tun kan yayi maka lahani marar gyaruwa. Ka san kuwa da muguwar rawa, gwamma kin tashi".

Abdul-Aali ya ji dacin da ya fito a kalamanta, hakan ya kara ingiza shi game da abubuwan da zuciyarsa ke karanto masa, na tsantsar son Mai-jidda.

"I don't care, duk abinda za ki fada, ki fada, amma ina so ki san wannan karon ba zan ja da baya ba, na yi kuskuren a baya, amma ba zan sake maimaitawa ba da yardar Allah. Domin kuwa Jidda KE NA KE SO!

Kuma hakan ba zai taba canzawa ba, idan ki na tsoron ki bari abin da ke ranki ya bayyana, saboda gudun bacin ran Dakta ko kuma tunanin me zai faru idan ya sani.

Then guess what Jidda? Dakta ya rasu, ke kadai ki ke ganinsa da rai, idan ki na ga aurena da za ki yi, zai muzanta dangantakata da tasa, to kuwa ki san haka za ki muzanta dangartakarki da shi.

Idan kika auri koma waye ne, ba ni ba, tunda kamar yadda suke ba muharramanki ba, haka ni ma ba muharraminki bane. Don haka na bar miki kiyi duk abinda ki ke ganin ya dace. Amma kar ki umarci zuciyata da ta daina sonki, domin, don ta so ki aka halicceta."

Hawaye ne daya na korar daya a idanunta, ba ta iya ce masa komai ba, ya fice daga dakin a fusace. Mama tana falo ta gama jin duk abinda ya faru tsakanin su.

Ita ta dade da sanin cewa da wata a kasa tsakanin Abdul-Aali da Hauwa tun kafin yau musamman yadda yake yawan sintirin zuwa Dutse ganin su tun dawowarsa.

Amma sanin Hauwa ta san zai yi wuya Abdul-Aali ya samu yadda yake so. Tana shiga dakin ta samu Mai-jidda tana share hawayenta da sauri.

"Hauwa lafiya dai na ji kamar hayaniya"

Yau ta ga ta kanta kar dai Mama ta jisu? Da wani ido za ta ganta yanzu? Duk Abdul-Aali ne ya jawo masu wannan bala'in. Yaya za ta fara kallon idon Mama ta-ce wai Danta ya mata tayin ya maye gurbin daya Danta da ta rasa, bayan ta san tare suka yi kukan rashinsa?

"Babu komai Mama, Ni zan wuce kar dare ya min" Mama ta kare mata kallo ta-ce "To shi kenan Allah ya kiyaye hanya, ki gaida wurin su Umman, akwai sakon da na hada a leda yana falo sai ki kai mata."

"To ta gode Allah ya bar zumunci, ya karo girma."

Nan Mama ta ji wani dadi a ranta, tabbas lokaci ya yi da Hauwa'unta za ta dawo gida.

Tana fita ta same shi a mota ba ta ko kalli inda yake ba ta fara takawa za ta isa bakin titi domin ta nemi abin hawa zuwa gidan Yaya Maryam. Amma ganin yana bin ta, ya sa ta tsaya, bude glass din ya yi ya-ce.

"Ki shiga na kai ki." Ba tare da ya kalli inda take ba yake magana, hakan ya sa ta bude gidan gaba ta zauna sannan suka tafi, ba wanda ya-ce wa Dan-uwansa komai.

Shiru ne ya ratsa motar sai sanyin A.c dake tashi nan Mai-jidda ta ji tsikar jikin ta na tashi, a hankali ta sauke glass din motar saboda hayaniya ya Dan shigo, ko za ta samu sassauci.

"Sorry, A.cn ya miki yawa ne?" ya tambaya hade da kai hannu ya kashe na'urar ya sauke glass din bangaren shi, sai da suka isa kofar gidan Yaya Maryam ne ya-ce "Allah ya kiyaye hanya, gobe muma za mu wuce. Sai Allah ya dawo da ni."

Ta juyo ta dube shi idanunta cike da hawaye, ba tare da ta iya cewa komai ba gudun kar ta saki kuka ta fice daga motar. "Jidda kenan..." ya fada tare da sa motar a reverse.

*******

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top