Haduwa da Rabuwa...
"Yau dai ya kamata na ga Hauwa, da fatan dai ba ta kasa yadda ake ta fada ba". Abdul-Aali ya fada yayin da ya zauna a kujerar falon Dan-uwansa Rayyan.
"You won't be disappointed, wai me ya sa ka damu ka ganta ne?"
"Saboda ina son na ga macen da ta narka zuciyar Dan-uwana. She melted the ice. Wa yake zaton Dr. Rayyan zai so wani abu, bayan littafansa?"
"Abdul-Aali ba ka da kyau, kai sai yaushe za ka kai ni?"
Abdul-Aali yayi shiru, yana murmushi ya-ce. "Tun zuwana, ba mu hadu ba, amma ina tunanin zuwa, kar ka damu zan neme ka".
Dariya Rayyan ya yi, "Kaman da gaske, ni inaga da wa kai su Hajiya suka matsawa lambar ma."
"A dai faro daga saman zai fi"
***********
Watannin su uku da soma wannan tafiyar. Rayyan ya aika aka yi masa tambayar auren Mai-jidda. Wanda ba su san da neman ba, sai da abin ya ba su mamaki, wai Mai-jidda ce za ta yi aure.
Wannan ya sa Mai-jidda ta kira Dan Kano. "Maganar gaskiya na ke fada maka, ka daina kirata a waya. Allah aure zan yi."
"Me ya sa ki ke min haka Hauwa, ko ganinki kin haramta min, yanzu ina fama da wannan, za ki dauko magana mai daci irin haka ki fada min?"
"Da gaske nake, ka yi hakuri, na yi ta kokarin fada maka hakan, kai ne ka ki fahimta. Amma Insha-Allahu Allah zai hada ka da rabonka, wacce za ta so ka kamar yadda ka ke so-na, domin ni kam na samu wanda na ke so."
"It hurts Hauwa, ki daina fada. Allah ya ba ki sa'a a rayuwa, amma ni ba zan daina sonki ba, har karshen rayuwata."
Sai da ta ji tausayinsa ya kamata.
"Yau ma ba za ka fada min sunanka ba?"
"Mai sonki." Ya fada, sannan ya kashe wayar, ta duba tana girgiza kanta.
Washegari Rayyan da Abdul-Aali suka nufi Dutse ganin matar da Dan-uwansa, kuma abokinsa zai aura. "Gidan Yayanta za mu sameta, iyayenta suna Limawa".
"Yaushe ku ke shirin sa ranar bikin na ku? Saboda na san shirye-shiryen da zan yi, ka san wurin aikin namu sai a hankali." Abdul-Aali ya tambaya.
"Kar ka damu, na isa na yi aure, ba Dan-uwana? Idan ka na so ma ka zabi Date shi kenan?"
Abdul-Aali ya-ce. "To ba damuwa, mu je dai na ga ko ta dace da Dan-uwana tukuna."
*****
Mai-jidda na kammala aji biyu aka daura aurenta da Dr Rayyan'u Sani, ba wata hidima aka yi sosai ba baya ga Fatiha da aka shafa. Dokta ya hada liyafa wa abokansa, yayin da Umma da Baba suka yi iyaka kokarin su wajen yi wa 'yarsu gatan da ya dace.
Mabruka ta-ce. "Ikon Allah, yau dai Allah ya nuna mana, idan anyi magana ni sai na yi aji uku na yi aure, ni ba zan bawa kowa kofa ba, ni na so Dokta?
Ke ma kin san baya gaba na. Ga shi dai karshen tikatiki tik! Allah ya nuna mana. Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyaba."
"Ameen, Allah ya kawo mana na ku mu gani".
"Bayan duk kin kwace kyawawan." Mabruka ta fada cikin zolaya.
"Ai na bar miki Hafiz". Suka yi dariya, can da yamma Yaya Maryam ta sa aka kara sharewa Mai-jidda gidanta aka goge tsab! Sannan ta ta sa keyarsu, duk suka tafi suka bar amarya a gidanta.
Ranar ba wanda ya kai Rayyan farin ciki, saboda ya cimma burinsa na ganin Mai-jidda a gidansa a matsayin matarsa. Ango dai ya shigo gidan shi cike da son matarsa, don haka bai jira komai ba, ya angwance.
Rayuwarsu gwanin sha'awa, ba abin da Mai-jidda take muradi irin ta ganta a gefen Rayyan dinta, wasu lokutan ya kan yi tafiya, domin koyarwa a wasu makarantun a matsayin (Visiting Lecturer).
Haka take wuni ta kwana sukuku! Idan shirun yai mata yawa, ta kira shi su yi hirarsu. Wasu lokutan kuma idan karatu ya sha kanta ma ba ta da lokacin yin hirar.
Wasu lokutan yana tafiya take komawa gidansu, ta yi zamanta, haka Mama (Hajiya Zainab) za ta yi ta zuba mata gata iri iri, ba dama ta tashi za ta yi wani gyara a dakin Mama.
Sai ta-ce a'a ta huta, ita da take da karatu sosai. Yaran gidan su Rayyan duk suna boko sosai, duk da dai mahaifinsu bai yi wani zurfi ba a bokon, amma bai hana ya ga ya tsaya yaransa sun yi karatu ba.
Rayyan shi ne babba a gidan, kowa Yaya Rayyan yake ce masa, sai Abdul-Aali, Mukhtar ke bin bayan Abdul-Aali, sai dai akwai tazara tsakanin su, ba kamar tsakanin sa da Rayyan ba. Shi Mukhtaar Likita ne.
Sai kanwarsu Suwaiba ita kuma English ta karanta tana aure a Kaduna. Kannen su biyu kuma Sulaiman da Kasim suna babban aji a Sakandire.
Dan zuwan da take yi gidan idan Rayyan ya yi tafiya ne, ya sa ta dada shakuwa da su duka, kowa yana ji da ita a gidan, musamman da ya kasance ita aka fara aurowa, haka idan (Weekend) ya yi gidanta ake zuwa a ci abinci. Kasancewarta faram-faram, ya sa nan da nan kowa ya saba da ita.
Gashi ba ta boye yadda take ji da Rayyan dinta, duk abinda suka zo, suka samu a gidan, idan ta ba su, sai ta-ce su tsaya sai Rayyan dinta ya fara tukun. Har suka fara mata tsiya ta-ce. "Ku dai fadi koma meye ne, ina da kamar shi ne?"
Mukhtaar ya-ce. "Babu, haka shi ma bayi da kamar ki."
Rayyan yayi murmushi, ya-ce. "Su daina dora miki, ina da wanda ya fi-ki ni kam".
Mai-jidda ta tsume ta-ce. "Dakta Yaya za ka fada min haka a gaban su?"
"Na fi son kowa ya sani ai, don ba da jimawa ba za ta haifo min wanda ya fi ta." Mai-jidda ta yi saurin barin falon, ai kuwa ba a dade ba.
Maganar Dokta ta zama gaskiya, ta fahimci cewa tana da juna biyu. Haka ta yi ta faman renon ciki da karatu, idan ta dawo gida Dokta ya takarkare yana kula da ita, haka za ta mike kafafu ya yi ta matsawa yana mata sannu, da ta gane kanta shagwaba iri-iri, ba wacce ba ta masa. Wani lokacin ofishinsa take zuwa ta rakashe, sai tana da Lectures ta tafi aji.
"Ki yi lokacin ki ne, ba ki san kwakwar abin cikin ke sawa ake miki haka ba ko?" Ya fada yana murmushi.
"Ni wataran na kan rasa me ya sa ka auro ni? Shin don na tara maka 'ya'ya ne ko kuwa don ka na so na." Ta hada rai tana neman rigima, haka zai biye mata su yi ta yi.
Cikinta na da wata takwas da dan dauri ne, bikin Abdul-Aali ya tashi, ba haka ta so ba, amma ba yadda ta iya haka ta shiga hidima, randa aka daura auren Abdul-Aali ta yi likis! Don haka tana dakin Mama.
"Hauwa'u anya ba za ki koma gida haka ba, na ga yau din nan fa kamar cikin ya kara sauka."
Mai-jidda tana shiru kawai, amma tun da rana take jin ta ba daidai ba, ciwon baya ya kan dan taba ta, amma yanzu zamanta sai ta ji ya tashi gadan-gadan tun tana matsewa har ta fara wash! "Lafiya kuwa Hauwa'u? Ina wayar ta ki a nemi Rayyan din ku tafi asibiti".
Mai-jidda ta lalubo wayarta da kyar ta nemi wayar Rayyan, amma (Network) ba kyau bai shiga ba, ana cikin haka, sai ga Abdul-Aali ya shigo gidan ya samu halin da ake ciki. "Abdul-Aali, su Sulaiman ba su waje ne su zo su kai Hauwa asibiti tun dazu take cikin wani irin hali, mijinta ba a samun wayarsa."
Ya dubi gefen da Mai-jidda take ta kasa zaune bare tsaye, a tsume ya-ce. "Mama idan kun shirya, sai na ajiye ku a asibitin kafin nan a samu mijin nata."
Mama ba ta yi wata wata ba, ta zari mayafi, Suwaiba ta taimakawa Mai-jidda zuwa mota, sai da suka shiga motar. Mama ta koma gida. Zuwa lokacin an fadawa Rayyan halin da ake ciki, don haka gida ya yi ya dauko jakar haihuwarta, domin ya same su a asibiti.
Abdul Ali sai duba agogo yakeyi ya gama kosawa ta haihu ko mijinta ya zo ya samu ya tafi, ya tsani asibiti. Ga abokansa sun matsa masa da kira ya ma rasa wani irin naci ne dasu.
Suwaiba ko ganin ya gagara tsaye bare zaune ta zaci damuwar Maijidda yake ciki.
"Yaya Abdul ka kwantar da hankalin ka, za su fito ai, wani lokacin yana daukar lokaci, idan an ci sa'a kuma ta haihu da wuri."
"Yanzu duk lokacinnan da ta dauka bai isa ba, za ta kara wani lokaci ba ta haihu ba?"
Suwaiba ta-ce. "Sosai, wasu fa kwana suke su wuni wasu har kwanaki" Yana fita suka hadu da Rayyan a hanya, ya nuna masa inda suke.
"Abdul-Aali, thank you. Kawai ina ga ka je gida, kar ka tsaya anan, ga shi za a kai amarya."
Sai bayan zuwansu da awa uku Mai-jidda ta haiho Danta, ana fito da yaron Abdul-Aali ya gan shi, ya karbe shi bayan Rayyan ya masa addu'a. Ba tare da bata lokaci ba, ya bar asibitin.
*****
Tana gama hutawa, aka turata dakin gefe, inda aka ba ta Danta a hannunta, ta dubi Dokta ta-ce "Kamar wasa fa abu ya taso, wayarka ba ta shiga, sai Abdul-Aali ne ya kawo mu asibiti."
Rayyan ya kalleta cike da tausayawa. "Weldon dear, kin yi kokari. Allah ya raya mana".
"Ameen, ban ga Anty Suwaiba ba?"
"Ta je gida dauko kayan Tea, za su taho da su Mama. Abdul-Aali kuma ya wuce gida, kin san yau shi ango ne."
Mai-jidda ta yi kwafa a ranta, lallai ba ta san tsanar da Abdul-Aali yayi mata ya kai haka ba, a halin da taken nan har ace masa ta haihu, amma ko sannu bai ce mata ba, ya tafi shi ta amaryarsa yake.
Ta dubi jinjirinta a hannunta ta ji wani dadi yana ratsa ta, kwanansu daya a asibiti aka sallame su, gidansu Rayyan ta koma inda Mama take ba su kulawa sosai.
Tamkar yadda Ummanta ke ji da ita, haka Mama take ji da ita. Yaya Maryam nan take zuwa duba su kullum.
Ana saura kwana biyu suna ne. Umma ta zo ta duba su, sannan ta koma. Yaro ya ci suna Muhammad. Rayyan kullum yana kusa da iyalinsa, sai dare ya yi yake komawa gida. Abin mamaki har aka yi suna, ba labarin Abdul-Aali bare matarsa a gidan.
Ba ta yi magana ba, ganin ranar ma Mama ta yi maganar rashin kawo masu amaryar ta sa. Sai ana gobe za su koma Portharcourt din su ne ya kawota.
"Anty Hauwa, ki yi hakuri fa, ba ki ganmu a suna ba, sweety ne ya-ce na hakura da zuwa, sai bayan suna saboda ribibi ga shi ban gama huce gajiyar biki ba."
"A'a ba komai Hamama, ke da ki ke amarci, me ya kai ki fita suna, kuma na san lokacin ko kin zo ma ba za ki sake ba, saboda jama'a da dama ba ki sansu ba, amma a hankali dai idan ya kai ki ko ina, za ki saba da kowa ki sansu su san ki".
Nan Hamamatu ta ji dadin kalaman Mai-jidda, haka suka sha hirarsu. Da ta tashi tafiya ta ajiye wata jibgegiyar leda ta-ce. "Wannan na yaro ne da naki Sweety ya-ce a kawo maku". Mai-jidda ta yi mata godiya, sai bayan ta tafi ne, ta kalli ledar, ta ja tsaki.
"Ina ruwana da wani kayanka." Ta dauka ta je ta nunawa Mama kayan ta yi godiya sannan ta koma dakinta. Bayan sati uku ta koma gidanta. Kasancewar ta samu mai aiki karatunta zai zo, da dan sauki ga shi ya zo karshe.
********
Tana (Semester) dinta na karshe ne, ta fara kula da canji daga Rayyan, musamman yadda bai cika janta da hira ba kamar da, sannan lokuta da dama ta kan same shi a falonsa yana waya, daga ta shigo, sai ta ga ya kashe, yana cewa babu (Network). Hakan ya sa ta tsargu, amma ba ta bari ta zarge shi ba, ta same shi da maganar.
"Ya yi barci ne?" Ya fada tare da shafa kan Muhammad dake hannun Mai-jidda.
"Eh, ya sha wankan ruwan dumi ai, sai gobe kuma idan Allah ya kai mu."
"Ina ruwan Sarkin daru." Za ta kwantar da shi ne, ya-ce ta miko masa, ya kwantar da yaron a jikin sa yana duban T.V, a gefen sa, ta zauna, sannan ta-ce. "Dakta, ni kam dai magana ce a baki na".
Sai da ta samu hankalinsa ta ci-gaba. "Na kula kamar kwanan nan akwai wani canji a tare da kai, kuma ka kasa sanar da ni ko meye, gudun kar na sa abin da ba shi bane a raina. ya sa nace zan maka magana, shin wata matsala ce a tare da kai ko kuwa wani abin ka ke boye min ko na yi maka?"
Cike da fargaba take sauraren amsar da zai ba ta, domin ta kula da yadda idanunsa suka koma, bayan tai masa wannan tambayar. Ya juya ya kwantar da Muhammad a kujerar falon, sannan ya-ce mata. "Ki kwantar da hankalin ki, babu komai daya ciki."
Kallon da take masa ne, ya sa ya fahimci ba ta gamsu da wannan amsar ba. Murmushi ya yi ya-ce. "Ki kwantar da hanaklinki, ba aure zan yi ba. Na ga kallon tuhumar da ake min kenan".
"Ni ce maka na yi tunani na kenan? Idan ka ga dama ka yi mana". Ta fada tare da daga kanta cikin rashin kulawa, jawota ya yi jikinsa ya sumbaci saman kanta ya-ce. "Uhmm! Kamar da gaske, bayan na san me ya sa ake zuwa ofis dina wuni."
Ta dago da sauri ta-ce. "Ni ba abinda yake kai ni, sai don na tayaka hira, idan kuma hakan yana takuraka.
Shi kenan sai na daina, daman ai da na je da ban je ba, na san ka na waya da wasu, tunda tun kan bikin mu ma, na san yadda 'yan mata suke maka caa!
"To ba ga shi ba, idan ance kishi, ki ce ba haka ba."
"Ba dole na yi ba, abinda ka ke so, ai shi ka ke yiwa kishi."
Da haka Rayyan ya kawar da tambayarta, ba tare da ya amsa ba. Mai-jidda ba ta sake dago maganar ba, ganin tunda tayi masa magana, ya koma kusan kamar da, sai dai ya-ce mata ayyuka sun masa yawa a wannan lokacin, don haka ta maida hankalinta wurin jarabawarta ta karshe.
********
Shirye-Shiryen auren Mabruka ne ya taso gadan-gadan, saboda satin da za su gama jarabawa za a daura auren, kasancewar bikin ya zo bagatatan!
Sun dage kwarai wajen karatu, don ganin sun gama cikin nasara, ga Muhammad ya dada wayo sosai. Duk inda suka shiga kuwa, kowa son yaron yake yi.
Mai-jidda tana gidan wunin Mabruka ne, wayarta ta yi kara, ta duba ba ta gane lambar ba, don haka ta dauka a tsanake. "Assalamu-alaikum".
"Wa'alaikumus-salam!" Mamaki ta ji da jin muryar, don haka ta cire wayar a kunnenta, ta duba, sannan ta ci-gaba da magana.
"Ina wuni."
Ba tare da ya amsa gaisuwarta ba, ya-ce. "Me ya samu wayar Yaya Rayyan ba na samunsa tun jiya?"
"Ina tsammanin (Network) ne".
"Idan yana kusa, ki ba shi wayar".
"Ina gidan biki ne..."
"Idan kin koma, ki ce ya kira ni."
Ita ta rasa meye matsalar wannan mutumin, kullum abin shi karuwa yake yi. Ta dade da sa shi a gefe, ya kira wayarta ma ko gaisuwa ba ta cancanta ba, ta tabbata abin na da matukar muhimmanci, idan ba haka ba, ta san ko duniya za ta nade ne, ba zai taba kiran wayarta ba.
Tana zuwa gida ta samu Dakta ma shigowarsa kenan, don haka bayan sun natsu ta-ce. "Kanin ka ya kira yana neman wayarka baya samu, wai ka kira shi da alama kiran na da muhimmanci".
"Me ya sa ki ka ga kamar hakan?"
"Saboda na san ko sama da kasa za su hade. Abdul-Aali ba zai taba kirana ba, ban san ma yadda aka yi yake da lamba ta ba."
Dariya Rayyan ya yi ya-ce. "Hauwa, ni dai ban san meye Abdul-Aali yai miki ba, haka ki ke fushi."
"Tab! Ni na ke fushi ko shi yake fushi, haihuwa na yi fa, ko barka bai min ba, yana jibgani a asibiti, ya juya ya tafi, ko sannu bai min ba fa."
"Oh, don Allah kar ki sani dariya, yanzu yadda na gajin nan. Yaya zan yi idan mutane biyu da na fi so duk duniya suna fada da juna? Kin ga ai ni za ku kayar.
Don haka ki yi hakuri ki masa uzuri, kar ki manta ranar fa shi ango ne, ashe ya yi kokari ma da ya jibge min ke a asibiti kafin na zo." Ya fada tare da shafo fuskarta. "Miko min wayar tawa, sai ki sama min abinci kafin nan."
Ta yi yadda ya-ce. Muhammad yana kan kafafunsa yana wasa, ta ajiye abincin ta koma taho da ruwa ne, ta ji maganar sa a waya da Abdul-Aali, duk da karshen maganar ta tsinkaya a dalilin rotsa kofin da tayi a kasa.
Ba ta damu da kwashe fasasshen glass din ba, da gudu ta iso falon ta fada jikin Dakta, yayin da yake dubanta cikin mamakin me ya jawo fashewar abu.
Amma tana shiga jikinsa ya gane ta san komai. Kuka take yi tsakaninta da Allah, da kyar Rayyan ya sa ta yi shiru. "Meye haka Hauwa? Ki daina kuka mana, ko an fada miki shi kenan, komai ya kare?"
"Yanzu Dakta, tuntuni ashe abin da yake damunka kenan, ka ki ka fada min? Ashe ban cancanci na sani ba, nayi maka addu'a.
Na kula da kai, meye amfanin lokaci na da na dauka na ke zubawa a wani karatu, idan ban san halin da mijina yake ciki ba, na taimaka masa, ka yi mana adalci da ka rufeni da wannan batu?"
"Ki kwantar da hanakalinki, me ki ka ji nace?"
"Is it worse?" Ta tambaya tare da goge hawayen da suke ta tunkudar juna a fuskarta.
"For now, dai an samu Dan tsiro ne (Growth), amma karshen wannan watan zan tafi U.S ayi bincike sosai".
Mai-jidda tana hawaye ta-ce. "Daga yau idan ka sake boye min wani abu. Ban yafe maka ba, komai rintsi kar ka sake boye min komai game da rayuwarka.
Lafiyarka lafiyata ce. Yaya ka ke son na yi, idan na tsinci kaina a tsakiyar wannan abu ba tare da warning ba? Shin ka na ganin zan iya rayuwa?"
"Ki daina wannan maganar, addu'a ita-ce gaba, ba ga shi nan ba na yi wata shida da samun labarin tsiron kuma kin taba ganin na kwanta ciwo? Don haka ki kwantar da hankalinki, kawai addu'a za mu yi Allah na tare da mu".
"Na ji, Insha-Allahu za ka samu lafiya, su Mama da Abba sun sani?"
"Abdul-Aali ne kawai ya sani, kin san tsakani na da shi, sai Allah, saboda haka ki daina fada da shi, yana min ciwo a nan". Ya fada tare da nuna kirjinsa gurbin zuciyarsa.
"Zan yi kokari na, sai dai ba laifina bane, don ya tsane ni."
Dariya ya yi, ya sumbaci, saman idanunta da ta lumshe su. Kukan Muhammad suka ji da sauri ta mike, ta manta kwata-kwata da glass din da ta fasa yaron ya yanke.
Allah ya sa ma ba mai zurfi bane yankan, da sauri ta sa abin kwashe shara ta kwashe. Yayin da Rayyan ke gyara ciwon yaron. Tana gamawa ta karbe shi a hannun Rayyan. Tana jijjigawa, sannan ta sa masa nono a baki.
Ya tsaya yana kallonsu, yayin da ya share kwalla a gefen idanunsa ba tare da ya bari ta gani ba.
An fara azumi, wannan ya bawa Mai-jidda damar dagewa da addu'a kan lafiyar mijinta, domin watan da ya gabata ya je asibiti an sake yi masa gwaje-gwaje.
Ganin duka alamomin cutar ba su gama bayyana ba, suke tunanin idan an ci sa'a za a iya aiki a ciro tsiron da ke cikin kwakwalwar sa, sai dai ba anan damuwar take ba, domin jejin daga kodarsa ta watsu zuwa kwakwalwarsa, don haka aikin babba ne.
Da yamma shigowarsa ya sameta, tana aikin buda baki a kicin. "Yaya dai Madam, sannu da aiki." Ya matso kusa yana leka tukwanen da ke kan murhu. "Me ake shirya mana ne haka, gida sai kamshi yake yi".
"Za ka gani ai, har an gama karatun ne?"
"Eh, su Mukhtaar ma sun min waya suna isowa."
"To ba damuwa, ni ma na kusa kammalawa Insha-Allahu."
"Bari na watsa ruwa kafin nan. Muhammad ya yi barci ne?"
"A'a Yaya Maryam ta yi aika dazu ya bi A'isha suka tafi." Dokta ya yi dariya, sannan ya wuce ciki. Tana gamawa, ta kimtsa komai a falo, saboda yau duk anan suke da shirin shan ruwa.
Shakuwar su Dakta da 'yan-uwansa yana ba ta sha'awa sosai, musamman idan ka gansu da iyayensu, za ka dauka ba su da wata damuwa a duniya, hakan ya sa gaba ki dayansu sun girgiza da jin labarin cutar da take tare da Dan-uwansu.
*******
"Anty Hauwa wai ina Muhammad ne, gidan ya yi shiru da yawa."
Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. "Yau kam gidan Yaya Maryam zai kwana sun tafi da A'isha dazu."
Shigowar shi ne ya sa ta yi shiru, yayin da kannensa suka fara gaishe shi, kamar ta yi shiru, amma ta gaishe shi, tunda ko idon Yayan nasa bai ji nauyi ya gaishe ta ba. Sama-sama ya amsa mata, ta tabbata da su biyu ne, ko kallon inda take, ba zai yi ba, yanzu kuwa har da cewa. "Ina Muhammad?"
Sulaiman ne ya ba shi amsa. Mai-jidda kuwa ta koma ciki ta bar su, domin ana kokarin kiran Sallah. Tana kammala asham, ta fito ta tattara falon a kwance ta sami Rayyan yana kallon labaru.
Da sauri ta taho gefen shi. "Dakta lafiya dai ko?" Ta fada tana shafa kansa, don ta ji ko lafiya.
Hannayenta ya rike ya-ce. "Lafiya kalau, haka za ki rinka kidimewa, daga kin ganni a kwance? Gajiya-ce kawai".
"Ina su Mukhtar. Yaya su ba su shigo ba?"
"Sun wuce daga masallaci, yau kam ina ga zan shiga da wuri, saboda na samu isasshen hutu."
"Za ka iya azumin kuwa gobe, na ga idanunka sun yi ja, ba dai kan bane yake ciwo ko?"
"Zan iya, kar ki damu. Na kammala da cikin jami'a ma, kin san dama shekaru hudu ne kuma sun cika, don haka ina da isasshen lokacin samun hutu."
"To bari na tara maka ruwa, sai ka sa a jikin ka, ko za ka ji dama-dama".
"Kar ki damu." Mai-jidda ta bi shi da kallo, ta san daurewa yake yi, yadda ya runtse idanun sa, da ya zo tashi.
Hannunsa ta riko ta-ce. "Yaushe ne komawarka asibiti?"
Ba ta yi aune ba, ta ji ya tafi luuu! Da sauri ta tare shi, amma ya fi karfinta, ga wani kakkarwa da yake yi. Mai-jidda ta kidime, banda kuka ba abinda take yi, can jikin ya mace ya daina kakkarwan, ta gyara shi a kidime take kiran sunan sa "Rayyaan, me ya faru ka bude idanunka....
"Inna-Lillahi'wa-Inna-Ilaihir-Raji'un!" Da sauri ta nemi wayarta, kanta ya kulle ta rasa wanda za ta kira. Da sauri ta danna lambar Mukhtar. "Mukhtar, ku yi sauri ku dawo Dakta ya fadi, ku yi sauri don Allah".
Da gudu ta tafi kicin, ta debo ruwa ta sa masa, ta dan bubbugi fuskarsa, ko zai farfado. A hankali ya soma tari, ta yi wata ajiyar zuciya tana hamdala, ta gyara masa kwanciya.
Bayan kusan minti sha biyar, wanda suka fi ko wane lokaci tsawo a wurin Mai-jidda, sai ga su Mukhtaar, nan da nan aka wuce da shi asibiti, a hanya ne Mukhatar ya kira Abba yake fada masa abin da ake ciki.
Mai-jidda kam kan a shiga asibiti ta canza kamanni, tamkar ita-ce marar lafiyar. Likitan dai ba abinda yake kokarin yi, illa ya daidaita hayyacin Rayyan saboda ya daina suman, don yayi kusan biyu daga gida zuwa yanzu.
Bayan Abba ya fito daga ofishin Likitan ne ya dawo dakin da Dakta yake, Mai-jidda ta gaishe shi, ya amsa, sannan ya dubi Mukhtar ya-ce. "Kai, mayar da Hauwa gida ta huta. Sulaiman zai zauna."
Mai-jidda ta dubi gefen da Rayyan yake kwance, idanun sa a rufe tamkar mai barci, amma kuma ya samu hakan ne, da taimakon drip dake manne a hannunsa.
Wanda Likitan ya dura maganin barci a ciki. Ba tare da ta musa ba, ta bi Mukhtar, sai dai suna fita ta-ce. "Don Allah mu bi gidan Yaya Maryam na dauki Muhammad".
"Na zaci a can zai kwana, ko ke ma za ki zauna a can, idan ya so sai mu je ki dauki abin da ki ke bukata ko?"
"Ba komai, zan koma gidana, tunda za a iya neman wani abin a gida. Mukhtar kai Likita ne, shin ba abinda za ayi wa Dakta ya warke?"
Mukhtar ya yi shiru cikin tunani kafin ya-ce. "Kar ki damu sauki yana wurin Allah, kuma za mu yi iya ka kokarin mu, domin Yaya Rayyan ya samu lafiya, ina ga daman yana shirin komawa UCLA a America.
Saboda Treatment, to kin ga ba za mu bata wani lokaci ba. Zan yi magana da Yaya Abdul, sai a san yadda za ayi a matso da tafiyar, tunda ya fara samun Attacks."
Mai-jidda ta runtse idanunta, wasu hawaye masu zafi suka biyo fuskarta, ta samu Muhammad ya yi barci, don haka Yaya Maryam ta-ce ta bar shi.
Nan ta yi ta ba ta baki akan ta daina kuka. Mukhtar ya maida ita gida, sannan ya koma asibiti. Ranar dai Mai-jidda ba ta runtsa ba, addu'a ta kwana yi, sai da ta yi sallar asuba barci mai nauyi ya kwasheta.
A firgice ta farka, karfe takwas, ta wanke kwanukan jiya, sannan ta shirya ta fita, kai tsaye asibitin ta wuce.
Ta samu ya tashi a barcin, Likitan dai ya-ce zai kara rike shi, sai ya dan samu karfin jiki, kafin ya sallame shi.
A ranar aka kammala magana akan shirye-shiryen tafiya asibiti. An nemawa Mai-jidda Visa za su tafi tare da Mukhtaar kasancewar Abdul-Aali ba zai yiwu ya tafi ba saboda aiki.
A hannun Yaya Maryam ta bar Muhammad, ta je Dutse tayi masu sallama, sannan satin da ya zagayo suka daga zuwa Los Angeles, domin duba lafiyar Dakta.
Da yake Rayyan yana koyarwa a cikin LA ya san garin sosai, sun yi masauki sannan aka yi waya domin jin lokacin da za su shiga asibitin washegari.
Suna zaune a daki ne Dakta ya-ce mata "Ba na so ki daga hankalinki, ba komai Insha-Allahu. Ina so ki daure zuciyarki, wannan satin za a fara gwaje-gwaje ne kafin su san me za a yi".
"Ba komai, Allah ya sa a dace. Allah ya ba ka lafiya, wannan ita-ce babbar addu'armu."
***********
Barka da Sallah my people. Ku ajiye min nama na sai na taba gashi da suyan kowa.😎
Poor Rayyaan he'd been hiding his illness for long.😔
what do you think about these two?
My heart goes out to them.
So what now?
I have a surprise whether it's a twist or a pleasant surprise you have to read the next update to find out.
Thank you for your love.
Keep voting and commenting.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top