DAN KANO1
Assalamu alaikum,
I hope you're all fine.
p.s massive twist ahead
Tafiyarta Dutse, ya sa ta ji dadi kwarai, ta ji dadin ganin Ummanta, wanda ta yi kewa sosai, haka Muhammad tun isarta ya makale mata.
Duk inda za ta yana biye yana ba ta labari kala-kala. Ta samu fushin Baba ya ragu. Amma sai da yayi mata fadan abin da ta yi, na tahowa yin aiki ba tare da izinin mijinta ba.
"Umma ki na ji Baba, har yau fadan bai kare ba."
"Ai dai gwamma yayi miki, da hankalinki ace kin yi haka, me za ki fadawa su A'isha da suke tasowa. Ya min daidai ai, da ya dauke ki ba sallama. Gobe kya kara tsallake umarninsa."
"Yanzu dai Umma ya wuce, ku yi hakuri."
"A haukan naki ne za mu kau da kai mu yi hakuri, yanzun me ya hana ki tafiya? Wancan karon kin ce aiki, to yanzu kuma ban ga zaman me ki ke yi ba."
"Umma fa daman, idan Muhammad ya yi hutu, zai zo ya dauke mu mu tafi can".
"To, na sanki ne ai sarai, sai ki bijiro da wani abu daban."
Mai-jidda ta san idan Umma ta fara, ba tsayawa don haka ta-ce. "Yaya labarin auren Yaya Abbakar ne?"
"Au bai gaya miki bane a waya? Ai an riga an kai goro kam, yanzu zancen lefe yaketa fama, ya kaiwa Maryamu wasu kudade ma, don ta shiga masa kasuwa."
"Lallai ma Yaya Abbakar shi ne ya yi shiru, ko labari babu, ko ba komai ni ma ai sai na bada tawa gudumawar.
Umma ba ga irinta ba. Kano kawai na tafi, amma abubuwa na faruwa, ba kwa fada min, idan na tafi wata uwa duniya kuma, sai ta Allah kenan."
Umma ba ta ba ta amsa ba, don tana ganin bata lokaci ne.
Sai da ta huta son ranta, sannan ta shirya ta tafi gidan Yaya Hamza, tana ta murnar haduwa da Anty Fauziyya, sai dai tana shiga gidan.
Jikinta ya mutu, don ganin halin da Anty Fauziyya ta ke ciki. Fuskarta a kumbure, alamun ta sha kuka. Mai-jidda ta-ce, Wai, Yayanta ya kwafsa kenan.
"Anty Fauziyya, lafiya na gan ki haka?"
Kuka ta kara fashewa da shi, don daman ranta ya gama kufula, saboda rashin sanin wanda za ta fadawa kukanta, to amma Mai-jidda kusan abokiyar shawararta ce, don kullum idan dayansu na da matsala, to dayan yake samu.
"Banda Hamza ne..."
"Me ya faru kuma, har yanzu maganar ce?"
"Ai ke kam, yanzu ma komai ya lalace, yau baram-baram muka yi kan ya fita. Kamar ni wannan abin baya damuna, ke kanki kin san irin damuwar da na ke ciki game da rashin haihuwar nan, amma idan ya tashi tamkar ni ba na son na haihu, haka yake min."
"To, amma kuma da abin nan fa bai dame shi ba, na rasa me ya sa yanzu zai daga hankalin sa? Sannan komai fa yin Allah ne, abinda ki na samun cikin. Miscarriage ne matsalarki, kuma da za ki kula da shan magunguna, komai zai daidaita Insha-Allahu."
"Ai yanzu ba kan wannan bane, last month mun je asibiti, a kai min gwaje-gwaje. To shi kenan sai Likita ya-ce wai (Infection) ke jawo min bari. (Miscarriage) dina.
Dole na kiyaye abubuwan da suke kawo kamuwa da cutar (Infection), na yi maganinsa, sannan mu ci gaba da gwadawa har Allah ya sa mu dace".
Mai-jidda ta dubi Anty Fauziyya cike da tausayi. "To ba ga shi an samu abin da yake jawowa ba. Ai Alhamulillah! Daman farkon samun sauki, to gano cuta ne. To meye matsalar anan?"
Anty Fauziyya ta goge hawayen fuskarta. "Mai-jidda kin san yadda na ke da tsoron kishiya a rayuwata?"
Kwarai Mai-jidda ta sani, don wataran abin Anty Fauziyya har dariya yake ba ta.
"Eh, yanzu kuma da ni ki ke yi kenan."
"Ba haka bane, maganar gaskiya ce, to wannan dalilin ya sa duk inda na ji labarin wani abu da zai sa na rike mijina na kara daraja a idanunsa , to nan na ke bazama, don na fi kauri ta wannan wurin, hakan ya sa ba kalar maganin matan da ba na amfani da shi.
In takaice miki zance dai. Hamza na ganin ajiyata komai ya banbame, domin kuwa ya kaiwa Doctor, nan Likita ya-ce, to ai wannan abubuwan da na ke ta amfani da su, su suka jawo min Infection."
Mai-jidda ta jinjina maganar. "Tun daga mota ya fara min masifa, ta inda yake shiga, ba ta nan yake fita ba, ni kuma shi ne da safe raina ya baci, na rama maganganun da ya fada.
Don Allah duk ba don shi na ke ta faman wannan saye-sayen magungunan ba? Yanzu wai haushina yake ji, saboda ni na hana mu samun haihuwa."
"Hmmm! Anty Fauziyya kar ki ce wai na bi bayan Yaya Hamza, amma ni tun ba yau ba na sha fada maku, wannan kayan duk shirme ne.
Ba wai nace kar ki yi gyara bane, amma dai ki rinka sanin inda za ki saya, ki kuma lura da hannun wa ki ka saya, saboda akwai marasa kyau.
Sannan ni na rasa me yake damun mata yanzu, duk inda mace ta ji abin mallake miji ko shi menene, sai ta karba ta afa, ko ta cusa ba tare da ta san da me aka yi shi ba.
Ko yaya aka yi shi. Sannan yaya lafiyar sa a jikinta, ko kuwa me zai mata nan gaba. Yanzu dai kawai abunyi shine ki natsu ki jira, idan ya huce kadan sai ki bashi hakuri.
Ke kuma sai ki koma aikin nature. Tunda gaki ga komai da zaki bukata cikin ingancin lafiya a kitchen dinki.'
"Sai kinga asarar kudina da ya min gaba daya ya juye komai a dustbin, harda wanda na saya dubu ashirin."
Maijidda dai da kyar ta gimtse dariyarta.
Anty Fauziyya ta buga uban tagumi. "Yanzu ni na rasa me yake min dadi? Sai kin ga yadda ya bar gidan nan, ba mu taba fada irin na yau ba. Ga shi ga-rin neman kiba, na samo rama."
"Kar ki da mu. Insha-Allahu. It's not late, idan ya dawo, ki lallaba shi, ki ba shi hakuri ki nuna masa nadamarki. Ki ci gaba da zuwa asibiti kuma har Allah ya ba ki lafiya, ai ba a cire rai a rahamar Allah. Insha-Allahu za mu daga yaron Yaya Hamza da Anty Fauziyyan mu".
"Na gode kwarai Mai-jidda."
Sai da Mai-jidda ta tabbata hankalin Anty Fauziyya ya kwanta, sannan ta-ce za ta koma gida. Bayan kwana biyu da suka yi waya, ta ji muryarta wasai! "Iye, an gyaro ta kenan. Dama ai mun san fushin masoyi, hutu ne.".
"Hmm! Ke dai bari, ba irin kashedin da bai min ba akan wannan harkar. Ai ni ma na hakura, ba dole ba. Ace da Iya Inna In-ji 'ya'yan mayya."
"To ya yi kyau. Ki gaishe shi."
"Zai ji, ki gaida Muhammad da su Umma."
*****
Muhammad na kammala jarrabawarsa. Mai-jidda ta hada kayansa, suka koma Kano, saboda Abdul-Aali ya fada mata yana tahowa karshen sati. Gidan Mama ya makale, saboda ya fi gane can.
Tarba sosai ta shiryawa Mai-gidan, tun shigowar sa yake mata kallon yabawa, saboda adon da ta yi. Da dare ta kawo masa Tea ne a Parlo ta samu wuri ta zauna a gefen sa. "Kun kammala shirin ku dai duka ko?"
"Eh, ba abinda ya rage. Sai dai kwanaki nawa za mu yi?"
"Kin gan ki da neman magana ko? Ina ruwanki da kwanakin da za ku yi, ke dai ki dauki duk abinda ku ke bukata."
Shiru ta yi tana tunani, ita ba ta son zuwa ta zauna a can gaba daya, ba wanda ta sani. "Tunanin me ki ke yi?"
"Kawai dai ni ina tunanin zaman namu ne gaba daya a can da zan fi so ka bar mu anan".
"Ina ce dai mun gama magana, kafin tafiyata, yanzu kuma me yayi saura?"
"Wai ina tunanin ko za ka dan canza shawara ne." Ta fada gami da dan karya wuya.
Wani kallo ya mata kasa-kasa, "Ke ba ki san yadda na ke ji ba, idan ba kya tare da ni ko?"
Mai-jidda a take ta ji wannan balli-ballin ya dawo cikin kirjinta. "Dadin Mimie kenan, da, da ba na nan, mutuwa ka yi?"
"Dan-uwan hakan ne ai, yanzu ko daidai na ke jin kaina." Kafin ta amsa masa ne. Wayarsa ta dau ruri, don haka ya daga.
Ji kawai ta yi ya-ce. "Na'am sweety. Yaya ki ke da yaran?'
Kut! Wato ita ce ba daman ta kira waya, amma shi za a kira shi, idan yana tare da ita ko? Sannan shi kuma har da wani amsa mata, tamkar shi kadai ne a falon. Haushin da ta ji ne, ya sa ba ta tsaya sauraron sauran zancen ba. Ta mike za ta bar falon.
Ji ta yi ya riko hannunta, yayi mata nuni da ta zauna. Tabdi! Lallai ma, haka ta daure ta jira, ya gama magana da Hamamatu, saboda ba ta son masa gardama, yana kashe wayar ya-ce. "Ina za ki je da?"
"Wace irin tamabaya ce haka? Dama wato da gaske, idan ka na can ma haka ka ke waya da ni a gabanta ko?"
Abdul-Aali ya yi murmushi ya-ce. "Ke fitinarki ma ta daban ce, don na yi magana a gabanki, sai me?"
"A'a ni dai gaskiya ba na so, idan har za ka yi magana da ni, ban bukatar kowa ya ji mu, ina ce waya na kira, aka ce min ba a kiranka, sai dai kai ka kira?"
"Jidda, kenan. Na ji zan daina waya dake a gaban kowa, shi kenan?"
"Ba shi kenan ba, haka ni ma idan ka na tare da ni, lokacina, lokacina ne, ba na son a bawa kowa, sai dai idan lalura ce ta taso, to. Kuma batun gaskiya ne ai, ba wani abu ba."
"To ranki shi dade."
Jidda ta juya idanunta, cikin wani salo.
"Tunda ki na Mood din Ideal wife, sai ai min tausa." fuskarsa kunshe da murmushin tsokana.
"Dadin Mimie, don Allah ka bar wasa, sai da safe."
"Ke dadi na dake, sai ki yi ta noke-noke, bayan kuma ni na san komai. Anjima kadan za ki zo ki na buga min kofa." Ya fada yana wannan murmushinsa na daban din.
Kunya ta kamata, ta yi kasa da kai, bakinta mutuwa ya yi murus! Ai tunda ta yi kuskure, ta ja wa kanta abin magana a gun Abdul-Aali ta shiga uku. Haka ta fara masa tausa, kamar yadda ya bukata, idanunsa a lumshe. Sai ya dan bude, ya dubeta ya yi murmushi.
******
Sai washegari suka je gaida su Abba. Nan ne suka taho da Muhammad, yana ganin sa kuwa, ya makale masa, ya sha labari kala-kala, tare da tambayar su Mimie. "Zan kai ka gunsu, za ka je ai?"
"Zan je, yaushe za ka kai ni? Mamana ta-ce da nisa".
"Gobe Insha-Allahu. Maman ka ta taba zuwa ne?" Ya fada yana kallon Mai-jidda.
"Kai Muhammad surutun ya isa haka, ka bar Uncle Abdul-Aali ya huta."
"Mama labari fa muke yi".
"Ki rabu da shi, ba ruwanki, mun saki a maganar mu ne? Ba ka ban labari ba, grade nawa ka samu a School ma?"
Nan Muhammad ya yi ta zuba, tare suka ci abinci, wajen karfe takwas ya gaji, ya kwanta.
Isar su PH. Abdul-Aali yayi masu shatar mota zuwa gida, suna isa. Su Ramla ne suka taryi Dadin su, da gudu suna masa sannu da zuwa, kafin Hamama ta fito, kai tsaye ta wuce jikinsa tana masa sannu da zuwa. Mai-jidda aka bari da kau da kai.
Sai da suka gama sannu da zuwa, sannan Abdul-Aali ya sa yaron gidan sa ya shigo masu da kayansu ciki. Kamar yadda ya fada, gidan wadatacce ne.
Tsarin gidajen, dakuna uku ne da babban falo guda, sai kicin. Dakuna biyu, suna da (Toilet) a cikinsu, yayin da (Toilet) daya kuma yake wajen daya dakin.
Mai-gidan ne ya nuna mata dakinta, don haka ta shigar da kaya, tun sannu da dawowa Hamama ba ta sake ce mata komai ba. Nan falo Muhammad ya tsaya da su Mimie suka samu wasa. Mai-jidda ta karewa dakin kallo gefen kujerar dakin, ta ajiye akwatinsu, gadon babu bedsheet.
Allah ya so ta, ta yi guzurin komai, saboda rashin sanin yadda za ta samu wurin. Tana shimfida gadon, ta shiga ta watsa ruwa, ta ajiye duk abinda za ta bukata na bandaki a bandakin. Cikin shigar atamfa ta fito falon nan ta samu yaran, kamar tashin murya take ji a ciki, sai dai ba ta bada hankalinta kan hakan ba.
"Wane irin abu ne, za ki ce ba ki yi abinci ba? Sai ka ce ba ki san yau za mu taho ba?"
"Sweety kai ma ka san yadda ba na jin dadi yau da ciwon kai na tashi..."
"Amma dai ki na ganin irin dawainiyar da Jiddah ta yi zuwanmu Kano ko?"
Ran Hamama ya sosu don me ya sa zai yi ta koda matar sa a gabanta."To ai sweety ita lafiyarta kalau lokacin, haba ka tausaya min mana"
"Wannan rashin hankali ne kuma ba zan amince da shi ba, gwamma kin sani." Ya zari makullin mota ya fito cikin zafin rai, ganin Jiddah a falon ya sa ya sauke numfashi saboda bacin ransa ya ragu.
Cikin su ya zauna ya daga Ramla ya-ce "Wa zai raka Daddy yawo?"
Dukan su suka daga hannu, "To shi kenan Mimie dauko maku takalman ku da huluna sai ku zo mu tafi." Ya dubi Jidda ya-ce "ke ma shirya ki zo mu je."
Mai-jidda ta dube shi yanzu isowarsu kuma ina za su je? "Fita kuma?"
"Za mu je neman abinci, Hamama ba ta ji dadi ba don haka gidan ba abinci." ya fada yana sosa kai.
Jin haka ya sa ta mike ta je ta shirya, sai dai da suka zo fita ne sai ba ta ga Hamama ba ta-ce "Ina Mamin mimie?"
"Jikin ya motsa so, nace ta kwanta mu je mu dawo yanzu."
"Dadin Mimie, ku je da yaran kawai ba dadi duk mu watse mu bar ta ba lafiya, idan yaso sai ka taho mana da abincin."
Dubanta ya yi kawai ya rasa abin cewa, don haka ya kwashi su Muhammad suka tafi niyyarsa da Jidda ta je ko ruwa ba zai sayowa Hamamatu ba sai ta ci halinta.
Haka ya jido masu kayan cima iri iri suka zauna a falon shi suka ci kayansu, sai can Hamama ta fito fuska a murtuke, Mai-jidda tana mata sannu ba ko kunya ta sa baki ta amsa.
Abdul-Aali ya kalleta, ya san ba ciwon da take yi kawai shirme ne irin nata, don tun kan ya tafi dauko Mai-jidda ta tada hankali wai ita kam ba ta son ta zo mata gida.
"Gidan nan, gida na ne, kuma duk matar da na ke aure, ni na ke da ikon a kanta, wajibi ta bi duk yadda na ke so, saboda haka ki kwantar da hankalinki. Jidda za ta taho kuma. (I want you to be nice to her.)"
Shi ne ita kuma ta zabi tayi masa haka. Ya rasa me yake damun mata, idan sun tashi yin wani abin, ba su ko tunani, yanzu da haka za ta durawa yaran nan tarkace, duk don kar ta bawa kishiya abinci. Ya ja tsaki a fili.
****
Tana gyarawa Muhammad kwanciyar sa ne. Abdul-Aali ya shigo dakin yi mata sai da safe.
"Har ya yi barci?"
"Wai yau yadda suka sha wasan nan, ai dole ya yi barci da wuri. Ramla duk ta riga su ma."
"Ina ruwan Muhammad." Ya fada tare da shafa kansa. "Ba abin da ku ke bukata ko?"
"A'a tukun na dai, sai dai ko daga baya Yanzu kam Alhamdulillahi".
"To shi kenan mu kwana lafiya." Ya fada tare da shafa fuskarta.
A sanyaye ta amsa. "Allah ya tashe mu."
Ya rasa me ya sa yake jin Jidda har haka a ransa, ba wani sabo ya yi da ita sosai ba, amma koyaushe ya kalleta, wani natsuwa yake samu a tare da shi. A dole ya koma dakinsa, domin dakin da yara suke amfani da shi. Nan Hamama ta tattara ta koma, ita wai a dole ba za ta hada shimfida da Mai-jidda ba, zuwa ya yi ya yi kwanciyarsa.
Kwanansu uku a gidan, amma Hamama ba ta canza zani ba, don haka Abdul-Aali ya sameta ya bi-ta da nasiha, tunda dai ya ga fushin nasa, bai sa ta sassauto ba.
Ta nuna dai yayi mata afuwa. Amma har cikin ranta daga shi, har matarsa haushi suke ba ta, ko da ta fada masa haka. Ransa kal! Ya shiga, saboda Jidda tana jiransa.
Tana fitowa daga bandaki ne, ta ji wayarta na kara, hakan ya sa ta duba, ta ga ko waye. Hankalinta ne ya tashi. Ganin sunan kan Screen din.
Har bari ta ji ta soma yi. Amma ta ki ta daga. Daidai lokacin Abdul-Aali ya shigo dakin, ta yi saurin daga wayar ta yi Rejecting. Sannan ta kasheta gaba ki daya.
Yake ta yi, wanda ya fi kuka ciwo, yau lafiya karfe goma da rabi Dan Kano zai kira wayarta. Bayan sun daina waya, tun ran daurin aurenta? Anya ba gamo ta yi ba kuwa?
"Jidda, lafiya na gan ki haka? Me ya sameki?"
Da sauri ta damki bakin gado ta zauna, tana maida numfashi ta-ce masa. "Babu komai." Yau me Abdul-Aali zai yi tunani, idan ya ga wani yana kiranta a wannan lokacin, anya ba zai zargi ko haka take yi ba daman can?
Jin hannayensa da ta yi a kafadunta ne, ya sa ta razana ta dago idanu, tana dubansa. "Jidda jikin ki rawa fa yake yi, are you sure, babu wani abu?"
Da kyar ta hadiye yawu, sannan ta-ce. "Lafiya kalau. Sai da safe".
Nan da nan ta kudundune a gefen gadon, ganin haka bai matsa mata ba. Ya kwanta a bayanta hade da jawota jikinsa, ya sumbaci wuyanta
"Good night".
*********
What do you think?
Now the ultimate question remains: Who is Dan Kano?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top