DAN KANO 2
Kafin hutunsa ya kare ne. Bikin Yaya Abbakar ya taso, don haka ta tafi Dutse, saboda bikin, ran daurin auren ne. Ya taho da Hamama da yara. Nan da nan kuwa Mai-jidda tayi masu kyakkyawar tarba. Hamama dai ba a son ranta ba, Abdul-Aali ya tattarasu suka taho.
Haka ta tsaya tana karewa gidan su Mai-jidda kallo, daman haka tsiyar take, shi ne ake wani ji da ita? Tana tsegumi a ranta ne kawai, ta ga Muhammad yana bawa Ramla ruwa a cup, da sauri ta wabce ta-ce. "Yaya za ka ba ta ruwan famfo?"
Mai-jidda ta kula da hakan, don haka ta aika aka sayo carton din faro a shago. Ta bude ta-ce. "Yaro kam, duk inda ya shiga zai iya shan komai, kar ki sabar masu da ruwan roba kawai.
Saboda hakan ne zai sa randa suka sha wanda ba shi ba, ya sa su ciwo. Ko kuma ki rinka yi masu yawo da ruwansu."
Jikin Hamama ya yi sanyi, Mai-jidda ta san duk don ta gwada mata matsayinta ne, ta yi hakan, ba ta san duk wannan bai dameta ba.
Ko da suka tashi tafiya, kayan biki tirim! Mai-jidda ta warewa Hamama, ta sa mata a mota, don ita sai ran Litinin za ta koma Kano. Suna tafiya, ta koma dakinta ta samu Anty Fauziyya, wacce take kinshingide saboda gajiya. "Anty Fauziyya ke kam magana nake so mu yi, tun zuwa na maganar take cina."
"Lafiya? Me ya faru?"
"Kin tuna Dan Kano da na ba ki labari?"
Anty Fauziyya ta yi shiru cikin nazari kafin ta tuno "Oh, mai sonki da ki ke ban labari?"
Mai-jidda ta sauke numfashi ta ce. "Eh, yanzu ya addabi rayuwata. (Text) ba su karewa, ranan kam cikin dare ma ya kirani saura kiris! Abdul-Aali ya ga wayar. Tsorona daya, kar ya ga irin sakwanninsa ya zargeni, shi ya sa na ke son fada masa komai ko me ki ka ce?"
Anty Fauziyya ta yi shiru cikin tunani sannan ta-ce. "Gaskiya tunda ya fara haka, gwamma kin fada masa ko don gudun zargi. Ko ba komai za ki wanke kanki."
Ajiyar zuciya ta yi, ko me yake damunta da har da take son mutumin nan? "Shi kenan Insha-Allahu, ina komawa zan fada masa. Ba ki ga tashin hankalin da yake sani ba, yadda ki ka san wani aljani."
"Allah ya sawwaka. Ba komai Insha-Allahu, shi zai san matakin da zai dauka, idan abu ya kasa, sai ki canza lambar waya."
Hankalin Mai-jidda ya dan kwanta, bayan sun yi magana da Anty Fauziyya. Sai da suka taya Umma kimtse-kimtse, sannan kowaccensu ta koma dakinta.
Tana ta tunanin abin da zai biyo baya, idan Abdul-Aali ya ji labarin Dan Kano, ko dai ta yi shiru ne kawai ta canza lambarta? Kayya! Idan ya samu a wani wuri fa?
Tana tsakiyar tunani ne, ya shigo dakinta, ya samu Muhammad ya yi barci a kan cinyarta, ita kuma ta yi nisa a tunani, ba ta ji shigowarsa ba ma. Ji ta yi kawai ya daga Muhammad, ya kwantar da kyau, sannan ya-ce. "Jidda..."
Da sauri ta firgita. "Na'am".
"Lafiya kuwa me yake damunki ne kwanan nan?"
Wannan ne lokacin da ya kamata ki fada, ta yi tunani a ranta. "Daman akwai maganar da na ke so, na fada maka ne."
"Shi ne duk ki ka jeme, ki ka shiga damuwa?"
"To ai ban san yadda zan yi na fara fada ba, kayi min alkawarin ranka ba zai baci ba, idan na fada maka."
Kallonta yake yi sannan ya-ce. "Ina jinki menene?"
Riko hannunsa ta yi suka koma falonta, nan ta soma ba shi labarin Dan Kano, tun daga bin ta da yake yi a mota, kafin aurenta, har wayar da yake mata har dawowarsa rayuwarta, da kuma rabuwarsu da abin da ya soma yi yanzu. Ga mamakinta, ji ta yi ya kwashe da dariya.
"Dadin Mimie dariya na ba ka?"
Ya tsagaita ya dubeta. "Jidda, ba dole ki ba ni dariya ba?" Ta yi fici-fici da idanu tana kallonsa, ta rasa meye abin dariya a labarinta kaf! "Haba Jidda da dai na zaci you are smart Yaya za ayi ki dauka Dan Kano da gaske yana existing? Meye marabar Kano da Dutse da har ayyuka za su hana shi zuwa wurinki, idan har da gaske sonki yake yi?"
Ita ma kanta ta ga wautarta, "To kana ga na yi hauka ne, na ke ganin sakwanninsa a wayata? Idan baya existing, yaya ake yi na ke ganin sakwanninsa, na ke kuma jin muryarsa?"
"Wannan kuma wani ne kawai, hala yake miki wasa da hankali."
Mai-jidda ta ji ranta ya baci. "Ba wani wasa da hankali, ni na san me na ke ji idan muna magana. Kai dai kawai haushi ka ke ji, saboda kana ga shi na ke so, ba kai ba." Ta fada a shagwabe.
A lokacin ne ran Abdul-Aali yayi matukar baci hankalinsa ya tashi, me yake kallo, yana zaune da matarsa tana son wani? Kunar furuncinta ya zaburar dashi amma ya tuna ya mata alkawrin zai saurareta ba tare da ya bata rai ba. Don haka ya sauke numfashi sannu a hankali.
"Ko ba gaskiya na fada ba?"
"Ke dai kina da allergy da ni, kuma ko za ki yi yaya, duniyarki da tawa a hade take, ba ta rabewa."
"Allergy?"
"Allergy da soyayyata, ba kya iya bari ta shige ki bare ta nuna a jikin ki, ko a zahiri ko badini."
Ta kasa gane abu guda da Abdul-Aali yake fada. "Yaya aka yi? Ki fada min wani abu guda da zai yi Proving shi mutum ne kamar kowa, meye sunan sa?"
Nan ta fara inda-inda, tunda ko sunan sa bata sani ba, ita wace irin wawiya ce da ko sunansa ta kasa sawa ya fada mata, duk tsawon lokacin nan.
"Ban sani ba, amma dai wannan ba shi zai sa kace ba da mutum nake magana ba."
"Kina jin me kike fada kuwa?"
Tsumewa tayi hade da harde hannu a kirjinta, da kankance idanu tana dubansa "Naga ma abun nan kaman bai dameka ba, nima maganina da na fada maka."
"See you, ki dubeni dai cikin idanuna don baki da kunya kina fada min wai wani kike so idan yana existing da gaske ina Kano ina Dutse da bai taba zuwa ya ganki ba?"
Wayarta ta mika masa wurin sakonninta ya karanta da idanunsa, hankalinsa ya tashi sosai. Ranshi ya baci matuka sai dai ya rasa yanda zaiyi da wannan fushin, abu daya ya sani shine cewa matarsa tana sonshi komin yanda taso ta kaucewa hakan kuwa. Kuma shima yana sonta, kuma ya yarda da ita fiye da zaton shi.
Domin kuwa da wata ce ko kuma da bai yarda da ita ba a yanda yake jinsa a yanzu bai san me zai aikata ba. Sanin cewa Jidda tasa ce yasa hankalinshi a kwance ya nisa, lokaci yayi da zai cire damuwar Dan Kano a gidansa.
"Jidda, ko ta wani hali na fito miki NI KIKE SO, haka ni ma KE NAKE SO, saboda duk son da ki ke yiwa Dan Kano.
Kin danne shi saboda hakkin igiyar aure a kanki, kin nuna soyayyar mijinki, da yake zahiri ya doke na wanda ki ke yiwa waninsa a badini, so you truely do love me."
Da sauri ta ja da baya cikin tsananin razana da mamaki,"Kana nufin kaine Dan Kano?"
Bai san me zai tarar ba amma ya runtse idanu ya bude sannan yace "Ko me kika ce Hauwa?"
Bugun zuciyarta ce ya karu, yau ta ga ta kanta ba wanda ya san Dan kano Hauwa yake kiranta sai ita.
Inna-Lillahi'wa-Inna-Iilaihir-Raji'un! Abdul-Aali ne Dan Kano, yau ta shiga uku, tana son mijinta badini, tana tunanin sa wani ne daban, ba tare da sanin cewa shi take zama da shi ba.
"Amma ka cuceni, duk wannan lokacin kai ne Dan Kano, shi ne ka ke wasa da hankali na?"
Murmushi yayi mata sannan ya-ce. "Idan ba za ki so Abdul-Aali a zahiri ba, ai za ki so shi a badini. " Ya fada hade da lakace mata hanci.
Kasa ta yi da kanta sannan ta-ce. "Yaya ka ke son na yi? Kai ka kirkire shi, ka ci gaba da ja na ka yaudareni har na fada cikin son shi, kai ka kirkiri damuwar da kanka, meye laifina? Don na fada wannan tarkon?"
Wani abu yaji ya damke shi a kirji cikin jin ciwon kalamanta. Tabbas mutumin can ya masa barna ko ma wanene, shi ya hana Jiddansa sake zuciyarta ta amince da shi tun a karo na farko.
Tun ganinsa na farko da yayi mata a Dutse da ya raka yaya Rayyaan wurinta, duniyarsa ta dauke wuta domin kuwa farat daya yaji ta shige masa zuciya, ya mance mai ya kawo su, ya mance wa ya rako, ya mance matsayinsa a wannan yanayin shi dai fararen idanun Jidda kawai yake gani, da kyawawan hakoranta masu dauke numfashi idan tayi murmushi.
A take a nan yasan ya kamu da son Jidda, abun da bai taba faruwa dashi ba, kullum yana boyewa 'yan uwansa akan ya samu wacce yake so. Sai gashi ya samu wacce yake so da gaske amma yayansa da yafi so yana sonta kuma itama shi take so.
Wannan yasa ya yankewa kanshi barin duk wata mu'amala ko wani hulda da ya san zai hadasu, amma a rashin saninsa duk lokacin da ya nisantar da kansa daga Jiddansa iya tsananin tsumuwan da sonta keyi a zuciyarsa.
"Ina so a karo na farko ki fada min da kanki, kina son Abdul-Ali?" nan take ya samu kanshi da yi mata wannan tambayar domin he really needed to know, dole ya san wannan.
"Kina son Abdul-Aali a matsayinsa na Abdul-Aali? Kina sona as a person, ko a matsayin Dan kano, ko a matsayina na mugun mijinki mai sace ki, ko wanda bayi da sassauci, ko mai zuwa miki a mafarkinki, ko..." Sauke numfashi yayi yana dubanta.
Shiru tayi tana kallon wani intense kallon da idanunsa suke zubo wa nata kwayan idanun, ji tayi kaman numfashinsa ya canza sauti, tamkar abunda yake matukar son ji kenan kafin ya samu daidaituwar numfashinsa.
Lumshe idanu ta yi sannan ta-ce. "Kwarai kuwa, ina sonka. Ko kana tantaman hakan ne?"
Hancinta ya ja.
Sannan ya hada goshinsa da nata cikin ajiyar zuciya. Hawaye yaji sun cika masa idanu, amma bai bude idanunsa ba bare ta gansu. Ya san ko ba komai Yau soyayyarsa ta kafu cikin jini da zuciyar Jiddansa.
A hankali muryarta ta dawo dashi duniyar da suke a lokacin
"Wato shi yasa kake kirana da hidden number don kar naga lambar ka ko? To me yasa daga baya bana samun daya layinka?"
Shiru yayi cikin nazari sannan yace "Na bar UK a lokacin so bana amfani da wancan lambar." Fatansa daya Allah Yasa gajeren lissafin da yayi a kanshi yayi daidai, karantar kyakkyawar fuskarta ya koma yi.
Yana matukar son Jidda, kuma duk wani farin cikin rayuwa zai iya damka mata shi idan yana cikin ikonsa wannan yasa a wannan lokacin yaji ya tsani kansa da mata karya da yayi amma ya zamo lallai, wayarta kawai zai canza mata koda asalain 'Dan Kano' zai sake kuskuren tuntubarta, amma ya zamo lallai ya san ko wanene wannan mutumin.
Ta yi shiru tana tuno abubuwan da ta taba fadawa Dan Kano, nan ta rufe fuska ta-ce. "Wallahi sai na rama, ka cuceni da yawa, shi ne har da wani kirana ranar muka yi hira, bayan ka san Mamin Mimie tana nan a falon Mama."
Ya tuno lokacin da yazo shiga dakin maman yajita a kan waya har Hamamatu na mata tsiya, radadin da ya samu kanshi a wancan lokacin ba a magana, hakan ya sa ya hana kanshi fita daga dakin a lokacin ji yakeyi da za a daura musu aure a lokacin tsabar baya son ya bawa wani ma daman sake kalla masa ita bare yaji zazzakar muryarta dake ziyartar mafarkansa.
Murmushi yayi yace "Ba ki san yadda ki ke driving dina wild ba ko? Ina ga har yanzu da sauran ki a daukar darasin soyayyar da na ke miki, shi ya sa."
Kara ta saka tana zillewa "Na dauka na fahimta, ba sai ka gwada ba, na tuba." Ta fada yayin da ya janyota jikinsa.
"Tsaya tukun, ina da tambaya guda." Ta tsagaita dariyar da take yi. "Shin da gaske ka ke yi, za ka iya raba ni da Muhammad da ban aure ka ba?"
Fuskarsa ya yalwanta da murmushi ya-ce. "Jidda, koda zan rasa ki har abada ba zan taba ganin ki cikin-bakin ciki ba, don haka ba zan iya raba ki da Muhammad ba, na dai fada ne saboda kin san (You can't blame a man for trying)."
Mai-jidda ta sauke ajiyar zuciya, wato dama duk barazana yake mata. Hmm sai a gaishe shi.
Wani dogon ajiyar zuci Abdul-Ali ya sauke, cikin godewa Allah da garin bashi labari Jidda ta furta sunan da Dan kano yake kiranta dashi. That was close!
********
Bayan wata uku suka nufi asibiti saboda Mai-jidda haihuwa ta taso gadan-gadan. Abdul-Aali banda sintiri, ba abinda yake yi, ya kasa zaune bare tsaye.
Sai ya ji ashe abinda ya ji a haihuwar Muhammad, sunna ne, saboda ya kasa zama ma ya ga halin da Jiddansa take ciki. Can kuwa Yaya Maryam ta zo ta shaida masa Mai-jidda ta samu baby girl.
Bai yi wata-wata ba, ana miko baby. Ya sa hannu ya karbeta, yayi mata addu'o'i, ba karamin dadi ya ji ba, da ya ga kamannin Jidda da baby din.
Dokin wannan haihuwar yake yi, tamkar lokacin aka fara masa haihuwa, ba abinda ya rage su da shi, komai a wadace. Hamamatu dai mamaki take yi.
Ganin irin bare-baren da Abdul-Aali ke ta yi, sai ka ce baida wasu 'ya'yan. Su Mimie dai kaura suka yi side din Mai-jidda, saboda kallon baby.
Ran suna yarinya, ta ci suna Zainab, wato mai sunan Mama. Mabruka musamman ta zo suna, farin-ciki dai ba a cewa komai. Anty Fauziyya dai ba ta samu zuwa ba, kasancewar ita ma ta yi nauyi.
Hankulansu kwance Mai-jidda ta ki komawa PH, da haka, sai dai su su zo, hakan yayi wa Hamamatu daidai, saboda duk kyautatawar da take yi wa Abdul-Aalin idan yana gaban Mai-jidda, sai ya rinka wani bare-bare, na ban haushi, ita kuma ba ta jure ganin haka, amma suna nesa da juna, hakan ya fi mata sauki.
******
Soooo how do you like this chapter.😜
It's out Abdul-Aali is officially not Dan Kano, that leaves the question; Who is Dan Kano?🤔
Next update will be the end of this journey, and the big revelation too. You don't wanna miss that.
Thank you.
vote, comment a ton and share pleaseee.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top