BA'KO

Hakan ya sa ranar ya ba su (Assignment), ya kuma raba su gida-gida, kowane (Group) za su yi (Presenting) na su. Don haka da (Group) din su Mai-jidda suka zo yi.

Ya duba ya ga su biyu ne mata a (Group) din, don haka ya nuna ta ya-ce ita za ta yi (Presenting) nasu aikin. Abin ya bawa Mai-jidda mamaki, ganin ita ba ta wani yin shisshigi a ajin. Yaya aka yi ma ya san sunan ta?

Da yake ta saba da duka 'yan ajin, ba ta ji wani dardar! Ba, ta hau bayanin nasu aikin cikin murya mai taushi da gamsarwa a cikin turanci wadatacciya.

Tabbas! Ta burge kowa, yadda ta bada gamsasshen bayani, amma ba wanda ta fi burgewa irin Malamin na su, don haka sun samu maki cikkake.

Dr. Rayyan Sani, ya samu kansa a yanayin da bai taba samun kansa ba na damuwa da al'amarin dalibarsa guda, muddin ya koyar yaga ba ta yi tambaya ba, sai ya ji ko dai ba ta fahimci darasin bane, amma a hankali ya nemi share fagen Hauwa Kabir daga zuciyarsa da tunaninsa, saboda a ka'idar sa, babu hada sha'anin koyarwa da wani AL'AMARI na ZUCCI.

Bayan sun fito daga wani gwaji ne. Mai-jidda ta wuce wurin cin abinci da kawarta Mabruka, suna tafe suna hira kan gwajin da suka gama yi yanzu.

Suna shiga, suka fadi abin da suke so, wurin bai cika da jama'a sosai ba, sai dai teburin gefensu akwai mutum daya da yake zaune, ya ba su baya. Ba su ma kula da shi ba, sun fara cin abinci ne. Mabruka ta-ce.

"Don Allah ki bawa Hafiz lokacin ki, ni fa kun sani a tsakiya, wannan ya gwarani ta can, wancan ya matsa min tanan. Yanzu kam dai koma menene, ai kin san ba za ki yi wasa da karatunki ba, shi fa da gaske yake yi".

Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. "Ni fa ki na ba ni dariya, ban san sau nawa zan fada miki ba, ba Hafiz ba, ko ma waye ne, ba ni da lokacinsa yanzu, saboda ina da kayadajjen lokaci. So, idan zai iya jira, ya jira".

"Ni kam Allah ya sa Baba ya-ce ki fidda miji, muna komawa gida, na ga ta wannan ka'idar ta ki. Gaskiyar Umma ce da ta-ce ko sai an hada da rukiyya ne. Ki ga yadda Hafiz ya hadu, ga kudi ga kyau, 'yan mata Rushing suke a kansa, amma ya dage sai ke, ke kuma baya ma gaban ki sam".

"Hmm Mabruka, na ba ki shi kyauta".

Saura kadan ya yi dariya da ya ji ta fadi haka, ya kurbi abin shan shi ba tare da ya tanka ba.

Mabruka ta-ce. "Ai ke ma don kin san ke ya-ce yake so, idan ba haka ba, ba wani bata lokaci. Ke akwai ma wanda yake burge ki kuwa ma a duniya. Kin ga Dr. kowa na rubibin sa, wasu har ba su rasa Lakcan sa don kawai su ganshi, ke kuwa ko a jikin ki, ban taba ji ko hirar sa ma ki na yi ba".

"Akan me ya sa zan yi hirarsa, tsakani na da shi koyarwa, ya koyar da ni, na dau darasi, shi kenan. Kun tsaya ku na batawa kanku lokaci, ni ban ga meye abin rawar jiki ba anan. Yes, yana da kyau, yana da ilimi, and so what?"

Murmushi ya yi da ya ji wannan gaba ta hirar ta su. Mai-jidda ta ci-gaba da cewa. "Hala ma yana da matar da yake matukar so, take son shi, kun tsaya ku na kalle mata miji, ku na kus-kus! A kansa. Idan zai dauka a cikin duk masu son sa, wa zai dauka, wa zai bari? So bata lokacinku ku ke yi..."

Mabruka ta yi saurin taba Mai-jidda, amma sai da ta ci-gaba. "Sannan ki na ganin yadda yake wani shan kamshi, yana magana da kyar, kamar a turai aka haife shi, ni ban ga abin burgewan..."

Ganin sa ta yi a gabanta kawai ya zura hannaye cikin aljifayen wandon sa, kafafun sa sake da Loafers masu laushi.

Ta hadiye wani abu makut a wuyanta, hankalinta ya tashi, nan take kwakwalwarta ta faro tariyo abin da ta fada akan sa, ta ji ko ta kwafsa, amma ina kwakwalwarta ta daina tunani. Murmushi ya yi, maimakon ya hau ta da fada, ya ja kujerar gefenta, ya zauna.

"Hauwa'u right?"

"Malam, ka yi hakuri, ban yi niyyar... I'am so sorry!" Ta mike ta dau jakarta za ta bar tebur din, amma kallo ya bi-ta da shi ya-ce, "Zauna, mu yi magana".

Yau ta shiga uku, shi kenan zai sa a koreta a makarantar, tunda da kunnensa ya ji tana kushe shi. A sanyaye ta zauna. "Ina saurarenki?"

"Malam..."

"Ga ki, gani. Just tell me, fada min duka aibuna, kin san Dan-Adam ajizi ne, amma ina son mutum mai fadin gaskiya komai rintsi, so, fada min menene abinda ba kya so a tare da ni?" Mai-jidda ta dubi Mabruka, ta saukar da kanta kasa, sannan ta-ce.

"Ni ba abinda ya shafe ni da rayuwarka, duk abin da ka ke so, za ka iya yi rayuwarka ce, don haka, kayi min afuwa, idan na bata maka rai da wani furuci na".

Ta mike ta bar tebur din. Mabruka ta bi bayanta da sauri. "Yau mun shiga uku, kin ga abin da ki ka jawo mana ko? Me ya kai ki cewa baya burgeki, ya faye jiji da kai? Yanzu yaya za mu yi? Ga shi ya san sunan ki."

"Ba abin da zai yi, ki rabu da shi."

Mabruka tayi mata kallon ba ta ma san me take yi ba.

Suna fita, ya bi-ta da kallo. He liked the girl, tana matukar burge shi. Ranar dai duk yadda ya so ya hana zuciyarsa, tare da tunanin Hauwa Kabir ya kwana a ransa.

Daga ranar Mai-jidda ta kara shiga taitayinta, ba ta yarda ta yi maganar wani Malami a ko ina, sannan idan Dr. Rayyan ya shigo aji, ta daina ko dago kanta ne, saboda sai ya yi ta mata wani kallo na tuhuma, tamkar tayi masa wani gagarumin laifi.

********

Yau kam ya rigata fitowa, a wurinsa na kullum ya tsaya, har ya ga fitowarta, yau kamar da damuwa a fuskarta, ko don saboda ta yi latti ko kuwa saboda jarrabawar da suka fara, ji ya yi tamkar ya je ya cire mata damuwar ya dawo mata da murmushinta na kullum.

Nan ya ji wani abu ya kulle a zuciyarsa. Ji yake yi tamkar ya fasa tafiyar nan, amma kuma ya zama dole, tunda zai yi (Reporting) a sabon wurin aikinsa, ya so kwarai yayi mata magana game da abin da yake ji game da ita, amma ba ya so yayi mata katsalandan a karatunta.

Don haka yau ma ba tare da ya-ce komai ba, yana gani ta shiga abin hawa ta tafi, ba tare da ya san sunanta ba, haka ba tare da ya san gidan su ba.

Tana kallon mai motar nan ya tayar ya tafi, ta yi ajiyar zuciya, don wannan karo na hudu kenan da ta kula da shi, da farko ta zaci kawai hanya ce ke hada su, amma sai ta kula kullum sai ta hango shi a zaune a motar.

Da zarar ta shiga abin hawa sai ta ga ya tafi. Amma tunda bai taba mata magana ba, ba ta damu ba, sannan ko fuskar shi ba ta taba gani ba, ita dai ta san anan kullum take samun motar sa.

Wataran kuma sai ta fito yake fitowa. Wataran ta kan ji kamar ta same shi ta tambaye shi me ya sa yake bin ta? Amma kuma ta ga rashin dacewar hakan, idan ya zamanto wani abu ne daban, ba ita yake bi ba.

Suna duba wani darasi ne. Auwal ya-ce. "Mai-jidda ni ban tambayeki ba, ko kin samu waya?."

Ta dube shi a cikin rashin fahimta "Waya kuma Auwal?"

"Eh, ranar wani mutumi ya zo nan nemanki, ya samu za mu shiga aji, ke ya nuna. Ni kuma ganin sa a tsanake, ya sa na fada masa sunanki, na kuma ba shi lambar wayarki ma".

"Mabruka, idan nace miki me ya sa ki ke kula su Auwal, sai ki ce yana da hankali da son karatu, yanzu idan banda kai Auwal. Yaya za ka bawa kowa lambar wayata, bayan ya nuna maka ban san shi ba, asali ma kai ka fada masa sunana?"

"To yanzu dai ki kwantar da hankalinki, tunda bai kiraki ba."

"Gaskiya kar ka sake min haka Auwal, ba na so."

Mabruka tana kunshe da dariya, suka yi ido da Auwal. Sannan suka shiga aji.

***********

Suna zaune a gindin bishiya, tana bitar takardarta na jarrabawar da za su shiga zanawa, wanda kuma shi ne na karshe a wannan zango, daga shi sai kuma aji biyu, sai ga Auwal ya nufi inda suke zaune, ita da Mabruka da wasu (Course mates) din su. Ita ya nufa ya-ce.

"Hauwa idan kin fito wannan jarrabawar. Dr. Rayyan na nemanki a ofis dinsa". Sai da ta ji wani ras! Yau ita kuma me ya hada ta da shi, da zai aika ta je? To ko dai ta yi wani shirme ne a jarrabawarta? Kai me ya sa zai fada mata, idan ma ta yi shirmen?

Ita kadai dai sakawa take yi tana kwancewa, da kyar ta natsu, ta zana wannan jarrabawar. Mabruka ta roka suka je tare. Hannunta na rawa, ta bude ofis din ta shiga. Kansa na kasa yana nazarin wani abu, ta shigo ta gaishe shi, ya nuna masu wurin zama ya-ce, su zauna.

"Yaya jarrabawar dai?" Ya tambaya yana duban Mai-jidda.

"Alhamdulillahi! Mun gama yau."

"To ya yi kyau, tunda kun gama yau, ba shigowa makaranta kenan?"

Mai-jidda ta fara jin haushin tambayoyinsa, me zai kawo su to tunda ba a komai.

"Sai dai idan ka na so ka ci-gaba da Lectures, za mu iya shigowa."

Ya yi murmushi ya-ce. "Wata alfarma na ke nema, tunda ba kya makaranta da fatan za a ba ni?"

Mabruka ta dubeta hade da zare idanu, ta dan taba kawarta, alamar ta amince su ji meye ne. "Allah ya sa zan iya."

"Lambar wayarki na ke so, sannan kuma da sunan unguwarku, ina da magana da mahaifinki".

Da sauri ta dago idanu tana dubansa cikin tsoro ta-ce. Shi kenan ta fadi jarrabawarta. To amma fa ta dage. Yaya aka yi haka? "Malam ai ba a garin nan yake ba."

"A ina yake?"

"Yana Dutse, amma don Allah duk abin da ka ke da niyyar fada masa, ka yi hakuri kar ka fada. Idan ni ce da kuskure, zan gyara, kar ka bari ya sani". Ta fada a sanyaye.

"Kar ki damu, rubuta min address din anan da kuma lambar, idan har kin amince, ba laifinki zan fada masa ba." Da sauri ta rubuta masa, tun kan ya canza ra'ayinsa, ya fadi aibunta gun Baba.

"Shi kenan?"

"Idan ban gane ba, zan kiraki a waya ki fada min."

Kai kawai ta daga masa ta-ce. "Sai anjima."

Ta tashi suka fita, suna fita. Mabruka ta maketa a kafada, tana wani murna kamar an mata albishir da kujerar Hajji. "Me ye haka? Ke dadi ma ki ke ji wannan mutumin zai kai karana gida, ki na wani murna ko? baki san yanda zan kare ba a hannun Baba."

"Oh, Allah! Wataran kamar na ba ki aron kwakwalwata na ke ji, ke yanzu ba ki gane komai ba?"

"Me kuma zan gane, bayan ke muguwa ce, ki na farin ciki da damuwata". Mabruka ta-ce. "Kawata Dr. Rayyan ba karar ki zai kai ba, zai je gidan ku ne, saboda ke, saboda yana son ki".

Anan Mai-jidda ta tsaya cak! Sai kuma ta yi wani tunanin, ta-ce. "Kawai don mutum ya karbi lambar waya, ba shi bane yake nufin yana so-na, kuma ni na fada miki ba zan kula kowa ba, sai nan da shekara biyu Insha-Allahu".

Murmushi Mabruka ta yi cikin jin dadi ta-ce. "Mai-jidda and Dakta, wai I can't wait. Tsaya ma tukun, wai me ya sa duk hadaddun mazan nan ke kadai suke so, zan raba gari dake, ko ni ma wani zai ganni ya taya".

Mai-jidda ta san halin Mabruka kwarai da zolaya ta-ce. "Kya ji da shi ai, idan dai maza ne."

Ba ta sake tunanin Dr Rayyan ba, ta wuce gidan Yaya Maryam, ranar murna ba ya ita, ta ji wani sayau a ranta, kasancewar ta gama jarabawarta.

Damuwarta daya a wannan safiyar, da ma wanda ta shude, ba ta ga motar nan da take yawan gani ba, idan ta zo tafiya makaranta. Don haka ta yi fatan komai lafiya.

Bayan kwana biyu ta wuce Dutse, tana Allah-Allah ta ga Ummanta, don wannan (Semester) din sau uku kawai ta zo gida. Ba ta wani tsaya hutawa ba, ta bazama gaisuwar 'yan-uwa, ta dawo gida.

*********

Wata ranar Juma'a da yamma ne ta same shi a kofar gidan su. Tsayawa ta yi cak! Kamar ta ruga da gudu ta koma inda ta fito, to amma me zai sa ta gudu?

Tunda wajen Baba ya zo, iyaka ta gaishe shi, ta wuce cikin gida, ya yi abin da ya kawo shi, ya tafi shi kuma. A tsanake cikin kula ta karasa inda yake.

"Sannu da zuwa." Ta fada a sanyaye, don zuciyarta na ta mata tsalle. "Yaya aka yi ka gane, ba ka kira wayata ba?"

"Ba wuyar ganewa. Yaya hutu?"

"Lafiya kalau, ka shigo ciki mana, ko ba ka yi sallama bane?"

"Ban samu kowa bane, shi ya sa." Hala ya dade a tsaye anan, sai ta ji wani iri gaba daya. Ta shigar da shi falon Baba, ta wuce cikin gida ta samo masa abinci da ruwa mai sanyi, kafin ta aika yaro ya sayo mata drinks a shagon kofar gidan su.

Ta kawo masa komai, sannan ta yiwa Umma magana ta-ce. "Umma Malamin makarantar mu ne ya zo ganin Baba, kuma bai dawo ba tukun, ko za ku gaisa?"

"To, ayya ina ga bai san yana tafe ba ko? Amma kuwa ya kusa dawowa, ya dai jira shi".

Mai-jidda ta koma falon ta same shi. "Ka yi hakuri fa, Baban ya kusa dawowa yanzu, sai ka same shi."

Ta dan yi shiru tana tunanin abin da ke ranta kafin ta-ce. "Amma dai ka tuna maganar da muka yi da kai a makaranta ko?"

"Hauwa kenan, na tuna, ki kwantar da hanakalinki, wani abu daban zan tattauna da Baba, ina fatan ba za ki damu ba?"

Ta yi wani ajiyar zuciya, sannan ta-ce. "Ba komai, bari na gwada wayarsa na ji."

Tana kokarin danna wayar ne, sai ga sallamar Baba a falon. Tayi masa sannu da zuwa, sannan ta kawo masa ruwa, ta samu suna gaisawa da Dr. Rayyan.

Bayan sun gama ta-ce. "Baba wannan Dr. Rayyan ne. Malamin mu a makaranta, ya-ce ya zo wurin ka ne, yanzu ma da zan kira ka a waya."

"Ayya, sannu da zuwa. Yaya hidima da fama da Dalibai?"

"Alhamdulillahi! Yallabai, sai godiya".

Mai-jidda ta mike ta koma cikin gida, kamar ta labe ta ji me Dokta zai hada shi da Babanta. Amma ta yi tunanin rashin dacewar hakan, don haka ta yi wucewarta daki.

Can Abdulmajid ya kirata, wai ta je falo bakon zai tafi, ta samu Baba ya fita a falon, don haka ta-ce. "Har kun gama maganar?"

Murmushi ya yi ya-ce. "Eh, kuma Alhamdulillahi na samu abin da ya kawoni".

Ta dube shi a tsarge cikin rashin fahimta. "Baba ya yi min izinin na nemi aurenki, da fatan zan samu kofa a wajenki?"

Mai-jidda sai da ta ji kamar an naushi cikinta, yayin da take koshe dam! Saura kiris! Ta saki fitsari don razana.

"Malam, aure kuma... Ni?" Ta rasa me daya take ji, bacin rai ne ko razana ko kuma haushi?

"Kwarai kuwa, akwai wata matsala ce?"

Matsala yake tambayarta? Kwarai kuwa akwai babbar matsala.

"Kawai dai na ga, kai Malamina ne, kuma ina karatu, yanzu kuma ..."

"Wannan ba hujja bace, na gan ki, kuma na yaba da halin ki, da na tambayi Baba izinin neman aurenki kuma bai sanar da ni cewa ba yanzu zai miki aure ba, saboda haka idan ki na da wata hujja, ina saurare?"

Ranta bai mata dadi ba, akan me zai zo kai tsaye wurin Baba? Wato daureta yaso yayi don kar ta masa gardama.

"Tunanin me kikeyi? A tunani na haka addini ya koyar mana ko kuma kin fi so na fara zuwa ta gunki tukun?"

Taji mamakin yanda ya karato damuwarta amma yafi ta gaskiya don haka murmushi Mai-jidda ta yi ta rufe idanu, cikin jin kunya, daganan Dr. Rayyan Sani ya san shi zai yi nasarar saye zuciyar Mai-jidda. Sun yi sallama da cewar sai ta ji daga gare shi.

*******

A daidai wannan lokacin ta fara samun wayar. Mai-jidda ta manta fedes da batun Auwal, tana gidan Yaya Hamza aka bugo, bakuwar lamba ta gani. Ba ta cika son daukar lambar da ba ta da ita ba, amma gudun kar abin kila yana da muhimmanci yasa ta daga. "Hello."

"Assalamu-alaikum".

"Wa'alaikumus-Salam." Rashin dago muryar ya sa ta-ce. "Wa ke magana don Allah?"

shiru

"Da Hauwa na ke magana?"

"Eh ita-ce. Sai dai kai ban gane waye bane?"

shiru

"Wani bawan Allah ne, na samu lambarki a cikin makaranta wurin abokan karatunki, da fatan ba za ki damu ba?"

Nan da nan Maijidda ta zabura ta zauna, wato wannan ne mutumin ko? Nan da nan taji fushi ya taso mata. "Gaskiya ban ji dadin yadda ka bi abokan karatuna, ka amshi lamba ta ba."

Shiru taji kamar mai shi bazai amsata ba. Kafin taji muryarsa "Ayi mun afuwa, amma na ga ya dace mu yi magana ne, ni kuma ba na son samunki a bakin titi, wannan ya sa na karbi lambarki, don ki ban address, sai na zo gida mu tattauna".

"Ni ba a zuwa gidan mu."

Murmushi ya yi mai sauti ya-ce. "Saboda me ba a zuwa gidanku?"

"Don Allah, ka yi hakuri, ba na son mu batawa kanmu lokaci, domin akwai wanda na ke gani yanzu."

Ransa yayi masa nauyi da jin batun ta, amma ya-ce. "It's not fair, ko dama fa ba ki ba ni ba, za ki sallameni".

"Tukun ma a ina ka sanni? Yaya zan ba ka dama, bayan ban san ko kai waye ba?"

Murmushi ya sake yi "Yaya za ki san ni waye, bayan ba ki ba ni dama ba?"

Maijidda ta juya idanunta wannan ya faye bakin naci. "To shi kenan, na ji. Ni ba a Kano na ke da zama ba".

"A ina ki ke, ni zan zo duk inda ki ke a fadin duniyar nan."

Ya ba ta dariya, wannan mutumin wani majnuni ne kawai. "Sai anjima". Ta fada hade da kashe wayarta.

Anty Fauziyya ta-ce "Mai-jidda ke da waye haka?"

Tana datse wayarne tace "Ke dai rabu da shi, wani ne kawai ya bi-ni makaranta ya amshi wayata a hannun abokan karatuna, tun lokacin bai kira ba, sai yanzu kawai wai shi a dole yana so ya zo na san shi, zan ba shi dama."

Anty Fauziyya ta yi dariya. "To ki ba shi damar mana?"

"A'a ni da na fara kula Dakta, kuma wane dama zan ba shi, ni ba na son tara samari Wallahi".

"To sai ki fada masa ya hakura ai ko". Daukan kaskon turaren wuta tayi da zimman kunnawa.

"Na fada masa ina tare da wani. Ki rabu da shi kawai".

Nan suka shiga wata hirar, ta manta fedes da batun mai waya.

*********

A wannan hutun sau uku Dr. Rayyan yana zuwa, kafin a koma makaranta kuwa Mai-jidda ta yi nisa, ba ta da zance sai na Dokta, har dai Yaya Maryam ta-ce "Barka kanwata da lafiyarki, dama Dakta kawai ki ke jira."

"Yaya Maryam, ni dai ina sauraron sa ne zuwa mu ga abin da hali zai yi."

"Ahaf, tunda ki ka sa kai, ai shi kenan, anyi an gama, in-ji mai kashi a gado."

Ba wanda ta fadawa a cikin kawayenta yadda suka yi da Dakta. Sai Mabruka, nan ma ta isheta da bin diddigin abin da ya faru da ya je ganin Baba ne.

Idan ya shiga aji kamar bai santa ba, haka zai koyar ya fita, ita ma idan ta tashi kamar ba ta san shi ba, ba ta zuwa ko ofis dinsa, sai dai ana komawa gida, za ka same su makale da juna.

*******

Tana dakin Umma aka sake mata waya. "Hauwa kenan, kuma shi kenan sai ki ka manta da ni, bayan ina jira ki waiwaiyeni."

Ta gane muryar sarai, don ba irin muryar da za ka manta bane, murmushi ta yi ta-ce "Hmm! Na dauka mun gama wannan maganar da kai ai?"

"To, yaya mutanen gida?"

"Lafiya kalau."

"Ni fa da gaske na ke miki, son ki na ke yi, kuma ina matukar bukatar ganinki, domin mu yi magana ta gaske, ke kuma ko gidanku, kin ki ki min kwatance."

"Don Allah bawan Allah ka yi min afuwa, amma a ina ka sanni?"

"Kullum da safe, idan za ki wuce makaranta, na kan gan ki a bakin titi za ki hau abin hawa, tun daga lokacin na ji zuciyata tayi min na'am da ke, wannan ya sa na kasa hakuri har sai da na biki cikin School ranar".

Gaban Mai-jidda ya fadi, yau ta hadu da gamonta, wato shi ne dai mutumin nan, mai mota da take gani. Ita yake bi wato?

"Bi-na ka ke yi?"

"Raina ya gan ki, kuma KE NA KE SO, ba zan iya hakura ba, hakan ya sa na dau wannan matakin, ki yi wa zuciyata adalci, ta samu ganinki, ko za ta huta da dawainiyar da ki ke yi da ita".

Wannan mutumin ya yi kwas, ko sunansa ba ta sani ba, amma ya fara sawa tana ji tamkar ta san shi.

"Ka yi hakuri Malam, abu ne da ba zai yiwu ba."

"Ni ban taba ganin mai saurin karaya ba irin ki."

"Ni ce na karaya? Ni ban karaya ba, kawai dai tsoro ka ke ba ni." Ta fada masa abin da ke cikin ranta.

Murmushi ya yi ya-ce. "Ki daina tsorona, ni Dan cikin Kano ne, ko yau ki ke so, ki aika ayi miki bincike a kaina." Maganar babba ce kenan. Mai-jidda ta fada a ranta.

"Sai anjima". Ta fada hade da kashe wayar.

Amma wannan bai sa Dan Kano ya bar kiranta ba, a haka har ta fahimci cewa bai da mata sannan, ta fahimci shi mutum ne da ya lakanci asalin soyayya. Don idan yana mata magana hatta tsigar jikinta tashi yake yi, hakan ya sa ta san cewa shi ba abokin yinta bane.

Saboda a bangare guda, ta san Dakta tana son shi, yana da addini, ta yarda da aqidarsa, sannan kuma ta san komai game da shi. Don dai Dan Kano, ba abin da ta sani game da shi, sai garin da ya fito da kuma cewa baida mata, sai kuma iya soyayyarsa, don dai ko sunan sa ya ki ya fada mata, wai sai ta yarda ya zo Dutse. Ita kuma ta-ce babu wannan ranar.

******

So, what do you think?😉

Are you getting Maijidda's character yet?

Zamu samu RayHa ne ko kuwa?

Mu hadu a babi na gaba.

To ga kuma Dan kano mutum ko aljan?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top