AN YANKA TA TASHI...
Watanni biyu kenan rabon da ta sa Abdul-Aali a ido, sai dai jefi-jefi su kan yi waya, nan ma idan ya kira baya mata magana irin ta da.
Iyaka ya tambayi lafiyarsu ita da Danta, sai kuma aike da yake bayarwa ta hannun Mukhtar a ba su. Har kasan ranta hakan yana damunta.
Shin ko wani boyayyen shiri ne yake da shi, wanda ya sa shi yin hakan? don ita al'amarin Abdul-Aali na ba ta tsoro.
Wannan zuwan Mukhtar da ya yi, ta zaci kamar na kullum ne, sai yake ce mata "Anty Hauwa fa kati na taho miki da shi, aiki ya sameki, sai ki rabawa jama'armu na nan".
"Haba, Mukhtaar har abin ya tabbata kenan? Masha-Allah! Allah ya nuna mana lafiya, ya sanya alkhairi."
"Ameen-Ameen, na ga alamar dai zan riga ki, tunda har yau Alhaji Yusuf bai ce komai ba".
"Kai ni rabu da sha'aninsa, ni auren ma ba shi bane a gaba na yanzu, nan wani wai shi Jamil ya zo ya karaci shirmensa, ina jinsa. It will never be the same".
"Yaya za ayi to Anty Hauwa, haka rayuwar take sai hakuri. Amma fa akwai solution, sai dai idan ke ce ba ki so".
"Solution? Ni din wata matsala ce da za a solva ni?"
Ya yi dariya ya-ce. "Kusan haka, don ni dai ko da Dakta yake kwance, ce min ya yi baya son bacin ranki kuma ba zan bari, ina ji, ina gani ba, ki na cikin bacin rai, alhali akwai yadda za ayi na kawar da shi."
"Wanda shi ne mene fa?"
"Yaya Abdul-Aali!"
Mai-jidda ta hada rai, No wonder, ita dai ta san dole sai yana da wani Plan, idan ba haka ba ai shirun ya yi yawa, yanzu kuma kanin sa ya turo ya yi mata ta karkashin kasa kenan.
"Ban san muna haka da kai ba Mukhtaar. Na dauka kai kam ko kowa ba zai bi bayana ba, kai me taya Dakta kishina ne, amma kuma har da kai?"
"Ko kadan ba haka bane, kasancewata tare da ke din ne, ya sa na ga dacewar hakan, domin Yaya Abdul-Aali ne mutum na farko da ya zo min a rai, idan na duba na ga wanda zai sa ki farin-ciki."
"Wa ya fada maka hakan?"
"Ni dai kawai na sani, ko kuma ki na so na tona ne?"
Murmushi ta yi, "Ba sai ka na da abin tonawan ba."
Mukhtaar ya yi dariya, sannan ya-ce. "Tsakanin ki da Allah, duk randa na zo garin nan, ba ki jin kamar ki tambayeni me ya sa ba ki ganin Yaya Abdul kwana da yawa?"
Shiru ta yi, domin tamkar ya bude zuciyarta ya gani. Amma kuma ba za ta taba amincewa ba.
"Kai dai sannu da kokarin dikake."
"Tunda sun yi haka, ni dai na yi shiru, sai kin shigo dai, idan kuma ki na son ki san dalili, to kar ki damu zan fada miki, duk lokacin da ki ka shirya".
Haka suka yi sallama da Mukhtaar, ya tafi ya bar ta da tunani tirim! A zuciya, na rashin samun mafita.
Satin da ya kama ne, suka yi waya da Mabruka, sun zo Kano, don haka idan ta dan huta, za ta iso mata Dutse. Murna dai ba a cewa komai a wurin Mai-jidda, kusan shekara guda kenan rabonta da aminiyarta.
A kwance take, ta ji wayarta na kara. A tunaninta Mabruka ce, don haka tana dagawa ta-ce. "Har kun iso?"
Muryar da ta ji ne ya sa ta yi saurin tsuke bakinta. "Ke ma Assalamu-Alaikum!
Kunya ne ya kamata. "Haka ake amsa, waya ne?"
"Ban san kai bane, na dauka kawata ce Mabruka".
"Wato kowa cikin doki ake, daga wayarsa tawa ce, sai anyi min yanga ko? Ba ki ga Message dina bane jiya?"
Nan take ta tsume. "Oh Message dinka? Ban gama fahimtarsa bane, shi ya sa ba ka ga amsa ba".
Ya san sarai tana da niyyar wasa da hankalinsa ne, don haka ya-ce. "Shi kenan, idan ki ka dauki lokaci mai tsawo wurin fahimta kuwa, sai dai ki gani, a aikace".
Mai-jidda ta gyara zamanta ta-ce. "Ba za ka iya ba."
"Try me!" Kafin ta-ce wani abu, ya kashe wayar, tana cikin tsuma, ta ji wayar na sake kara, tana dagawa ta-ce. "Idan kayi min haka, za ka yi da na sani..."
"Woah, me ya yi zafi haka, da wa ki ke magana Mabruka ce fa, mun iso, ina ga fa sai kin turo Abdul-Majid mun bata hanya".
"Oh sorry, to bari ya zo yanzu, kuna daidai ina ne?"
Nan da nan ta sa aka je aka iso da su, a falon Baba ta saukesu, kasancewar tare da Hafiz suka zo, sai da ta tarbesu suka gaisa tukun. Hafiz ya-ce. "Mai-jidda, mun ta jira mu ji an kira mu biki, amma shiru, hakan ya sa muka taho da kanmu".
"Kai Baban Farida, kai ma har da kai, ka daina bari Mabruka tana fada maka tatsuniya."
Hafiz ya yi dariya sannan ya-ce. "Tatsuniya ko? Mun dai san Koki ta Gizo ne, saboda haka idan ta yi tsami, za mu ji ai."
"Zama da madaukin kanwa....". Mai-jidda ta fada tana dariya.
"To ni dai na bar ku, zan duba wani aboki na a cikin gari, kafin nan kun gama gulmarku".
"To mun ko gode. Ke tashi mu shiga ciki." Ta daga Farida a hannunta tana mata wasa, suka dawo ciki, nan suka sake gaisawa da Umma, kafin su koma daki. "Yau kuma Alhaji Yusuf din ne ake ta yiwa diri haka?"
"Hmm! Ai da Alhaji Yusuf ne da sauki, na san ranar karewarsa ni da Abdul-Aali ne".
Mabruka ta zaro idanu tana kallonta. "Abdul-Aali, kanin marigayi?"
"Shi fa".
"Me ya faru da muguntarsa da tsanarsa har ya hadaku ku ke waya?"
Mai-jidda ta dauki tumbler ta zubawa Mabruka lemo, sannan tace "Wai wani dogon labari kenan". Mai-jidda ta-ce. "Ai abin ba a cewa komai sai du'a'i, tun ina tunanin wasa yake yi, na fara tunanin zai ji kunya, ya janye, yanzu kam abin ya zamo na karfi da yaji ne".
Mabruka dai ta kasa rufe baki. "Yau kin shiga uku, kin ga abinda ki ke yiwa maza ko ga shi kin je kin janyo wa kanki Engr Abdul-Aali Sani".
"Allah ya shiryeki Wallahi, ba ki san yadda na ke Allah-Allah ki iso ba, mu yi shawara". Nan Mabruka ta gyara zama kan gadon Mai-jidda da kyau hade da tankwashe kafafunta.
"Ina aka tsaya da batun Alhaji Yusuf kuma?"
"Yana shawara." Mai-jidda ta fada hade da juya idanunta. "Na tsani komai ma ni yanzu, ba abinda yake min dadi".
"Ba abinda zai miki dadi, saboda ba ki samu abin da ki ke so ba". Ta fada hade da kurban lemon da Mai-jidda ta zuba mata.
"Ni ba abinda na ke so, baya ga kowa ya barni na huta."
Mabruka ta yi dariya ta-ce. "Allah ya bude miki idanu, yanzu me ku ke ciki da Engr Abdul-Aalin?"
Mai-jidda ba ta da amsa, illa mika mata wayarta da ta yi ta bude mata Message din da ya turo mata jiya.
Zare idanu ta yi, bayan ta gama karantawa. "Kin san idan ya yi haka, ba ki da mafita? Yaya za ki kalli Abba da Mama, bayan kin ki amincewa?"
"Taimake ni dai, nace maku Abdul-Aali mugu ne, duk duniya ba na biyunsa."
Mabruka ta yi dariya sosai, sannan ta-ce. "Dole dai mu san mafita, tsaya ma tukuna, ya fadawa matarsa zai yi aure?"
"Eh, haka dai ya fada min kwanaki da nace zan mata waya".
"Amma ki na tunanin anya ta san ke yake so?" Mai-jidda ta yi shiru, tana tantamar hakan, don yadda ta san Hamamatu kamar yunwan cikinta, da tana da labari da ta dira a Dutse.
"Ba ta sani ba. Me ki ke nufi?"
"Lokaci ya yi da za ta san cewa Abdul-Aali ke yake so..."
"Ke fa ba ki da kyau, za ki je ki sa ta daga hankalinta a banza, bayan ni ba auren sa zan yi ba."
"Oh, ke yana nan ya kidima miki rayuwa, ke kuma sai ki zauna banda kuka da tausayin kanki, ba abinda ki ke yi ko? Shi ma ai yana da duniyarsa, saboda haka sai ki dan wargaza masa, zai sarara miki."
"Ni gaskiya ki sake shawara, wannan bai min ba, duk abin da zai sa na bata da Mamin Mimie, ba na son sa, hakan ya sa tuntuni ban sanar da ita ba, saboda kowa ya san yadda take son mijinta."
"Allah Sarki, mijinta kuwa ga shi ya bige da haukar son matar Dan-uwansa. Kai wannan gida naku akwai kallo, don Allah ki amince ya aure ki mana."
"Da ma ba ki zo ba. Farida ta fi-ki amfani." Ta fada tana bankawa Mabruka harara.
"Maganar gaskiya, ke me ya sa ba ki son maganar auren Engr. Abdul-Aali?"
Murmushi ta yi ta-ce. "Ke ma kin fi-ni sani, har sai nayi miki bayani?" Idanunta suka kawo kwalla, ta yi saurin hadiye su.
"Yau ina ganin ikon Allah, na san ba ni na fara fada miki wannan maganar ba, amma kin yi wa kanki adalci kenan?"
"Ban san me na yiwa kaina ba, abin da na sani shi ne zuciyata ba tawa bace da zan bada ita ga wani."
"Yaushe ne auren Mukhtaar din?"
"Sati na sama. Insha-Allahu, za ki je ne?"
"Idan kin gayyace ni ba. Ko ba komai zan duba Mama, ya kwana biyu ban ganta ba, dattijuwar kirki, ai ko albarkacinta ma ya ci ki saurari Engr."
"Na ji, shi kenan." Har sai yamma Hafiz ya dawo ya dauke su. Mai-jidda ta cika Farida da kyaututtuka iri-iri. Kwana ta yi tana tunanin abin yi.
***********
Ta tashi a aiki ne suka fito da Walida, suna sallama, inda kowacce za ta wuce gida, sai ga motar Alhaji Yusuf. Walida ta-ce.
"Mai-jidda ga mutumin ki fa". Mai-jidda ta-ce "Mutumina ko mutumin matarsa."
"Ni kin ga tafiyata, Mai-gida zai dawo daga tafiya, bari na je na kammala aiki na, sai da safe."
Kafin ya yi Parking. Walida ta zille ta bar Mai-jidda, hakan ya sa Mai-jidda tsayawa daga bakin ofis din, don su gaisa. Amma sai ta ga yana kiranta a waya, ba tare da ya fito daga motar ba.
Alhaji Yusuf baida dama. Cikin taku daidai ta karasa har motarsa. Yana bude motar, ta gane nufinsa, ta shiga su tafi. "Yallabai da fatan ba sace ni ka zo yi ba, da yammacin nan?"
Dariya ya yi ya-ce. "A tsakanina da ke, waye ya iya sata, bayan ke har cikin jiki na ki ka shiga, ki kayi min sata?"
Mai-jidda ta yi murmushi, ta bude kofar motar ta shiga. "An wuni lafiya?"
"Alhamdulillahi! Sai dai na kasa sukuni har sai na taho ganinki, hakan ya sa ki ka ganni da yammacin nan."
"Yallabai, wai har ni ce zan hanaka sukuni? Ayi min afuwa, to me zan yi? Ka samu sukuninka?"
Murmushi ya yi, ya tada motar, ita dai tafiya kawai ta ga suke yi, ba tare da ya fada mata komai ba. "Abu daya na ke so, kuma kin san shi. Hauwa, mu yi aure."
Ta dube shi cikin yanayi na sakin fuska, ai ko dama can maganar da suke yi kenan. "Ba wata shekara ba, ko wani wata, mu yi aure cikin wannan watan."
Wannan ya sa ta ke masa duban mamaki. "Ina sonki da yawa, kuma ba na son na rasa duk wani dama da zan samu na mallakarki a matsayin matata." Kallonshi takeyi idan don kyaune da fasali da ma abun hannu Yusuf karshe ne, domin kana ganinshi kaga wadannan a zaune tare dashi, haka nan ilimi. Gashi yana da shekaru don a babu a babu ta san zaiyi arba'in da biyar, so kwarai tana ganin kimanshi.
Musamman yanda ya iya kalaman kwantar mata da hankali duk lokacin da ya ganta cikin damuwa. Ko bai fada ba ta san yana sonta sosai. Matsalar dai daya ce ta gidansa.
"Yusuf." Ta kira sunan sa a tsanake. "Kai ma ka san na amince da kai, kuma babu wata wasa a tsakanin mu, ni a shirye na ke da na aureka, muddin kai ba ka da sauran matsala da iyalinka."
Ta dubi yatsunta ta-ce. "Ni dai fatana ya zama ko na amince gaba kar a kuma samun wata matsala, idan ka gama warware matsalar Yayata, to shi kenan ko gobe za ka iya isowa gida, wannan ba laifi."
"Kar ki damu da wannan, mun zauna mun yi magana sosai. Kuma ita ma (Hajiya). Mum dina ta fahimci komai, don haka babu sauran abin da za ki yi shakku akai."
A gaban (Sahad Stores) ta ga sun yi Parking, nan suka shiga ya mata saye-saye, sannan suka koma gida, wajen biyar da rabi suka isa kofar gidansu Mai-jidda.
"To Hauwa, na gaishe ki, ni zan koma kenan Insha-Allah."
"Amma yanzu za ka koma, ba za ka bari zuwa da safe ba, idan Allah ya kai mu?"
"Kar ki damu, mun saba tafiyar dare, zuwa issha Insha-Allahu ina Kano. Gobe dai ku na da baki".
Mai-jidda ta yi murmushi mai hade da 'yar jin nauyi sannan ta-ce. "To Allah ya kai mu, ya kuma kiyaye hanya. Sai da safe kenan."
"Allah ya kai mu lafiya, take care."
Wani yaro ya kira, ya sa ya shigarwa Mai-jidda da sayayyar da ya narka kudi wurin yi mata su, bayan ya fito, ya dauki kyauta yayi masa, sannan ya shige.
Umma tana ta kallon yaro, sai shigowa yake yi da kaya niki-niki a hannu.
"Mai-jidda, kasuwa ki ka wuce ne daga wurin aikin?"
"Hmm! Umma, Sahad muka fito da Alhaji Yusuf, yanzu ya ajiyeni, ya wuce Kano. Yana mika gaisuwarsa ma."
Umma ta rike haba sannan ta-ce. "Da dai ba ki da wannan rigimar, na rasa amfanin sa a yanzu, me ya kai ki sa shi kashe kudi da yawa haka?"
"Umma, musamman ya daukeni a wurin aiki muka tafi, haka duk abin da ki ka gani, sa ni a gaba ya yi, sai da na dauke su. Ni ko yanzu zan iya mayar masa da su."
"To Allah ya amfana, amma kin san Babanku ba zai so hakan ba, musamman yadda ki ke karbar kayan hannun sa." Mai-jidda dai shiru ta yi, ba ta ce komai ba.
Bayan an idar da Sallah ne, ta watsa ruwa, suna cin abinci da Ummanta, sai ga Abdul-Majid ya shigo. "Yaya Mai-jidda, ke kam ba ki san wani abu ba?"
"Don Allah, idan za ka yi magana, ka yi kai tsaye, meye na kame-kame?"
"Ke dadina dake ba kya more zance Wallahi. To dama zance miki ne, ki shirya ki fito Injiniya na son ganinki ku yi magana, tare da shi muka yi sallar magarib a masallaci."
Yau ta ga ta kanta da shegen nacin wannan mutumin, yanzu kuma ko me ya kawo shi? Don ya ga sakon da ya turo mata, bai yi tasiri ba, shi ne zai kinkimo kafafu ya taho da kansa.
******
A falon ta same shi, ko ruwa yau ba ta fito masa da shi ba, don ya riga ya kai ta makura.
A tsume ta gaishe shi, maimakon ya amsa mata gaisuwar, sai cewa ya yi "Dole ki bata rai, ki na kau da kai, kin san ba ki da gaskiya, shi ne har da wani ficewa yawo da wannan mutumin ko?"
Ta dago kai fushi har diga yake yi a fuskarta ta-ce. "Na sha fada maka ba ruwanka da wanda ya zo wurina, don haka ban ga meye damuwarka ba."
Ya sauke ajiyar zuciya, domin kansa ne yayi masa zafi sosai. "Na ji ba ruwana, amma idan har za a rinka daukar min ke ana zuwa yawo, ai atleast na cancanci na sani ko?"
"Wannan ma bai shafe ka ba. Yaya su Mama?"
"Lafiyarsu kalau, suna gaisheki."
Bayan ya amsa mata ne ya-ce. "Jidda, har yau ba ki ce komai ba, wannan yana nufin shi kenan, na yi duk abin da na ga ya dace?"
"Wannan kam ai tuntuni radin kanka ka ke yi, don haka damuwarka. Ni dai na fada maka matsaya ta, domin kuwa tsakani na da kai, ba maganar so, bare kuma aure, idan za ka hakura ka daina bata lokacin ka, da ya fi mana duka."
"Me ya sa ki ke wahalar da ni ne, eyye Jidda?" Ya fada a marairaice.
"Ba zancen wahala, ni na fada maka ra'ayina game da kai, ba zai yiwu bane, asali ma gobe Alhaji Yusuf zai yi tambaya. Insha-Allahu saboda haka ka ga magana ta kare."
Wani tashin hankali Abdul-Aali ya tsinci kansa a ciki marar misaltuwa. "Na ji Jidda, tunda haka ne.
Amma kuma ina son ki san I won't go down, ba tare da fighting a kanki ba. KE NA KE SO! Kuma KE ZAN AURA Insha-Allah, don haka ki zauna cikin shiri."
"Kana nufin ko ina so, ko ba na so sai ka aureni?"
Murmushi ya yi mai kashe jiki ya-ce. "Oh Jidda, kina so za ki aureni, sai dai ki ki furtawa ko ki ki nunawa, saboda kar nace miki na fada miki. Amma ba za ki yi nadama ba. Insha-Allah."
Jin shi kawai take yi, ta san babatu yake yi kawai, tunda ita-ce mai amincewa, zabinta za ta aura, ba abinda zai sa ta auri Abdul-Aali kuwa.
Ta rasa ma yadda aka yi, kamar ba ciki daya ya fito da Dakta ba, koman su daban, a bangare guda Rayyan mutum ne mai hakuri da gentleness, sannan ga tausayi akan abin da yake so.
Daya bangaren kuma Abdul-Aali mutum ne mai naci, nuna isa da zafi akan abin da yake so. Haka suka rabu baram-baram! Ranar.
*****
Farin ciki ne fal! Ya cika ta da yamma da Abdul Majid ya zo ya sanar da Umma bakin Baba sun iso. Ko ba komai, yau idan aka yi magana mutanen Alhaji Yusuf shi kenan, domin ta riga ta san abu guda, muddin Baba ya amsa abu, to ba me sa shi ya canza.
A daren Alhaji Yusuf ya shaida mata. "To, gimbiya an samu Baba da magana kuma ya yi farin-ciki da zuwan su, ya kuma bada lokaci ya-ce zai same su da amsar tambayar."
"To Allah ya sa a dace, na ji dadi kuwa".
"Na gode sosai Hauwa, ba abinda zan ce miki, domin ba ki san irin farin-cikin da na ke ciki ba."
Haka nan ita ma ta tsinci kanta da farin-ciki, domin ko ba komai ta kusa ta yar da kwallon mangoro, ta huta da nacin kuda. Take ko tayi waya ta fadawa Yaya Maryam abun da yake faruwa.
"Maa sha Allah nayi murna kwarai, Allah sanya alkhairi ya kade fitina."
"Ameen Ya Maryam, ina su Aisha suke?"
"Tana ciki tana home work ne inaga."
"To ki gaishe su, sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya."
********
Da safe ta shiga gaida Baba ne, yake cewa "Ni Hauwa, ban gane abu guda da yake faruwa ba?"
Nan ne gaban ta ya fadi, me kuma yake faruwa? "Jiya da safe Alhaji Sani ya kirani a waya yake min maganar ki da Dan wajensa Abdul-Aali, sannan kuma da yamma, sai ga mutanen Yusuf Takai sun zo min da makamanciyar maganar."
Nan ne gaban Mai-jidda ya shiga dukan uku-uku! Yaya Abdul-Aali zai turo? Bayan ba ita bace ta sa ya yi hakan, ai kuwa za ta cewa Baba ba ta son sa.
"To duka dai nace zan waiwaiye su. Yaya za ki sa duka su sameni lokaci guda, bayan kin san yadda tsakani na yake da Alhaji Sani?"
"Baba, dama fa Abdul-Aali ba wai mun daidaita bane da shi."
"Ban gane ba ku daidaita ba, bayan ina ganin ko wane sati biyu ko sati yana sintirin kan hanya dominki?"
Tayi shiru, ai ta san yawan zuwan Abdul-Aali sai yasa Baba ya yi magana, don dama shi bai cika son tara samari ba.
"Ni dai idan zan ba ki shawara, tunda kin ga Abdul-Aali dai Dan-uwan mijinki ne mai rasuwa, kuma ko ba komai, kin hada jini da su. Ko don kulawar Dan nan da kuma mutuncin da yake tsakani, ina ga zai fi dacewa, ki koma wancan gidan."
Mai-jidda kuwa tashin hankali ne ya hana sashin iya furucinta dake kwakwalwarta ya motsa, bare ya aikata aikinsa na magana...
Jin ta yi shiru Baba ya-ce. "Kar ki damu da maganar shi Yusuf, ni zan san yadda zan masu magana, amma idan kuma ki na ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, fani'iman. Zabi naki ne".
Mai-jidda dai tana zaune, ba uhm! Ba uhm-uhm! Can ya-ce ta tashi ta je, ba tare da ta ce komai ba, ta bar falon.
Kwananta biyu tana tunanin wannan batu na Baba, bugu da kari ga sakon da Abdul-Aali ya turo mata kwanaki.
Hakan ya sa a safiyar kwana na biyun, ta-ce "Umma dai na yi shawara ne, na ke son na fada miki".
Umma ta-ce. "To shawara kuma?" Abin ya bawa Umma mamaki ganin kwanakin nan duka. Mai-jidda ba ta da lokacin komai daga aiki sai tunani, randa ba ta tunani kuwa, to sai a sameta tana kuka.
"Na amince zan auri Abdul-Aali". Ba Umma kadai ba, har ita mai bayanin furucinta ya ba ta mamaki kwarai. Abdul-Majid kuwa da yake bakin kofa, kwashewa ya yi da dariya ya-ce. "Umma Wallahi wani abu ya shiga kan Yaya Mai-jidda".
Harararsa ta yi. "Wa ya ce ka sa baki a maganar mu?"
"Wai gani na yi duk duniya, ba wanda ki ka tsana irin Injiniya, haka kawai ki tashi a barci ki ce shi ki ke son ki aura, ai dole nace an samu matsala."
Umma ma dai ta zargi hakan har cikin ranta, amma dai sai ta-ce. "Wani abu ne ya faru Mai-jidda? Ko dai dole aka saka ki?"
"Umma, na canza ra'ayina ne, ko kuwa don nace ba na son sa, sai ya zama ba zan iya auren sa ba?"
"A zamanin nan wa yake auren rashin so? Amma tunda haka ne, shi kenan, zan fadawa Baban ku. Allah ya sanya alheri." Mai-jidda ta ji wani abu ya wuce mata a wuya da kyar.
*******
Satin da ya kama ne, ake ta hada-hadar bikin Mukhtaar, gidan a cike yake da jama'a kasancewar an kwana biyu ba ayi biki ba a gidan.
Jama'a da dama sun samu halarta, wannan ya sa su Mai-jidda ba su ga ta zama ba. Suwaiba ma ta taho da yaranta daga Kaduna.
Sai dai duk inda Hamamatu take, to Mai-jidda ba ta cika sakewa ta yi hira ba, saboda nauyin ta da take ji, tana mamaki da har yanzu ba ta san ita Abdul-Aali yake nema ba.
Ta kuma rasa hanyar da za ta bullowa abin, don haka ruwansa idan ya ga dama ya fada. Gidan Mukhtaar dake Jan-bulo za a kai amarya, don haka kasancewarsu gidan maza, ba wata hidima sosai za ayi ba, sai walima da aka shirya na zuwan amarya.
Ranar Asabar da yamma ta koma gidan Yaya Maryam da Mabruka, nan suka dan taba hira, kafin Hafiz ya zo daukanta, dukkan su mamakin Mai-jidda suke yi.
"Meye ku ke min wani irin kallo? Ku ka matsa da cewa na tausaya masa, na duba albarkacin su Mama ko kuwa Muhammad, abin da na duba kenan kuma na amince, za ayi finalizing komai, sannan ku na min kallon zombies."
"Kawata shin kina farin-ciki da zabin ki?"
Mai-jidda ta-ce "Eh mana, me zai sa na amince, bai cin hakan?" Ta rangada masu karya.
"To Allah ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana lafiya." Ta tashi zuwa kicin ne. Yaya Maryam ta-cewa Mabruka. "Kin yarda da gaske ta amince?"
"Hmm idan dai Mai-jidda ce za ta aikata, ki daina mamaki, abin tausayin dai Engr. Abdul-Aali ne."
Mabruka na tafiya ta shirya ta-ce. "Yaya Maryam zan koma na san war haka an kusa kai amarya."
"Ba za ki jirani mu tafi tare ba?"
"Ke da nawan (Saibi)kin nan, sai dai na tafi da A'isha, kya shirya Nabil ku taho tare." Suka wuce kai tsaye gidan bikin, suna zaune ne Mai-jidda ta-ce.
"Wai yau Mukhtar ba dama buri ya cika, tun dazu ya kasa zaune, shi ayi a kai masa amaryarsa, yana ji da Kamilar san nan."
Kwafa Hamamatu ta yi ta-ce. "Hmm! Duk na lokaci kadan ne, lokacin da zai tashi maka mata wulakanci, kina ina?"
Mai-jidda ta dubeta a razane, saboda ta manta da halin da ake ciki "Yaya kike kallona haka? Ko kina nufin ba ki san Abdul-Aali aure yake shirin yi ba?"
Mai-jidda ta nemi yawu, ta hadiya don ta jika makoshinta da ya bushe. Nan da nan ta rasa, a take ta bude ruwan da ke gefenta ta kwankwada, sannan ta-ce. "Mamin Mimie, haba dai, ke kuma mu bar maganar nan".
"Da gaske na ke fada miki, ai namiji, sai a bar shi, yana can sai bare-bare yake yi, a garin nan suka hadu. Allah kadai ya san ma ko yana can wurinta, shi ya sa ma ki ka ga ban yi wani dokin tahowar ba."
Mai-jidda dai banda ware idanu, ba abin da take yi, ta rasa yadda za ta kashe maganar ba tare da tona kanta ba. Sannan tana tunanin yadda za ta yi, duk randa Hamama ta gane ita mijinta yake so.
"Ai mazan ne sai hakuri, ke dai ki kwantar da hankalinki, ki zuba masu idanu. Allah ya shige miki gaba".
"Ameen, na gode Anty Hauwa, ni na dade da share maganar a raina, shi kansa Abdul-Aalin na dade da sa shi a gefe, zaman yarana kawai na ke yi."
"Akan me ya sa? Mijinki ne, sai ki bari don zai yi aure, ki nisancen shi? Ban ga dalilin hakan ba, ba sai ki jira ki ga anyi auren ba ma tukuna?"
Hamamatu ta yi murmushi ta-ce. "Allah ko? Na yarda dake Anty Hauwa, ke dai sai mun zauna, za mu yi shawarar abin yi."
"A'a ki samu dai Anty Suwaiba sune manya."
Tana fadan hakan a ranta ta-ce. "Abdul-Aali ka cuceni, da wane ido zan kalli Mamin Mimie, bayan ka hada mu fada?"
****
Ran lahadi da safe ta gama gyara dakin Mama, kasancewar kafa ta dan dauke, tana zaune tana karyawa. Ya shigo cikin uwar dakin. Ba tare da ta ce masa komai ba, ta ci gaba da cin abincinta. "Ba tayi ne abin ma?"
"Bari na sa Yahanasu ta sako maka wani, wannan ya kare."
"Miko min shi zan ci haka nan." Ya fada yana kallon yadda take shan kamshi.
"Wai kai matarka bata baka abin karyawa bane, ka fito za ka cinyewa mutane nasu?"
Kasa-kasa yake kallonta. "Jidda ki yi abinda ki ke so, miko min Plate din".
"Ni ban gama ba." Ta fada fuska a gintse.
Gani kawai ta yi ya sauko ya zauna, ya sa hannu a cikin Plate din abincinta.
A razane ta dube shi, sannan ta-ce. "Allah ya shiryeka Wallahi. Kai ba ka ma jin nauyin Mama, ko ba komai gidan nan a cike yake da jama'a".
"Ban gansu ba anan, ke kadai na ke gani, kuma ko ni ne na yi batan kai? Kamar dai wancan satin, an min tambayar auren ki, kuma har da kudin aure na bayar, saboda haka, idan za ki ci abinci, ki san da cewa tare da mijinki za ki ci, ko kuma ki jira sai ya koshi, ki ci."
Idanunta ta kada, sannan ta zare hannunta, ba ta ida cirewa ba, ya rike ya-ce. "Zauna ki karasa."
Yau tana ganin ikon Allah, wata tsiyar sai a wajen Abdul-Aali. "Ka san me ka ke shirin yi kuwa? Jiya Mamin Mimie take fada min halin da take ciki, a rashin sanin cewa ni ce matar da za ka aura, ka san ba kyau yanke tsakanin zumunci ko?"
Kofin shayinta ya dauka, daidai setin gun jam bakinta ya sa bakin sa, ya kurba a hankali, sannan ya ajiye. Mai-jidda tana kallonsa, kamar ta fincike shayinta.
"Me na ke shirin yi, ko me muke shirin yi? Na danne bakinki, nace miki ki amince da aurena? Ke da kanki ki ka ce kin amince, don haka kar ki yarda ki dora min laifi."
"Ai duka Dan-uwan dayan ne, idan ba ka matse baki na ba, ai na amince ne, bayan ka yi min barazana da abinda ka san ba zan ki ba ko? So cheap of you.
Ba za ka iya sa macen da ka ke so, ta so-ka ba, sai ka bi ta karkashin kasa. Har da sa Abba a cikin maganar". Idanunta ta sake juyawa. Ta ja tsaki a ranta.
Kallonta ya yi ta kasan idanu, ya dade bai ji abin da yake ji yanzu ba game da ita. Hakan ya sa ya yi saurin mikewa, don ya wanke hannunsa.
Amma kuma ganin Hamama da ya yi a tsaye ne, ya sa shi tsayawa cak! Mai-jidda ta mike, don ta ga me ya hana shi tafiya, kasancewar tsawon Abdul-Aali ya tare mata kofar.
Tana mikewa, ta ga Hamamatu a bakin kofar dakin, ji ta yi tamkar za ta fadi, don tsabar tashin hankali, ta daga idanu ta dubi Abdul-Aali ta hadiyi sauran abin da ke bakinta.
Kafin ta san abin fadi, jin saukar mari ta yi a fuskarta. Daidai lokacin da Abdul-Aali ya daga hannu zai rama mata. Mai-jidda ta yi saurin rike hannun shi, ta matsa da baya.
Hamamatu ta-ce. "Dake ni Abdul-Aali, ka mareni. Munafukai. To Allah ya tona asirin ku, wato abin da za ki min kenan Anty Hauwa? Amma, kin ba ni mamaki kwarai, yadda na ke ganin girmanki da mutumcin ki.
Ashe za ki iya cutar da mutum kamar ni? Kai kuma shi ya sa ka ke ta kaffa-kaffa, kar na san matar da za ka aura, wato ka san sharrin da ka kulla kenan ko?"
Ta sauke hucin numfashi ta-ce. "Ke kuma idan shi namiji ne zai iya aikata hakan, ashe ba ki san ciwon 'ya mace, na 'ya mace bane?
Har ki na da bakin ba ni shawara, kin cuceni, kin shige jiki na, kin san duk wani sirrina, sannan kin zagaya za ki auri mijina. To Allah ya fi-ku munafukai."
Hayaniyar da ke tashi a dakin ne ya sa su Mama shigowa, tana ganinsu su uku, ta san an yanka ta tashi kenan....!
Mama ta-ce "Lafiya? Me yake faruwa?" Cikin kuka Hamama ta-ce. "Mama ki na gani, ashe Abdul-Aali wai Anty Hauwa zai aura, shi ne ya yi ta boye min. Yau Allah ya tona asirinsa, na dawo na ba shi wayarsa, ya manta.
Ashe shi kam ya taho wajen rabin ransa ne har ma tare suke cin abinci, yanzu ashe ko kunyar Dan-uwanka ba za ka ji ba. Yana mutuwa za ka aure masa mata?" Magana take yi, ba ta ma damu da Mama na wurin ba, don bacin rai.
Mama ta dubi Hamama ta-ce. "Zauna Hamamatu, ki kwantar da hankalinki ki yi hakuri..."
"Mama yaya zan yi hakuri, bayan sun cuceni? Idan dai har ya aureta, to ni kuwa ba zan zauna ba gidanmu zan koma."
Abdul-Aali ya shafo sumar shi cikin damuwa. Mai-jidda kuwa tuni ta koma gefen gado ta zauna, sai kuka take yi. "Ya isa haka nan, ki saurareni. Na san da ciwo abin da ki ke ji yanzu.
Amma kuma kin san komai da lokacinsa da kuma qaddarar sa, don haka ba na so ki tada hankalinki, da ki ka san zai kara aure, ai kin kwantar da hankalinki, saboda Hauwa zai aura, ai ina ga da sauki ko?
Tunda kin san halinta kuma ita ma ta san naki, amma don Allah kar ki sake cewa za ki tafi, ki yi hakuri ki yi zaman ki, ke da gidan ki kuma ina za ki je?"
Hmmm! Inji mai ciwon hakori, ita jin Mama kawai take yi, dama ta dade da sanin cewa ta fi son Anty Hauwa a kanta, don haka mikewa kawai ta yi ta bar dakin. Da sauri Abdul-Aali ya bi bayanta zuwa mota...
*****
Whew! that was long and intense
So, what will you say about this chapter?
Hamamatu 😔 my heart goes out for her...
Nayi nan update sai Litinin in sha Allah 🏃🏻🏃🏻🏃🏻
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top