intro/teaser
Assalamu alaikum masoyan litattafan chuchujay,nice din dai nasake dawowa bayan kamalla littafina na yar arewa wanda yake na kudi so babu complete Dinsa a wattpad.
Yanzu ma haka ina tafe muku da sabon littafina mai suna KALUBALENAH.
Wanda zan fara kawo muku, kuma wani abun dadin free novel ne so you can get access to it via wattpad, for those of you that are asking Mai yasa ban dora complete novel yanzu a
wattpad so it because previous novels din danayi na kudine but wannnan kyauta ne kuma sadaukarwa ga maryam shehu gana ,
Ina fatan zaku so shi ku kuma karbesa hannu biyu kamar yarda kuka karbi sauran novels dina.
Follow my wattpad account @chuchujay ,
Vote ,comment and share the book to your friends fisabilillah ,you won't regret doing that insha Allah .
All rights reserved ®
Banyarda wani ko wata su sauya mun littafina ta kowacce irin sigar ba please a barmun shi a yarda na tsarasa dan Allah.
*
DEENAH OTHMAN ALI.
Tunda ta fara rayuwar ta bata tunanin akwai wanda zai zauna ya saurari kukanta kamar yarda take bukatar aji,
Ita mutum ce da take da tsoro musamman tsoran mutanen da suka fita a matsayi da arziki,
A kullum tunaninta taya zata boye musu taya zatayi rayuwarta ba tareda tayi chudanya da su ba?
Duk da haka ba tayi aune ba sai da tsana da rashin kaunarsu yayi tasiri ya kuma cigalaba a zuciyarta sakamakon yarda sukayi kokari wajen tura mata tsanarsu,
Ta tsani duk wani mai kudi dan gani take dukkan mai kudi mutumin banzane kuma bully and sadist,
Masu cutar da nakasa dasu dan su ji dadi.
BINYAMIN IBRAHIM MAIKUDI
Mutum ne shi mai zafin rai da zafin zuciya ,sau da dama yakanyi abu cikin zafin zuciya ba tareda yasan yayi ba wanda a lokacin ma idan baiyyi ba ji yake kamar ya kashe kansa saboda bakin ciki ,amma sau da dama bayan ya aikata abun ke dawo masa kuma ya dame sa shiyasa ya kasance shi mutum ne mai nesa da mutane ,bai ciki shiga harkar kowa ba gudun kar ma ayi ta tabace wanda dalilin hakane yakesa mutane da dama ke kiransa da mutum mai girman kai,
Ya tsani talaka saboda irin abunda ya shiga tsakaninsu dasu dan haka yake tunanin kowane talaka halayyarsu daya kana basu helping hand su kuma suna neman hanyar da zasu cutar da kai.
AZAD KABIR MAIKUDI
Mutum na abokai mai wanda abokai kan saurin influence nasa zuwa ga bullying na kasa dasu wanda sun kasance basu da aiki sai cin zalin dukkan wani na kasa dasu amma lokaci daya shigowar deenah cikun rayuwarsu yafara sauyasa.
WIDAD SULTAN NA'ABBA
Yarinya shagwababiya wadda aka bata ta da kudi,
Mahaifinta mai kudine na gaske wanda Allah ya dora masa balain santa duba da ita kadaice yarsu ,
Komai take so yi mata ake,yarinya mai gadara da isa,yarinya mai jin taka uban kowa kuma babu abunda zai faru,
Sarauniya a dukkan inda taje indai harka ce ta wulakanta na kasa da ita ,
Iyayenta sun dorata akan hanyar ita din sarauniyace kuma ta taka dukkan wanda yazo gabanta babu abun da zai faru saboda ita din diyarsu ce,
Da wannan bazar take rawa take taka mutane yarda zuciyarta ta raya mata ta taka.
Ku biyoni dan jin yarda wannan chakwakiya zata kasance,salansa na daban ne ,ya kunshi abubuwa da dama,
And I'm sure zaku so shi,
Yana nan tafe ,
Share fissabilillah 🙏🏼 and
Don't forget to follow my wattpad account @chuchujay.
And Kar Ku manta kyautane.
Nagode.
Chuchujay✍🏽
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top