chapter 8
KALUBALENAH
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU
Tunda hajiya fattu ta fara musu faɗa bata tsagaitaba dan acewarta abun ba karamun bata mata rai yayi ba domin tsakaninta da mahaifiyar binyamin akwai wannan babban fachalancin shiyasa kowa baya san dan uwasa yaga wallensa ,
Bana san abu makamancin wannan ya kara faruwa a gidan nan shine maganar ta na karshe bayan ta musu izini da su tashi su tafi.
Haka tsakanin zainaba da ɗiyartata yakasance babu wani muamala mai daɗi da suka saba dan sosai mahaifiyar tata tayi fushi da ita,
Kwana uku kenan suna cikin wannan yanayi ,
Bata amsa gaisuwarta ko ta mata, sosai deenah taji rayuwar ba dadi dan hakan bata taba shiga tsakaninta da mamin nata ba ,
Ita tayarda ta dauki cin kashin koma wanene akanta amma a shirye take ta kuma daura damara, bazata taba bari acima mahaifiyarta mutunci ba indai tana raye ,
Haka a kwanakin takanje sashen hajiya babba mace mai mutunci wadda tasan darajar mutum kuma sosai take jan deenah ɗin a jiki duk da har a lokacin deenah ta kasa sakin jikinta,
kaltu ce ta shiga tsakanin mami da deenah wanda deenah ta dau alkawarin bazata kuma rashin da'a ba ammafa a zuciyarta ta kudiri idan ba a kuma wulakanta mata uwaba kenan dan zataje to any extent Akan maminta .
Tunda sabani ya shiga tsakaninta da binyamin bata kuma haduwa dashi ba sai a yau monday data shirya dan zuwa makaranta,
Alhaji babba ya umarci su azad da su ringa tafiya da ita makaranta tunda gida daya suke amma koda sau daya hakan bai taba faruwaba dan kafun ta fito ma sun umarci driver ɗinsu da ya tafi ya kaisu makarantan karma ace azad ,
Bata taba damuwa ba dan maminta na bata kuɗin mota so bata taba laruwa da wani,
Tana cikin sauri dan gudun kar tayi late, kwatsam sukayi kicibis a babbar harabar gidan,
Idanun sune suka sarke guri daya,
Har zata wuce ta dakata tareda dawowa baya ta tsugunna har kasa tace yaya bilya ina kwana ,
Tashi tayi kamar kuma ba ita ta gaidasa ba ta taka dan barin gurin,
Zafin nama yasa ya fincikota dan wuya yake da ita ,
Dangwarar da ita yayi gabansa yace ke "wanene yaya bilya ?
Ni tsaran wasankine ko?
Idan kika sake bude kazamin bakinkinan na miyan kuka kika kara ce mun yaya bilya sai na karyaki wallahi ,
Useless girl get out of my sight.
Tashi tayi ta fara takawa ko a jikinta daman ta gaidasane gudun kar ya nemi wani abun ya manna mata sannan menene idan ta kirasa bilya taga dai duk sunansane sannan ba ita tace a saka masa bilyaminu ba za 'ana wani bata sharia ana kiransa da wani binyamin to bazata fada ba.
Tsaki yayi lokacin da ta bacewa ganinsa yana mai kara maimaita yaya bilya din da tace masa "
What a stupid girl.
Tayi sa'ar samun abun hawa da wuri dan bata mayi tunanin baza tayi latti ba,
Kai tsaye ajinsu ta nufa ,da sallama bakinta ta shiga ajin wanda tama riga ta saba da duk shigowa sai sun mata dariya,
Tayi mamaki yau yarda babu wanda ya dara bisa sallamar tata ,
Kujeranta ta nufa direct dan zama ,
Har zata zauna ta tsinkayi muryar deen yana faɗin "deenah kar ki zauna kan seat ɗinnan,
Sai a lokacinne ta kula da abunda ke malale kan chair din nata amma kafun ta farga an zaunar da ita da karfin tsiya,
Nuna deen widad tayi da hannu tace "kar ka kuma shigar mun sabgata ,
Don't you ever fucking dare cos trust me sweetheart you won't like me.
Wani irin takaici ne ya ratsa deenah jin yarda gum din ya rike mata skirt gam gam,
Dariya su benazir suka fara suna mai mata wakar loser, inda suka fara mata Video suna masu cigaba da dariya suna kiranta da loser ,
Ihun da sukeyine ya jawo hankalin azuzuwan dake kusa dasu .
Neman hawaye deenah tayi ta rasa illa tafukan hannayenta da tasata rufe fuskarta dan best solution a yanzu da zata rabu da gum dinnan shine ta yage skirt din ko kuma ta balle button din dake gefen sa ta cire da kujerar but she need privacy.
Kafun kace me video ya samu a wayar duk wani dalibi na set dinsu dake cikin class group din.
Jitayi a rungumota ,bude idanu tayi dan ganin wanene,
Sabreena ce kawarta da bata taba nema ba tunda suka hadu,
Murmushi sabreena tayi mata tace its okay ,
Bari natayaki lifting chair din muje ki cire,
Cikeda fitina widad tace" Sabs wannan fa ba business dinki bane ba just don't get involve.
Hannunta ta kai zata fincike sabreena daga jikin deenah ,
Bige hannun sabreena tayi tace "no widdy I'm already involved and I bet you don't wanna mess with me,so be careful,
Tsaki widad tayi ta koma ta zauna inda su benazir suka koma kowa ya samu guri ya zauna,
Kama mata chair din sabreena tayi suka fita,
DA kyar ta raba jikinta da chair din sannan ta saka kayan sport dinta duba da lokacin sport din yayi,
Zama tayi akan dogon bench din da ke cikin locker room din tana kallan sabreena dake kokarin raba skirt din da gum din,
Kin san widad ne?
Ta tsinci kanta da tambaya ,
Dan murmushi sabreena tayi tace we are twin sisters daughter's ,
Mamana da mamanta twins ne.
Kada kai deenah tayi tace you're nothing like her .
I don't know why she hates me ,but nasan bazai wuce dan im from different background da ku bane ,you see my parents are not rich ,my dad is late and Mami na is a maid and nasamu scholarship dinnan ne ta hanyar inda mamina ke aiki and we live there Sannan ni i don't see anything bad about my background tunda ba sata ne muke yi ba halak muke nema so mene laipin mu?
Bansan maine damuwanku rich kids ba,
Sha nayarda tunaninku ba irin namu bane,cos mu a kullum tunaninmu ya zamu rayu,
Tasowa sabreena tayi ta zauna kusa da deenah ta rike mata hannu kana tace"trust me deenah wani lokacin talakan yafi mai kudin kwanciyan hankali,
Wani lokacin kudi matsalane cos regarding your future babu Mai barinki kiyi abunda kikeso attimes our parents force their decisions on us and we have no choice but to follow sabida a kullum zasu ce mana its for our best.
Kingan ku kana rayuwa freely but at times mu bamu samun wannan freedom din,its just the money.
You see kamar ni i hate piano practicals din da nake zuwa but my mom love it and Idan nace bana so a kullum tana faɗa mun its for my best so I had to abide by it,
So being poor doesn't make you a less human and ki manta da su widad bullying a jininsu take just be ignoring them cos I might not be always around .
Murmushi deenah tayi mata tace "nagode sabreena ,
A tare suka fita dan zuwa field bayan sun gama shirinsu na sport,
Suna kokarin fita daga gurin widad da tawagarta suna danno kai dan shiga,
Basu kula su ba suma basu kula suba suka fita.
Zazzauna suke akan kujerun dake field din daga gefe suna jiran sabon basketball coach din da akace an musu,.
Hira sabreena ke jan deenah dashi inda suke hiran kamar dama sun dade da sabawa ,
Bayyanar coach din ya bama deenah mamaki sosai ,
Ihun cheer team ne ya dauke mata hankali daga kansa sakamakon fitowar yan mazan kowanensu cikin sport wears ,abunka da kajin gidan gona yawancinsu kaji shejaransu sai ka karyata saboda yawancinsu they look 18,
Bayan sun karasone new coach din ya Fara introducing kansa as Binyamin maikudi kuma shine new coach dinsu temporary,sai a ranan take jin wai shi din babban dan wasan basketball ne,
Tabe baki tayi ,
Tabota sabreena tayi tace brother ɗin su azad ne ,
Ain't he handsome?
Yake kawai ta mata ta daga kai batareda tace komai ba,to
Mai zatace ,
Haka yinin ranar ya kare babu wanda ya kara takalar ta kansan cewar tana tare da sabreena ,
Haka Shima biyamin duk da ya ganta sai ya zabi da yayi ignoring nata.
Haka rayuwarta ta cigaba da kasan cewa cikin orchid da kuma wajen ta,baza dai ta kirata mai dadi ba tunda dadin a gun maminta kawai yake sai kuma gun hajiya babba da ta kanje su sha hira wanda a yanzu sun shaku da juna sosai,
Ranar wata juma'a tana zaune a aji taji ana ihun gagarumin birthday ɗin da za'ayi na azad wanda bata tsaya jin sauraran details din birthday ɗin ba cos baya gabanta.
Kai tsaye ana tashi ta tunkari hanyar fita ba tareda ta jira kowa ba,
Tana kokarin sakkowa daga kan stair na karshe taji an watso mata ruwa tun daga kanta,
Daga idanu tayi dan ganin wanene ,
Widad ce tsaye da yan koranta suna mata dariya,
Jitayi ta kasa hadiye wannan dayan kashin ,da zafin nama ta juya dan haurawa saman dan idan batama widad duka ba bazata fanshe ba ai talauci ba hauka bane.
CHUCHUJAY.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top