chapter 7
KALUBALENAH.
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
7
A tare deenah da maminta suka ɗaga kai dan san ganin wanda ya shigo ɗakin,
Kallo ɗaya deenah ta masa ta ganesa dan takanga hotonsa a wayan ihsan,
Cike da fitinanniyar masifa ya karaso ɗakin yana mai faɗin,
"Who the hell are you guys"
And mene kuke mun a falo haka ,
Juyawa yayi ya fita yana mai kiran Ammi"cikin wata irin shagwababbiyar siga".
Da sauri mami ta tako inda deenah ɗin take ganin tana kokarin taɓa fasassun kwalaben dake kasa a zuzzube,
"Mami wallahi bada sane na ne na fasaba.
Ganin yarda ta firgice da barnar da tayi yasa ta jawota jikinta ta rungume tana mai faɗin"
Ya isa ai kowa yasan tsautsayi sannan wannan abun da kikaga ya fashe to lokacinsa ne yayi koshi mai abun idan da ace yana hannunsa zai fashe tunda wa'adinsa yayi bari yanzu zan gyara gurin,
Rufe bakinta keda wuya ammi ta shigo tareda shi a bayanta yana wani kwaɓe fuska,
Maike faruwa anan ne zainaba?
Tsugunnawa mami tayi cikin biyayya tace wallahi hajiya tsautsayine deenah na tayani aiki abunnan ya zame ya faɗi ,
Cikeda da wata kasalaliyar muryar wulakanci yace "
Tsautsayi ?
Ammi kinajin wani bullshit ba?
Beside wama ya basu izinin shigo mun part,ammi kinsan fa i hate kazaman mutanen nan they are hungry wolfs abu kaɗan suke jira su kwashi na kwasa yanzun ma who knows Ko sun satan mun wani abu cos talakawannan chance kaɗan suke jira basu iya talaucinsu ba,
Kayi hakuri ranka ya daɗe shine kawai abunda mami ke iya furta wa,bawai batajin zafin abinda ke faruwa bane a'a tana danne wa ne a matsayinsu na masu nema a kasan su,
Wani irin bakin cikine yazo magogwaron deenah ya tsaya jin yarda yake musu diban albarka har yana kiransu da barayi inda mahaifiyarsa kuma ke tsaye tana sauraransa,
Gyara tsayuwa amminsa tayi a karo na farko kuma tayi magana ,
BINYAMIN take it easy umm,laipinane dan asibe ne bata nan so na roka fattu ta bani mai aikinta so kagani ba laipina bane cos bansan suna da barna ba amma an maka laipi kayi hakuri kaji son,
Don't mind yan aikinnan kar ka bari su bata maka mood dinka oya maza kaje kashirya ka fito kan alhaji babba ya fara nemanka,
Kara kwabe fuska yayi cikeda kyamarsu yace "No ammi sai kin fara dubasu ki tabbatar basu mun sata ba cos nasan zaiyyi wuya talaka ya kasa sata a guri.
Cigaban hakurin da mami ke masa shine ya ke kara tunzura deenah,
Cikin murya kuka tace "_
Mu ba barayi bane sannan dan muna nema karkashinku bashine ya mayar da mu wulakantatuba halak ɗinmu muke nema ,
Namaka barna cikin rashin sani amma bashine ya baka damar wulakantamu ba dan yarda kake dan adam muma haka muke ,kake ta wani fama kwabe fuska kwazozan ƙato da kai ,koni bana ma mami haka a shekaruna sai kai ƙaton banza.
Jin dakin ya yi jum kamar an dauke wutane yasa deenah tayi realizing abunda take faɗa da kuma inda take,
Dagudu ta rabe ta fice a dakin zuciyarta na dukan uku uku,
Mami da gaba daya ta kidime ce ta cigaba da basu hakuri dan ita kanta batayi tsammanin deenah zata fadi haka garesu ba.
Rike kugu biyamin yayi cike da mamaki yace ,
Ammi naji da kyau kuwa?
Ni poor a** little begging bitch dinchan ke kira katan banza,
Ammi katan banza fa.
Wata dariyan yayi irin ta mamakin nan yace katon banza fa ammi,
Kallansa ya maida kan mami da kanta ke kasa yace "hey old woman Ki shirya barin gidannan keda yarinyan ki mara tarbiya ,mumuna yar kyauyen chan saboda ta ja maki balai.
Fuuu ya wuce bedroom har yana kokarin bige mami da tayi saurin kauce masa.
Tashi ki bace mun and make sure kun hada jakanku kamar yarda yafada maki,
Idan ance kubama yaranku tarbiyya sai ku ki alhalin kunfi kowa sanin talauci sai da tarbiyya .
Sum sum Mami ta taso dan barin sashen ranta fal takaicin abunda ya faru,
Chan ta Tarar da deenah tana kuka,
Kotakanta bata biba ta koma chan karshen gadonsu ta zauna tana mai dafe kai,
Ganin haka yasa baba kaltu cewa ,"ai ke kya faɗan abunda ya faru tundaita ta gagara sai kuka da ta zauna tana mun,
Cike da bakin ciki ta fada mata abunda ya faru tana mai karawa da cewa, "ai na gode sosai da kika jawo aka zageni har ana kokwanto akan tarbiyar dana baki,
Yau ko duka ya rufeni dashi ba zakice masa katon banza ba ballantana zagine kawai kuma ni banga inda yake fitowa a jiki ba,ai shikenan sai ki fara hada mana kaya kanki kika yiwa .
Kuka sosai deenah ta sake fashewa dashi na bakin ciki bana dana sani ba ,dan jin abunda maminta ke faɗa na kan ta hada musu kayansu sai taji dama zazzaginsa tayi ta rama abunda ya faɗa musu sai a koresu da hujja.
Bangaren binyamin kuwa koda ya shiga bathroom tunanin abunda ya faru kawai yake ,wai shi yar wannan yarinyar sa'ar kaninsa zata kira da katon banza,
Saurin tsane jikinsa yayi bayan ya fito kana ya shafa mai yana mai Allah Allah ya ida yaje ya samu Alhaji babba tunda ko kai ka dauki mai aiki saida yardarsa za'a koresa shima kuma sai da dalili babba wanda dalilinsa baza a kirasa da karami ba,
Knocking ya ji a bakin kofarsa ,cikeda masifa wadda a zahiri idan ka kalleta bazaka kirata masifa ba yace who is that*
Daga bakin kofar ihsan tace bro nice ,
Bai sake cewa komai ba wanda alamune na ta shigo so ta sa kai ta shiga ,
Zama tayi kan stool din dake gefen mirror while shikuma ya cigaba da taje gashinsa ba tareda ya damu da san sanin menene ya kawota ta ba dan muradinsa kawai nasan ganin su deenah sun bar gidan shine a gabansa ,
Ganin bazai kulata bane yasa ta katse shirun ta hanyar cewa"
Bro nasan you dont wanna listen but it's about deenah, dazu naji ammi na maida maganan ,
Dan Allah brother kayi mata hakuri ,deenah yarinyane mai kirki sannan nasan ta faɗi abunda tace ne bisa kuskure shes a nice girl when you get to know her dan Allah brother MiN give her another chance"
Wani kallan banza yayi mata a lokacin da ta kare zancenta kana ya rike kugu yana mai facing dinta "why should i get to know her ,
Ni sa'anta ne ,
Beside ni kinga nayi maki kama da class na talaka ?
Dukkansu barayine and to hell with her being nice "shit,
All I fucking care about shine a yau sai ta bar gidannan.
Get out".
Kallansa ihsan tayi da fuskar damuwa tace "brother MIN nasan kanada bad experience akan talaka amma that doesn't mean dukkansu barayyine beside an mafi samun barayi cikin masu kudin cos a koda yaushe burin mai kudi daya shine yaya zai kara arziki,
Brother Deenah is not any talaka give her another chance,
Are you done?
Ganin bashi da alamun wasa ne yasa tace "yes"
Kamo hannunta yayi kiii yayi waje da ita ya watsa bakin kofa ya mayar ya rufe..
1 hour later.
Shiru deenah da maminta zaune suna jiran tsammani ,
Sallama kaltu tayi tace zainaba ana nemanku sashen Alhaji babba and ki kwantar da hankalinki shidin mutum ne mai adalci ni na tabbata bazai biyewa binyamin ya kore ku ba akan dan abunda bai taka kara ya karya ba ,
Deenah yarinyane and nasan ta fadi duk abunda ta fadane a matsayinta na wadda bata iya jure acima mahaifiyarta mutunci kuma ta wannan ina tare da ita saboda babu maiso acima mahaifiyarsa mutunci yayi shiru.
Maza kuzo muje ,
Babu musu suka tashi jiki a sabule karma ace zainaba,
A babban falon da suka zama baki daya suka tarar da su,
Jiki a sabule suka karasa ciki bakinsu dauke da sallama bisa jagorancin kaltu,
Umarni Alhaji babba mutum mai kwarjini ya basu su zauna,
Nifa granny im not here Dan mu maida abunda ya faru kawai inasan a kori matarnan da yarinyanta daga gidannana cos I wont stand them ko kadan saboda yar wannan yarinyan idan ina ganinta gidan nan zan iya maketa ko wane lokaci,
Sai da ya kai aya Alhaji babba ya kallesa cike da nutsuwa yace ka gama?
Bai basa amsa ba ,sanin bazai basa dinne ba yasa ya maida dubansa kan su deenah yace "ke deenah ko maza taso a bayan umminki ki dawo nan gabana ina ganinki,
Da fargaba deena ta tashi ta karasa tana jin kamar ta gudu musamman irin yarda biyamin ke mata wani banzan kallo ga kuma idanun hajiya fattu a gefe da ammin binyamin dana hajiya Babba wadda tunda ta amsa gaisuwarsu batace komai ba dan In Alhaji babba na guri shi keda magana,
Durkusawa deenah tayi tace Alhaji gani,
Tambayarta yayi abunda ya faru,zanzan ta zayyana masa komai ba tareda ta boye nata kuskurenba,
Kallan binyamin yayi yace kai kana da laipi binyamin,
Bance ita bata da laipi ba duka kuna dashi,
Bude baki yayi zaiyyi musu ya dakatar dashi.
Nuna mami yayi yace ita mahaifiyar deenah ai zata haifeka mai yasa zaka ci mata mutunci haka kuma kayi tunanin yarinyarta zata yi shiru,
Ai baka dau hanyar mutunci ba saboda ko kaine ba za kayi standing a cima ita amminka mutunci ba har ana kiranta barauniya ,
Yanzu I won't make this long,
Deeanah da mahaifiyarta bazasu bar gidannan ba ,ina nufin zasu cigaba da aikinsu saboda ni banga abunda sukayi wandaya cancanci kora ba,
sannan inaso kai ka fara bawa maifiyarta hakuri bisa rashin ɗa'ar da kayi mata sai ita ma ta baka hakuri and case close,sannan babu talaka sai bawa mafi munin aiki gaban ubangiji,ka kiyaye,
Zainaba ce ta ɗan gyara zama tace alhaji amin afuwa zan tsoma baki,ni ina ganin ba sai ya bani hakuri ba wallahi ban dauka da komai ba..
"A'a mami ya baki kawai dan nima bazan bashiba idan bai baki ba ,
Jawota maminata tayi inda shikuma ya zabura yana mai faɗin kana dai ji ko grand pa,
Yar dariya alhaji babba yayi yace naji ai ba akan bata take ba ,
But..
No buts binyamin kawai ka bada hakuri .
Kasa yayi da Kansa cikin takaici yace kiyi hakuri i was wrong,
Dan murmushi deenah tayi tana mai fadin "shege kaya a ranta inda a fili kuma tace nima kayi hakuri na kiranka katon banza ,bazan karaba but idan ka kuma ma mamina rashin kunya zan kuma.
Wani kallo yamata na tsana kafun ya tashi fuu ya fice a dakin ,
Bayansa amminsa ta rufa bayan ta musu sallama,
Yar dariya kakan nasa yayi ya kalli deenah yace "deenah just be avoiding him and banda fitsara,
Kasa tayi da kanta tace insha Allahu,ayi hakuri.
"Nikuwa ina san yarinyar ,ko za tana zuwa tana dan mun tausa da hira in bata komai,
A Karo na farko hajiya kaka tayi magana.
Babu komai fattu ta faɗi tana mai murmusawa a zuciyarta kuma tana mai san ta kebe da zainaba da diyarta.
CHUCHUJAY.✍🏽
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top