chapter 4

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

4

Da sallama suka shiga cikin falon da jagorancin hajja aysha,
Yaran da suka tarar a kofar shiga gurin ne kaɗai a falon ,
Zama hajja aysha tayi tace azad hajiya fa?
Kamar baijita ba haka yayi sai a karo na biyu da ta kara tambayane ya kalleta "
Yace"
I thought you called when you fucking coming ,
And no one asked y'all to have a seat but y'all do without manners ,
Tsaki yaja yana mai tashi a gurin, bai kaiga fara takawaba muryar datijjuwar dake tattakowa daga kan stairs din dake cikin falon ta karaɗe da sautin da take cewa .
"One step azad just one step and I will make you regret being born.
A cikin takunta irin na manyan mata ta tako a hankali har ta karaso ,
Kallansa tayi da wani irin banzan kallo kafun tace on your kneels,

Babu musu yayi abinda ta umarcesa idanunsa cike fal da tsoro,
"Kana Hauka ba?
Wadannan sa'aninka ne ?
How dare you talk to them the way you just did ?
Inajin tarbiyyan da na baka bai isa ba ,yanzu kafara basu hakuri har sai sun hakura ,
Bai musa ba ya fara basu hakuri,
Hajja aysha ne tace "
Hajiya Allah ya wuce babu komai ai yarone".

Ai da cewa yarone kafun ki farga suke kwacewa,will you get out of here and wannan ya zama na karshe da zan kara jin kayiwa wanda yafika rashin da'a.

Sum sum ya tashi a gurin yana mai hararan deenah wadda tayi lakur a gefen zainaba,
A hakimce ta dawo da fara'ar fuskarta garesu tace"hajja aysha barkan ku da zuwa ,
Gaisawa sukayi cikin mutunci da girmamawa inda hajja aysha ta gabatar mata da su zainaba,
Cikin girma da azirki ta karbesu kafun tace sharuɗan ta basu da wani yawa guda ɗayane wanda shine bata san zirgazirgar idan Alhaji yana nan kuma aikin ta ba wani mai yawa bane zatana yin share share ne na cikin gidan da wanke wanke sannan za'a bata daki a sashen da masu aiki suke,
Sannan ya zama tashigo tayi aikinta very early saboda ita tana da kishi akan mijinta dan haka bata yarda wata mai aiki ta gittasa ba indai tana san su zauna lapia cos yana daya daga cikin abubuwan da yasa yan aikinta basu lasting,

Sunkuyar da kai zainaba tayi bayan ta gama jin dokokin hajiya da kuma albashin ta wanda bata gaba tunanin zai kai haka ba,
Cikin ladabi da biyayya tace "insha Allahu hajiya zaki sameni mai rikon gaskiya da amana sannan indai Alhaji ne baki da damuwa akansa bazan taba zama maki matsala ba ta nan bangaren,
Dan murmushi hajiyan tayi tace then the deal is sealed,
Ba fahintar abunda tace da turancin zainaba tayi ba amma a yanayin fuskar hajiyan ya nuna mata ta karbeta.

Bayan sunyi sallama da haule da hajja aysha ne wata dattijuwar mai aiki wadda  zata fi zainaba ta musu jagora zuwa dakinsu da zumar washe Gari zata fara aiki,
Dakuna ne guda hudu a jere wanda yake dauke da masu aikin shashina hudu dake cikin gidan ,
Kallan dakin zainaba take cike da mamakin wai dakine na masu aiki ,
Gadaje ne wanda zasuci mutum biyu harda space ,aje jakansu zainaba tayi a gefe .
A'a ga wardrobe din Da zakusa kayanku,
Cewan matan da ta rakosu tana mai karasawa gaban wardrobe din,
Babu musu zainaba ta dauki jakarsu ta saka a ciki batareda ta tsaya cire wa ba dan duka duka kayan nasu nawama suke,

Nan ne dakinmu ,ni sunana kalthume kuma nice babbar mai aiki a gidannan,
Shekarata goma sha biyar ina aiki a gidanan,
Ni mai aikin sashen hajiya Fattu ce a da wato wadda zakina ma aiki kenan,
A yanzu kuma nice mai saita masu aikin gidan wato nice mai sa kowa ya tafi gurin aikinsa a kan lokaci,
Hajiya fattu itace hajiya ta biyu a cikin gidan Alhaji SALIHU MAIKUDI wato matar AlHAJi KABIR wanda shine dansa na biyu ,yaransu uku,
Azad shine babba sai mubarak dayake binsa sai autarsu Hajara ana kiranta farhana dan sunnan hajiya babba kwatakwata taci wato hajjo mahaifiyar Alhj kabir,
Hajiya fattu nada kirki sosai amma guri daya zaku saku matsala shine idan taga kina hulda da mijinta dan tana da zafin kishi sosai da sosai akan mijinta.
Gidan dake chan gefe dana hajiya fattu gidan Alhaji IBRAHIM ne wanda shine babban ɗa a zuriar ta Alhj salihu ,
Shima matarsa ɗaya tunda mutane kan ce alaadar gidance auran mace ɗaya ammafa sai macen da kake masifarso gudun cutuwarka ,acewar mutane mahaifin nasu yafi amincewane da auren mace daya saboda gudun rashin adalci amma hakan baisa ya hana ka ƙarawa ba idan zakayi adalci wanda babu wanda ya ƙara din dan tunanin yaran nasa ɗaya da nasa.
Hajiya mardiyya itace matar Alhaji ibrahim wanda suma yaransu uku ,babban shine BINYAMIN wanda bama yaƙasar gaba daya dan tun yana da shekara goma yake kasar ketare  gidan antynsa inda nan yake karatunsa yanzu shekara tara zuwa goma kenan,
Sai kanwarsa ihsan sai mai bimata Abubakar wanda shine wurin tsarar azad ,

Sai daya bangaren dake yamma da gidan Alhaji ibrahim wanda yake gidan kaninsu kuma autansu Alhaji MAMMAN
Matarsa daya hajiya muna,basu wani dade sosai da aure ba dan duka duka basufi shekara biyar ba sannan Allah bai basu haihuwa da wuri ba ,
Diyarsu daya Habiba yarinya yar shekara uku,

Sai sashen baki wanda sau tari hajiya karama ce ke yawan sauka cikinsa,
Yarinyar dan uwan Alhaji salihu ne da ya raina tun yarinta,marainiya ce uwa da uba,itace binyamin yake hannunta,  sai sashen da yafi ko ina girma wato sashen Alhaji babba da matarsa hajjo,iyayen gida kenan .
Kowane sashe dana lissafa maki yana da mahadimta biyu biyu.
Dan Allah zainaba ki kiyaye yarda zaki zauna lapia saboda zama lapia yafi zaka dan sarki,
Karki bari wani abu ya hadaki da hajiya fattu ta bangaren mijinta ,
Yasunan yarinyanki inata surutu ban tambaya ba .?

DEENAH ,
Sunana deenah mama kaltu,
Dariyar jin daɗin sunan da deena ta kirata tayi tace Yarinya mai hankali,
Allah ya miki albarka ,yarki na da nutsuwa ta maida maganan kan zainaba ,
Yaran gidannan binyamin kawai ne baya kiran sunana amma kowa kalthume basu duba girmana kuma iyayensu basu hanasu,tun abun na damuna ya dawo ya daina dan na fahimci matsayina na mai aiki ne sannan maine dan sunce ma kalthume din tunda dai iyayensu na mutuntamu ,kedai Allah ya bawa kowa rabunsa na alheri.

Ameen suka fada a tare.

A hankali suka fara gudanar da rayuwarsu cikin gidan na maikuɗi,
Sosai zainaba ke takatsantsan wurin ganin ta kiyaye abunda hajiya fattu bataso wato kula mata miji,
Yauma kamar kullum bayan ta gama aikace aikacenta ta fita a Ɗakin dan zuwa cin abincin rana,
Bata tarar da deena a dakinsu ba sannan babu mama kaltu,
Bata shiga ba ta fara neman deena a cikin tamfatsetsen gidan da in bakasan kansa ba sai ka bata aciki ,
A chan babban basketball field din dake gidan ta hangota zaune kan swing ,
Karasawa gareta tayi tana mai sakin ajiyar zuciya ,
Zama tayi gefenta tace "deenahn mami nan kika zo kika zauna ashe mami ke chan tana faman nemanki ,to taso muje muci abinci ko,
Kallan zainaba tayi da wata irin fuskar tausayi kafun tasa kuka tace "
Mami dan Allah kisani a makaranta ,yau bakiga wulakacin da yaran hajiya fattu ya mun ba gaban abokansa harda cemun jahila kuma mami ya dinga zagina da turanci noset kawai na dauka aciki,
Dan shiru zainaba tayi tana mai jin takaicin yaran dan ta kula duk yaran gidan yana kan gaba wajen fitsara da rashin ta ido a haka kuma mahaifiyarsa na kallo ,takan tsawatar masa amma fa ita kadai bata yarda wani ya tsawatar masa ba,
Shafa kanta zainaba tayi tace wannan ne kadai matsalarki?

Kada kai deenah tayi"eh mami"
To karki damu insha Allahu zan saki makaranta .

Haka kuwa akayi da yardar uwar dakinta ta samu wata makaranta mai dan kyau ta gwamnati ta sata dan karfinta kenan a yanzu,
Haka nan deenah ta fara zuwa makarantar ba tareda ta damu da irin chin kashin da su azad suke mata ba,

Kamar kullum zainaba ta tashi da sassafe da taimakon mama kaltu ,
Gefenta taga babu deena wanda ya tabbatar mata da ta shiga bayi,
Bayan lokaci kankani sai ga deena ta fito tana rawar ɗari,
Kallan yarda take karkarwar zainaba tayi tace ke kam deena baki jin magana nace maki ki daina wankan sassafennan ,wane ma zai gane bakiyi wanka ba idan kikayi kwaskwarima dinki kika tafi makaranta,
Zama deena tayi tana shafa mai tace mami harda duban wanda baiyyi wanka ba fa ake ,
Nikam banasan amun wulakanci kan abunda nafi karfinsa gwanda kawai nayi wankana ko mama kaltu,
Murmushi mama kaltu tayi tana mai jin san deena har ranta tace wannan haka yake deena kiyi wankanki amma fa da ruwa mai zafi,
Haka zainaba ta shiga bayi tabarsu sunayi,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali a cikin gidan na maikudi,
Tunda deena ta fara makaranta yazama babu ma mai ganinta dan daga boko tana tashi abinci kawai take dawowa taci ta wuce islamiyya,

Duk result din deenah da zai fito abun alfaharin zainaba ne ,
Tanajin dadi sosai a wani bangaren kuma tana ji aranta dama zata samu wadataccen kudin da zata saka deenah a makarantar kudi koda ta karamin kudice ,
Ranar suna zaune suna hira da kaltu take tambayarta inda zata samu makaranta mai karamin kudi,

Aji uku take na js yanzu ko?

Eh zainaba ta bata amsa tana jinjina wai yanzu sun kusa shekara biyu a gidan,

Dafata kaltu tayi tace ki kwantar da hankalinki,
Alhaji babba yana bawa yara hudu scholar a babbar makarantarsa dake cikin garin nan,
Makarantan datayi fice kuma ta kunshi shahararrun yaran masu hannu da shuni,
Amma akwai masu hannun jari cikin makarantar wadanda suma akwai yayansu a makarantan cikin su kuwa harda abokan masu gidan ,
Makarantar ta wuce dukkanin tunanin mutum wajen haduwa sannan malaman dake kowayar dasu jiga jigan masu jan kunne ne,
Nasan deena nada kokari to amma ta kara taci na farko a jnr exam dinsu insha Allahu nikuma zan shiga nama hajjo magana deena zata samu shiga cikin wannan shararriyar makaranta ta"
ORCHID HIGH SCHOOL.

Where deenah's new life begin.

Orchid high school.

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top