chapter 36
KALUBALENAH.
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
36.
Kwanci Tashi babu wuya, deenah da maminta sun kwashe wata guda a gidan mimi wanda deenah ta saki jikinta sosai da sabbabin dangin nata,
Babu wanda Ya ƙara mata maganan cikinta wanda a yanzu yake wata uku da satika,
A lokacin da laulayin Ya tashi mata sosai Mami da mimi sun nuna damuwarsu mutuka amma sai suka danne ,
Mimi Da kanta ta kaita Ganin likita ya duba ta ya bata magunguna dan mami cewa tayi bazata je ba saboda tana fushi da ita.
Bayan sun dawo ne mimi ta rakata Har ɗakinta ta kalleta da kyau tace "deenah nasan baki san magana akan cikin nan sannan nima bana san na maki magana akansa but atleast ko dan maminki yakamata ki buɗe baki sannan kinsan dole zaki faɗi wanene uban cikin so why are you doing all this to us ,
Maminki tana cikin Baƙin ciki sosai akan wannan al'amarin musamman idan tana tuna marin da aka mata sabida Ke sau da dama takan yi tunanin ko tafaɗi ne wajan maki tarbiyya,
Kallanta tayi cikin sassanyan yanayi tace "deenah ina zargin wani abu wanda nake tunanin zargina ba kuskure bane amma inaso ne ki faɗa mun da bakin ki and i will fight the world for you,so ki faɗa mun koda kuwa a matsayin stranger ne ba a matsayin uwa ba.
Kuka deena tasa tana Mai faɗin"Mami i was wrong,ban ma kaina kuma ban ma mami adalci ba amma mimi kamar yarda na faɗa cikina wallahi dan halak ne ba shege ba,
Shiru mimi tayi tana nazari kafun tace "kina nufin a da aure kika samu.
Kaɗa Kai deenah tayi alamun eh.
Abun ya daki mimi cos a iya saninta babu wanda yasan deenah nada aure hasalima shine yasa ake faɗin tayi cikin shege.
Gyara zama Mami tayi tace "okay stop crying deenah na ,now tell mimi "what happened".
Cikin fargaba ta fara bama Mimi labarin abunda Ya faru daga farko Har Tafiyar binyamin da Kuma rasa contact da tayi dashi.
Shiru mimi tayi tana nazari, ga wani Mamaki da ya cikata ,ta sani soyayya ce ta saka deenah tafka wannan wautar dan wauta ce karara.
Cikin sheshekan kuka da tsoro deenah tace "mimi dan Allah kar ki faɗa ma Mami sabida bazata iya dauka ba sannan nasan bazata taba yafe mun ba sabida bata taba amincewa da alaka ta da biyamin ba,
Murmushi mimi tayi tana tunanin ta yarda zata bullowa wannan babban al'amarin,
Gyara mata pillow tayi tace "oya kwanta ki huta zamu yi magana saboda wannan maganan babbane and i won't tell your Mami amma ki sani dole zata sani saboda tafi kowa chanchantar ta sani ɗin,amma ba zan faɗa mata yanzu ba sai na gano bakin zaren.
Bayan kwana uku da maganan mimi da deenah tana kwance taga message dinsa kamar a mafarki"Dee where on earth are you?
Ta karanta message ɗin yafi sau ba adadi,
Bayan message ɗin kuma sai kiransa ya fara shigowa kamar bazai dai na ba,
Take wani irin haushinsa da kuma sabon fushin da take dashi ya harzuko mata,.
Ganin kiran nasa Yaki karewa ne yasa ta dauki wayan a kiran da ya kuma na yafi a kirga,
Bata jira abunda zaice Ba Cike da fushi tace "don't you ever try calling me again,
Let me be,idan Kuma ka sake kirana zan maka abunda zamuyi dana sani baki daya ,and set my divorce letter and send it via message sai ka koma gida amminka ta aura maka yarinyar da taga ta dace da kai.
"Dif ta kashe wayanta tasaka wani kuka,
"Da Baki masa haka ba you should have talk,
Daga kai tayi ta sauke cikin na mimi,
Shigowa mimi Tayi tace if i guess right binyamin ne ba?
Kuka ne yakwace mata cikin kuka tace "shine mimi,he used me and dumped me mimi and mamansa have the guts to slapped mami .
Zama mimi Tayi ta jawo kanta ta dora kan kafadarta tace"shush everything is going to be okay,yanzu ki tashi muje mu sanar da maminki abun da ya faru and i will talk to daddy zamuje chan gidan he will have to divorce you indai kinji you're convinced and I'm not saying that what you did was okay, deenah abunda kikayi baiyyi ba kuma baki kyauta Ba,
Kin zaɓi daɗin Bakin ɗa namiji akan maminki wanda kinsan ke kanki Baki kyauta mata ba,and yanzu Gashi you're pregnant kina tunanin idan yace Ba aure tsakaninku sannan shaidunsa ma suka faɗi haka kece a ruwa fa,
This is your mistake so learn from it.
So?
Sniffing tayi tace"im ready mimi ,na shirya faɗa ma mami da su daddy ,cikina na binyamin ne sannan we got married ,ammar da ihsan Da kuma malamin sune shaidata ,
I want to see yarda amminsa zatayi da wannan gaskiyann.
Shafa kanta mimi Tayi tace oya share hawayenki ,as far as sun sani it dosent matter your mami is here ,im here and your grandparents are here,your whole family as a team so ki kwantar da hankalinki, ko sunki mu zamu rike kuma mu kula da abunda kika haifa ai namune.
...koda Mami taji maganan auren deenah ba karamun razanata abun yayi ba cos bata taba tunanin young deenah ɗinta zata iya bin wani namiji ta aurensa Ba batare da ta sanar da ita ba,
Kuka sosai deenah ta saka a lokacin da Mami ke faɗin bata kyauta mata ba sannan bata kyauta ma kanta ba,
Hakuri ta ɗinga bata akan hakan da ta aikata amma mami tace ta rabu da ita dan abun ba karamun dukanta yayi ba ,
Haka zalika koda aka sanar da su daddy abun ya mutukar girgizasu dan Har karamun faɗa sai da daddy yayi mata amma kuma da yayi wani tunani sai ya bama zuciyyarsa hakuri dan abunda tayi yafi da ace ta aikata barna.
Daddy ne ya kira grandpa dan Ya sansa sosai shiyasa koda yaji binyamin ɗan wanene yace abun zaizo masu da sauki.
A ranar suka duguntsuma suka nufi MAI KUƊI mansion,
Kasan cewar Mai gadin yasan da zuwansu yasa ya buɗe masu a lokacin da sukayi horn ,
Babu abunda kirjin deenah yake illa dukan tara tara a lokacin da suka shiga gidan ,
Iso aka masu zuwa babban guest room ,
Tunda suka shiga deenah bata ga idan da ta Sani ba wanda hakan yayi mata daɗi,
Basu dauka lokaci Mai girma Ba grandpa ya shigo yana mai dogara sandarsa,.
Guri ya samu yana mai faɗaɗa fara'arsa amma a lokaci ɗaya he was confused da yaga falon dauke da ahalin Alhaji NA'Abba ciki kuwa harda mami da deenah wanda bai san Mai ya Kawo su ba ko ya haɗasu.
Bayan sun gaisa ne daddy yace"Alhaji Ai maganan nan ta dangi da dangi ce,Dan abunda ya Kawo mu ya shafi mutane da dama a gidan ka ,kagan na farko ya shafi jikanka Binyamin shi yamafi shafa ,sai iyayensa da duk wani babba ma a gidannan dan maganar bata mu da kai bane kaɗai.
Da mamaki grandpa ya Kalli daddy kana yace okay Babu damuwa bari na umarci kowa ya hallara Allah ma kuwa yasa shi binyamin din jiyan nan da dare ya sauka gidannan.
Cikin kankanin lokaci kowa ya hallacci gurin ciki kuwa harda auntyn binyamin dake states da suka zo tareda ihsan da taje hutu gunta.
Tunda ya shigo yake kallan deenah,
Itama ɗin shi take kalla Ganin yarda ya wani lalace Baki ɗaya ,
Mamakin abunda ya haɗata da MRS MAIKANO yafara,
Koda ya dawo gidansu Ya fara sauka ,yayi mamakin da yaga gidan a kulle ,koda ya bude ya shiga take yaga alamun gidan ya kwana biyu babu kowa a ciki so kai tsaye ya wuce gidansu dan yasan definitely tana chan ,
Amma nan ma ga mamakinsa bata nan ,koda ya tambayi mama kaltu sai ce masa tayi sun bar gidan ita da maminta amma sai bata faɗa masa dalili ba ,shima gudun kar tayi tunanin wani abu ,yasan babu wanda ya isa ya tambaya ,hajjo ce kaɗai ita kuma tunda ya dawo bata gidan taje unguwa ,a lokacin da ta dawo kuma dare yayi ga a daren yana ta gwada layinta amma baya shiga,
Sai da safe ne ya tura mata message sannan ya fara kiranta amma taki dauka ,
Yaji mamaki a lokacin da ta dauka tana faɗa masa maganganun da yaji Kamar an soka masa takobi a zuciyansa,a magananta ya tabbatar masa akwai damuwa amma ya rasa wazai tambaya damuwar.
Guri ya samu Ya zauna yana jiran yaji mai ke faruwa,
daddy ne yayi gyaran murya yace Alhaji abu biyu zuwa uku suka kawo mu gidanann ,
Da fari dai ,meet my grand daughter DEENAH,
Yarinyar ɗiya ta Maimuna gata nan zaune ,
Da mamaki kowannensu ya kalli deenah,
Cike da ruɗani ammi tace "tayaya tazama jikarka ?
Hala da aka koresu daga gidannan gun wani malamin sukaje ya jefa masu fatsarsu kan babban kifi amma idan ba haka ba wanne magana ne wannan,dukkan mu babu wanda baisan matsiyata bane jinin karuwai.
Kala nan hajiya mardiyya "deenah ɗiya tace ni nahaifeta da cikina sannan a iya saninki dani baki taba jin inda aka kamani ina karuwanci ba haka zalika maminta da kika daga wa hannu kika mara wanda muna nan zuwa kan batun sabida ba tsoranki ne ake ba ,ai talauchi ba hauka bane sananan da kika tsinci deenah cikin talauci bashine ya maida ta less human ba sannan a yanzu ina Mai tabbatar maki da ita ɗin irin arzikice sabida last dana tuna baki fini dukiya ba.
Mimi ta faɗa ranta a mutukar Bace dan a harzuke take da ammi.
Mari ?
Grand pa ya Maimaita dan bai san Anyi ba,.
Daddy ne ya katsesa ta hanyar faɗin "muje kan babban abunda ya kawo mu Alhaji wannan duk Ai maganan daga baya,
Yanzu maganar da ta Kawo mu magana ce akan cikin dake jikin deenah wanda sanadinsa ya Kawo fitarsu gidannan wanda Allah ya jefa su cikin ahalinsu.
Ciki? binyamin ya faɗa da mamaki.
Eh ciki mimi ta maimaita tana Mai jin haushinsa.
Gyaran murya daddy yayi Ya cigaba yace "eh kamar yarda kuka sani muka sani deenah na dauke da ciki sannan kafun ta bar gidannan sai da ta shaida maku cikinta ba shege bane da ubansa ,sannan da aure aka samesa ,sannan shi wannan cikin jinin gidan nan ne.
Dariya ammi da tafi kowa Baki Tayi tace"tanan kuka bullo kuma kenan,sai ku faɗa muji wake da shi.
Cike da fusatar rainin wayan da Ammi ke masu uncle sultan yace Gashi nan ɗanku zaune binyamin ku tambayesa.
Binyamin?
Baki ɗayansu suka haɗa Baki wajen faɗa.
CHUCHUJAY.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top