chapter 35
KALUBALENAH.
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
35.
Daddy yaso su fito cikin gari ya siya masu gida amma baffa ya kiya a cewarsa baza su iya barin rigarsu ta iyaye da kakanni ba wanda dole daddy ya hakura badan dai yaso ba,
Haka daddy ya nemi a bashi Adda mu tafi da ita yasa tayi karatu ,
Da fari baffa yaki amma daga bisani kuma da su garga suka basa baki akan kwadayin mata ilimin tunda su basuyi ba ,
Haka nan ya hakura Ya bita dafatan alheri,
Shekara ɗaya mukayi a nan jalingo din cikin gari, daga baya kuma muka dawo nan abuja ,
Sosai daddy yake temakawa su baffa ta duk hanyar da zai iya wanda sau da dama baffa kan nuna ya bari haka amma daddy ya kasa dainawa saboda babu abunda zai yi musu ya biya su.
Nan muka dawo abuja da zama ,daga bisani kuma na haɗu da abokin yayana sultan wanda Bai zaman gidan mu ba ,hasalima shi dukkan rayuwarsa na nan abujan koda muke nasarawa,
A lokacin da na hadu da abban farouk Anyi fama dani akan na auresa na sake sabon rayuwa tunda ya nuna yana so na amma na saka kwakwan OTHMAN da kuma abunda na haifa da aka shaidan yanzu babu.
Da kyar dai na hakura akayi auren wanda banyi tsammanin irin zaman lapian da na samu dashi ba ,
A lokacin da na haifi farouk da shekara biyu Allah yayi masa rasuwa,
Daddy yayi na dawo gida amma na kiya saboda nafisan farouk ya tashi gidan mahafinsa dan haka daddy ya bani adda ta dawo gidana da zama ta ciga ba da karatunta wanda a yanzu take aikin jarida .
Kunji yarda tawa Rayuwar ta kasance.
Cike da tausayawa Mami ta fara bata labarin abunda ya faru dasu har da cikin deenah bata boye mata ba,
Taji ba dadi sosai amma bata San a yanzu ta fara questioning deenah dan bata da dama saboda bata santa ba,
Amma a labarin da zainaba ta bata ta dan zargi binyamin tunda ta gansu tare sannan sau da dama shike dropping nata a school kuma su tafi tare and she can sense akwai abu tsakaninsu ,danne abun tayi amma zata jata jikinta a hankali .
Ɗakuna aka basu, babu musu deenah ta karɓi dakin saboda she needs her privacy,
Daki ne Mai kyau ,kayanta ta buɗe wardrobe ta saka gaba ɗaya jakan saboda bama ta da karfin aikin saboda tana san tayi digesting reality din dake gabanta,
A hankali tunanin BINYAMIN Ya fara dawo mata ,
Shin ina ya shiga?
Ko Yama manta da ita ne?
Allah kadai Ya barwa kansa Sani.
Shafa cikinta tayi a hankalin tace "i was really stupid da na yarda da auren da babu kowa nawa da ya amince, amma still banyi dana sanin samun wannan cikin ba dan shine tambarin soyyayata ,bazata kuma nemansa ba indai har bai zo ba ,
Mikewa tayi kan gado tana Tunanin yarda zata cigaba da boyewa iyayenta asalin cikinta.
Ya kamata Ko kowa Bai Sani ba maminta ta Sani dan ya kamata ace ta sani koda kuwa bazata yarda da ita ba dan yanzu Mami ta daina yarda da ita baki daya,
Tana kan bacci taji alamun ana kallanta ,bude idanunta tayi ta sauke su a kanta,mikewa tayi tana mai gyarawa tace MRS MAIKANO?
wani iri taji a ranta,kamo hannunta tayi tace ,deenah bazan ce dole ki karbeni a matsayin uwa ba sannan bazan taba kokarin kwace gurbin zainaba ba ,nice na haifeki amma zainaba ce uwa a gareki dan nasan bazan kai ya ita ba,
Amma still bazan cire ran zaki kirani mahaifiyarki ba ,
Rashin ki wasn't easy and i know akwai wata alaka mai muhimmanci tsakanina dake a ranar da na fara haduwa dake ,
Jikina ya bani ke wata barice ta jikina ,
Ki huta dan in Allah Ya kaimu gobe inasan na kaiki gidan daddy ki ga kakanninki.
Zansa adda ta Kawo maki abinci cos Nasan zaki fin jin dadin ci ke daya.
Tashi tayi tana mai goge kwallar dake shirin zubo mata ,
Tasa kafa zata fita kenan Muryar deenah ta hanata a yayin da tace "MIMI ".
Juyowa tayi dan kamar a mafarki taji abun,
Da gudu deenah tazo ya faɗa jikinta tana mai sheshekar kuka,rungumeta Tayi tana mai jin deenah din har ranta .
Washe gari da safe deenah tafara Tashi a gidan ta fito dan kama Yan aikace aikace domin baccin ma babu shi gaba daya a idanunta,
Ganin farouk tayi zaune yana video game da adda ,tayi mamaki saboda ko bakwai bata karasa ba.
Farouk na ganinta Ya mata alama da hannu yana mai faɗin"sis come over here.
Sis?
Ta maimaita tana Mai Kallansa,
Kallanta yayi yace Uhum,you're my elder sister mimi told me that and i like you,
Ina San na samu sister dama i only have adda and she's my aunty and she's boring and outdated amma ke naga alaman you will be fun,
Kunnensa adda ta kama tace boring and outdated ko its okay zaka zo har inda nake ka sameni,
Dariya suka saka tare inda adda ta kalli deenah tace kinji naughty kaninki ba ,
Its okay bari naje ja haɗa mana kalaci,
Bari Nazo muje deenah ta faɗa .
A'a deenah zauna Ke da farouk karki wani damu Im set,
Bata Kuma cewa komai ba ta zauna kusa da farouk da yace oya sis can you play a video game,
Murmushi tayi tunawa dan abokiyar yinta sabs da kwana biyu basuyi magana ba,
Daukan ps din Tayi tace "i use to play with my bestfrnd and trust me i always beat her up,
Dariya yasa yana Mai dafe goshi,
Yace sis ko elder cousin ɗina wid bragging ɗinta kenan and i always beats her up and inajin dadin yarda nake defeating nata so i really miss her ,tana school .
Umm thats good so lets battle,tunda suka fara take bashi chance ya cinyeta wanda yana ganin yayi winning zai wani ihun murna yana yeeehhh".
Suna kan yin game din mimi ta fito,zama tayi gefensu cike da sha'awan yarda taga ƴaƴan nata suna nishadi,
A tare suka gaidata suka cigaba da game ɗinsu wanda suna hakan mami ma tafito,
Bayan sun kammala breakfast ne suka shirya domin zuwa gidan daddy ,mimi ta kirasu tace zata kawo musu surprise dan haka yayanta ma yazo ,mahaifin nata da yasan surprise dinta bana banzane yasa ya maida abun serious dan haka kafun kace menene ya kira yayan nata da matarsa.
Mintuna marasa yawa ne suka kaisu gidan ,
Farouk ne ya fara buɗe kofan mota ya fita yana mai rugawa gidan da gudu yana mai faɗin "old couples faroukuuu is here".
Dariya deenah tasa jin abunda ya kira kakannin nasa dashi,
Shiga sukayi a tare ,tunda suka shiga idanunsu ke ka deenah musamman da sukaga kamanninta da Mahaifiyar maimuna kamar an tsaga kara,
Kallan su suka maida kan maimuna wadda bayan zamanta Ko gaisawa basuyi ba tace "daddy ,Ummi,yaya meet my daughter DEENAH, yarinyata da othman wadda Alhj Ali marna yace ta mutu alhalin bata mutu ba ,wannan kuma matar othman ce wadda itace ta raini deenah all this while .
A tare suka saka Salati wanda nan take idanun Ummi suka ciko da kwalla,
Daddy ne ya kalleta da kyau kana yace"zo nan jikata zo ,come here and feel your family ,
Wasu hawaye ne suka fara bin kuncin deenah wanda bama tasan lokacin da suka fara fitowa ba,
Da sarsarfa ta Tashi ta nufesu tana mai jinta a wata duniya wadda ta kasa fassara wace iri ce ,
Jikin daddy ta faɗa,
A hankali yake shafa kanta kana ya kalli ummi yace "i told you da dadewa ummin muna,i told you inajin a jikina abunda maimuna ta haifa na raye kuma ko ba dade ko bajima zaizo garemu,yanzu gashi munyi hakuri sannan munyi addua".
Share hawaye Ummi tayi tace 'haka aka yi,Allah kuma da ya Tashi hukuncinsa sai ya dauke ta gidan marasa mutuncin nan,
Babu abunda zamu ce maki zainaba sai dai Allah ya saka maki da aljanna,
Ke din ba kishiyar maimuna bace ,Ƴar muce kamar ita ,
Ke ɗin yanzu ahalin muce ba ahalin marna ba,kin zama mu mun zama ke ,daddy ka sake ta nima naji duminta.
Yar Dariya daddy yayi yace "kina kishi kenan Allah ya bayyana amaryata ,
Gyaran muryar yayan maimuna ne ya jawo da hankali kowa inda yake faɗin"daddy nima dai a barni na gana da diƴata ko.
To kinji deenah maza je ki gaida uncle Dinki da matansa,
Babu musu tayi gurin da suka zauna dan gaida su,
Mamaki ne ya kamata Ganin mutumin da bata taba zatan ta haɗa iri da shi ba ,
Shima da mamaki yake kallanta dan sarai ya ganeta ,fuskarta fuskace da bazai taba mantawa ba,
Deenah OTHMAN Ali ba ,
Ba Ke ce Yarinyan nan da sukayi case da WIDAD ba?
Da mamaki ta kaɗa kai tace nice ,
Dafe goshi yayi yace OMG"what a small world,
Im sorry my daughter ,kiyi hakuri akan dukkan abunda ya faru a baya,na goyi bayan WIDAD without knowing that yarana biyu ne a tare,i knew about how she constantly tortured you amma nayi shiru sabida ita din ƴata ce which i know i shouldn't have done that.
Shiru dakin Ya dauka dan dukkansu suna da labarin Yarinyar da WIDAD ke bullying a school .
Share hawaye Mami tayi wadda bama ta da labarin wai deenah nashan wahala a hannun wasu a makaranta,tasani kuma deenah tayi shiru ne gudun kar ta shiga damuwa amma still da ta faɗa mata.
Karfin gwiwa deenah ta hada tace "uncle its okay ,ni komai ya wuce a gurina sannan ni ban taɓa rike widad a raina ba ,ban taba jin na tsaneta ba duk da kuwa na tsani actions nata da halayyarta amma yanzu i have a big reason not to hold grudges against her.
Haka kowa a gidan Ya dinga kokarin nunawa deenah da maminta soyayya ,
Kwana sukayi gidan Alhaji NA'ABBA daddyn maimuna wanda ya ɗinga bata labaran kuruciyar Maimuna.
A lokacin da ta sanar da sabs dangantakar ta da WIDAD bakaramun mamaki sabs tasha ba ,so deenah is her cousin's ,cousin , already dama deenah yar uwa ta dauketa,
Koda sabs ta sanar da widad batace komai ba dangane da abun amma a cikin zuciyarta sai take jin kunyar komawa Nigeria tayi facing auntynta mafi soyuwa a gareta gaskiyar ta jitane wani iri and she's getting hard to digest it.
CHICHUJAY.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top