chapter 34

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

34

CHUCHUJAY✍🏽

Tunda suka fita a gidan babu wanda yace ma kowa komai,
Bangaren deenah ji take kamar ta rungume Mami tace mata Mami ga uban cikina kuma aurene mukayi ,Amma ta sani shime gaman babu kyau.

Tsaye ammi tayi bakin titi zuciyarta na mata wani irin kuna ,
Tana da isashen kuɗin da zata kama masu gida Dan ko kan su fito hajjia fattu saida ta bata isassun kudi sannan ta tabbartar mata da idan har tana san wani abu ta kirata zata taimaka mata,
Sosai Mami taji daɗi tana Mai kara jin hajiya fattu har ranta,
Kaltuma tayi tayi ta karɓi wani abu a hannunta Amma Taki Amma ta mata alkawarin duk inda ta nufa zata kirata,
idan takama gida Mai zasuyi?
Bazai iyu ace sun zauna sun sa kuɗin da suke dashi gaba ba sun cinye ga kuma dawainiyya dake kansu dan ko ma menene bazata taba bari deenah ta zubda cikinta ba ,
Karshe dai ta yanke shawarar su bar garin baki daya su koma gari mai saukin rayuwa,
Zata fara tafiya kenan wata mota ta wucesu inda daga bisani kuma sai tayo baya a hankali ta tsaya dai dai gabansu ,
A hankali a ka sauke glass ɗin motan inda idanun deenah suka sauka cikin na MRS MAIKANO da yaranta farouk a gaban mota ,
Fitowa tayi tace deenah?

Dan murmushi deenah tayi tana Mai faɗin ina wuni,
Kallan mami tayi cikin girmamawa tace hala mamin Kice.......
Shiru tayi takasa karasa maganan da take da niyan yi a lokacin da idanunsu suka sarke,
Cike da mamaki da kuma kidima Mami ta kalleta cikin wata irin murya ta rashin tabbatarwa wadda ke dauke da alamar tambaya tace "MAIMUNA?.

Cike da mamakin itama tace ZAINABA?
Kece ko kuma mai kama da itane?

Hawaye ne suka taru a idanun Mami wadda bata kaiga amsa ta ba ta faɗa jikinta wanda gladly ta mayar mata suka sa wani kuka a tare,

Gefe deenah ta tsaya da mamaki kafun cikin tashin hankali ganin abunda ke faruwa a gabanta tace "Mami meke faruwa ne ?.

Raba jikinsu sukayi inda Mami ta kama hannunta dan san ta tabbatar da ita ɗince ba mafarki ba saboda tabbas Maimuna ce a gabanta ,tasan hakan saboda koda kuwa nan da shekara masu yawa wanda sukafi hakane taga maimuna to tabbas a kallo daya zata ganeta,

Cike da wata irin murya wadda bata misaltuwa MRs Mai kano tace ina zakuje hakan ?

Share hawaye Mami tayi tace maganace Mai tsayi wadda ba ita ke gaban mu ba yanzu,
Ina kika shiga tsawan shekaru masu yawa haka?

Ajiyan zuciya tayi tace labarine Mai tsayi ,yanzu kizo muje gidana zakiji komai.

Ita dai deenah Yar kallo ta zama ,tayi mamakin yarda suke magana wadda ta kanta ta tsinci kanta cikin duhu,
Idan kunneta da idanunta basu jiye mata da gane mata karya ba to mamin ta tasan MRs maikano, Sani kuma bawai na fisha ba ,amma kuma tambayar dayace ,ina suka san juna kuma wacece MRS maikano ga maminta?
Rasa wanda zai bata amsa tayi dan haka tashiga bayan motar kamar yarda maminta tayi dan san jin amsoshin tambayoyinta,

A bakin wani katafaren gida suka tsaya,
Da kanta ta fita ta bude gate dan shigar da motanta wanda hakan ya bama deenah mamaki,dama akwai masu kuɗin da basu da gate man?

Shigar a motan tayi cikin tanfatsetsan harabar gidan inda direct tayi bagaren da aka faka motoci biyu masu tsadan gaske ta faka wadda suka shigo da a Gefe,

Kallan yaran kusa da ita tayi tace "farouk oya buɗe ,
Babu musu yaran ya bude yana Mai faɗin Allah yasa dai Adda tayi mana abinci mai daɗi cos mimi im starving for real,

Dan murmushi tayi ta shafa kansa ,
Dan murmushi deenah tayi tana mai kallansu cike da sha'awa,

Koda suka fito ta masu jagora zuwa cikin gidan,
Gidane wanda ya hadu iyakar haduwa ,
Kana shiga bama sai an faɗa maka  kuɗi sun zauna a gidan ba ,

A falo suka zazzauna ,da gudu farouk yayi ciki yana Mai kwala kiran adda a bisa umarnin mahaifiyarsa,
Kallanta ta mayar kan Mami tace "zainaba shekaru masu yawa.

A lokacin da na saka amun binciken ki a kan tudu shekaru goma da suka wuce nayi bakin ciki da aka kawo mun labarin wai Allah ya maki cikawa ,
Ke kadai ce dama ke raina a garin sai kuma othman wanda idan na zauna na tuna baku sai nayi bakin ciki mutuka,

Sallamar adda ce ta katsesu,
budurwace irin manyan yan matan nan da suka jima ba suyi aure ba,
A hankali ta Tako Har inda suke hannun farouk cikin nata ,
Zama tayi ta gaidasu Baki daya inda Mami da maimuna suka amsa deena kuma ta gaidata sanin ta fita,

"Mimi munyi Baki kenan ,ina kuma kika samu Mai kama dake hakannan sosai?
Adda ta tambaya lokacin da idanunta suka sauka kan na deenah.

Wani faduwa gaban maimuna yayi jin abunda adda ta faɗa".
Kallan mami tayi wadda tayi kokarin goge hawayen da suka zubo mata da ta tuna fa ba itace ta haifi deenah ba ,tasani ko ba dade Ko bajima maganan zai fita deenah ta sani amma bata taba kawowa akanta ba cewa ranar kusa take,
Ta kanji a ranta maimuna na da rai amma idan ta tuna tana kan kila wa kalane sai ta danne abun a zuciyarta ,
A yau ranar tayi daya kamata deenah tasan komai,
Cike da bayyana murna Mami tace"dole dama kaga ƴa tana kama da mahaifiyarta koda kuwa ta jini ne,
Eh Maimuna deenah ɗiyar kice ,
Yarinyar da kika haiface DEENAH.

Da karkarwar Baki maimuna tace yarinyana ,jaririyane ce deenah?
Dama bata mutu ba?
Daddy yace mun ta mutu?.

Take wasu hawaye suka wanka mata fuska inda ta kurama deenah idanu wadda itama ta shiga cikin kidima da tashin hankalin abunda ke faruwa".

Tashi tsaye deenah tayi tana Mai kaɗa kai idanunta na Kawo ruwa tace"Mami dan Allah kar ki hukuntani ta wannan hanyar sabida cikin dake jikina ,wallahi mami cikina ba shege bane,kar abunda na aikata ya zama silar da zaisa ki datse alakar dake tsakanin mu ta ƴa da uwa ,Mami  dan Allah kiyi hakuri ki tashi mu tafi,

Ganin yarda ta ruɗene yasa Mami Jawota cike da tsausayin ta da kaunarta ta rungumeta sosai a jikinta tace shuush ,deenah ki nutsu .

Tashi adda tayi ta kama hannun farouk da ta fahimci abun babbane suka bar gurin,

A hankali Mami ke shafa bayanta inda   take faɗin "deenah ki nutsu,laipinane da tun farko ban faɗa maki ba ,ada nayi tunanin rashin amfanin haka amma a yau lokaci yayi da dole ki sani,
Bani na haifeki ba,itace aynahin Mahaifiyar da ta kawo ki duniya ,
A ranar da ta haifeki ta bace ,iyayenta sunyi nacinki amma daga karshe mutanen gidan suka shaida masu kin mutu inda suka gargaɗeni akan nayi shiru wanda soyayyarki da tsoran karna rasaki yasa banyi magana ba ki yafe mun diyata".
Ɗa sheshekar kuka Mami ta karasa maganan ,

Kuka deenah take wiwi saboda wannan gaskiya ce mai ɗaci a gareta dan ita a rayuwata bata san wata uwa ba da ta wuce maminta ,rana tsaka babu ma yarda za'ayi a zo akawo mata wata ace wai itace mahaifiyarta,take abubuwan yarinta suka fara dawo mata da gorin da akan ma Mami akanta wanda ita bata gane komai.

Kuka sosai maimuna ta Saka tana Mai jin kaunar deenah har ranta,ta Sani dama zayyi wuya deenah ta karɓeta matsayin uwa saboda a shekarunta na duniya zainaba ta Tashi ta sani a matsayin kowa nata,
Ita kanta she is not asking for much,tasani bazata taba iya rike gurbin zainaba ba a zuciyar deenah.

Cikin wata irin raunanniyar murya tace "na sani bazan taba kamo matsayin zainaba a zuciyar ki ba ,ba guduwa nayi ba,a ranar da na haifi deenah babu abunda nake tunawa illa haihuwarta ,nabar gidan da dare sannan ina tunawa an buɗe mun kofa ne ance kawai kije wanda a halin yanzu bazance wanene ba,
Tunda na fita nake ta tafiya ba tare da nasa ina zani ba nayi tafiya Mai tsananin yawa ,
Bana cikin hankalina kawai dai ina tafiya ne kamar wadda ake aikawa ,
Tafiyar da nayi kina kalla kinsan hankali baza dauka ba ,nasha wahala mutuka,
Ina cikin Wannan tafiya wadda taki karewa ne na Faɗi saboda azaba ,ban sake sanin halin da nake ciki ba ,
Sai da na dauki wata guda a kwance kana wata safiya rabar asabar na farka .
Bansan inda na ganni ba a zabure na Tashi ina kalle kalle inda jikina da ruhina da wata murya akaina take faɗa mun nayi gaba ,na Tashi na tafi ,
Tashi na keda wuya wata dattijuwar mata ta shigo dakin fuskarta dauke da fara'a tace "bako ya taci,
Daga magananta da kuma shigarta zaka gane bafulatanece ,sai a lokacinne na kara lura da dakin da nake mai zubin bukka,
Fita tayi tana Mai kwala ma baffa kira wanda babu bata lokaci shima ya shigo yana Mai murna yana fadin"bako Shannu ,miyetti Allah kataci yaro ka bammu soro aradu sosai ,watanka daya a hutu ,
Kafanki ki ma she godia yayi cau ,

Kallan kafata nayi sai a lokacin na kula da taban raunika da take kunshe da ,
Tafiyar danayi ce tasa kafafunta faffashewa,wadda na dade kafun na kara takawa.
Cike da rauni Da tsoro nace ina nake?
Tafiya zanyi ,
Babu abunda kawai nake Faɗi sai tafiya zanyi,
"Nafaɗa maka boddi yaron nan ba cau ,ba cau ,an mashi kucci ne ,aradu shi anka mashi".

Zama baffa yayi yace "yaro nan kana rigan laddi,
A nan shiyan jalingo,
Chan nagano ka shume zani kiwo ,Allah yaca da sauran numfashi gaba garga da ba-petel sukance a kawoka jida kana san taimako wannan.

Ayi kamar ba Ayi ba ".

Suna cikin haka garga da ba -petel suka shigo matasa samari guda biyu masu kama ɗaya wanda daga bisani na gane yan biyu ne,

Mutanen kirki ne da suka kula dani kamar tasu duk da basu sanni wacece ba ballantana daga inda nake ba wanda cikin wani ikon Allah bani da bakin faɗa duk da kuwa ina sane amma a duk lokacin da nayi yunkurun faɗan wacece Ni sai na kasa ,
Nayi yunkurin guduwa sau babu adadi suna kamoni ,
Da taimakon Allah da taimakon baffa wanda Ya duku fa wajen mun magani inda da taimakon Allah na warke ,sai dai fa nakasa faɗan wacece Ni wanda haka ya dameni mutukar gaske ,
Tabbatar mun baffa yayi akan xan faɗa amma zai dau lokaci dan asirine mai wahalar warwarewa wanda aka mun amma a sannu zan warware,

Haka nan na sake sabuwar rayuwata da baffa da badɗo da yaransu uku ,garga ,ba-petel da yar kanwarsu adda,har naci shekara biyu tare dasu,
Hakannan Nakan bi baddo da adda tallan nono cikin gari ,
Wata rana mun fita Kamar wasa adda da badɗo sunje mana cefane wani dattijon mutum yazo siyan nono gurina ,
Yana ta kallona nima ina kallansa kamar na sansa amma narasa inda nasanshi,shi nasa kalla yana mun kallan sani ne amma yana tantama ni dince sabida sak na koma bafulata da kuma shigarsu,
Tunda na koma gida nake Tunanin wannan mutumi,
Bayan kwana uku ina zaune garga na bani labarin barkwanci ina dariya duk da kuwa banjin daɗi  dan ranar bansamu fita ba ma badɗo da adda kawai suka fita.

Yana kan Sani dariya baffa da garga suka dawo daga kiwo suma suka zauna muka dora daga inda muka tsaya,
Ina mutukar kaunar ahalin dan a lokacin sune ahalina,kwatsam sai adda da baddo suka shigo da sallama bayansu kuma wannan mutumin na ranar ,
Dukkamu su muke kallo inda daga bisani daddy na ga shigo bayansa kuma Ummi na ,
Cikin ikon Allah suna shigowa na kama sunansu wanda baffa Yace dama shine maganin asirin da akamun ,muddin naga wanda na Sani shaƙiƙina na faɗi sunansa ya kare,

Iyayena sunsha kuka da takaici musamman da sukaji uwar Tafiyar danayi nayi daga nasarawa zuwa jalingo,
Wannan bawan Allah dana fara haduwa dashi abokin daddyne wanda yana barin gun ya kira daddy ya shaida masa yaga mai kama dani a jalingo,

Sosai daddy ya musu abu arziki kamar ba a rabu ba .

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top