Chapter 33

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA .

33.

Wai ni mamin deenah Baki kula da deenah kuwa gaba ki ɗaya ta chanza jikinta Yayi wani kyau ya buɗe wanda ni kallo ɗaya nayi mata na fahimci akwai wata a kasa,sannan ga yan kananan ciwokan nan da take ga amai ba fa laipa ba ,duk da nasan deenah yarinya ce mai hankali da nutsuwa da kuma kamewa amma tabbas ɗan yau ba abun a shaidesa bane .

Da kallon Rashin fahimta Mami ta kalli mama kaltu inda a lokaci guda zuciyarta tayi mata wani irin lugudan masu ,idan ta fahimci inda maganan mama kaltu ta dosa fa kenan deenah na dauke da ciki kenan?
Da sauri takawar da wannan tunanin tana maiji aranta da ace ba kaltu ce ta faɗi maganan nan ba da babu abunda zai hana tayi mata mutukar rashin mutunci na jifan deenah da take kokarin yi da munanan alkaba'i amma a zahiri kuma sai ta danne tace"
Bana tunanin abunda kike tunani shine ,kai bama shi bane kawai dai larurane.

Dafata mama kaltu tayi tana Mai ɗan murmushinta irin na manya tace "na tabbata idan naga mai ciki ina gane ta wannan wata baiwace da Allah yayi mun ,kana ban taba kuskure ba ,ba kuma zan fara kan deenah ba ,
Zainaba deenah yaron ciki gareta dan jikinta da idanunta sun nuna ,idan kuma baki yarda ba ai abunnan na Zamani yawa gareshi ayi gwaji dan shi abunan abun tsoro ne .

Shiru Mami tayi tana tunani tabbas itama ta kula da chanjin deenah amma ko da wasa tunanin deenah nada ciki bai faɗo mata ba dan ta yarda da irin tarbiyyar da ta bama deenah tasan bazata taba mata haka ba koda wasa.

Zan Kawo PT mamin deenah a gwada sai mu tabbatar amma dai tabbas bani tantama,

To kawai Mami ta iya cewa wanda kamar an jefo deenah din haka ta shigo cikin dakin,
Da kallo Mami ta bita daga sama har kasa wanda a lokacinne take kara ganin ƙibar da kuma budewan da deenah din tayi, amma kam indai ciki deenah tayi ta kashe ta,

Zama deenah tazo tayi gefenta tace mamina hirar Mai kuke keda mama ne dan naga yarda kuka ci serious haka akwai magana'

"Eh akwai deenah "
Mami tafada zuciyarta Cike da fargaba kana tace yaushe kika ga jininki na karshe?

Batareda wata damuwa ko tunanin wani abu ba ta ɗanyi shiru kana tace wannan watan ne na biyu amma mami nafi tunanin circle ɗina ne zai chanza shi yasa last month banyi ba dan wani lokacin naji ance yakanyi haka,

Wata kwalla ce ta ziraro ma Mami a gefen kuncin ta tace "deenah ina fatan ba abunda nake tunani bane ,ina fatan kamar yarda kaltu ke hasashe ba ciki gare ki ba ,ko da yake ina zakiyi ciki Bayan baki kula kowa,

CIKI?
Murya biyu ta faɗa a tare ,
Deenah da kuma ammi da ta zo gurin dan neman mama kaltu kan zata tantance mata sabbin yan aikin da zata dauka a sashenta,

A tare Mami da mama kaltu suka juya dan kallanta,
Karasowa ciki tayi tace "biri yayi kama da mutum,ni dama nasan za'ayi haka tabbas ,Allah ya rufamun sannan ya rufama binyamin asiri ,aikuwa wa'adin zamanki gidannan ina mai tabbatar maku da yayi.
Fuu ta juya ta koma inda ta fito,

Wani irin kuka mami tasaka tana Mai faɗin ,shikenan deenah kin gama damu,
Duk irin tarbiyyar da na baki ?shekara nawa ina gina ta sannan a kullum nuna maki nake illar alaka da maza wanda gashi kinyi kunnan uwar shegu da hakan kin jawo mun abun kunya ,
Cikin shege fa deenah.
Wani kukan ta sake fashe wa dashi inda mama kaltu ke faɗin"mamin deenah bafa a tabbatar ba da gaske ki kwantar da hankalin ki ,insha Allahu ma mune mukayi kuskure .

Gashi kina kalla kaltu batace komai ba ,kina kallan idanunta kinsan bata da gaskiya Ai da tana da gaskiya zata kare kanta,

Kasa deenah Tayi da kanta inda kirjinta keta dukan tara tara ga wani hawaye da taji yana mata zarya wanda ita kanta baza tace Gashi na menene ba ,gaba daya harshenta yayi mata nauyi,

Tashi Mami tayi tana Mai hada hanya tabar dakin.

Kallan deenah mama kaltu tayi tace "deenah kiyi magana ,kina dai kallan halin da kika saka mahaifiyarki a ciki ,ki koda karyata maganan damuke zargi ne ko maji dadi amma wannan shirun naki yana nuna akwai damuwa fa ,cikin shegefa.

Ba tare da ta dago kanta ba tace "mama kaltu ni ban sani ban ko ciki ne dani amma kuma koda shine ni cikina ba shege bane .

Da mamaki mama kaltu ta kalleta ,tace cikin ki ba shege bane?
Kenan a zahiri kinaso ki faɗa mun Tunanin mu na kinsan ɗa namiji ba kuskure bane.

Shiru deenah tayi batace  komai ba,

Salati kawai mama kaltu take har tabar dakin tabar deenah wadda sai a lokacinne ta rusa wani irin kuka Mai daci,
Tabbas idan cikine gareta ta kade dan mai cikin ma bata san halin da yake ciki ba sannan ta kudira a ranta bazata taba ambatar sunansa ba koda za a kasheta indai bashine yazo ya fada matsayinta garesa ba,tasani koda tace cikinsa ne babu wanda ma zai yarda da ita dama ace ihsan na nan ne.

Ta dade tana kuka ita kadai a dakin kana ta Tashi ta shiga bayi ta dauro alwala dan yin sallar la'asar.

Gaba ɗaya Mami ta fita hanyarta ,tana kalla mamin na haɗa kayanta da dare,
Ba tare da Mami ta kalleta ba tace ki tashi ki hada kayanki tunda kinyi sanadin da zai tona mana asiri wanda nasan zamanmu gidan nan ya kare sannan inaso kisa a ranki zuwa safiya ki shirya nemo uban shegen cikin da ke jikin ki idan ba haka ba zan baki mamaki.

Washe gari kamar yarda sukayi zato kuwa wuraren karfe tara na safe aka aiko kiransu a fadar grand pa,

Tunda suka shiga kan Mami da deenah ke kasa karma ace na Mami dan ji take kamar kasar ta tsage ta shige ciki ta huta,

Daga chan gefe suka rakuɓe musamman ganin yarda bacin rai ya bayayyana karara a fuskar grandpa domin koda suka gaidasu hajja ce ta amsa amma shi kam Ko kala baice ba,

Mahaifiyar azad ce ta shigo daga karshe wadda itama maganar ta dake ta sosai sannan Gashi a karkashinta suke dole tana ciki tsamo tsamo,

Likitan gidan ne Ya shigo wanda Bayan sun gaisa da grandpa yace masa "yauwa maza Dr maina inaso amata pregnancy tests ne kamar yarda na maka bayani a waya sanann inasan result din ASAP and na jini nake so bana fitsari ba sabida inasan idan na yanke hukunci ya zamana ban shiga hakkin kowa Ba.

Babu musu Ya diba jinin Deenah wadda gaba daya zuciyarta ta kekashe dan ta riga da tasan dole ne ma subar gidan ,dauke idanunta tayi lokacin da suka sauka cikin na ammi wadda ita ta kawo karar a cewanta Deenah zata zama bad influence ga yaransu muddin ta cigaba da zama gidan.

Ba a dauki Lokaci Mai yawaba Dr maina Ya dawo da result din test ,
Cike da hope hajja tace "ahap ni nasan duk maganar nan da kuke shirme ce deenah bata da wani ciki,
Kai maina fada masu da bakinka.

Cike da sagewar gwiwa maina ya mikama grandpa result din yace the result is positive sir,
Deenah nada ciki na wata daya da sati uku,
Kasa Mami tayi da kanta tana Mai jin hawaye suna bin kuncinta daya bayan daya,

Ahap dama Ai na faɗa, ni fa tun farkon haduwa ta da yarinyarnan nasan karuwa ce Allah ne yasa yaranmu sunfi karfinta ,kana kallan idanunta kaga jarababbiya.

Wani kukan Mami ta sake fashewa da shi jin kalmar da ammi ke jifan deenah da su.

Im very disappointed in you deenah"
Hajja ta fada tana Mai matsar kwalla ,
Hajiya fattu kuwa neman abun fada tayi ta rasa ,amma a ranta kuwa ji take babu dadi sosai,

Gyaran murya grandpa yayi Ya kalla Dr maina yace zaka iya tafiya Dr ,
Babu musu Dr Ya wuce inda ya rage daga grandpa sai su mamin da hajiya fattu da ammi.

A gaskiya kin mutukar bani mamaki Deenah, na dauka ke din yarinya ce mai nutsuwa ,koda kuwa wani ya faɗa mun abu maka mancin wannan akanki banni yarda,
Amma wani hanzari ba gudu Ba kamar yarda na faɗa da farko ina san yanke hukunci ne ban zalinci kowa Ba,
Kinsan wani Lokacin mata kan facing rape case so i will ask you this once sannan bana san kiyi mun karya ,
Ki faɗa mun gaskiya were you raped?

Kasa deenah tayi da kanta kafun tace "Grandpa im sorry dana baka bad impression akaina sannan i was not raped cikina dan halak ne ba shege ba.

Wani irin tsaki Ammi tasa tace "ban tuna lokacin da mukaji labarin aurenki ba ,ko kuwa mitsiyatan danginki ne suka Maki aure daga kyauyenku mijin ke bin dare ?
Wazaki raina ma wayau a nan Ko kin ga munyi kama da jahilai?

Dakata ammin BINYAMIN ,this is getting somewhere Bari muji ta bakinta,
Kikace cikinki na halak ne Mai hakan ke nufi, sannan ya akayi yazama halali?
Grandpa ya tambaya .

Cikin kuka tace "ka yafe mun grandpa bazan iya fadan komai ba amma cikina ba shege bane,

Tsam hajja ta Tashi dan barin gurin dan ta lura deenah nasan wasa da hankalin kowa ne, ina mutum ya taba samun ciki sama taka,
Kallan da Deenah taga hajja tamata ba karamun tabata yayi ba saboda ya nuna yarda Deenah tayi breaking mata zuciyarta.

Gyara zaman glass grandpa yayi zaiyyi wata maganan Mami ta Tashi kan gwiwowinta tace "ka yarda damu ranka ya dade amma mun kunyata ka,
Bani da idanun da kuma bakin da zan iya fara magana ,na faɗi wajen bama ƴata tarbiyya mai kyau na dauka laipi nane sannan nayi alkwarin zan dauketa muyi nisa da gidannan sabida kunyar da ta sani naga alamar bata shirya hakura da kunyartar dani haka ba,
Mungode da komai .

Shiru grandpa yayi baice komai ba dan dama koda Mami bata nemi zasu tafi ɗinba zai sallamesu ne dan dokar gidansa ne duk wanda ya karyata Sallama ne,

Jan hannun Deenah Mami ta fara wadda keta faman kuka Mai taɓa zuciya,

Scholarship ɗinta yana nan ban janye mata ba saboda nata ne koma chanchantar ta ne,
Grandpa ya faɗa Ya Tashi da fushi yabar gurin dan basu taba expecting haka a gareta ba.

Suna kokarin fita ammi ta biyo bayansu ta kama hannun mami ta juyo da ita,
Kafun Mami tafarga ammi ta sauke mata tafin hannunta akan kuncinta,
Da mamaki Mami take kallan ammi,

A zabure hajiya fattu ta mike inda Deenah ma ta kalli ammin da mamaki,
Cike da izza ammi tace ,na mareki ne sabida ƴarki da ta ringa kokarin rabani da ɗana wanda Allah bai bata sa'a ba taje chan wani ya ɗirko mata shege ,daganan kuma sai a yi gaba wama ya sani ko ke kika koya mata iskancin .

Da zafin nama Deenah ta kwace hannunta dagana Mami ta shiga tsakaninsu .

Kallan ammi take cike da bacin rai kafun tace"ina ganin mutincinki matuka da wallahi babu abun zaisa na hakura da marin da kika ma mami,
Kinci daraja daya ,
Sannan wannan cikin nawa da kika zagi insha Allahu akwai ranar da zaki yi dana Sanin zaginsa sannan ki rubuta ki aje ni deenah na zamar maki kabewar kan kabar..
Kafun ta karasa Mami ta sauke mata nata marin a fuska kana ta finciketa ta suka fita,

Kallan hajjia fattu ammi tayi tace "kinga ba fattu irin mutanen da kika kwaso mana ,wai harni waccan kazamar yarinyarke faɗawa magana ,
Imagine fa,
Tsaki taja ta fice tana Mai kara jin haushin da tsanar deenah sosai a ranta.


CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top