chapter 3

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

Tofin Allah tsinen da ake binsu da shi bai tsaya a cikin gidan ba sai da suka biyosu waje har ana tara musu mutane dan ƙaranta,
Abun bai kara batawa zainaba rai ba saida taji an fara jifansu ,"wannan wane irin bala'i ne"?
Da kyar suka samu suka kubuta shima dan wani dattijon bawan Allah Alhaji razaki da suke balain jin kunya a garin kasan cewarsa babba kuma mai faɗa aji .
Tafiya suke tayi a kafa don fita babban titi saboda duk wanda suka tsara cikin yan achaɓan cikin garin sun san babu mai daukarsu dan maganar kamar wuta haka taci garin kafun kace me mutane dayawa har sun tsinci labarin,
Tsaye deenah tayi dan dauriyarta ta kai karshe tace mami nagaji wallahi sosai kuma kema nasan kin gaji ga jakar kayanmu da kike dauke da, mu huta mana kuma gashi ina jin yunwa har yanzu kuma ba muzo cikin gari din ba ,
Gefen wata bishiya ta hango ta kama hannunta tace "maza zo muje chan muzauna tunda kin gaji deenahna sai ki huta kadan tunda kince kin gaji nikuma kinga da kaya a hannuna bazan iya daukan ki ba,
Hutu kalilan sukayi kalkashin bishiyan suka tashi suka cigaba,
Basu suka isa cikin gari ba sai daf da ana kiran magreeb,
Kai tsaye suka nufi gidan wata kawarta da sukayi yarinta tare wadda dama tasha bata tayin takawo deenah gidanta amma takiya ,
Bata rasa gane gidan ba wanda yake cike da maza bakin kofar gidan sunata hira gefe kuma ga nan mai awara wadda sunayi suna siya suna ci"
Ta gefen gurin suka raɓe suka shiga gidan bakinta dauke da sallama,
Kallo daya zakayi wa matar gidan dake zaune kan tabarma tana cin abinci kasan kilalliyace ,
Tsame hannunta tayi daga cikin shinkafar da take ci cike da mamaki tace "wanake gani kamar zainaba yau a gidana ni haule bismillah ku shigo mana"
Dan fadada fara'a zainaba tayi tace itace dai zainaba da kika sani haule,
Karasowa ciki sukayi haule na bude musu tabarmar da suke kai tana mai fadin ku zauna dan Allah zainaba,su deenah yan mata zo zo nan mamanki taji duminki,
Babu musu deenah ta fada jikinta duk da bata wani wayeta ba,
Bayan mintina kalilan haule ta cika masu gabansu da abinci da lemo.
Saida sukaci suka koshi sukayi sallah suka huta sannan haule da zainaba suka zauna ita kumah deenah ta koma ta kwanta dan a gajiye take sosai ,
Zaman hira suka fara inda zainaba take labarta mata abunda ya korosu daga garin ,
Gyara zama haule tayi tace "dama ni na dade da sanin kabiru dan akuya ne amma kasan cewarsa mijinki yasa nayi shiru bance komai ba tunda duk ɓacin mijin ka bazakaso wani ya faɗa ba ,
Amma naji dadi sosai da kika kawoni a ranki kuma kikazo gurina ,insha Allahu komai ya kare kiyi zamanki anan har iya irin lokacin da kikeso bazan taba damuwa ba ,
Murmushi zainaba tayi tana mai jin dadi da Allah ya azurta ta da kawa irin haule ,
"Banki ta taki ba haule ,nago
de sosai da irin kaunar da kike nuna mun da kuma tayin da kika mun na zama dake naji dadi wallahi sosai Allah ya bar kauna amma ni da so samune inaso nabar garinan baki daya saboda deenah Mufara wata rayuwa a wani gun ,inasan na bawa deenah rayuwa mai kyau mai inganci,
Bana so ace yau deenah ta fuskanci wani bakin fenti na rayuwa a lokacin da take kawo girma shiyasa insha Allahu gari na wayewa nake san mutafi wani garin duk da har yanzu ban gama yanke shawarar garin da zamu ba .
Shiru haule tayi tace karki damu kawata "
Acikin gari biyunnan ki zaba ni kuma zan kaiki inda zaki zauna,
Abuja ko lagos wanne kikesan zuwa daga nan,shiru zainaba tayi tana nazari kafun tace "ina ganin kamar abujan zaifi tunda kinga arewaci nena nigeria amma kuma naji ance rayuwar garin da tsada kuma masu kudin duk nan suke tarewa kina ganin rayuwa zata iyu mana achan ,
Murmushi haule tayi tace to ai abujan wani bin sunace duk da masu kudin namu duk suna chan amma fa akwai unguwanni na talakawa inda zakaje ka zauna hankali kwance amma dole fa sai kayi sana'a kuma nasan ke dai banda matsala dake indai kan sana'a ne ,zan kaiki na kuma baki jari ,akwai wata kawata dake zaune a chan tana da gida kuma hayane take sawa a gidan zan kaiki insha Allahu ki shirya zuwa gobe muje dama ina da zuwa abujan,
Godia zainaba ta fara yimata babu kakkautawa inda take faɗan mata tana da yan kuɗi da jarin bazai zamar mata matsalaba "

"Duk da haka dai zan kara maki yan kuɗi ,nifa nan da kike ganina likafa ta bude ne nan da wani satin ma dubai nayi saro kaya.

Yar dariya zainaba tayi tace Kin ki dai kiyin aure"
Sakin baki haule tayi tace "oh ni haule ke yanzu har kin ma manta daya mazan suke kikesan tura ni,ba da haule ba nikam sai nayi kuɗi.

Kada kai zainaba tayi tace haule kenan kina nan da halinki na sai kinyi kudi ai ba kowane namijine yake namijin hofi ba akwai na kirki yanzu misali kiduba marigayi othman duk da dai ya aureni ne badan yana sona na ba amma hakan baisa ya wulakantani ba ,yana girmamani kuma yana ganin mutuncina sannan yana kulawa dani daidai yarda ya kamata to mai mace take nema kuma gurin namiji bayan wannan?
Kedai kawai kiyita addua sai kiga Allah ya kawo nagari ,

Manta kedai kinji zainaba mazannan ni tsoro suke bani amma ta bakin naki Allah ya kawo na garin ameen.

Washe gari sammako suka daka na zuwa birnin tarayya abuja ,
Basu suka isa ba sai da aka kira sallar magreeb kai tsaye gidan kawartata suka nufa wanda ke lokogoma ,wasu madaidaitan gida dake jera iri daya nan suka shiga ,
Wata hamshakiyar mata suka tarar a gidan wadda tana ganinsu ta karbesu hannu biyu biyu kuma faram faram ,
Duk da batasan da zuwan su ba amma hakan bai hanata ciyar dasu da shayar dasu ba,
Bayan sun huta ne haule ta zayyana mata abinda ke faruwa,
Shiru tayi da ta gama sauraren haule tace "to haule nidai zainaba yarda take yar uwarki nima najita a raina kamar yar uwa amma wani hanzari ba gudu ba ,ni da kika ganni nama daina harkar haya dan na siyar da duk wani gidan da nake haya dasu saboda zan bar abuja ,amma akwai wata attajirar hajiya da take neman mai aiki dattijuwa kuma zasu baki gurin zama ,idan babu damuwa mu gwada mana,
Ya kika gani cewan haule".
Shiru zainaba tayi tana tunani kafun tace kina ganin babu matsala da mutanen gidan kinga inada yarinya babu wata matsala,
Murmushi hajja Aisha tayi tace "ni dai bana tunanin akwai matsala dan hajiya mutuniyar kirkice danni duk zamana a garinnan bantaba zama da mata wadda tasan darajar dan adam ba irinta ,bana tunanin zaku samu wata matsala muddin kika rike gaskiya da amana zakiji dadinta ,kuma gidansu babban family house ne da ya kunshi zuriarsu kuma dukkansu mutanene masu wayewa.

Ba tareda fargaba ba zainaba tace ta amince wanda a take hajja aisha ta kira hajiyar ta shaida mata ta samu mata mai aiki inda hajiyan tace ya kawo mata ita washe gari.

Washe gari bayan sunyi karin kumallo hajja aysha ta musu jagora zuwa gidan da zainaba zatayi aiki a nan cikin lokogoma .

Tun a tamfatsetsan bakin gate ɗin gidan zainaba ta tabbatar da su din kauyawane ,
Maigadi ne ya bude musu lokacin da ya shaida hajja aysha,
Kalle kalle zainaba da deenah suka shiga yi ganin manyan gine ginen dake cikin estate din da ya kunshi dukkan family din ,
MAIKUƊI family house kenan hajja aysha ta faɗa lokacin da ta faka motanta a space din baki,lallai kam maikuɗi ,zainaba ta kara tana mai jin dar dar a cikin ranta ,
Bangaren da hajja aysha ta musu jagora suka nufa a tare,wata yarinyace ta fito hannunta dauke da waya tana latsawa tana wani ya tsine,
A shekaru bazata wuce deenah ba wanda hakkan ya bawa deenah da zainaba mamaki ɗan ko ba'a fada masu ba wayarta ne,
Kallo daya yarinyar ta musu ta dauke kai tani wani taunar chewing gum kamar wata karuwa ,
Wani yaro wanda zai iya finta da shekara daya ne ya fito yana mai fadin "oh widad ke kullum sai kin bata ma mutane rai i bet you don't want us to be late yanzu ai and didn't i told you Kar ki zo gida zanzo na sameki.
Yarfe hannunta tayi tana mai cewa "
Azad bafa dole bane zuwa lesson dinnan you can get the fuck out "
tana kai aya ta raɓe ta gefensu har tana buge deenah dake gefen zainaba a rakube.
Tsaki yaran da ta kira da azad yayi ya koma cikin gidan.
Allah Mai Iko Kawai zainaba tafada aranta inda hajja aysha ta musu jagora cikin tamfatsetsen falon.

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top