chapter 23

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

23.

Kai tsaye sashen amminsa ya shiga bayan rabuwarsa da deenah,
A zaune ya tarar da ita tana waya da wata ƙawarta ,
Zama yayi dan jira ta gama ,yana kula da irin kallan da take masa na mamaki ɗan tunda abun faɗan ta da deenah ya chanza sosai a gidan ,

Hanging wayan tayi ta kallesa ,
Gaida ta yayi cikin ladabin sa na ko yaushe ,

Amsawa tayi kana tace "hope I'm safe '.
Yes "ya bata amsa kafun yace "ammi na yarda ni ɗanki ne sannan na yarda kina da dukkan right a kaina amma at times i need to choose what i want sannan nasan ke me san abunda nake so ne so please ammi yau ma nazo maki nan ne akan abun da nake so which is Deenah".
Ammi ina san deenah ,ina mutukar santa har ila adadin da nake ji idan har na rasata zan rasa rayuwa ta ,tsugunnu yayi gabanta yana mai rike hannunta yace "ammi i want this girl in my life dan Allah ammi ki yarda na aureta and ina mai tabbatar maki zaki sota fiye da yarda kike tunanin ,na yarda da hakan sabida nasan wacece deenah ,
Dan Allah ammi kar kice mun a'a saboda ni yanzu amincewar ki kawai Nake nema kafun na sanar ma Abba ,

Kallansa tayi da kyau kana tace kana san deenah ?
Daga mata kai yayi alamu Eh"

Itama tana sanka ne?

Dan murmushi yayi cikin tuna yanayin tata soyayyar ta kunya kana Yace "fiye da tunanin ki ammi ,im positive idan aka raba deenah dani halin da zan shiga zata shige sa ,

Mikewa tayi tace aikuwa zata mutu saboda ban haifeka ba domin na mika ma ɗiyar masu aiki,mitsiyata wadanda ke cin arziki kasan mu ,wallahi babu wanda ya isa ,
Kuma inaso ka Sani muddin abbanka Ko kakanninka sukaji zancen nan na kana wani San aure ta kasa aranka saina tsine maka .

A'ah Ammi "cewan ihsan dake shigowa jin hayaniyan ammin,

Karasa shigowa tayi tace"haba ammi mana abun Ai bai kai nan ba dan Allah,sannan menene aibun deenah ne nikan being a maid is not a crime fa and yaranki ya nuna yana santa why not give them your blessings,

Bazan bayarba "tafaɗa a hasale ,bazan bayar ba dan ubanki ,bari kiji kema duk ranar da kika kawo mun ɗan matsiyata to wallahi haka ne zai faru dake and itama shegiyar yarinyar bari naje na sameta na cimata ita da uwarta kila ta sa ta cire karyar san da take ikirarin tana maka ,

Riko hannunta yayi yana hawaye wanda ya basu mamaki yace "ammi kiyi hakuri kar kije ki cima su deenah mutunci,
Badai maganan ne baki san ji ba naji bazan sake maki ba sannan su abba ma bazasu ji ba .

Tashi ya fice a sashen nata yana Mai ganin wani dumm,
ɗakinsa Ya wuce kai tsaye yaɗan kwanta yana Mai jin damuwa fal ransa
Rumtse idanunsa yayi yana Mai jin kansa na ɗan sara masa ,
Ihsan Che ta shigo kasa cewar bai ma kofar key ba,
Zama tayi a gefensa tace brother kayi hakuri da maganan ammi dan Allah kar kaje ka sama kanka damuwa, buɗe idanunsa yayi ya kalleta Yace sis i love deenah wallahi tsakani da Allah,bansan mai nene damuwan ammi ba ,i want this girl and this girl want me so menene aibun haka?
I choose this girl to spend the rest of my life with" so who's problem is that?

Mai yasa ammi take san kasheni da raina ?
Kwallan da baisan ta ina ma yake fito masa bane yayi tsalle zuwa kan kuncinsa wanda hakan ya mutukar tsorata ihsan and ta yarda da cewa tabbas binyamin yana san deenah.

Lallashinsa tayi sosai kafun ta bar dakin.

Washe gari bai kasa a gwiwa ba ya nufi Gurin Mami dan neman tata yardar amma ga maminkinsa nata fushin ma yafi na ammi dan ita tunaninta kawai zai yaudarar mata yarinyane,
Tunda ya bar gidan a ranar yake walagi a titi yana Mai tuno hawayen da ya gani a kuncin deenah lokacin da mami ke faɗin bata yarda ba ,

Wayansa ya ciro Ya kira best friends ɗinsa da tun yarinta suka Tashi haka zalika har girmansu a states ,
Number sa na states yayi ta gwada wa bai shiga ba so sai ya danna na sister ɗinsa aina dan san jin ko ya sake layine dan tunda ya baro states they hardly get in touch wanda yafi maida sa laipinsa,

Ringing ɗaya aina ta dauka jikinta na rawa dan tana balain san binyamin wanda yake nuna mata Ko in kula ,
Da wata irin murya ta ce hello cike da rawar kai"

Ammar fa bana samun layinsa na states "
Ya tambayeta briefly dan Ya washi rawar kan aina musamman idan yana Guri ,

Cikin wata siga tace la brother meen Ai yaya ammar yau kwanan sa uku a nigeria yanzun nan ma ya tashi a falo muna kallo tare ,brother ihsan fa?

Kashe Wayan yayi ba tareda ya bata amsan tambayar da tayi masa ba dan bashine abunda yasa shi kiranta ba ,

Kallan mamman su tayi bayan ta kashe wayan tace mamma guess who called me ,
Kallanta hamshakiyar mahaifiyarta tayi tace i guess ba sai Nayi guessing ba cos naji kin ambaci sunan binyamin ,
Binyamin ?
Ammar da Ya shigo ya faɗa yana Mai karasowa da saurinsa yace hope baki ce masa ina naija ba cos trust me yana chan yana cika ban kirasa ba da Zan dawo cos that's the first thing i always do,
Dan taɓe baki aina tayi tace " to brother kasani dai i cant control my self gabansa ni kam na riga na faɗa masa ,
Cije lebensa na kasa yayi yace shit "
Aina oh no,
Mamma i have to go ,see you later bye ,
Yana kai karshen zancen sa ya fita yana Mai dialing layin binyamin ɗin wanda take ta ringing yaki dauka ,
Yasan halin abokin nasa Da fushi indai akan alakarsu ne ,

Tashi aina tayi tana Mai faɗin mamma bari na bishi dan dama na daɗe rabo na da ihsan,
Kallanta mamman tayi tace a dai ja aji aina yanzu kina zuwa yasan danshi kika zo,
Dan zama tayi tace Allah Ko mamma?

Ehen ki bari zamuje zuwa na musamman zan kira mahaifiyar tasu nasan she would be more than glad ,
Aje wayanta tayi tace wallahi mamma har fa nafara hakura da shi kiran nan nawa da yayi ya dawo mun da sabon tsumi,
Dariya mahaifiyar tasu tayi tace ,kar ki damu ɗiyata a wannan karan zaki samesa indai kika kwantar da hankalinki kikayi duk yarda nace .

Asalinsu ,
Ammar Buhari asalin yan garin bauchi ne wanda aka haifesu a nan cikin garin abuja ,
Iyayensa dana binyamin abokai ne wanda saboda iyayan ne yayansu suka kulla tasu aminan takar ,
A da ihsan bata da kawar da ta wuce aina amma daga baya gabanin girma sai suka fara baya baya da juna musamman da ihsan ta kula zubin tarbiyar aina ba irin tata bace sannan ga aina yarinyace wadda bata san shawara ,
Mahaifiyarsu hajia Balaraba shuwa arab ce wadda ita kaɗai take a wurin mahaifinsu Alhaji Buhari farouk ,
Yaransu biyu a duniya ammar da aina ,
Basu da tsarin tara iyali da yawa wanda hakan ya faro ne daga ita maihaifiyar su ammar ,
Hajiya balaraba irin iyayen nan ne da idan yayansu nasan abu she will go to any extent dan ta sama musu farin cikinsu ,
A lokacin da aina ta nuna tana San binyamin taso tayi mata fighting akan abun amma daga baya da taga aina ta zama very busy da career ɗinta na modeling yasa ita ma ta watsar da batun ,amma a yau kuwa ta kula soyayyar binyamin ta dawo sabuwa a cikin xuciyar ainanta ,
Kuma ta sa aranta zata sama mata shi a duk yarda take san sa.

.....kamar yarda ammar yayi expecting kuwa binyamin fushi yayi dashi dan yana jin wai ammar na naija Ya juya kan motarsa ya koma gida ,
Dakinsa ya wuce kai tsaye ya kwanta dan Ko cin abinci baya so in fact yunwar ma shi baya ji,
Yana kallan kiran deenah na ta shigo masa waya yaki ɗagawa dan bashi da kwarin gwiwar mata magana a yanzu dan shi kansa bai san ta ina zai fara ba,

Karatun Quran yasa Ko zai ji dan sassauci ,
Aikuwa a hankali ya fara jin zuciyarsa da hankalin sa sun fara kwanciya,
Cikin mintun kalilan kuwa bacci barawo yayi awan Gaba dashi.

Yana tsaka da bacci wanda ya fara masa nauyi yaji kamar mutum na kansa yana kallansa,
Sharewa yayi ya kara gyara kwanciyarsa Ya cigaba da baccin sa ,

1 hour later .

Da salati a bakinsa ya farka duba da sallar magreeb da yaji ana kira ga kuma yunwa da ke nanukar yayan cikinsa,
"Wayyo Allah Ya faɗa a razane ganin mutum zaune a kan couch ɗinsa yana video game,
Tsaki yayi da ya gane ammar ne yace "kai fa ɗan iskane ,
Wama ya baka izinin shigo mun ɗaki nane sannan zaka zo ka zauna mun kasan yarda wannan jar fatar taka keda tsoratar da mutum sannan ace mutum ya Tashi daga bacci mai tsayi yayi arba da ita .

Yar dariya ammar yayi dan ya riga ya saba da irin wannan iskancin da binyamin ke masa akan haskensa wanda shida aina duk na mahaifiyarsu suka ɗauko,
Maido da kallansa yayi garesa yace at least da kaɗan na fika,

A"haba malam f*ck u*.
Kai kasan haskena bai yawa haka ba, yanzu bama wannan ba uban menene ya kawoka i thought kai yanzu baka da mutunci tunda wai har kayi kwana uku a garin nan baka ne me ni ba,

Look here man we are all at fault fa ,kai tunda kazo garin nan ka nemeni ne,?
Ni jikina Ya bani ma kayi wata beb ne da ta ɗauke maka hankali daga kan kowa dan aunty ma tace mun tunda kazo sau uku kawai kuka yi waya,

Hannunsa ya tura kan sumarsa da ta fara Tashi yace man share lemme just have a hot shower na fito muje muyi sallah muje favorite eatery dinmu cos on God im famished .

No"cewan ammar ,inasan naci delicious pasta ɗin baby ihsan,

Dariya binyamin yasa yace "kai fita" ihsan yanzu ta wuce baby sai dai lady i guess rabonka da ka ganta kama manta ,Anya ma zata tuna ka ,dauka dai wayana ka kirata ka faɗa mata in bata komai ta shirya mana garden dining cos eating there would be fun hirar ma zaifi dadi,

Wayan binyamin Ya dauka bayan shi kuma ya shiga bayinsa domin wankan.

CHUCHUJAY

Share fisabilillah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top