chapter 19

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

KALUBALENAH

19.

A wani irin yanayi azad Ya nufi part ɗinsu yana kuka ,
Mahaifiyarsa ce dake saukowa daga sama ta gansa ,
Saurin saukowa tayi tana rafka salati ganin hawaye na bi masa kunci wiwiwwi,
Rikesa tayi ta jijjigasa tana Mai faɗin kai Lapia".
"Ba Lapia ba mommy im sick and i think im dying "
Mutuwa kuma azad na shiga uku Mai ya faru ,
Kaninsa mubarak da suka shigo tareda kanwarsu farhana ne ya fara kuka jin abunda mahaifiyarsu ke faɗin na Wai Mutuwa,
Mommy whats going on".
Nima abunda nake san Sani kenan mubarak ,azad ina sauraranka waya mutu,
cikin kukan yace ,mommy babu wanda ya mutu amma ni zan mutu idan na rasa deenah ,
Wallahi mommy ina santa and i want to marry her".

Wait !wacece deenah ,who's deenah .
Dan tsaki mubarak yayi yana mai rabawa ta gefensu Dan wucewa kafun yace "mommy duk gidannan wacece deenah idan ba so called best friend ɗinsa ba kuma yarinyan mai aikinki, farhana abeg muje na koya miki assignment ɗinchan Bro Abubakar na jirana zamu danyi football match,

"Inajin Mai aikin ma mutum ce and wallahi abubakar let this be the last time da zan maka warning akan kiran deenah mai aiki.

Uhmm lallai brother wai deenah sha shes beautiful .

Wani banzan kallo ya bawa farhana wadda tayi saurin tsallakawa ɗan bin bayan Mubarak.

Ajiyar zuciya mahaifiyarsu tayi wadda bama tasan uban da zata ce masa ba,
Dafa kafaɗansa tayi ta kama hannunsa ta kaisa falo ta zaunar kan kujera ,
Sai da yayi sheshekansa Mai isansa sannan yayi Shiru yana aajiyan zuciya duk tana kallansa ,
Matsowa kusa dashi tayi tayi gyaran murya ta nemo wananan motherly baiwan da Allah yayi mata tace "azad look here,kana kuka ne over nothing,mene wani kana san deenah zaka aureta yarinyan da take kusan tsararka ,kaifa yanzu sa'ar aurenka habiban Uncle mamman ce kaga she's just five itane dai dai aurenka,amma deenah,
Oh come on my kid don't get distracted,
Mu kashe maganan daga ni Sai kai azad please banasan kowa yaji maganan wata deena Dan Allah azad.
Shiru yayi baice mata komai ba amma deep cikin zuciyansa ya gama kudirar niyyar hakan ba abune Mai iyuwaba bazai taba yarda ba koza'a mutu a dawo bazai taba yarda ba shine wanda zai mallaki deenah ba binyamin ba .

........jaraba kawai ammi take tana kumfar baki,ta inda take shiga ba tanan take fita ba almost hours nawa da faruwar Abun amma a yanzu ma dasuke cin abincin dare bata hakura tayi shiru ba,
Aje spoon Abba yayi da karfi yace "wai nikam madam menene damuwar kine kike ta magana guda ɗaya wadda babu wanda yasan tushenta.

Abba kaima dai ka faɗa wanda take faɗannan ma dominshi yaki zuwa yaci abinci and Bai masan tana yi ba ,
"Cike da masifa ammi tace "oya Tashi kibar Gurin nan ,maza dauki abincinki kije chan dakin yayan naki ki karata dama halinku ɗaya ai ,
Dan murmushin ihsan tayi ta dauki plate din abincinta Dan ammi dama ta gargadesu akan kar su kuskura abbansu yaji maganan amma hakan Bai hanata mita ba duk da a faɗan bata fito takamaimai tace ga akan abunda take ba ,

"Alhamdulilah cewan Abubakar,
Tashi yayi tsan badan ya koshiba amma Sai rashin san hayaniyarsa ga ya ga alama mahaifiyartasu yau hayaniya take ji ,
Tashi shima Abba yayi yana Mai faɗin bari Nima na tashi Tunda duka kin koremu dama ina saurine,
Batace masu komai ba ta cigaba da cin abincinta Tana Mai ayyana abubuwa da dama akanta .

Bangaren deenah kuwa bata samu daman magana da mahaifiyarta ba sai da dare bayan sun gama cin abinci wanda yake kamar al'ada suke haduwa su uku suka ci,
zama gefen Mami tayi tace "mamina dan Allah ki yi hakuri kar kiyi fushi dani ,
Wallahi Mami ni bani nasa Yaya bilya faɗan abunda ya faɗa ba hasalima ni bansan abunda yasa ya faɗi hakan ba,

"Kina tunanin ban lura da irin farincikin da kike ba saboda ya faɗi hakan ba deenah ?
Kinaso kijefa Mu cikin matsala ko?
Kin rantse da Allah Sai kin jefa Mu cikin tarkon matar nan ko ?
Mama kaltu gatanan kilan zatafi jin magananki kifada mata wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa ,
Baki mama kaltu ta shiga bama Mami inda take mai kara tunatar da Deenah akan da kiyaye ,
Da kyar suka samu suka shawo kan Mami wadda tsakaninta da Allah take tsoran duk wani abu da zai haɗa ta da ammi...

"Meet me outside the compound "shine message ɗin da ya shigowa deenah cikin wayanta lokacin da ta gama shirinta na zuwa makaranta ,
Dan murmushin jin dadi tayi ganin binyamin ne ya tura mata sakon,amma tuna faɗan maminta yasa ta ma kanta fada ta tura masa sakon
"No ka wuce zan biyo su azad.

"I'm still waiting kiyi sauri"
Ganin reply ɗinsa yasa ta tabbatar da bazai tafi ɗinba,
Harzata fita maminta ta kirata tace "ga kudin mota a hakura da bin su azad dinnan,at least zan iya baki kudi since Alhamdulillah akwai daidai mu,
Bata mata musu ba ta karba Dan ta fahimci Mami daga jiya zuwa yau kiris take jira tace wani abu,

Su azad basu fito ba Dan haka tayi sum sum kamar wata munafuka ta fita a gidan dan zuwa ga binyamin,
Chan nesa da gida ta hango motansa,

Sum sum kamar munafuka takarasa ta buɗe tana waige waige ,
Dariya yasa lokacin da ta shiga motan,
Ɗan kallansa tayi ta haɗe rai tace "
Mene kuma Allah Sai na tafi dama Ai Mami taban kuɗin mota,

Haɗe hannayensa yayi yana mai gumtse dariyarsa yace tuba nake Dee.

Batace komai ba illa murmushin da tayi Dan wannan sabon sunan na Dee da yake faɗa mata dadi yake mata ,
Tada motan yayi yace bari mubar unguwanmu tunda naga alaman tsoro kike,
Badai tace masa komai ba ya ma mota key suka dauka hanya ,

Mintuna kalilan suka kaisu cikin makarantan,
Parking yayi a inda ya ke parking kana ya kalleta ganin tana Mai kokarin bude murfin motan,
Murmushi yayi yace hajjaju Ai ban buɗeba tukunna and i blv bakiyi latti na zuwa makaranta ba so magana zamuyi,
Gyara zamanta tayi duk da tasan maganan mene itama tanaso a yita din,
Gyara zamansa yayi yana Mai facing dinta yace "deenah duk wani abu da na faɗa a gaban Mami da ammi i mean it,ina sanki deenah ,bansan yaushe hakan ya fara ba but all i know shine na kamu da sanki mai tsanani sannan ni bandamu da duk wani abu da mutane zasuce ba saboda ba Dan mutane nake sanki ba dan Allah nake sanki kuma shi shaida nane ,bani da komai bani da kowa a gabana face ke ,
Banso Abun Ya kasance a haka ba hasalima Banso faɗan abunda yake zuciyana ba Har Sai kin gama orchid but i guess muna namu ne shikuma Allah na nashi ,
Sannan soyayyar da nake maki bawai ta wucin gadi bace deenah i want to marry you,
Just look at me am not getting any younger ,i have everything da ɗan adam zai nema a rayuwa but ni ban cika ba idan har ban mallake ki ba deenah,
I will take care of you da dukkan rayuwata ,i will give you a good life ,bazaki taɓa kuka dani ba insha Allahu ,sannan ina mai daɗa tabbatar maki zaki sameni a duk yarda kikeso and ni idan da so nane na aureki kina gama orchid ,but that doesn't mean zan tsayar maki da karatunki ,"NO"
Zan baki duk wani ilimi da kikeso a duniya duk wani qualifications da kikeso kisamu akan ilimi zan tsaya maki ,i will support you and be with you in the journey daga nan har china idan ma chan kikesan zuwa zan biki, yardarki kawai nake nema,
And yes im not forcing you into this idan kinji baki sona ki faɗa mun ,i want to know saboda na sake kara dage damtse wajen zana soyayyata a zuciyarki saboda na gama gamsuwa cewa ni dake are meant for each other so i will never back up ,
Kije ki bama Abun thought and ki dauka dukkan lokacin da zai isheki zan jira.

Wani irin yanayi deenah ta tsinci kanta ,
Kallansa tayi tana Mai jin wata irin kwalla na bimata kunci ,
Bakinta na rawa tace yaya bilya Mai yasa zaka soni?
Baka sanni ba fa ballantana asalina sannan ni ba yar kowa bace ba kuma ni mairaniyace bani da kowa daga ni Sai Mami na wadda itace uwata kuma itace ubana sannan yaya bilya ammi bata sona kuma nasan bazata taɓa sona ba sannan Mami na ma tace nabi a hankali nidai tsoro nakeji.

Kallanta yayi da kyau sannan shi yasani niyarsa game da deenah mai kyauce ,
Dan murmushi yayi yace deenah kina sona ?
Shiru tayi batace komai ba illa kasa da tayi da kanta saboda kunya,
Licking lips ɗinsa yayi na kasa yana Mai rike karan hancinsa cos yanajin kamar He's trying to force her"

Deenah look bazan maki dole ba like i said earlier amma kije kiyi shawara da zuciyarki indai kikaji kina sona ni duk wani abu da kike kira matsala a gurina ba matsala bace,
"Wai ko Dan ammi bata sanki ,ni bai damuna cos ni ina sanki kuma nine zan zauna dake ba ammi ba and I'm very sure she will come around saboda babu wanda zai zauna dake yaji bai sanki,
Sannan about ban sanki ba shima ki ciresa a ranki cos cikin lokacin da na kwashe tare dake nagama sanin wacece ke kuma ke na zaba ,sannan sanin labarinki kece kike da ikon sanar dani ni kuma na saurara sannan duk muninsa babu abunda zai chanza a cikin sanda nake maki ,and duk wani tsoro da kikeji ki daina saboda nidai banida matsala ta wannan fanin tunda ni naganki nace inasanki and nothing will change that.

She was very touched to the extent that ta kasa magana illa kallan window da tayi tana Mai san tare kwallar dake shirin fito mata tace "ni na kusa latti,
Babu musu ya bude lock din motan inda itakuma ta bude ta fice da sauri hartana hada hanya.

DEENAH taji an ambaci sunanta.

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top