chapter 11

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA

11

Kai tsaye part ɗinsu yayi da ita azad na biye a bayan sa zuciyarsa babu daɗi,
Allah yasa ammi bata gidan dan haka ya ajeta a babban falon dake gidan ya maida kallansa kan azad yace,je kira ihsan ta taimaka mata,
"Eh brother I guess tana bukatan mouth to mouth ne,
Rike kugu binyamin yayi yace ina shi yasa nace ka kira ihsan ta taimaka mata ,ko kuwa ni ko kaine wani zai bata sai naji,
Bai kara wani musun ba ya nufi cikin main gidan dan kiran ihsan,
Abubakar ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ,
Kallo ɗaya yayi masu ya dauke kai zai wuce"

Kai zo nan"
Babu musu ya taka dan amsa kiran yayan nasa ,
Allah yayisa mutum mai ɗan banza miskilanci shiyasa baya shiga sabgar kowa dan magana ma shi bawai ta damesa bane,

Mai ya haɗa yayinyar nan da waccan mai kama da mayun"

Licking lips ɗinsa yayi kana yace "bro how should I know,
Widad is always a bully ita nature nata ne so about deenah bansan mai ne tsakaninsu ba  maybe you should ask azad shine dan ajinsu"
Yana rufe baki su ihsan na saukowa inda take faɗin yanzu shine babu wanda ya ko pressing mata chest ta ne cos ta sha ruwa ne kuna so ta mutune ".

Dan tsaki binyamin yayi yace "da muna so ta mutu da baki ganta ba a nan and last i remember she's not our muharamma so why should we touch her boob's ?
Spare us the doctor shit and tend to her  .

Karasowa tayi tana mai bata tamaiko ta hanyar pressing mata chest ɗinta kafun tace "
Last I remember bro bance kutaba boobs ɗinta ba,
Tsaki yayi yabar gurin yana mai cewa azad ya biyosa wanda ya rasa dalilin da yasa yayanasa keta umartarsa da ya biyosa ,
Sai da sukaje compound ya kalli azad din da serious face yace "
What's going on"

Sniffing azad yayi yace brother idk how to put it amma deenah tana shan bullying hannun su widad saboda status nata ,so yau ne widad ɗin tasan deenah suna aiki a gidannan ne so shine da faɗa ya shiga tsakaninsu deenah din tayi backfiring which she never did".
Shiru binyamin yayi yana mai jin wani bakon lamari a cikin zuciyarsa dangane da abunda azad din ya fada masa amma lokaci ɗaya ya danne abun ta hanyar faɗin ,idan da kwadayi ai da wahala mai yasa bazasu zauna a matsayinsu da Allah ya sasu ba ,
Allah ya taimaketa i was fast da tuni ta mutu kaga karshen kwadayi kenan,
Imagine bata iya swimming ba,tsaki yayi yace "Allah ya kyauta kana ya bar gurin.

Binsa da kallo azad yayi yana mai jin rashin dadin abunda binyamin din ya faɗa,
Juyawa yayi dan komawa yaji halin da deenah ke ciki,
zaune ya tarar da ita jikinta lullube da abun rufa wanda ihsan ta dauko mata bayan ta bata dry riga tasa,hannunta kuma dauke da coffee mug,
Zama yayi gefen ihsan dake faman mata sannu yace deenah sannu,

Kaɗa masa kai kawai tayi bata ce komai ba ta cigaba da sipping coffee din,
Ina big Bro din?
Ihsan ta tambaya tana mai kallan kofa,

Ya wuce.

Oh kajifa yayi saving nata yakuma tafi big bro nada moods kaman wata mai ciki,
Shiru deenah tayi tanasan fahimtar abunda suke faɗa wanda zuciyarta ke san karyata mata ba binyamin ne ya taimaketa ba,
Sallamar ammi ce ta katse musu maganar da suke,
Turus tayi ganin su zaune sunsa deenah gaba,

Lapia mai mai'akin nan mara ɗa'a take yi a falona kan kujeru na ,tashi maza tashi tafaɗa tana mai takowa cikeda ƙyama ,
And uban wa ya bata cup ɗin binyamin take shan abu a ciki,
Fizge blanket ɗin tayi ,baki ta saki ganin rigar ihsan jikinta,
Gabansu ihsan ta shiga tace "
Ammi please tafada pool ne shine big bro yayi saving nata ya kawota gurina  and ta jikine so na bata rigana ta cire jiƙaƙƙun,.

Cikeda balai ammi tace aikuwa sai ta cire a kona dan wallahi bazata jawo maki talauci ba dan saka rigarki da tayi tsiya zata iya raɓarki,
Kama rigar tayi tana kici niyar yagawa inda ihsan da azad suka hau kiran sunanta akan tayi hakuri,
Kuka deenah tasa ganin ammin na neman mata tsirara,

Hankaɗqata ammi tayi bakin kofa da karfi wanda ta faɗa daidai kafar binyamin da shigowarsa kenan,
Dago kai deenah tayi cikin kuka ta kallesa Tana mai rike gaban rigan da ammi ta fara yagawa,
Hannunsa sanye cikin aljihun wando ,cikin nutsuwa ya kalli amminasa kafun ya maida kallan kan deenah yace"
Ke tashi ki bace mun a gurin nan,
A kidime ta kallesa ,
Wata tsawa ya buga mata akan ta tashi ta fice a gurin,
da gudu ta tashi ta fice a gidan tana kuka,

Kallan amminsa yayi yana mai takawa gareta,
"Ammi please maine kikeyi haka ma yarinyanan salan ta rainaki cos kinsan yaran talakawan nan da rainin tsiya ,
"Nayi din ka dakeni kaji ubana"
Munafiki kana zaginsu kana taimakonsu ,
Natsani yarinyannan ,wallahi da ace a karkashina take da tuni abicinta ya kare a gidannan ,shegu irin maita,tana kai ayar zanceta ta wuce sama tana mai jin zafi a ranta dan a wuya take dasu deenah tun abunda ya faru .

Barin gurin binyamin yayi ya nufi sashensu inda azad ma ya fita agida while ihsan Ta bi bayan amminsu .

Bangaren deenah kuwa tana fita kai tsaye bangaren su ta nufa,
Tsaye tayi bakin kofar ɗakinsu tana mai saisaita kanta gudun kar maminta ta fahimci tana da damuwa,taji dadi da ta tarar mamin na bacci dan haka kai tsayee ta bude wardrobe ɗinsu ta ciro doguwan rigarta ta material tasaka ta cire ta ihsan ta tura can kasan kaya.

Washe gari bayan ta gama tattara musu ɗakinsu ta kalli maminta wadda taji sauki tace mami bari naje sashen hajiya kaka,
"To sai kin dawo nima bari na tashi naje na dan kakkama aikin da ya rage".

"Mami Ki bari na dawo sai na yi ai tunda jikinki ba wani dadi.

Tashi mamin tayi tana mai faɗin"bari kiga je abunki ni da kike gani haka kwana daya nayi ban aikinnan ba ji na nayi duka ba dadi yanzu kuma Allah ya bani lapia ai sai na koma kan aiki ba,

A tare suka fita ,

Tun a bakin sashen hajiya kakan take jiyo dariyar ihsan tana mai faɗin "wallahi grandma da sake ban yarda ba .
Sallama tayi bayan ta nemi izini ta shiga falon,
Zaune hajiya kaka take a kujera ta mimmike kafafunta ihsan na kasa tana matsa mata inda binyamin ke zaune yana mai daddana wayarsa kamar ma baya jin hirar da suke

Gaidasu deenah tayi inda hajiya kaka tace ma ihsan"
Tashi dama ba wani iyawa kikayi ba gaba daya yaran gidannan baku wani iya tausa ba amma deenah kuwa hannunta Allah ya sa masa albarka"

Oh grandma ma Deenah zata school ne zakiga mai danna maki tsohuwar kafar nan taki .

Ita dai deenah babu abunda take sai murmushi inda rabin hankalinta na kan binyamin wanda still hankalinsa na kan wayansa ,
'Yaya bilya ina kwana,
Ta tsinci kanta da faɗa,

A hankali ya dago idanunsa ya dora akanta da mamaki,
Dariya deenah da hajiya kaka suka saka,
Aje wayan yayi a cinyansa yace ke zo nan.
Matsawa tayi gefen hajja dan ita tama saba da bilya din
nan and batasan lokacin da ta faɗa ba,

Ganin ta makale ma hajiya kaka ne yasa yace "
Hajja ki jama yarinyar nan kunne Allah ta fita harkana,
Kar kuma ta sake cemun bilya ko wani yaya cos we are not related Zan zaneta wallahi,

Kallansa hajiya kaka tayi tace yo wai ni da kike ta kumfar baki ne akan wannan bilya din nace sunanka ne ,mene na damuwa kuma yaya ai girmane aka baka,

Daga chan bayan deenah tace yo ni hajiya idan ma baisan yayan sai na bari na koma yallabai bilya ai ,kuma ni dama godiya zan masa akan taimakon da yayi mun jiya,
Wani tukukin takaici yaji jin ta kara dagula masa suna wai yallabai bilya ,
Bai bi ta kanta ba ya tashi ya fita dan muddin ya tsaya zai iya sabama hajja ma ba deenah ba cos yana balain jin haushin bilya ɗinnan da take kiransa dashi ,in general ma shi baya san tana shiga masa harka saboda dalilai da dama.

CHUCHUJAY.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top