chapter 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
1
A zabure ta miƙe sakamakon sassanyan ruwan da taji saukarsa a jikinta ,
Salati tasaka tana kallan wadda ta jikata da ruwan tace "amma dai salima kina ganin yanayin sanyin garinnan kika zo kika watsa mun ruwan nan mai shegen sanyi da asubar farin nan maye laipi idan kikazo kikace deenah ki tashi asuba tayi?
Jifa da kofin ruwan salima tayi jin muryar mahaifiyarta tace cikin ƙaraji da mamaki"yanzu deenatu fitsarin kwance kikayi wa ladi akan katifa ,
Ince saida tamiki gargaɗi jiya da dare?
Ladi shigo kiga kaniyar da deenatu ta maki,
Kamar guguwa haka ladi ta shigo tana fadin "kan ta balain nan fitsari fa?
"Aradu zo ki duba shine dai ta miki gandar gandar da ita"
Kasa magana deenah tayi sakamakon dukan da ladi ta rufeta dashi tana zazzaginta ta uwa ta uba,
Sai da tayi mata lis lis kafun ta jata ki ta watsar a kofar dakin mahaifiyarta tana mai fadin"
Fito fito zainaba,fito kiga abunda shegiyar yarinyar da kike ikirari taki tamun ,to wallahi daga yau ta daina kwana dakin su salima sai dai kuyi mata guri tsakaninku keda kabiru tana kwana tsakiyarku,
Zainaba mahaifiyar deenah itace ta fara fitowa jin kwarajin ladi kafun mijinta da already dama ya tashi yana shirin fita masallaci ya mara mata baya kafaɗarsa dauke da sallaya,
Kallan banza basu ishe shi ba ya raɓa ta gefen su ya wuce ,
Tsaye zainaba tayi zuciyarta na kuna ganin yarda deenah ke kuka a tsugunne a kasa ,
Bata dai cewa ladi komai ba har ta gama balain ta har tana ce mata barauniyar miji ,
Barinta gurin keda wuya zainaba ta kalli deena tace sai ki tashi ai ko ki shiga ki sake kaya kizo ki yi sallah kiyi shirin makaranta kuma,
Wani kukan mai cin rai deenah ta sake fashewa da tace "wallahi tallahi mami banyi fitsari ba salima ce fa kawai ina bacci tazo ta sheka mun ruwan sanyi a jikina shine tana jin muryar baba ladi fa tace wai fitsari na mata ,
Rabiatu dake labe kanwar salima ce ta fito tace wallahi hakane mamin deenah batayi fitsari ba jiƙata ne wallahi ya salima tayi ,
Dan murmushi mamin deenah tayi tace "toh ai ba komai duk wanda yayi nagari dan kansa ,
Kamo deenah tayi wadda har lokacin bata daina kuka ba tace tashi muje kisake wadannan jiƙaƙƙun kayan kizo kiyi alwala.
Kullum haka rayuwar gidan take kasancewa ,babu wanda ake chima kashi aka kamar deenah da zainaba ,ba daga mutanen gidan ba har ma da me gidan nata ,
Gidansu deenah gidane na zuria mai yawa irin gidannanne da mutane ke ma laƙabi da gidan gargajiya .
Duk fadin unguwar mai suna "kan tudu dake cikin garin nasarawa babu lungun da ba'asan gidan Marna ba kasan cewar gidane irin na gado wanda anyisa ne tun kaka da kakanni.
Marigayi othman ali mahaifi ne ga deenah wanda harkata neman kudi ta fita dashi cikin garin nasarawa inda a nan ne ya hadu da wata diyar attajirin mai kudi a lokacin da ta kawo masa saka iskan taya wanda dama sana'ar sa kenan,
wasa ta maida gurin wajen zuwanta dan othman ya shiga ranta.
Ita ta fara nuna tana sansa ,tun yana zizzillewa ganin tafisa ta ko ina har yazo ya mika wuya dan babu ma yarda za'ayi mace kamar MAIMUNA ta kawo maka tayin soyayyarta Kayi watsi da ita.
Lokacin da mahaifinta ya nemesa da yazo ya gansa ya razana sosai musamman da ya fara shiga tamfatsetsen gurin da suke kira gida ,
Yanayin yarda iyayenta suka Karbesa shine abunda ya kara darsa masa soyayyarta dan sun karbesa ne hannu biyu biyu babu ƙyara babu Nuna shi din kaskantacce ne a gabansu,
Jagora suka nema da yayi musu zuwa ga iyayensa ,
Bai musu ba duk da yasan mahaifinsa malam Ali marna mutum ne mai mugun zafin rai da kafiyar tsiya ,
Lokacin da magabatan maimuna sukaje ma malam ali da yan uwansa na gidan marna da maganar auren ba karamu tirja akayi ba dan su a cewarsu sun riga da sun masa mata zainaba wanda yar uwarsa ce kuma marainiyar Allah dan haka bazasu yi naam da wannan auren ba,
Da ƙyar dai da sudin goshi suma suka nace kasancewar yarsu ta nuna tana sansa kuma babu abunda take nema agurin iyayenta ta rasa dan haka baza a fara akan othman ba,
Sharadai iyayen othman suka kafa masu inda sukace lallai sai dai a daura masa aure da ita maimunan da kuma zainaba a rana daya kuma nan gidan a nan maimuna zata zauna tare dasu basu yarda ya fita da ita ba,
Da fari iyayenta basu yarda ba amma ganin yarda maimuna ta kafe yasa mahaifinta yace yaji ta aminta amma sai ya gyara mata inda zata zauna,
Basu musa ba sukayi na'am inda aka gyara bangaren da sukace nan ne na othman din,basu ware ba har inda zainaba zata zauna,
An Daura auren zainaba ,maimuna da othman wanda suke zama irin na aminci dan ko kadan maimuna bata nunawa zainaba wani abu a matsayinta na uwar gidansa ,itama zainaba din ganin alherin maimuna yasa ta kwantar da hankalinta duk da kuwa yarda take kishin othman wanda daidai gwargwado yana kwatanta adalci duk da kuwa maimuna ce mafi soyuwa a gareshi.
Kasancewar maimuna yar hutu wadda bata saba wahala ba yasa take balain shan wahalar rayuwar gidan,
Da gayya kishiyoyin surukuwarta wadda bata raye da matan yan uwan othman su ladi ke bata kashin wahala musamman gurin surfe da chasa dawa da gero,
Wahala babu irin wadda maimuna bata sha ba hannunsu ,duk lokacin da othman yakai maganar gaban manyansu sai su haushi da faɗa akan yana nuna banbanci tsakanin matan nasa biyu ,
Meye laipi idan ana nuna wa lalatacciyar matarsa da batasan zaman gidan aure ba aikin da ya wajabta "acewarsu "
sau sa dama zainaba kan fito dan shigar mata amma sai su haye mata akan bata da zuciya dama ai"
Kasancewarta mace mara hayaniya sai dai kawai tayi shiru ta kama ma maimuna tana mai bata hakuri,.
A shekara da ta zagayo da aurensu maimuna ta haifo yarinyarta mai kyau mace wadda Allah ne kawai ya rayata dan da cikinta ma bakaramun wahalar su ladi tasha ba dan akwai lokacin da har tabarya ladi ta buga mata akan ciki dan kawai tasata aiki tace mata bazata iya ba dan tayi nauyi sosai,
A washe garin ranar da ta haihu suka nemeta suka rasa ,
Neman duniya othman yayi mata ,tashin hankali sun shiga sosai amma babu maimuna babu alamunta ,
Mahaifinta yayi kuka yayi kuka na rashin maimunatu dan da ace kudi zasu dawo da ita to da tuni ta dade da dawowa amma shiru ko da mai labarinta bai samu ba.
Zainaba ce ta cigaba da rainon yarinyar da ta ci suna Deenah dan tunda ta auri othman ko ɓari bata tabayi ba,
Har ranta take jin soyayyar deenah kamar ɗiyar da ta haifa a cikinta,
Wasa wasa Othman ya Fara jinya wadda aka kasa gane gabanta da bayanta ,
Anyi maganin anyi amma abu yaki ci yaki cinyewa ,babu abunda yake ambata sai maimuna diyarsa da matarsa zainaba,a kullum ka zauna dashi,
Jadadawa ɗan uwansa amanarsu yake yana faɗin kabiru idan bani ka rike mun amanar iyalina,
Jinyar wata biyu yayi Allah yayi masa cikawa.
Haka zainaba ta cigaba da rainon deenah duk da batajin daɗin yarda ake kyararta akan yar amma haka ta danne ta kudiri niyyar babu ruwa ko iskan da zaisa ta bar deenah ta wulakanta .
Lokaci guda zainaba na zaune cikin gidan kabiru ya fito akan yana san aurenta tunda dama shi kanin sa ya bawa amanarta ,
Na'am iyayensu sukayi da abun duk da bata so amma kasan cewarta mace mai kawaici sai ta amince,
Balai gurin matansa ladi da talatu ba'a sa masa rana kar ma ace ladi wadda itane uwar gidansa,
Wahala babu wadda bata sha ba gurin su ita da deenah ,ko ina babu dadi baga kakannin ba baga matan kabiru ba baga shi kansa kabirun ba dan bata taba sanin mugun mutumin banza bane sai da ta auresa.
Zaman gidan take amma zama kawai na hakuri shima saboda deenah ,
Gaba daya dukiyar othman sunyi bankan bankan akai ga wata tsana da suke wa deena wadda ta faro asaline daga mahaifiyarta .
iyayen maimuna sunsha bin didigi akan ɗiyar maimuna amma karshe malam ali yace musu ai Wannan ƴa babu ita kuma ya ja kunnen kowa akan baya san kuma yaji wata magana daban musamman daga bakin zainaba wadda itama tsoro ya hanata magana ,
daga bisani ta tsinci labarin barinsu garin dan an shaida wa mahaifin maimuna an ganta a jalingo wanda hakan yasa sukayi balaguro da sa ran ganinta a garin.
CHUCHUJAY
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top