8

Fitowarta kenan daga cikin gida. Gabadaya yinin ranar a susuce tayi shi tun bayan data dawo daga falon Abba. Batasan dalilin dayasa ta zauna tasha kuka ba ita dai kawai taji wani irin tukukin bakin ciki yayi mata tsaye a makoshi saida tayi kuka tukunna ta samu taji sauki a cikin zuciyarta. Bacci ne ya dauketa dan bata farka ba sai dataji kida ya kauraye ko ina a cikin gidan. Firgigi Batul ta tashi idanunta suna sauka akan agogon dake cikin dakin. Karfe uku na rana har ta wuce.

Cikin hanzari Batul ta shiga wanka ta shirya tsaf cikin kayan da Maama ta basu. Babu kwalliya ko kadan kan fuskarta sai kwalli da vaseline dinta data shafa akan lebenta. Kallon kanta tayi cikin madubi tana mai murmushi. Dukda kuwa cewar murmushin cike yake da wani kalar bakin cikin da ita kanta batasan dalilinshi ba.

Fita tayi tana rokon Allah yasa Maama bata neme ta ba. Amma koda ta nemeta da anzo an kirata har daki. Mutane ne makil a babbar farfajiyar gidan. Duk da girman wajen amma saida ya cika mak'il. Ga wani kalar decoration anyi mai matukar daukar hankali. Ga masu zuba abinci nan sunata aikinsu su kuma masu kida suna nasu. Masu daukar hoto ma haka. Tabbas ita dai hidimar masu kudi daban take, dan kuwa komai yayi kyau kallo daya zakai sai ka maida ido ka kara kallo.

Hango daya daga cikin masu aikin gidan yasa ta lallaba taje wajenta. "Hannatu, Hajia batace ga aikin da zamuyi ba?" Ta furta tana dan daga murya dan kuwa kidan dake tashi a wajen yasa dakyar mutum yake iya jiyo dan uwansa.

Juyo Hannatu tayi tana kallonta tana dan yamutsa fuska. Dan haushinta masu aikin gidan kaf sukeji saboda special treatment din da ake bata a haka. Ita kuwa Batul tasan sarai ba wani treatment da ake bata banda wannan daki da aka raba masu wanda shima aikin Abba ne, dan da Maama nada hali gidan zata bari gaba daya ba dakin ba.

"Babu aikin data saka mu. Tace dai mu jira inda zata rika hangomu saboda in tana bukatar wani abun." Can kasa ta amsata tana wani bata rai karshe ma sai ta matsa daga inda Batul din take tsaye.

MC ce keta bayani tana kara sheda masu yanzu ango da amarya zasu shigo. Kamar ance Batul ta daga ido haka ta hangosu daga inda take a tsaye jikin bango. Kasancewar gate din dama tuntuni a wangale yake yasa suka shigo hannayensu cikin na juna. Gayu kau da tsantsar kyau Yusrah tayi shi dukda fuskarta rufe take da dan net kuma kanta a kasa yake tana tafiya. Fuskar Khalil kuwa wani kalar murmushi ne me matukar kyau kwance. Murmushin ba karamin fito da tsantsar kyawunshi yayi ba.

Daka ganshi ba sai ka tambaya ba kasan yana cikin tsananin farin ciki. Hannayensu dake sarkafe cikin na juna Batul ta kalla tana hadiyar wani abu a cikin makoshinta. Kara kallon fuskarshi tayi charaf kuwa idanunsu suka hadu da nashi. Jingeni take da bangon har yanzu. A maimakon ta dauke idonta sai taji kawai bazata iya ba, kallonshi take gabanta yana tsananta faduwa shima din kallonta yake yaki dauke idonsa. Yusrah ce taga ta dan janyoshi alamar zata Mashi magana, hakan yasa ya cire idanunshi daga Batul ya duka yana fuskantar amaryarshi, fuskarshi cike da murmushi me ban sha'awa.

Tunda Khalil ya hangota yaji wani abu ya dan taba mashi zuciya. Ba sai ya tambaya ba yasan kayan dake jikinta irinshi ne yan aikin gidan Maama ta dinka masu dan ga sauran nan gefenta ma tsaitsaye babu dai wanda ya kulata. Bazaice wai tausayinta ne ya dan taba shi ba amma tabbas ya dan ji babu dadi. Ko dan maganar da Abba ya mishi ne dazu da safe?

Wannan karan ma Yusrah ce ta dan tabo shi wanda hakan yayi nasarar kauda tunanin a ranshi ya juya yana bata gaba daya hankalinshi. Ba karamin kyau ta mishi ba, ji yake shi dama a tashi wannan taron a barshi shida amaryarshi. A takure yake kuma yaken dole yakeyi. Hannun Yusrah dake jikin nashi ya dan matsa a hankali yana tsareta da idanunshi dake cike da zallar kaunarta.

Juyowa tayi ta sakar mashi wani kalar murmushin da saida yaji tamkar ta narkar masa da zuciya ne. "Babe, ya naga kana kallona? Su Maama suna kallon mu fah," ta furta da muryar zolaya tana kokarin zare hannunta. Kara riko hannun yayi idanunshi suna zagayawa dan yaga ina zai gano teburin da iyayen nasu mata suke akai.

"Hankalinsu baya wajenmu. Baki ga kowa abinci yake ci bane? Nima a barni naci abinci na mana," Ya furta cike da zolaya yana magana can kasa cikin kunnuwanta. Koda kana tsaye gefensu ne bazata taba iya jin maganar da Khalil yayi ba.

Juyowa tayi da wani kalar mamaki a fuskarta. Dan ba karamin mamaki bane ya daure mata kai. Koda wasa Khalil bai taba mata wata magana kwatankwacin haka ba. Inma ba daga karshe karshen nan ba koda zasuyi wayar awa biyu duk ita ke surutun yana biye mata.

Dariya takeyi kasa kasa. "Yunwa kakeji?" ta tambaya tana jujjuyawa. Daga mata kai yayi yana tsareta da fararen idanunshi.

Hasna na ce gefensu tazo yi masu video shi yasa Yusrah ta daga kai tana mata murmushi. Da fulatanci ta fara mata magana, "Hasna Hammanku fa yunwa yakeji. Wa zakisa ya kawo mana abinci please? Nima rabona da abinci tun jiya da daddare."

Binta yake da kallon mamaki ita kuma tana mashi dariya kasa kasa. "Bari na kira waccan yaren ta kawo maku." Abinda Hasna ta fada kenan tana wucewa.

"Zakiyi bayani yarinya," Khalil ya furta da muryar kashedi ita kuma Yusrah tana dariya kasa kasa.

Tunda Batul ta baro jikin bango da take jingine tana kallon mutane sunata hidindimunsu, masu cin abinci naci, masu yin rawa nayi, kar ayi maganar masu daukar hotuna. Tunda Hasna ta fada mata abunda zatayi gaban ta yake faduwa shi kuwa Khalil samun kanshi yayi da kasa dauke idannshi daga gareta. Kallonta yakeyi yadda take tafiya a tsanake. Kayan data saka a jikinta idan ba an fada maka ba bazaka taba cewa ba bafulatana bace. Haskenta irin mai tsananin kyau da cika ido ne, wannan ko a cikin igbos din ya tabbatar mahaifiyarta kyakyawa ce asalin gaske.

Dauke idonshi yayi yana sauke numfashi a hankali. Yau ce rana ta farko daya tsaya ya kalleta fiye da yan sakanni. Har taje wajen masu abincin ta karbo ta fara takowa garesu ya kasa dauke idonshi daga gareta. Daka ganta kasan a takure take kuma cikin matsananciyar damuwa.

Shigowa tayi inda aka ware domin su ta tsaya tana dan kallon teburin dan taga ina ne zata ajiye masu plates din. "Ina yini?" ta gaishe da Yusrah murya kasa kasa. Ko kallon banza Yusrah bata mata ba.

Batul bata yadda idonta ya hadu da nashi ba, dan matsar da kayan decoration din dake kan table din tayi ta dora plates din kafin ta juya ta koma. Lemuka da ruwa ta dauko ta dawo ta iske har ya fara cin abincin. Dan shine ma yake bawa Yusrah tanaci tana yar fira da kawayenta dake zaune kan table din dake dan gefe dasu. Kallonsu tayi sau daya ta dauke idonta daga garesu ta ajiye robobin ta juya zata koma.

"Amso man nono," ya furta cikin yaren fulatanci. Duk kuwa da cewar ta gane me yake nufi, dan zuwa yanzu tana dan tsintar yaren kadan kadan dan zata iya yini cikin gidan inba dole ba babu mai yin hausa. Juyowa tayi sai a lokacin ta daga ido ta kalleshi.

"Ban gane ba," ta fada a sanyaye. Ya juya yana bawa Yusrah abincin a baki ya dago yana kallonta idonshi cikin nata.

"Ki karbo man nono," ya furta da hausa yana me dauke idonshi daga gareta. A karo na farko data fara tsintar kanta da jin haushi Khalil wanda ita kanta bata san menene dalilin yin hakan da tayi ba. Juyawa tayi ta koma wajen masu zuba abincin ta karbo ta kawo mashi. Iske su tayi sunata wasa da dariya suna cin abincin suna kallon mutanen dake tsakayan filin suna rawa.

Ajiyewa kawai tayi saman teburin ta juya zata koma inda ta fito ta tsinkayi muryar Yusrah tana cewa "Keh!" a dan kara tana binta da wani kallon wulakanci.

Juyowa Batul tayi tana dan runtse idonta a hankali. So take ta bar wajen nan ta koma daki ta zauna ita dai wata kila yin hakan zaisa taji wani sauki a zuciyarta. "Na'am," ta furta a hankali idanunta suna kan yatsun kafarta.

"Jeki waje bakin gate ki shigo da wani friend dina. Baisan kowa ba kuma bayajin Hausa balle Fulatanci. Zaki ganshi fari ne, ko ince bature ne da kin ganshi ma zaki ganeshi." Ta furta tana wane yarfe hannu tana mata bayani da yaren Fulatanci.

Sakake Batul ta tsaya tana kallonta dan a abunda ta furta baifi kalma biyu ta gane ba. Yusrah ganin tayi tsaye bata wuce ba kuma batace komai ba yasa ta dago ta kalleta. "Bakiji me nace bane? Ko zaki barshi a waje ne tsaye tun dazu?" tana furta haka kira yana shigowa wayarta. "Hello Sam, I'm so sorry, one of the maids will come and get you now, okay?" Ta furta tana me bawa abokin nata hakuri.

"I don't understand Fulani." Batul ta bata amsa cikin yaren turanci tana kafe ta da ido.

Maimaita mata abunda tace tayi da turanci kafin Batul ta wuce shi kuma Khalil ya tsaya yana kallonta. "Babe, waye Sam kuma?" ya tambaya yana kurbar ruwa.

"Friend dina dinnan dana taba fada maka? Munyi secondary school tare dashi lokacin Daddy yana Ambassador na US kafin mu dawo Nigeria. We've been friends tun lokacin, shine bestfriend dina. Ayyuka suka mashi yawa sai yasa bai samu yazo sauran events din ba. Jiya ya biyo flight din dare kawai dan ya samu wannan event din." Bayani take mashi hankalinta kwance tana murmushi alamar taji dadin bakin nata da abokin nata yazo.

Wayar Khalil ce da tayi kara yasa bai bata masa ba ya daga wayar. Abokinshi ne, Bilaal wanda shine ya rokeshi akan ya taimaka ya siyo mashi wayar da zai bawa Batul dan shi kam bashi da lokacin zuwa ya siyo mata waya. Magana sukayi yana fada mashi yana waje yaga mata sunyi yawa wajen da kyar ya iya shigowa. Ta cikin wayar Bilaal yaji kamar ana hayaniya.

A gaggauce Bilaal ya mishi sallama ya kashe wayar. Tun abun bai shigo wajensu ba har kowa ya fahimci kamar rigima akeyi a waje. Tun abun yana waje suka shigo cikin gidan. Batul Khalil ya hango idanunta sunyi jajur kamar an watsa mata yaji a ido bayanta kuwa wasu turawa ne su biyu. Daya daga cikinsu sai sauri yake yana bin bayanta ita kuma tana kara hanzari wajen wucewa.

Ganin zata tsere mashi yasa ya riko hannunta yana janyota gab dashi dan tazarar dake tsakaninsu Khalil ya tabbatar suna iya jiyo numfashi juna. Gani yayi a hankali Yusrah ta mike tsaye tana daga ma daya daga cikinsu hannu wanda ko bai tambaya ba yasan shine abokin da take magana akai. Yana kallo ya sakar mata da murmushi yana takowa inda suke zaune. Idonshi yana kan Batul yaga da hanzari ta janye hannunta daga rikon da gayen ya mata taja baya tana watsa mashi wani kalar mugun kallo.

Cikin abunda bai wuce sakan biyar ba gayen ya kara matsawa inda take. Wannan karan kafadarta ya rike yasa dayan hannunshi yana dago habarta. Gab da fuskarta yakai tashi wanda hakan yasa Batul ta rufe ido ta watsa mashi wani kalar lafiyayyen mari, yana kokarin kara janyota zuwa jikinshi yasa ta kara zabga mashi wani marin a dayan kuncin wanda hakan shine dalilin janyo hankalin ilahirin mutanen da suke wajen a kansu.

Khalil baisan ya taka ya isa wajen ba sai lokacin da baturen nan ya finciko Batul da wani bala'in karfi fuskar nan tayi ja sosai kamar danyen nama. Idanunshi sun rine sunyi jajir tsabar bacin rai. Ya daga hannu zai wanketa da mari Khalil ya rike hannunshi gamgam yana tsareshi da idanunshi da suke cike da zallar bacin rai. "Don't you dare lay a hand on her!" ya fada da kakkausar murya.

Baisan meyasa ba amma ganin yanda baturen nan yake rikota sai ya tuna mashi a maganganun da wadancan mazan sukayi a kasuwa, a take yaji wani kalar bacin rai ya ziyarci zuciyarshi. Da wani kalar mamaki Batul ta juyo tana kallonshi dan ko za'a kasheta bazata taba tunanin wai Khalil zai ma nuna yasan abunda akeyi a wajen ba.

Maama ce da wasu tsiraran kawayenta suke takowa zuwa wajen domin suji abunda yake faruwa. Dan kuwa hatta DJ ya tsaida kidan da yakeyi kallo ya koma wajensu. Fizge hannunshi baturen yayi daga rikon da Khalil ya mishi yana wani yarfewa.

"Wuce cikin gida." Ko kallonta Khalil baiyi ba ya furta hakan. Sumsum kuwa gudu gudu sauri sauri haka ta bar wajen dan dama tana tsoron Maama ta iso wajen dan b atasan me zata mata ba. Khalil bai dauke kanshi daga gareta ba har saida ya tabbatar ta shiga cikin gidan kafin ya maida kallonshi kan baturen. "Get the hell out of here!" Ya fada da kakkausar murya, ko kallon inda Yusrah wacce take magana tana fada mashi tare suke da abokinta baiyi ba ya fice ya fita daga gidan baki daya.

Domin samun complete littafin zaku iya man message ta Telegram a kan naira 1500 while it's ongoing. Da ya zama complete it will be 2000 naira.

You can reach out to me ta wannan number din a telegram: 08132526951

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top