7
Yau ne ranar daurin auren Khalil. Tunda Batul ta tashi da asuba gabanta yake wani bala'in fadi ta rasa duniya me zatayi taji sanyi a zuciyarta. Ita dai tasan tabbas ba wai tana san Khalil bane, ko daya. Balle wai ko tayi tunanin kishi takeyi. Tana alakanta abunda takeji a zuciyarta da rashin sanin makomarta a wannan auren wanda har yau babu wanda yasan dashi face su uku. Kuma batasan yaushe za'a san dashi ba. Watakila har ya mutu babu wanda zaiji balle ya gani.
Tunda tayi sallar asuba take zaune kan sallaya babu abunda takeyi sai istigfari. Har yau bata manta da maganganun da Malama Hauwa tayi mata ba, ko da wasa Batul bata wasa da ibada da kuma rokon Allah. Kofar dakinta taji an kwankwasa saida gabanta ya fadi. Gidan cike yake makil da mutane, amma tasan hakan bazai hana Maama yin wulakancinta ba idan taso.
Tashi tayi jiki a sanyaye taje ta bude kofar. Ganin daya daga cikin masu aikin tayi wacce ta mata dan guntun murmushi. "Gashi inji Hajia tace wadannan kayan zamu saka yau." Tana fadin haka ta mikawa Batul kaya cikin leda ta juya ta wuce abunta ba tare data jira amsarta ba.
Batul komawa tayi cikin dakin ta bude kayan tana dubawa. Kusan wata daya daya wuce dama anzo an dauki awon kaf masu aikin gidan, to wata kila wannan dinkin ne za'a masu. Yau zasuyi 'mother's eve' a gidan bayan an kawo amarya da maraice. Da mahaifiyar Yusrah da Maama kawaye ne tun suna secondary school har yanzu, dan zama ka iya cewa sun zama aminai balle yanzu da suka hada auren yaransu.
Dalili kenan Maama tace ita zata shirya masu mother's eve wanda suka gayyaci kawayensu na nesa dana kusa. Dole Maama tayi masu wannan hadadden dinkin don kuwa bazata so ace ta gaza ba koda kuwa ta fuskar ma'aikatan gidanta ne.
Batul wanka tayi ta shirya amma bata saka kayan ba sai anjima zata saka. Fita tayi ta kama ayyukan da suka kasance nata duk kuwa da cewar sadidan Maama tayi hayar wani cleaning company sukazo suna gyara gidan tun lokacin da bakin biki suka fara yin yawa dan mace ce mai matukar kaunar tsafta.
Tana ta kallon agogo har karshe sha biyu tayi. Bayan Sallar Juma'a za'a daura auren Khalil da Yusrah kamar yadda aka daura nasu auren bayan sallar Juma'a. Ko zai tuna da nasu auren? Yar dariyar bakin ciki tayi dan kuwa tasan bazaiyi ba. Koda ya tuna saidai dan bakin ciki ba wani abun ba.
Aikowa akayi Maama tana kiranta bayan duk mazan sun wuce masallaci. Gabanta ke dukan uku dan ita har gobe tsoron matar nan take. Gashi har yanzu batayi mata maganar abunda ya faru bayan sun dawo daga kasuwa ba wanda tasan wannan aikin Abba ne dan inba dan haka ba kashinta da ya bushe a cikin gidan nan.
Koda ta gaisheta hade da matan da suke zaune cikin falon nata babu wanda ya amsa gaisuwarta. Saima daya daga cikinsu da tace, "Wannan ce wannan K'abilar da kike complain about?" a tare sukaja tsaki suna yan maganganu. Wasu har da cewa sai tayi hankali dan tsafi a wajen Igbos karamin abu ne ba babba ba.
Ita dai Batul kanta a kasa ko dagowa batayi ba har Maama ta gama abunda takeyi ta dago tana kallonta. "Bangaren Abba zaki gyara. Banso nazo naga koda digon datti a wajen, kina jina?" Ta furta murya cike da tsananin tsana.
"Eh Hajia." Ta amsa muryarta tana rawa. Harta juya zata fita taji wata mata tayi magana da fulatanci wanda hakan yasa Maama kiranta.
"Ke, dawo nan!" Maama ta furta da alamar bacin rai a muryarta. "Ba'a kai maki kayan danace zaku saka bane yau?" Ta tambayeta a hasale.
"An kai min," Batul ta amsa tana dukar da kanta gabanta yana tsananin faduwa.
"To me kike nufi da kayan dake jikinki?" Wasa Batul ta farayi da yatsunta dan batasan amsar da zata bata ba.
"Kiyi hakuri yanzu zanje na saka." Wani dogon tsaki Maama taja alamar ta bace ta bata waje. Da hanzari Batul ta fita daga falon har tana kusan tuntube tun kafin wata kuma ta kara wata maganar.
Bangaren Abba ta wuce kai tsaye bayan ta kwaso kayan da zatayi amfani dasu wajen gyarashi. Duk kuwa da cewar tasan a gyara yake tsaf sai abunda baza'a rasa ba amma kuma haka ta zage ta kara gyarashi dan har ruwa zaka iya zubawa a kasa kasha ba tare da kaji kyankyami ba. Gaba daya dakunan dake bangaren sai da ta gyara ta wanke bayuka da komai. Data shiga kitchen ne ta lura da uban wanke wanke wanda tasan abincin daren jiya ne da aka kaiwa abokanshi aka manta babu wanda ya daukosu.
Wanke wanke tayi tsaf ta gyara kitchen din ta kuma sakawa ko ina turaren wuta. Tana tsakar goge gogen abubuwan dake falon taji alamar bude kofa. Juyowa tayi gabanta yana dan faduwa dan kuwa tasan kila Maama ce ta shigo ta duba abunda takeyi sai taga Abba ne yake shigowa fuskarshi dauke da murmushi yana waya.
Wata kalar ajiyar zuciya ta sauke wacce batasan tana bukata ba tukunna ta dukar da kanta kasa ta cigaba da goge gogen ta. Saida ya gama wayar yana zaune akan kujera yana kallonta da wani kalar tausayi tukunna yayi gyaran murya. Tunda ta ganshi ya dawo tasan an gama sallar har an daura auren. Batasan kwata kwata ta bata lokaci har haka ba sai yanzu.
"Abba ina yini?" Ta furta murya can kasa tana wasa da tsumman data gama goge gogen dashi.
Murmushi yayi, "Lafiya lau Batul. Aikin ne aketa yi?" ya tambaya da tausassar murya.
"Eh Abba. A kawo abinci?" ta dan daga kai ta kalleshi kafin ta kara dukar da kanta.
"Aa Fatima bar abincin nan. Daga wajen reception nake. Bacci ma nakeji ba'a gama ba na dawo gida. Banso rashin baccin nan kwana biyu yasa hawan jini na ya tashi shine na shigo in danyi bacci ko awa daya sai na koma mu cigaba da gaisawa da mutane." Dan daga kai tayi alamar ta gane. Hakan daya fada kawai ya tabbatar mata da an daura auren Yusrah da Khalil. "Amma dai naga baccin nan bazai yiwu ba dan sai kirana mutane keyi zasu wuce zanje muyi sallama. Zansha maganin ciwon kan kawai in yaso yau sai na kwanta da wuri."
"Allah ya kara lafiya, Abba," ta furta murya a sanyaye.
"Zo ki zauna nan Fatima," ya furta yana mata nuni da kujerar dake kusa da wadda yake zaune. Kafin tayi taku daya ya dauko wayarshi. "Zo ka sameni a bangarena." Yana furta hakan ya kashe wayar ya aje.
Ba sai ta tambaya ba tasan wanene, Khalil ne. Ita kuma har ga Allah har zuciyarta bata san ko ganinshi tayi. Takowa tayi tazo wajen kujerar da Abba ya nuna mata. Amma maimakon ta zauna kamar yadda ya furta sai ta zauna a kasa. Ba'ayi minti biyar ba sai ga Khalil ya shigo. Kamshin dayake shine abu na farko daya fara isowa gareta kafin taji karar takunshi yana takowa har cikin falon. Kamshin jikinshi ya hadu dana turaren wutan dake konewa a falon wanda hakan ya bada wani kalar kamshi mai kwantar da zuciya.
Waje Khalil ya samu ya zauna a kujera. Gyaran murya Abba yayi yana mashi nuni da Batul. "Bakaga inda ta zauna bane ita?" simi simi Khalil ya gyara babbar rigar dake jikinshi ya zame saman carpet din shima ya zauna.
Dan dagowa Batul tayi charaf kuwa idanunsu suka hadu dana juna. Yayi wani kalar haske ya kara wani bala'in kyau. Gashi kallo daya zaka mashi ka tabbatar yana cikin tsananin farin ciki wanda koda an tambayeshi shi kanshi bazai iya misalta farin cikin ba. Wani abu ne taji ya soke ta a cikin zuciya, tunowa da yadda fuskarshi take a ranar da aka daura nasu auren duk kuwa da cewar bata manta yadda akayi akai auren ba.
Abba gyaran murya yayi a lokaci daya suka dago suna kallonshi. "Ibrahim, an daura maka aure da Khadija yan awanni da suka wuce. Kamar yadda sati biyu da suka wuce aka daura aurenka da Fatima gata a nan zaune. Amma yanayi ya hana mu bayyana aurenka da Fatima wanda har gobe ina mai tsananin baki hakurin hakan, Fatima. Dan Allah kiyi hakuri ki gafarce mu, babu macen da zataso tayi aure amma bata da yanci a matsayinta na matar mijinta sai ta zama mai aikin gidansu." Abba ya furta da raunanniyar murya yana kallonta. Kara dukan da kanta Batul tayi dan ya sosa mata inda yake mata kaikaiyi.
"Banso Allah ya kamani da hakkinki Fatima. Kuma ki sani nan bada jimawa ba zan bayyana auren dake tsakaninki da Ibrahim. Ki kara hakuri akan wanda kikeyi, kinji?" Dagowa tayi tana kallon Abba taga tsantsar damuwa akan fuskarshi.
"Babu komai Abba. Baku mani komai ba face tsantsar alkhairi da kuma ceton rayuwata da kukayi. Kullum cikin rokon sakayyar alkhairi nake a gareku, Abba." Muryarta na rawa ta furta hakan. Haka abun yake har kasan ranta amma kuma hakan baya nufin babu wani abu da yake darsuwa a zuciyarta.
"Khalil, ka siya mata wayar da kuma kayan danayi maka magana akai?" Abba ya furta yana tsare Khalil da ido. Dan tunda akayi abun nan bai kara sakar mashi fuska ba. Ko sauraranshi ma bai kara yi ba sai yau. Haushinshi yakeji sosai ba kadan ba.
"Hidindimu ne sukayi man yawa Abba, amma..."
"Amma me? Ina fatan kana sane da hukuncin wanda da mijin da baya adalci a tsakanin matanshi zai fuskanta a ranar tashin alkiyama, Khalil? Duk abunda kakeyi a rayuwarta karka kuskura ka manta da cewar Fatima matarka ce, kuma itace matarka ta farko. Kuma ko bayan babu raina Ibrahim ban yarda ka saki Fatima ba duk rintsi duk wuya saidai in ta bullo da wasu halayyar da musulunci ya haramta a zauna da mace mai yinsu, kana jina?"
"Abba..." Khalil ya furta a hankali.
"Na fada maka. Allah ne ya kaimu sallah a wanna masallacin ranar, kuma nayi imani da Allah ne ya sanya mani tunanin na aura maka Fatima a ranar. Allah baya kuskure, Khalil. Kana sane da ba wannan masallacin zamuyi sallah ba a ranar amma motarmu tayi zafi dole muka tsaya gefen masallacin shi kuma direba yaje ya nemo ruwa, ko ba haka akayi ba?" A hankali Khalil ya daga kanshi. "Kome kaga ya faru a rayuwa to tabbas yana da dalili. Idan har ka saki Fatima koba yanzu ba, inhar ba akan wadannan dalilin dana fada ba, bazan taba yafe maka ba Ibrahim."
A razane Khalil ya kalli mahaifinshi wanda shi kuma Batul yake kallon da take shashekar kuka a hankali. "Kaga wannan baiwar Allar? Ka kula da ita, Khalil. Karka shiga hakkinta dan kuwa amanar Allah ce a wajenmu, na roke ka. Kayi adalci a tsakanin matanka. Kaji tsoron Allah. Ni kuma insha Allahu nan bada dadewa ba zanyi abunda ya kamata ku dawo kuna zama tare tamkar yadda kowane ma'aurata sukeyi, kunaji na?"
A tare suka daga kansu Batul tana kara zubar da hawaye na tausayin rayuwarta. Ita wannan alwashi na Abba banda tayar mata da hankali babu abunda yayi. Juyowa Abba yayi yana kallonta. "Ko kina bukatar wani abun ne, Fatima?"
A hankali ta girgiza kanta duk kuwa da cewar tana bukatar, amma gani take kamar ma ta zama butulu in har tace ga abunda takeso, banda duk abubuwan da sukayi mata. "Karka manta da wayar a yau dinnan nakeso ka siyo mata ita. Su kuma suturun kana iya bari bayan ka sami natsuwa. Kuma abunda ya faru a kasuwa banso ya koda kwatankwacin abun ya kara faruwa, kana ji na? Matarka ce yadda Yusrah take matarka a yau. Duk kima da darajarsu daya a wajenka, kana jina?"
"Eh inaji Abba."
"Idan kuma har ka zalunceta Khalil, sai Allah ya saka mata ta hanyar da baka taba tsammani ba. Nasan kaima biyayya kamun akan auren nan, ka sani watarana zakayi alfahari da Fatima a matsayin matarka, insha Allahu." A tare Batul da Khalil suka dago suka kalli juna. A karo na farko yau Khalil ya kalleta ba tare da tarin tsana ko jin haushi a idonshi ba, kawai dai ya kalleta kamar yau ya fara ganinta da can wani abun yake kallon ba ita ba.
A hankali ta janye idonta daga gareshi ta maidasu kan carpet dake gabanta tana cigaba da goge hawayenta. "Nagode Abba." Ta furta da wata kalar sanyayyar murya. Abba baice komai ba ya tashi ya barsu nan zaune kasa kowa da abunda yake rayawa a zuciyarshi.
Kamar yadda Abba ya furta, Batul ita da kanta tasan biyayya tasa Khalil ya yarda har ya aureta bawai dan zuciyarshi taso ba. Babu namijin da zaiso a daura mashi aure da macen da bai sani ba bai taba gani ba daga roko a masallaci kuma ana sauran sati biyu ya auri macen da yake matukar so da kauna. Yayi kokari sosai ba kadan ba, kuma shima ya cancanci ta gode mashi.
"Kayi hakuri..." haka kawai taji nauyin ta kira sunanshi, "Hamma." Ta furta hamman a wani kalan sanyaye wanda saida ya dago ya kalleta kafin ya kauda kanshi gefe. Kuma kamar wanda aka dasa a wajen ya kasa tashi. "Nagoda da duk abunda kuka man kaida Abba, bazan taba iya saka maku da wannan alkhairin ba, Allah ya saka maku da mafificin alkhairin shi. Kuma ina baka hakuri, nasan ka takura da duk abubuwan dake faruwa. Sannan ina rokon Allah ya baku zaman lafiya da matarka." Matarka...sai kace ita din ba matarsa bace. Saida ko a matar ma wata tafi wata 'yanci. To ko ba'a fada ba tasan Yusrah itace asalin mata a zuciyar Khalil.
Tunda dai bakuyin comment kila zanbar preview chapters dinnan a nan kawai.
Domin samun complete littafin zaku iya man message ta Telegram a kan naira 1500 while it's ongoing. Da ya zama complete it will be 2000 naira.
You can reach out to me ta wannan number din a telegram: 08132526951
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top