6

A tsaye suka iske shi cikin falon sai zarya yake yana tunani, jijiyoyin kanshi sun fito rado rado. Ko baka taba ganinshi ba kana ganinshi kasan tabbas ranshi a bala'in bace yake. Batul waje ta samu ta rabe ta zauna gabanta yana dukan uku uku dan tasan yau kam, dole rubutun kaddararta ya chanza salo. Wani sabon babi za'a fara rubutawa wanda ko ba'a fada ba dole yai mata wani kalar matsanancin ciwo.

Saida Khalil ya shigo ya zauna can nesa sosai da ita kafin Abba ya juyo yana kallonshi. "Ibrahim ashe baka da hankali? Ashe kai sakarai ne wawa wanda baisan ciwon kanshi ba? Wani kalar iskanci ne wannan? Dama kai dakiki ne wanda baisan hukuncin addini ba? Ina kallonka a matsayin me hankali me tunani har na yarda na baka amanar yarinya baiwar Allah, marainiyar Allah amma saboda kai munafuki ne kuma azzalumi shine ka yarda akaci amanata da kuma amanar Allah dakai?!" Da wani kalar karsashi yake magana, ga wani kululun bacin rai nan a muryarshi wanda in akace zaiyi kuka babu gardama a hakan.

Farkon fara kasuwancin Abba tun yana samartaka tsakanin Kano da Katsina ya farashi, dan haka duk wani samfari na zagi babu wanda Abba bai iyaba sai dai girma ne yasa ya daina wasu abubuwan dan kuwa ya dade a garuruwan nan kafin Allah ya bunkasa masa kasuwanci ya bude sashe a Abuja daga nan sai Lagos sai ma ya koma har kasashen waje yanzu ba adadi.

"Abba, zagina fa kakeyi..." Abunda Khalil ya furta kenan. Dan shidai yasan Abba bai taba mashi kallon banza ba balle har takai su ga zagi sai yau gashi Abba har marinshi yayi kan waccan kwailar yarinyar.

"Na zageka Khalil! Yanzu dan ubanka abunda kayi ba duka ya kamata a maka ba? Wallahi tallahi kaci sa'ar shekaru na sunja yanzu, baccin haka bugun bala'i zan maka yau saidai na kaika asibiti daga baya. Baka da hankali ne? Dama kai shashasha ne ban sani ba? Sakarai a haka kamar me wayau kamar kana da addini ashe kai tantagaryar jahili ne ban sani ba?!" Ihu ihu haka Abba yake masifa, inda yake shiga bata nan yake fita ba.

"Abba me nayi? Kayi hakuri in na bata maka rai amma ni ban..."

"Au bakasan abunda kayi ba? Bama kasan abunda kayi ba kace Khalil? Tashi kaje," Abunda Abba ya furta kenan kafin ya nemi waje ya zauna. Khalil ya bude baki zaiyi magana ya daga hannu ya dakatar dashi. "Tashi ka fitar min daga falo, minti daya bance ka kara a nan wajen ba, kanaji na?" Da kyar muryar Abba take fita yana kokarin danne bacin ran dayazo mashi.

Khalil sumu sumu ya tashi ya nufi kofa kafin muryar Abba ta tsayar dashi. "Idan ka shiga ciki ka fada ma uwarka an fasa aurenka." Abunda Abba ya furta kenan ko kallon inda yake ma bayayi. Da wani bala'in hanzari Khalil ya juyo yana kallonshi gabanshi yana dukan uku uku kamar zuciyarshi zata fito waje.

"Abba..."

"Zaka wuce ka bani waje ko sai na babballaka?!" Ya daka mashi tsawa wanda Khalil baisan lokacin daya fita daga falon ba dan yasan ran Abba yayi bala'in baci.

Saida Abba yaga fitar Khalil kafin ya juyo ya kalli Batul dake kallonshi mamaki ita kanta ya gama cikata dan kuwa bata taba tunanin Abba ya iya masifa irin haka ba. "Zo ki zauna nan kusa dani Fatima, kinji?" Muryarshi a hankali yayi magana kamar bashi bane wanda ya gama tada jijiyoyin wuya yanzu ba.

Ba musu Batul ta koma kusa da kujerar da yake zaune ta zaune kanta a kasa. Zuwa yanzu tayi nasarar tsaida hawayenta amma tsoro, fargaba da kuma bakin ciki sune ababen da sukafi komai samun mazauni a zuciyarta.

"Kiyi hakuri Fatima, bansan da wane kalar baki zan baki hakuri ba. Ki sani, wallahi ban yarda na aurawa Khalil ke ba dan na kawo ki nan a wulakanta ki Fatima. Ban yi haka ba kuma dan kizo a kaskantar dake a ci maki zarafi ba. Allah yaga zuciyarta, tunda naji bayanin Liman Allah ya sanya tausayinki a zuciyata. Kiyi hakuri da abunda ya faru yau, da wanda suka faru a baya dukda ban san dasu ba. Nasan banida hurumin rokar masu gafara daga wajenki amma dan girman Allah ki yafe masu. Sun zalince ki Fatima, ki yi hakuri kinji?"

Tunda Abba ya fara magana Batul taji hawayenta suna sauka daya bayan daya a kuncinta. Sai taji duk wani kunci da bakin ciki a hankali yana fita daga kirjinta. "Wallahi Abba baka min komai ba, dan Allah ka daina bani hakuri haka nan. Abba kai mahaifina ne, duk abunda kakeso umarni kawai zaka bayani ba wai ka rokeni ba. Na yafe masu Abba. Kayi hakuri Abba na sanya ka cikin bakin ciki."

"Baki man komai ba Fatima. Kuma nagode sosai da yafe masun da kikayi. Yanzu ki fada man, dame dame kike bukata?" Ya furta ya juyo yana kallonta. Shirun da tayi tana kallon kasa ne yasa ya kara magana, "Wancan yaron ya siyo maki wayar da kayan danace ya siyo maki kuwa?"

Kamar Batul tayi karya tace eh ya kawo mata sai kuma taga to Abba zai iya cewa ina wayar take ya gani? Bataso ace ta kara shiga tsakaninsu dan ita wallahi ba niyyarta kenan ba. Dan da ace tasan idan suka dawo zasuga Abba to da duk yanda zatayi ta sulale cikin gidan ba tare daya lura da ita ba da tayi. Ba sai an fada ba amma tasan uba da d'an basu taba samun sabani ba kamar na yau.

"Bai siya ba kenan ko? Ki barni dashi." Ita dai batace komai ba, kanta na kasa tana share hawayenta. "Tashi ki shiga ciki, Fatima. Ki toshe kunnenki da duk abunda zai faru cikin gidan kinji? Kuma ki kara hakuri, ina nan ina jira naga lokacin daya dace ace kin koma zame tare da mijinki."

'Mijinki.' Sai taji kalmar ta mata wani kalar nauyi a bakinta ta kara dukar da kanta.

Ganin tayi shiru kuma bata tashi ta tafin ba yasa Abba juyowa yana fuskantarta. "Ko akwai wani abun ne?" ya tambaya murya a sanyaye.

"Dan Allah alfarma zan rokeka, Abba." Ta furta murya a dasashe tsabar kukan datasha.

"Ina jinki Fatima. Kome kikeso insha Allahu zan miki shi kinji?"

"Abba kar kace an fasa bikinshi dan Allah." Ya bude baki zaiyi magana tayi hanzarin katse shi. "Dan Allah Abba kar kace Aa, kai kanka ka gayyaci mutane Abba, yau saura sati daya fah. Na yafe ma kowa wallahi, amma dan Allah kar ace an fasa, dan Allah na rokeka Abba."

Shiru yayi yana dan nazari kafin ya daga kai. "Naji na yarda."

"Nagode Abba." Tana furta hakan ta mike ta fice daga falon. Lokacin datazo shiga falon cikin gidan saida taji gabanta yayi wani bala'in faduwa dan batasan me zata tarar ba a ciki. Allah ya sota babu kowa dan da alama duk suna bangaren Maama, a hankali ta sulale ta wuce dakinta, wanda shine har yanzu ba'a chanja mata ba tun farkon zuwanta gidan.

Lokacin Maghrib har yayi, bayi ta fada tayi wanka ta dauro alwalla ta fito. Saida ta kammala sallah tukunna duk abubuwan da suka fara suka fara mata yawo a kai. A hankali a hankali ta fara zubda hawaye tana tausayin kanta. Dan kuwa a falon Abba kafin Khalil ya fita ya juyo ya kalleta. Wata kalar tsana ce da bata taba ganin irinta ba a idanunshi. Ko bata tambaya ba tasan idan yanzu akace wa Khalil ya tsana fiye da komai da kowa a duniya tabbas zaice itace. Kuka take kamar ranta zai fita dan kuwa inda ace tana da mafita daga halin da take ciki to yau babu abunda zai hanata nemar wa kanta mafita.

Ta dauka sai sama da kasa sun hade a cikin gidan nan amma da mamakinta kowa ya cigaba da hidimarshi kamar babu abunda ya faru. Duk wani tozarci da wulakancin da take tunanin Maama zatayi ma ga mamakinta sai taga babu ko daya. Kamar ma ta fita harkarta ne kwata kwata dan yanzu ko wannan gutsi gutsin aikin bata sakata. Indai tayi aikin da aka yankar mata shikenan. Sai ta wuni a daki babu wanda ya nemeta.

Tun ranar har yau bata kara ganin Khalil ba koda wasa. Ko muryarshi bata kara jiyowa ba. Abba ne dai kullum da safe zai aika a kirata da daddare ma kafin ya kwanta sai ya mata sallama. Abunda Abba yake ma Batul ko mahaifin daya haifeta be mata shi ba. Yau saura kwana biyu daurin auren Khalil gidan ya cika yayi makil. Ta dauka za'ace ta bawa wasu bakin dakinta amma sai taji shiru ba'ace ba.

Tun jiya aka fara event. Kullum da yamma zataji anata hayaniya ana shiryawa sai can gidan yayi shiru kowa ya tafi wajen event din sai kuma can cikin dare suke dawowa, wani lokacin ma sai tayi bacci. Ana gobe daurin auren Khalil wajen karfe goma na dare daya daga cikin masu aikin gida tazo tace mata Maama na kiranta.

Saida gaban Batul ya fadi, dan kuwa rabon da Maama ta kirata tun ranar da abun nan ya faru. Tasan bawai ta manta da ita bane, Aa, amma dai hakan ya mata dadi dan kuwa ta samu kwanciyar hankali nesa ba kusa ba. Tashi tayi ta chanja rigar dake jikinta dan kuwa ta daddara, ta dora doguwar hijab dinta har kasa kafin ta tafi sama bangaren Maama.

Zaune ta isketa da uban mutane a tsakiyar falon anata hidima. Daga can ta rabe ta gaishe dasu babu wanda ya kulata balle ma tayi tunanin zasu ansa. Daya daya dai ta lura da suna kallonta sai kuwa suka chanja harshe suna magana da yaren fulatanci. Masu harararta nayi, masu jifarta da kallon tsana suma suna nasu.

Saida Maama ta mula tasha iska kafin ta juyo ta kalleta. "Bangaren Khalil zakije ki gyara shi tas kafin mu dawo event dinnan dan akwai bakin da zan kai su kwana a can. Idan kinga dama kiyi me kyau in bakiga dama ba kiyi yadda kikeso nida ke ne cikin gidan nan."

"To Hajia." Tana fadin hakan sumsum ta fita daga bangaren tanajin wasu daga cikin matan dake falon sukaja tsaki ana jifarta da wasu kalar munanan kalamai.

Runtse ido tayi tana kokarin kwantar da bakin cikin dake cin zuciyarta. A hankali ta sauka kasa sai kuma ta tsaya tana tunani dan ita batasan inane bangaren Khalil ba. Husna ta gani anci uban gayu kamar bata taka kasa zata wuce ta dan matsa wajenta da hanzari.

"Dan Allah inane bangaren Hamman ku? Hajia tace naje na gyara kuma..." Tun kafin ma ta idasa maganarta Husna taja wani dogon tsaki kawai ta harare ta ta kara gaba. Tsayawa Batul tayi tana kallon ikon Allah.

Tunani tayi taje ta tambayi koda mai gadi ne, wata kila shi ya sani. Kafin ma ta karasa wajen mai gadin ta hadu da daya daga cikin ma'aikatan wadda itace ta nuna mata har kofar shiga bangaren Khalil. Godiya ta mata kafin taje ta dauka kayan da zatayi aiki dasu ta wuce ta shiga.

Dukda bangaren ba wani datti yayi ba amma haka ta tsaya ta gyara shi tsaf. Taga kayan turaren wuta haka tabi ko ina na wajen ta tabbatar yaji turaren wuta ta kunna duka ACs din dan ya kama sanyi yadda da sun dawo bacci kawai zasuyi.

Ta baya baya tana fitowa tana kallon falon taga in akwai inda ya kamata ace ta kara gyarawa dan kuwa dakunan sai da ta tabbatar komai yayi. Batayi aune ba taji ta buge da wani abu tana juyowa ta ganshi tsaye yayi wani kalar kicin kicin da rai kamar zai hauta da duka. Gabanta ne yayi wani kalar mummunan fadi tayi baya kamar zata zura da gudu.

"Meya kawoki nan?" Da ace Khalil yanada ikon daukar ranta tasan ko sakan daya bata karawa a nan inda take sai ta mutu. Yau ce rana ta farko daya fara mata magana amma kallo daya ta mashi taji dama be mata maganar ba dan wallahi ya tsaneta. Tsana mai tsananin gaske, sai taji wani tausayin kanta ya kamata tunowa da tayi cewar ita din matarshi ce.

"Ba dake nake magana ba?!" Ya furta da kakkausar murya ta dukar da kanta kasa. Tsawar daya daka mata ne yasa ta dan dago da niyyar bashi amsa sai ya mata nuni da kofa yace "fita!" babu musu Batul ta hadiya wani abu me daci a zuciyarta sumsum ta fice, a ranta tana tunanin gobe ne fa daurin aurenshi...


Domin samun cigaban littafin akan naira 1500 kacal, kayi magana ta Telegram ko whatsapp: 08132526951

Kindly note: Preview chapters kadai zan saka a wattpad. Complete is to be paid for.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top