4
Tunda Abba yasa kafa ya bar gidan nan Batul ta fara tantancewa. Dukda dama bawai ta saka a ranta bane zataji dadin zaman gidan. Amma bata taba dauka cewar kasantuwar Abba cikin gidan nan wani kalar rahama bane a gareta sai ranar daya tafi. Mutum ne shi mai yawan tafiye tafiye. Kusan rabin zamanshi ma a Lagos yakeyi amma Maama ta rufe ido fur taki yarda wai ita ba zataje ta zauna karin arna ba. Haka kawai ace duk inda ta juya taga kafirin Allah.
Maama irin matan nan ne masu bala'in kab'ilanci. Haka Abba yanaji yana gani ya barta ta zauna a Adamawa saidai in ya samu chance yazo ganin gida. Kuma be isa ya kara aure ba dan kuwa yakin basasa ne zai jama kanshi. Saukin abun ma shidin ba mutum bane mai ra'ayin mace sama da daya.
Kullum Batul sai tayi kuka take bacci. Tun daga rana ta koma cikin masu aikin gidan itama aka yankar mata nata aikin. Zagi da cin mutunci babu irin wanda ba'a mata gashi wadannan kanne nashi yan mata sun raina kamar ba mutum ba. Ita abun kwata kwata baya damunta dan kuwa in dai tsangwama ne da zagi da cin mutunci ta saba da hakan wajen wanda suke yan uwanta na jini ma balle wanda a ganinsu tazo cin arziki gidansu ne.
Abu daya da yake ci mata zuciya shine kafirta ta da sukeyi. Duk sadda suka nuna basu yarda da musuluncinta ba sai taji kamar ta zuba ihu. Ranar tana aiki aka kira sallah sai ta dakata dan tayi sallar ta dawo ta cigaba. Budar bakin Hasna sai cewa tayi, "Ko me zakiyi ma sallar? oho. Dama kin daina wahalar da kanki kina yan dungure dungure, dan nasan ko kasheki za'ayi bakisan abunda kike fada ba." Shiru kawai ta mata dan kuwa batasan me zata ce mata ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar ma Batul cikin kunci da wulakanci. Yau bikin Khalil saura sati daya amma tun ranar da Abba yace ya kawo mata abinci har zaman da take yanzu bata kara sakashi a cikin idanunta ba. Ita hakan be dameta ba, a zahirin gaskia batasan abunda ma ke damunta ba. Kawai tasan tana cikin matsananciyar damuwa da wani kalar kuncin da bata taba tsintar kanta cikinshi ba.
Ji tayi ana buga kofar dakinta kamar za'a balla ta. Cikin hanzari ta mike ta bude tana kokarin rufe gashin kanta. Wata kalar muguwar harara Hanan ta banka mata taja wani kalar dogon tsaki.
"Miye kike wani rufe kai sai kace wani gashin azo a gani kike dashi? Allah na tuba koda namiji ne ai ke a addininku ba zunubi kikayi ba dan namiji yaga gashinki. Sai shegen iyayi da karya da addini." Ta furta cikin kaskantar da mutum. Dukar da kanta kawai Batul tayi tana jira taji dalilin zuwanta dakinta dan kuwa tasan ba hakanan tazo ba dole sai da dalili.
"Maama tace kizo zamuje kasuwa siyayya." Tana furta hakan ta wuce fuu kamar zata tashi sama. Saida Batul ta saki wata kalar doguwar ajiyar zuciya kafin ta koma ciki dan shiryawa cikin gaggawa. Yau ta kammala aikinta da wuri dan tanaso at danyi bacci dan kuwa jiya cikin dare batayi bacci ba sallah kawai takeyi.
Cikin mintuna kadan ta fita daga dakin tayi hanzar waje inda ake ajiye motoci tana jiran taga fitowarsu. Saida suka share kusan minit sha biyar kafin suka fara fitowa daya bayan daya. Husna ta fara fitowa, sai Hanan sai kuma Hasna. Bayansu Maama ce tare da wata yar'uwarta cikin wanda suka fara zuwa biki.
"Micheal, muje ko?" Hasna ta furta tana wani yatsina. Dukda cewar kaf su ukun babu mai mutunci a cikinsu, to tabbas Hasna duk ta fisu iyawa wulakanci.
Ita ta shiga gaban motar su kuwa suka jera baya kowa yana danna wayarshi ita kuma Maama ita da Adama sunata lissafin abubuwan daya kamata su karo. Ita dai shiru tayi har aka isa kasuwar. Babu wanda ya tanka ta cikinsu haka suka fito ta rike jakar Maama suna tafiya cikin kasuwar nan ga wai bala'in zafin rana kamar mutum ya shik'e.
Duk shagon da sukaje sai su bata wajen minti talatin suna siyayya. "Hajia ya kamata ace an karo kayan bacci da inner wears sai naga wanda muke siya kamar bazasu isa ba." Adama ce ta furta tana kallon shagon dake gabansu wanda cike yake makil da irin kayan data ambata.
"Nidai bansan wasu wanda ya kamata mu kara siya ba kuma Adama," Maama tace.
Tun kusan minti talatin da suka wuce yan uku suka shiga cikin kasuwar dan suma sunada tasu siyayyar da basu ida ba. Daga ita sai Maama da Adama.
"To ai kamata yayi ace an kira shi Khalil din yazo ya zabi wanda yakeso. Haka akeyi musamman kayan bacci tunda shi za'a sakamawa ko?" Wata yar dariya sukayi a tare kafin Maami ta mikoma Batul hannu alamar ta bata ta jakarta.
Kiran wayarshi tayi tana jira ya dauka. "Hello, Khalil, kana ina?" Shiru tayi tana jiran amsarshi kafin ta furta. "Toh Alhamdulillah kana kusa ma kenan. Yi sauri gani nan kasuwa ina jiranka, kaji? Nan da minti goma dan Allah." Tana furta hakan ta kashe wayarta suka karasa cikin shagon suka zauna.
Minti goman basu cika ba Khalil ya kira Maama yana tambayarta wane shago ta bawa masu shagon suka mashi kwatance. Ita dai Batul dama tunda suka shiga a tsaye take su Maama ne kawai suka zauna kan kujerun da yan shagon suka basu, koda aka miko mata itama budar bakin Maama sai cewa tayi, "Wannan me suffar doyar? Ai su sun saba tsayuwa da bakar wahala, barta haka har mu tafi bazata gaji ba." Tanaji tana gani suka maida kujerar nan ta dukar da kanta batace komai ba.
Har ya iso kanta yana duke tana ta sakawa ta warware a zuciyarta. Bataji isowarshi ba saidai ta tsinkayi muryarshi yana sallama da yan shagon. Gabanta wani kalar yankewa yayi ya fadi, ta kara dukar da kanta dan har ga Allah bata ko fatan tama daga kai ta kalleshi.
"Ke Batul kike da suna ko wa? Bakiga Khalil ya shigo bane bazaki gaidashi bane ko yaya ne?" Adama ta furta tana watso mata wani kalar mugun kallo mai cike da tsana. Ita dai ta rasa me tayiwa mutanen nan dayasa suka mata kalar wannan muguwar tsanar.
"Banda abinki Adama kafiri har wata tarbiyar arziki zai bama danshi? K'abila ce fah, uwarta Igbo ce kinga kuwa duk wani rashin tarbiya kansu ya kare. Sa ma yarinyar nan ido kawai kiyi kallo. Ni na kosa Alhaji ma ya dawo ya kwashi tarkacensu ya maida masu dan bazan iya zama da muna musulma ba. Sai munahincin saka hijabi nan kuwa in kin bibiya ko Fatiha bata iya karanta maki saidai ki kasheta."
Yadda kasan an dauki guduma an sara wa zuciyar Batul haka taji. Tanajin mutanen dake shagon dama wanda sukazo siyayya sunata kallonta sai taji idanunta sun ciko da kwalla. Danne su tayi ta dago fuskarta saitin inda Khalil yake a tsaye, ko kallonsu ma bayayi, batasu yake ba shikam latsa wayarshi ma yakeyi.
"Ina yini, Hamma." Ta furta murya na rawa can kasan makoshinta. Daga mata kai yayi kawai ba tare da ya kalli inda take tsaye ba. Sunan da taji su Husna na kiranshi dashi kenan sai yasa ta kirashi haka. Ko haushi yaji tace mashi hakan? Miye ma ma'anar sunan?
Sadda kanta tayi kasa duk yanda taso ta hana hawayenta sauka saida suka zubo batayi kokarin taresu ba saima barinsu da tayi suka zubo ta juya a hankali ta share hawayenta. Tanaji suna nuna mashi kayan yana zaba. Sai wani shan kanshi yake irin shi an takura mashi dinnan. Daga wannan yace bayasan kalar, sai wannan yace hannu yayi tsawo, wancan wandon be mashi ba. A haka dai dakyar suka samu ya zaba. Akwai wanda Maama da Adama suka dage akan sunyi kyau kuma zasuyi dadin sakawa cikin damina, yace shi sam basu mashi kyau ba.
Dadai suka dage sai yace shidai bari ya kirata tagani in sunyi mata to sai a dauka in kuma basuyi mata ba gaskia saidai a hakura. Video call ya daga waya ya kira Yusrah nan take kuwa ta dauka cikin murya me dadi da gayu da yanga ta furta, "Babe, shine tun safe kaga missed call dina baka kira ba sai yanzu ko?" Cike da shagwaba tayi maganar.
A hankali Batul ta dan saci kallonshi taga ya maida dukkanin hankalinshi akan wayar yana wani kalar murmushi mai sanyaya rai. "Sorry Babe. I've been so busy ne shiyasa. Muna kasuwa ne da Maama tace na kiraki naga in kinasan wasu kaya..." ya furta wasu kalamai da fulatanci wanda ita dai Batul jinshi kawai takeyi. Mamaki ma take ashe yana magana? Dan ita har yanzu ko kalma daya be taba furtawa domin ita ba.
Daga haka suka cigaba da magana da fulatanci har suna yar dariya. Kallonshi takeyi tana tunani inama ace itama wata rana Allah zai bata wanda zai sota? Wanda zai aureta kamar yanda ake auren kowace mace ya bata kulawa ta musamman yanda ya kamata. Tanaji a jikinta daga ranar da Maama ta gane cewar wai aure Abba ya daura mata da Khalil din nata da takejinshi kamar tsoka daya a miya, to tabbas daga ranar igiyar dake kanta ta auren Khalil sai ta tsinke. Tsinkewa kuwa ta har abada ba komawa.
Batayi tsammanin ta lula duniyar tunani ba saida taji an bangajeta an shiga shagon, dama daga baki bakin kofa take. Dagowa tayi tana Hanan ce biye da Husna kowannen su rike yake da ledoji. "Maama, Hasna tayi staining kayanta sosai bazata iya barin shagon a haka ba," Hanan ta fada.
"To fah, batasan tana period bane ta fito babu pad ko yaya?" Maama ta furta cikin wani yanayi na nuna damuwa. Dan kaf duniya babu abunda ta hada da yaranta.
"Kinsan rushing take sosai, and yau ne first day dama yana mata haka sai yasa bata cika san fita ba ma first days din." Husna ta amsa, wayarta na kara kiran Hasna yana shigowa. "Hello, Hasna, eh mun fadawa Maama yanzu wannan yaren zata kawo maki hijab din jikinta, thank god ma ta saka hijab din."
Da wani kalar hanzari Batul ta kalli Husna data rafka mata wata kalar harara. Tunowa da tayi da rigace jikinta marar hannu ta shan iska dan bama ta ida kai mata har kasa ba. Sanin kalar zafin da akeyi yasa ta sakata ko hula babu a kanta kawai ta sako zumbuleliyar hijabinta. Gabanta wani kalar faduwa yayi.
"Yauwa aikuwa kin kawo shawara Husna." Maama ta furta tana juyowa ta kalli Batul da ta zaro ido gabanta na faduwa. "Ke, kuje Hanan ta rakaki shagon ki kaiwa Hasna hijab din jikinta. Ko ba komai an anfana da ita."
Kamar zuciyarta ta tsinke haka ta hadiyi wani kalar mugun miyau. "Maama wallahi armless rigane jikina, kuma bata kai mun har kasa ba, gashi babu hula a kaina." Ta furta murya na rawa zuciyarta na cika da tsoro dan ba sai an fada mata ba tasan bala'i ne ta janyo ma kanta.
A tare suka fashe da wata kalar dariya. "To shine me? Duba can," Maama ta fada tana nuna wata kafira da tazo wucewa da kayanta dasu da babu duk daya. "Ga danginki can ba, mutuwa tayi data fito haka? Hasalima bata iya saka wasu kayan inba su ba. Dallah malama wuce kije ki bata hijab dinki ta saka."
Kuka Batul ta fashe dashi. "Maama wallahi ni musulma ce. Babana musulmi ne, Mamana ta musulunta itama. Ban taba fita jikina a bude ba, dan Allah Maama bazan iya cire hijab dina ba. Akwai maza a kasuwan..."
"To dan akwai maza shine me? Kallonki akace zasuyi ko mi? Dama shi k'abilar mutum yasan wani abu wai shi suturta jiki ne? Tun ban saba maki ba ki wuce ku tafi."
Kuka take ringis kamar ranta zai fito. "Maama dan Allah, wallahi Allah zai tsine man, zan samu zunubi sosai, dan Allah." Hannayenta ta hade duka biyu a waje daya tana roko. Tunaninta daya, kalmar da Malam Zakariyya ya furta a ranar, 'Kedin yanzu matar aure ce...'
Tsaye Maama ta tashi fuskar nan a murtuke kamar an aiko mata da mutuwa tana kallon Batul dake kuka wiwi. Dan har wani a shagon cike da tausayi yace, "To Hajia ita waccan yarinyar a sai mata hijabin mana, da anje nan shagon kusa damu sunada dinkakku bai wuci dubu biyar ba sai a siya mata. Tunda tace tsiraicinta zai bayyana a kyaleta mana."
A fusace Maama ta juya tana kallonshi. "Malam ka fita a maganar nan ba abunda ya shafeka bane." Kafin ta juya wajen Batul a fusace, "Zaki wuce ko kuwa? Ina ruwana da wani musuluncin ki na munafunci? Kinaso in saba maki a cikin kasuwar nan ko?!" Da wata kalar kara tayi maganar da Batul ta razana tayi baya saida ta fadi.
Kuka ta fashe dashi dan tasan dole tayi abunda sukeso ko zata mutu. A hankali ta juya ta kalli Khalil tana fatan yasa baki. Tasan ba santa yake ba, hasalima zata iya cewa ya tsaneta dan kuwa ta gurbata wani tsari da yayi. Hada idanu sukayi ta mashi wani kallo me cike da magiya. Kallo daya ya mata ya watsar ya cigaba da latsa wayarshi kamar besan abunda ke faruwa ba.
Wani kalar daci ya mamaye mata zuciya. Tsawar da Maama ta daka mata ce tasa tayi zumbur ta mike tabi bayan Hanan domin zuwa kaima Hasna hijab din jikinta, zuciyarta na tafasa kamar zata fashe.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top