3

Tana ji Abba yanata bayani ita dai kawai iyakarta ido. Tunda suka shigo gidansu Khalil kallo kawai takeyi. Dukda tasan cewar su ba talakawa bane mukus, dan bata taba neman abinci a rayuwarta ba ta rasa, wai da sunan babu saidai a hanata da gangan. Ta dauka a unguwarsu Lawai masu kudi da kuma manyan gidaje, ashe ba komai bane. Gida ne wanda bata taba tsammanin zataga irinshi ba a rayuwarta. Kamar ba mutane ke ciki ba. Kuma Abba yace mata yaransu hudu kacal. To kenan su shida suke rayuwa a wannan uban gidan ko yaya?

Zazzaune suke a wani babban falo wanda har yanzu faduwar gaban da take ciki ta hanata ta dago ta kalleshi ta gama ganin girma da kuma kyawunshi ba. Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Mahaifiyar Khalil wadda kowa yake kira da Maama.

"Ya kikace sunanki?" ta tambaya a wata irin murya da ke nuni da tsantsar tsana da wulakanci. Da kuma rashin kirki. Dukda tasan Abba ya sanar da ita sai tayi hakuri da halinta da sauran yaran gida amma hakan bai hanata jin wata kalar faduwar gaba ba.

"Sunana Fatima Batul." Ta fada cikin rawar murya tana tunanin wannan wane irin gida ne.

"Aa ba kiyi kama da mai suna Fatima ba. Kina abu haka kamar wata kafirar usuli? Amma dai ke ba bahausa bane ko?" Ta tambaya cikin gatsali. Kamar Batul ta tashi ta ruga haka taji. Saida ta hadiyi wani kalar mugun yawu kafin ta daga kanta.

"Mahaifina bahaushe ne asalin garin Kano, amma kuma mahaifiyata Igbo ce." Abunda ta furta kenan tana damtse hannayenta. Babu abuna ta tsana kuma yake sanya ta cikin tsananin damuwa da tashin hankali kamar ace mata k'abila. Dukda tasan bawai kai tsaye ta kirata da hakan ba amma kuma ta karyata musuluncinta gaba daya ma.

"Yanzu naji magana. Tun farko da sunanki na Igbo din kika fada baki bawa mutane wahala ba." Batul dai bata tanka ba, hakan yasa Maama juyawa ta kalli Abba dake latsa waya dukda kuwa daka ganshi kasan hankalinshi yana kan maganar da sukeyi.

"Yanzu Alhaji daga zuwa gidan aboki zasuyi tafiya kawai sai ka taho da mai aikinsu? Tsakani da Allah idan muguwa ce fa? Kana fa ji tace ita ba bahausa bane igbo ce. Su dan zasuje London in basu iya zuwa da ita su maidata garin iyayenta mana. Nidai gaskia baza yarda ba haka kawai kaje ka janyo mana jafa'i..." Tana cikin magana ta juya yare ta fara fulatanci. Dukda cewar Batul batajin me suke cewa amma tasan Maama tana kara jaddada ma Abba bazata yarda ta zauna a gidanta ba.

"Ke Husna, shiga da ita dakin baki ta kwanta ta huta. Kuma a tabbatar an kai mata abinci taci, kinaji na?" Abba ya furta yana kallon daya daga cikin yan matan. Kamar bazata motsa ba dan saida ta kalli Maama kafin kamar an mata dole ta yunkura ta tashi.

A wani wulakance ta kalli Batul kafin tace, "Sai ki taso muje ai." Fuu ta wuce ko tsayawa kallonta batai ba. Jiki na rawa kamar zata fadi haka Batul ta mike ta bita. Har kusan zamewa tayi ta fadi kan tiles dinsu da sai sheki yakeyi kamar baa taba takashi ba.

Gudun kar ta tsere mata yasa ta rika gudu-gudu sauri sauri har Allah ya taimaketa ta samu ta cimmata. A kasa dakin yake, dama tanata Allah Allah kar ace a saman bene yake. Gani tayi ta tsaya bakin kofar tana wani harararta cike da tsana da kyama. "Ga dakin nan. Zan aiko kuku da abincinki." Saida ta watsa mata wani kalar kallo kafin ta juya ta wuce tana furta wasu kalamai da yaren fulatanci.

Wani kalar kududu ne ya tsaya ma Batul a zuciya dan kuwa tasan koda ace bata girmi yarinyar ba to tabbas bazata zama kanwarta ba saidai ace suzo shekaru daya. A hankali jiki a sanyaye ta bude kofar dakin, wani kalar kamshi da sanyin AC ya daki hancinta saida ta lumshe ido. Shiga tayi ta maida kofar ta rufe kafin ta karasa bakin gadon, a han ta hango jakar kayanta tana mamakin ya akayi jakar ta iso nan.

Zama tayi bakin gadon tayi shiru kafin ta mike ta shiga kofar da take kyautata zaton itace toilet. Wanka tayi tayo alwalla dan kuwa lokacin sallar azahar yayi. Bude jakarta tayi ta zaro wata doguwar riga ta saka ta saka hijab tana tunanin inane gaban domin tayi sallah. Can taji ana kwankwasa kofa, jiki a sanyaye taje bakin kofar ta bude.

"Husna tace na kawo maki abinci amma abincin be ida ba tukunna, shine na kawo miki snacks kafin ya karasa." Kukun ta kalla namiji ne da irin kayan girki a jikinshi.

Hannu ta miki ta karba farantin daya zubo mata snacks din a ciki. "Nagode," ta furta murya a sanyaye. "Amma dan Allah inane gabas inaso nayi sallah ne," ta tambaya tana kallon dakin irin ta kasa ganewa dinnan. Gabas din ya nuna mata ta mashi godiya kafin ta koma ta rufe dakin.

Sallar ta farayi tukunna tana zaune tana tasbihi tana kara rokon Allah ya saukaka mata zama da mutanen nan dan kuwa tun batayi awa daya cikakka ba cikin gidan nan ta tabbatar ma kanta cewar zata gane kurenta sosai ba kadan ba. Kara ji tayi an kwankwasa kofa ta mike tana gyara hijab dinta har takai bakin kofar dakin. Budewa tayi taga daya daga cikin yan mata ta cika ta tumbatsa kamar zata fashe. "Kizo parlour Abba yace muyi lunch." Tana fadin haka ta wuce fuuu kamar ta tashi sama. Batul da bala'in hanzari tabi bayanta dan kuwa Allah ya sani bata iya maida kanta wannan falon da suka baro dazu.

Tana shiga idanuwa sukayo kanta caaa kamar ta nutse. Saida taja dogon numfashi tukunna ta daga ta kalli kowa. "Ina yini, Abba," ta gaida shi. Sai ta juya, "Ina yini Maama?" Murya can kasa ta gaidasu tukunna ta taka sai kuma ta tsaya cak dan batasan ya zatayi ba. Kar ta zauna kan daya daga cikin kujerun dining din tayi laifi.

"Gaskia Alhaji bazan yarda ace wai damu zata rika cin abinci fah. Kai da kanka kace man me aikin gidan abokinka ce, daga taimako sai kuma ace family time din namu kuma sai munyi da wata bare? Ka hana ta zauna bangaren masu aiki can baya yanzu kuma ace damu zataci abinci?..." Maama ce ke magana cike da masifa. Hadawa take da hausa, da fulatanci da turanci duka tana bala'i.

"Haba Hajia, minene a ciki dan yarinyar nan ta zauna munci abinci gaba daya? Wani abu zai rageki dashi ko wani daga cikinmu?" Ta lura da yarda Abba ke lallaba Maama cikin taushi. Wata kila gudun rigima yake ko kuma yana gudun ya kara tado da wata husumar dan Allah kadai yasan yanda sukayi kafin ma ta yarda Batul din ta zauna.

"Indai zata zauna a rika cin abinci da ita a table dinnan to gaskia zan koma bangarena da cin abinci. In hakan yayi maka daga yanzu ma sai na fara," Maama ta fada tana kumfar baki tana kokarin mikewa tsaye.

Hannu Abba yayi mata irin alamar dakatarwa, "Aa abun be kai nan ba." Ya furta yana sauke ajiyar zuciya. "Amm..." juyawa yana kallon yaran da ke kallon Batul kamar su tashi su lakada mata bugun bala'i sai kuma ya kalli Batul din. "Fatima, zo ki zuba abincin ki koma daki dashi kinji?" kafin ta motsa sukaji motsin shigowar mutun falon, "Yauwa barshi ba, yi tafiyarki daki. Khalil, zo ka zuba abinci ya kaima Fatima guest room." Ya fada cikin muryar bada umurni kafin ya juya ya koma kan abincin dake gabanshi.

Ita dai Batul dukar da kanta tayi tanajin Maama na masifar wai Khalil ne za'a saka ya kaima me aiki abinci sai kace wani yaro, kafin ta fita falon sumsum kamar wata munafuka gabanta na tsananta faduwa. Ita tashin hankalinta bai wuci wannan tsanar datake gani a idanun mahaifiyar Khalil da kannenshi ba. Wai a hakan ma sun dauka a matsayin me aiki take a gidan, inaga sunji cewar ita matar Khalil ce? Har wani rawa jikinta yayi da tayi imagining abunda zai iya faruwa in hakan ta faru. Sai taji kwata kwata bazata so ace sunsan matar Khalil bace har abada. Dan wannan dakyar in har bazasu iya kasheta ba idan sukaji.

Tana daki zaune tana ta tunanin ya zatayi da rayuwarta? Ita wannan shine karo na farko data taba zuwa Adamawa bata taba zuwa ba kuma batasan kowa ba a garin balle tace zataje can. Ko cikin gidan nan ba lalle bane ta iya fitar da kanta balle tace zata bazama cikin gari. Kuma inma ace tana da inda zataje, auren Khalil da yake kanta tayi yaya dashi?

Tana cikin wannan tunanin taji an kwankwasa kofar saida gabanta ya fadi. Dukda cewar tasan shi zata gani a kofar hakan be hana gabanta faduwa ba lokacin data ganshi. Saida ta dan ja numfashi ta natsar da kanta kafin ta daga ta kalleshi karaf kuwa suka hada idanu ta maza ta dauke nata. Wayyo Allah! Wani kalar mutuke fuska yayi kama yaga an aiko mashi da sakon mutuwarshi. Nan take tsoronshi ya darsu a zuciyarta dan ba makawa tasan shima ya natse.

Ko dayake, dole ya tsaneta mana. Mutum saura sati biyu aurenshi ace an makala mashi wata matar wadda ko asalinta bai sani ba balle ayi maganar soyayya ma. Wanda mahaifiyarshi da yan uwanshi da daukacin al'umma kema kallon bare kuma bama su yarda da addininta ba. Ko itace bata tunanin wai bazata ki tsanarshi inda itace a shoes dinshi.

"Nagode," ta furta da hanzari tana karbar plate din ganin ta barshi tsaye rike da abubuwa a hannu. Bai kulata ba kawai ya juya ya wuce. Tsayawa tayi bakin kofar tana kallonshi. Wannan wace irin biyayya yakewa mahaifinshi haka da har ya yarda da auren nan kuma suka hada baki akawa mahaifiyarshi karya kawai dan a zauna lafiya.

Jiki a sanyaye ta koma dakin taci abinci. Daga dan kishingidawa kawai bacci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai can gab da maghrib. Allah yaso akwai agogo a dakin ta duba taga lokacin. Alwalla tayi kai tsaye kafin ta gabatar da sallar la'asar ta zauna tana jiran a kira maghrib tayi. Tunani ne cike dam cikin zuciyarta. Yanzu ta ina zata fara? Me zatayi miye bazata yi ba? Me zata kiyaye kuma? Gashi ba waya hannunta balle ta kira Hajia hauwa ta bata shawara. Bata lura ba saidai kawai taji hawaye na sauka saman kuncinta a haka har aka kira sallah.

Fitowa sukayi a tare daga masallaci, dukda a tare suke tafiya babu wanda yake cewa dan uwanshi wani abu. Sun kusa karasawa cikin gidan ne Abba ya juyo ya kalli Khalil daya hade rai daka ganshi kasan tunani ne fal cikin ranshi da kuma tsantsar bacin rai.

"Haushi na kakeji ko Ibrahim?" Ya tambaya da murya me taushi irinta mahaifin dayasan yaronshi kuma sukeda kyakyawar fahimta a tsakaninsu.

Khalil juyowa yayi ya kalli Abba kafin ya kirkiri wani guntun murmushi yana girgiza kai. "Aa Abba, haushinka kuma? Ni baka man komai ba balle naji haushinka." Ko kadan Khalil ba mutum bane mai yawan magana, da Abba ne ma zakaga sun zauna sun dade suna magana shima kuma rabin maganar harkar kasuwanci ne.

Yar dariya Abba yayi, "Aa Khalil a fadi gaskia. Yau dan Abba dai yana fushi dashi. Kayi hakuri kaji? Wata rana zakayi alfahari da abunda nayi. Munyi da niyya me kyau, kuma da niyyar taimako, muma insha Allahu Allah zai taimaka mana ya bamu taimako a ranar da muke cikin tsanani. Karka bari abun nan ya dameka kaji? Nan gaba kadan bayan auren naka sai musan yanda zaayi a fitar da maganar."

Dukar da kanshi kasa yayi yana jin wani bakin ciki yana mamaye zuciyarshi. Shi bai san wani kalar mutum Allah ya basu a matsayin mahaifi ba. Fisabilillahi wannan wace kalar rayuwa ce?

"To Abba insha Allahu, nagode." Ya furta murya can kasa yana jin kamar ya kurma ihu tsabar bakin ciki.

Tsayawa Abba yayi dan kuwa sunzo daidai wajen inda kowa zai wuce bangarenshi. "Cikin yan kwanakin nan kana iya daukarta kuje ka siya mata kayan sakawa, naga bata dauka wasu kaya ba kuma kaga ga taron biki za'ayi bai yiwuwa ace tana yawo ba sutura kaji?" Abba ya furta.

"To Abba, insha Allah." Daga haka Abba ya wuce bangarenshi, Khalil kuwa tsanar kunar da zuciyarshi take mashi juyawa yayi inda ake parking din motoci ya shiga motarshi ya bar gidan. Har wani kalar tafasa zuciyarshi ke mashi.

Yanzu fisabilillahi shi ya zaiyi da Yusrah? Ta ina zai fara? A tsarinshi mace daya wallahi ta isheshi, yanzu gashi Abba yaje ya janyo mashi wannan yarinya, Batul take da suna ko Fatima ne ma oho mata.

Yana cikin wannan tunanin kirin Yusrah ya shigo wayarshi, saida gabanshi ya fadi dan gani yake kamar ta riga da tasan abunda yake faruwa ma.

"Hello Babe," ya furta cikin sanyayyar murya.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top