2
Ruwa taji an shara mata kamar da bakin kwarya. Numfashi dogo taja tana kokarin motsa gabobinta taji wanne ya karye. Dan dukda ta suma bazata gane iya adadin dukan da suka mata tasan ba karamin duka aka mata na dukda tana saka ran anyi saurin cetonta kafin su illatar da rayuwarta.
Da kyar ta samu ta bude idonta amma koda ta bude hasken rana ya kashe mata idon dole ta maida shi ta rufe tana jan numfashi da kyar. Tanajin yanda jikinta ke nukurkusa yana mata wani kalar ciwo tsabar yanda ta jigata.
"Daukarta ka sata mota Khalil," taji muryar wanda ta tabbatar da shine mahaifin Khalil dukda bata gama sanin muryoyinsu ba. Kamar ta bude ido ta zura da gudu haka taji. Amma motsi kwakkwara ma ta kasa balle har ayi maganar tafiya.
Saida aka dauki tsawon minti biyu, dukda tana jiyo hayaniya da muryoyin yan uwanta maza wanda take kyautata zaton yan hisban da suka zo dasu ne suke kokarin kawo daidaito a lamarin. Can taji Baban ya kara cewa, "Daukarta mana, ko sai rana ta gama dukanta tukunna?" Yanayin yadda yayi maganar tasan ko Khalil baiyi niyyar abunda mahaifinshi ya umurceshi da yayi ba to tabbas dole yayi.
Cikin wasu yan dakiku taji alamar mutum gefenta. Dauke numfashinta tayi gabanta yana wani mugun faduwa. A hankali taji ya dagata cak kamar ba ita danginta ke cema 'me jikin doya' ba. Ta dauka babu wanda zai taba iya daukarta a rayuwa. Amma yanda yake tafiya da ita a hannunshi, dukda bawai ta bude ido ta ganshi ba, tasan ko yanada matsanancin karfi ko kuma ita dince bata da nauyi. Dan ko numfashinshi bataji ya chanja ba.
Motar ya bude baya ya kwantar da ita a hankali. Watakila be dauka tana sane da abunda ke faruwa ba dukda cewar jikinta wani kalar nukurkusa yake. Ji take dama ta kara sunar ko taji sauki. Gaban motar ya koma ya shiga ya kunna. Tunani Batul take to ina zai kaita kuma? Amma jin sanyin AC ya fara sirarowa ba tare daya motsa motar ba, hakan yasa ta gane cewar AC ya kunna mata.
Kara gyara kwanciyarta tayi cikin seat din tanaji kamar ana kwara mata ruwan sanyi, jikinta kuma yana kara mutuwa. Tanajin lokacin daya fita motar ya maida murfi ya rufe, saida tadan saki ajiyar zuciya saboda Allah ya sani duk a takure take. Har yanzu Allah be bata ikon kallon fuskarshi ba, amma kuma kamshin jikinshi data shaka lokacin daya dauko kadai ya isa ya sanar da ita wane kalar namiji ne shi.
Tana wannan tunane tunanen ne, da kuma tunanin yanda za'a kwasheta da yan gidansu har bacci barawo ya saceta.
❧
A hankali taji muryar Hajia Hauwa tana tadata domin ta tashi tayi sallar asuba. Da kyar ta samu ta amsata kafin taja jiki ta zauna tana tunani. Dan kwata kwata kamar ma d'imuwa ke neman kamata. Sai a lokacin ta tuna yanda akai ta kwana gidan Hajia Hauwa.
Tun bayan da aka gama rigima da dangin mahaifinta Hisba suka kama na kamawa kuma akaje commander din hisba ya tabbatar masu yanzu ita din matar aurece kuma mijinta da mahaifinshi zasu tafi ta ita wajensu.
Duk wata rigima dai aka gama tukunna Baban Khalil wanda a yanzu ta fahimci Abba suke ce mashi yace su fara kaita asibiti. Hakan kuwa akayi aka bata magungunan ciwon jiki sannan Malam Zakariyya ya roki Malama Hauwa kan cewar ta kwana wajenta dan gobe jirgin safe zasubi kuma da ita zasu wuce Adamawa.
Tafi minti goma tana tunanin wannan sabon babin da rayuwarta ta shiga kafin tashi ta shiga bandaki. Saukinta daya duk wannan ciwon jikin da take ji duk babu shi yanzu saidai wani irin bala'in nauyin da zuciyarta ta mata kamar zata fashe.
Wanka tayi ta hado da alwallah. Sai a lokacin ta lura da yar jakar kayanta da aka hado mata. Dukda tasan ba duka kayanta bane ciki. Dan kuwa Nne tana mata sutura sosai ba kadan ba. Hadiya wani irin abu daya tsaya mata a zuciyata tayi tanajin wani irin bakin ciki.
Da kyar ta samu tayi sallah ta zauna kan dadduma tana tariyo rayuwarta. Batasan lokacin data fashe da kuka ba tunanin yanzu kuma wannan babin da rayuwa ta bude mata ya zatayi dashi? Ba sai an fada ba tasan dole zatasha wahala.
Dukda cewar a iya lokacin da sukayi da mahaifin Khalil taga tausayinta a idanunshi kuma tana saka ran samun sauki daga gareshi. Amma bangaren Khalil, batasan me zatayi tunani akai ba. Dama ita bawai ta saka rai a auren soyayya bane ko wani abu. Kawai sai yanzu da hankalinta ya dawo jikinta take tunanin ya zasu kwasheta dashi.
Ba kowane namiji bane zai auri mata irinta a yanayin daya aureta kuma ace ya mutunta ta ba. Bama wannan ba, ya aureta ne da zummar ya saketa nan gaba ko kuwa? Ita bama tasan me zatayi tunani ba.
Kuka yake bil hakki da gaske. Dan wani kalar tausayinta kanta ne ya cika mata zuciya. Bataji karar bude kofa ba saidai taji zaman mutum gefenta. Juyawa tayi taga Hajia Hauwa ce zaune ga kuma tray din karin kumallo.
Cikin hanzari ta fara goge hawayen dake cigaba da kwaranyo mata. "Ina kwana, Hajia?" Ta furta tana kokarin gyara muryarta.
"An tashi lafiya, Fatima? Ya kika kwana jiya?" Maimakon Hajia Hauwa tayi yunkurin tashi sai ta kara gyara zama tana riko hannayen Batul cikin nata.
Jin dumin hannunta da kuma yanda take kallonta tamkar yadda uwa tana kallon diyar data haifa cike da tausayi yasa Batul tsaida kokarin da take na danne hawayenta ta barsu suna zarya saman kuncinta.
"Zuciyata zafi take, Hajia. Tsoro ne fal cikin raina. I don't know, bansan ko abunda ya faru ba is the right thing for me. Ina jin tsoro, Hajia." Magana take muryarta tana rawa, asalin rashin iya hausarta yana bayyana.
Maimakon Hajia tayi magana sai ta janyo ta jikinta ta rungumeta tsab. Wani irin marayan kuka Batul ta fashe dashi. Rabon da a rungumeta da niyyar lallashi har ta manta. Tun ranar da Nne ta rasu, shima kuma Nne ce da kanta ta rungumeta tana bata hakuri kamar tasan ranar zatabar duniya.
Kuka tayi sosai ba tare da Hajia Hauwa ta hanata ba. Sai can da taga tayi kukan me isarta ta dago da fuskarta tana share mata hawayenta.
"Kiyi hakuri kinji Fatima? Kowa da kika gani a duniya da kalar jarabtar da Allah yake mashi. Dan ya jarabceki a haka ba hakan na nufin baya sanki ba. Wata sa'in zakiga bawa ya shiga kunci da tsanani a rayuwarshi sai ya dauka tamkar bazai kara shiga farin ciki ba a rayuwarshi, amma idan yayi hakuri ya mika lamurranshi zuwa ga Allah sai kiga a hankali komai ya warware mashi.
"Nasan taki jarabawar akwai wahala. Babu uwa babu uba, babu dangi ko d'aya da zaki iya raba kiji dadi. Sannan ga tsangwamar duniya, rana zafi inuwa kuna. Kiyi hakuri Fatima, kisani Allah yana sane dake. Sannan Allah yayi alkawarin sauki bayan tsanani da wahala.
"Abu daya nakeso dake Fatima, kar kiyi wasa da addininki, kinaji na? Duk rintsi duk wuya karki manta da Allah da kuma addininki. Ki sani duk inda tsanani yakai tsanani, Allah yana tare dake. Kuma Allah yana inda duk bawanshi yake tsammanin shi.
"Ki koma Islamiyya Fatima, kinji? Kiyi riko da Al-Qur'ani domin shi din waraka ne, kinji? Allah be manta dake ba Fatima. Dan Allah karki manta da Allah. Zan rubuta maki number ta kinji? Duk in kina bukatar wata shawara ko wani abun ki kirani kinji? Ki daukeni tamkar mahaifiyarki kinji?"
❧
Kaf zaman da tayi cikin jirgi, a maimakon taji dadi da d'oki na cewar yau ta fara hawa jirgi, amma kalmomin da Hajia Hauwa ta fada mata ne suke mata yawo a kai. Har yanzu Allah be bata ikon ganin Khalil ba kuma hakan ita bema dameta ba.
Lokacin da zasu shiga jirgi ne Abba yaketa bata hakuri kan cewar su Business Class ne seats dinsu kuma duk kokarin da yayi kan ya samar mata seat a wajen itama amma ya gagara domin duka seats din an siyar. Saida aka kama ata economy. Ita yanda yake bata hakuri ma sai ya cikata da mamaki dan bataga wani abu a ciki ba. Zamanta ita kadai ba tare dasu ba sai ya bata daman yin tunani.
Tun tanayi da hawaye har zuciyarta ta kekashe kawai tanata kallon giza gizai. A haka jirginsu ya sauka. Koda tabi ayarin mutane suka wice arrival ita dai kallo kawai take tana tunanin ta wane bangare su Abba zasu bullo. Ganin bata gansu ba yasa ta samu waje ta zauna tanata raba idanu.
Kamar daga sama taji muryar Abba. "Batul!" Sunanta da taji yasa ta dago sai ta hangoshi tsaye shida Khalil dake rike sa jakunansu duka. Sai a lokacin taga fuskar Khalil.
Abu daya kawai zata iya furtawa, 'Fatabarakallahu ahsanil khaliqeen!' Domin Allah yayi halitta a wajen. Duk inda wani namiji yake Khalil yakai. Da ka ganshi kaga zallar bafullatani wanda yayi kyau har ya gaji. Ga kyau, haiba, cikar kamala sannan ga dukiya. Dan ba sai an fada maka kudi sun kwanta ba.
Saida Abba ya yafito ta da hannu sannan ta lura ashe fa tayi tsaye kallonshi kawai takeyi. Dukda kuwa daga nesa ne bazai fahimci cewar Khalil take kallo ba. Da hanzari ta dukar ta kanta ta taka tana karasawa wajensu.
"Abba kayi hakuri ban lura daku bane tun dazu," ta furta murya can kasa tana kallon fararen yatsun kafar Khalil da suka fito daga takalman shi. Hanzarin kauda idonta tayi tanajin Abba yana ce mata babu komai su karasa wajen direba.
Hakan kuwa akayi. Dole Khalil ya shiga bayan mota suka zauna tare da ita, shi kuma Abba yana zaune gaba gefen direba. Kamshin turaren Khalil ya gama cika mata hanci. Sai da suka zauna takunna ta fahimci har yanzu kusan awarsu 48 da zama ma'aurata amma ko kalma daya bata taba shiga tsakaninsu ba. Ita kau ta kawo kanta! Dan bama sai an fada ba ta lura da ba karamin miskili bane.
Tunowa da kalmomin Hajia Hauwa yasa ta fara tasbihi har taji wani sanyi yana shiga zuciyarta. Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Abba.
"Batul kina jina?" Ya furta da murya me tausayi. Muryar mahaifi, wanda hakan ya tuna mata da nat mahaifin data rasa, rasawa kuma ta har abada.
"Na'am Abba," ta amsa tana wasa da yatsun hannunta.
"Nasan ya kamata ace mun samu mun zauna domin tattauna wasu maganganu amma be zama lallai hakan ya samu domin karancin lokacin da nake dashi. Akwai wasu kalilan abubuwa da nakeson sanar dake dangane da ahalinmu.
"Khalil shine yarona na farko kuma shi kadai Allah ya azurtamu dashi namiji. Yanada kanne yan ukku ne dukansu mata ne masha Allah. Nasan duk zaki hadu dasu. Sai kuma mahaifiyarsu. Inaso ki sani sai kinyi hakuri da wasu abubuwan Fatima, kinji?
"Mahaifiyar Khalil macece me zafi amma kuma idan kikayi hakuri kika fuskanceta zaki gane yanda zaki zauna da ita cikin kwanciyar hankali. Da suma kannen nashi, kinji? Abu daya daya rage wanda shine babban abunda naketa tunani tun daren jiya..."
Itadai tunda ya fara magana gabanta ke faduwa, wani sabon tsoro yana cika zuciyarta fal tanata tunani.
"Kai Khalil, ka kuwa fada mata nan da sati biyu ne aurenka?" Saida ta dora hannunta saman zuciyarta dan wani kalar bugawa da kirjinta yayi wanda bata taba tsammani ba.
Tsaya...dama an saka mashi rana ne tuntuni kafin zuwanshi Kano suji tana bukatar taimako kuma dukda hakan mahaifinshi yasa ya aureta ko kuwa yanzu ne? Ita bama tasan me zatayi tunani akai ba.
"Aa Abba," taji Khalil ya furta ko dagowa daga wayarshi da yake kallo beyi ya amaa.
Saida Abba yayi shiru na wani lokaci tukunna ya sauke ajiyar zuciya. "Tohm Fatima, wata hudu kenan da saka auren mijinki Khalil, yanzu haka saura sati biyu aurenshi. Jin bayanin Malam Zakariyya akanki yasa nace bazamuki ceto rayuwarki ba."
Dan juyowa Abba yayi yana kallonta tayi maza ta dukar da kanta. "Nagode Abba, Allah ya saka maku da alkhairi. Duk abunda ka umurceni zanyishi cikin farin ciki. Bazan taba iya saka muku da irin taimakon da kuka man ba. Nagode, Allah ya biyaku da aljanna, Abba."
Tana fadin haka ta dukar da kanta, batayi kokarin share hawayen da suke neman gangaro mata ba domin kuwa tasan tabbas sakinta Abba zaisa Khalil yayi. Domin kuwa ya za'ayi kawai daga zuwa Kano taron kasuwanci su dawo gida da mata? Kuma matar ma yare? Inyamura? Dukda cewar musulma ce, ta tabbatar bazata taba kaucema lak'abin k'abila ba.
Gyaran muryar da Khalil yayi yasa ta runtse ido. Kila sakinta zaiyi sai kuma su koreta. Yanzu ina zataje?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top