12

Abu kamar wasa haka Batul takeji. Abba tsaye yayi kanta saida ta hada duk kayanta dake cikin dakin tukunna shi da kanshi ya rakata bangaren Khalil, shi ya nuna mata dakin da zata shiga kafin ya juya ya wuce. Tsoro ne fal zuciyar Batul, so take ta rokeshi akan ya barta ta zauna dakin data saba amma yanda Abba ya daure fuska tamau kamar bai taba dariya ba yasa tayi gum da bakinta amma ko ba'a fada ba Batul tasan Abba ya janyo mata wani bala'in da sai tayi kukan jini kila.

Ya hana a sakata aikin da ake saka masu aikin gidan dan har karo yan aiki su biyu yayi cewar duk abun da takeyi su su rikayi, ko kallon banza Maama bata mata ba. Kullum da safe zataje ta gaishe da su amma har rana irin ta yau Maama daidai da inda take kallo bata karayi ba. Jiya Abba ya tafi Lagos kamar yanda ya saba kuma bata tunanin zai dawo nan kusa dan taji Hanan tana tambayarshi yaushe zai dawo yace mata sai yaje Germany ko can zai iyayin sati biyu kafin ya dawo Nigeria.

Saida cikinta ya kada jin wannan maganan dan tasa a wasa wasa Abba yana iya yin wata biyu ma bai dawo gidan ba. Ko sati shida. Ta ina zata fara? Tunda Abba ya tafi da safe taje gaishe da Maama bata tanka ba dan har yau bata kara ansa gaisuwarta ba.

Tsugunnawa tayi yanda ta sabayi tace, "Hajia wane aiki zanyi?" Kullum sai ta tambaya kuma kullum bata samun amsa amma haka kawai yau takeji a jikinta zata samu amsa tunda dama wanda yake bata kariyar baya nan.

"Uban aiki zakiyi, kin jini ai ko? Munafuka, kafura kawai. Zaki bace man da gani ko sai na lakada maki shegen duka? Wacce babu Allah a ranta, kinzo kawai kin asirce man miji yanata abubuwa kamar bashi ba." Ko baka kalli Maama ba kanajin sautin muryarta zaka san abunda take fadi har kasan zuciyarta yake. Allah kadai yasan me Abba ya mata dan idan ba abun yayi girma ba bazata taba barin Batul tasha iska ba balle ma yau da baya nan.

Haka nan Batul jiki a sanyaye ta juya ta koma bangaren Khalil. Sai can yamma lis ta fito dan ta samu abunda zataci amma saidai bataga abincinta inda aka saba aje mata shi ba tun bayan bikin Khalil. Daya daga cikin masu aikin da Abba ya dauko ta gani ta tambayeta abincinta fah. Da yarinyar ta duba bata gani ba sai tace bari taje ta debo mata akan dinning.

Da farko Batul taso ta hanata amma jin har jiri take gani yasa tayi shiru ta tsaya jiranta. Dan har ga Allah in bataci abinci ba zata iya mutuwa takeji. Kuma tana sane tasan Maama so take ta horata da yunwa har taji bata iya jurar zama ta gudu ko tace ma Abba ta gaji ya maidata gida. Abincin ta kawo mata dan ita batasan matsayin Batul na da ba, wani kalar girma take bata a cikin gidan.

Godiya sosai Batul ta mata kafin ta koma bangaren Khalil tun a kan hanya ta fara cin abincin dan rabonta da abinci kusan kwana biyu kenan yanzu a tsaitsaye. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya mata, sai ta yini zungur bata saka komai a bakinta ba sai ruwa sai can da daddare ta lallaba ta samu Kamila ta dan debo mata sauran abincin da yan gidan suka rage. Godiya take mata ba adadi har ya zamana sun dan fara sabawa da ita.

Yau ma kamar dukda tana jin yunwa kuma tasan sai dare ne kawai zata iya zuwa ta samu Kamila ta debo mata abincin ba tare da kowa ya gani ba. Zaman kadaicin ne ya isheta ta fito da yamma ta dan zauna cikin rumfar dake kusa da bangaren da masu aikin gidan ke zaune. Giftawar Kamila ta gani ta daga mata hannu da murmushi a fuskarta. Cikin sati dayan da Abba yayi har ta rame idanunta sun dan shige ciki.

Saida Kamila taje inda zata sai gata ta dawo ta zauna kusa da ita. "Batul, yau lafiya na ganki da yamma a waje? Ko abincin kikeso na debo maki?" Har yanzu Kamila batasan wane kalar zama Batul takeyi ba a cikin gidan, ita duk daukarta itace batasan fitowa da rana sai dare, batasan dabara takeyi ba.

"Aa Kamila, banajin yunwa yanzu sai zuwa daren dai. Kawai na fito naga hasken rana ne, na gaji da zama cikin gidan shiru haka." Wayarta dake hannunta ta aje, dukda da wayar da calculator banbancinsu kadan ne. Har yau babu wanda ya taba kiran wayarta itama babu wanda ta kira. Babu data balle tayi downlaoding koda game ce ta rikayi.

"Laah, wai wayarki ce wannan?" Kamila ta tambaya tana daukar wayar daga kan cinyar Batul tun kafin ta amsata. Juya wayar takeyi tana washe baki cikin mamaki dan Kamila irin yaran talakawan nan ne amma wanda idonsu idon abun duniya. Wanda zaa iya cema Allah ya ragewa aya zaki. To babu abun gayun da bata sani ba da kuma yanda ake amfani dashi, kawai dai saidai ace bata dashi ne.

"Batul, dan yiman hoto dan Allah," wayarta ta mikowa Batul din bayan ta shiga camera ita kuma ta rike iphone din Batul tana wani posing dama ga background me kyau. Duk hotunan saida ta tabbatar bayan wayar Batul ya fito yanda zaa gane. Bayan an mata sun isheta tace Batul ta jira taje ta sanyo wasu kayan.

Ai kuwa har kusan maghrib Batul na aiki daya, sai chanja wurare suke ita kuma Kamila tana chanjo kaya ana mata hotuna wasu da wayar Batul din wasu kuma da tata saboda tanaso wayar Batul din ta fito a hotunan. Saida aka gama ne har an fara kiraye kirayen sallar maghrib sai Kamila ta miko mata wayar tace dan Allah ta turo mata ta whatsapp.

"Bana whatsapp, Kamila," Batul ta fada cikin ruwan sanyi. Ai kamar jira take, nan ta amsa dama akwai kati a cikin layin ta sai mata data kafin ta mata downloading whatsapp da instagram da kuma youtube sai games da Batul din tace mata tanaso. Karshe dai bangaren Khalil din suka koma tare Batul ta tayar da sallah tabar Kamila nan zaune a bakin gado tana aikin latsa waya, sai tayi tayi sai ta juyo ta kalli cameras din wayar tana cewa 'wayyo dama ni!'

Kamila bata bar bangaren Khalil ba saida ta tabbatar wayar Batul ta zama me anfani. Saida tayi adding dinta a wasu groups din novel saboda Batul tace mata tanasan ta dan rika karatu zaman shiru da tunani ya isheta. Ta tura hotunan karshe yau ita taje ta debo abincin ta kawo mata nan ba tare da Batul taje ba, sai can bayan isha'i ta tashi ta koma bangarensu.

Sai ya zamana Kamila ta maida bangaren Khalil wajen zamanta. Dan har abincin ba kullum Batul take fita ta karbo ba wani lokacin ita take kawo mata da kanta. Ranar kawai ta fito falo bayan tayi sallar la'asar sai ganin Kamila tayi da wani namiji zaune a kan kujerun daka gani kasan soyayya suke zabgawa dan zaune suke jikinsu yana gugar na juna.

Da wani kalar tashin hankali Batul ta kalli Kamila wadda hankalinta kwance. "Aunty Batul ga Jamilu ku gaisa, na shigo naga kina bacci sai yace a bari sai kin tashi sai ku gaisa." Da kyar Batul ta iya gaisawa da saurayin dan ji take kamar zuciyarta zata fito kirjinta.

"Kamila zo kiji," Ta furta hakan da yar rawar murya tana komawa cikin dakinta.

Tana shiga Kamila ta biyo bayanta tana murmushi hankalinta kwance. "Kamila bala'i kikeso ki jaman ko me? Minene haka kawai zaki kawo namiji har tsakiyar falo, Kamila? Wannan wani irin abu ne? Kawai saidai na fito inga namiji? Ni banma san me zance ba, na shiga ukku." Zarya kawai takeyi tsakiyar dakin ji take kamar zuciyarta ta fito ta huta. Yanzu idan Maama ta gani fa? Me zatace masu? Wannan wace kalar jarabawa ce?

"Ji Batul, miye abun tashin hankali a ciki to? Kawai zuwa yayi mu gaisa fah, ai ba laifi bane. Kuma naga kina bacci..."

"Dan girman Allah dakata, Kamila. Wallahi ni kaina da kika ganni a wannan bangaren bakisan dalilin zamana a nan ba, kina gani ban isa naci abinci ba sai kin taimaka kin debo mani shima cikin dare. Ki tausaya ma rayuwata ki sallami bawan Allahn nan ya wuce tun kafin masu gidan nan su fuskanci wani abu, wallahi ban shirya shiga wani tashin hankalin ba." Hawaye har sun fara taruwa cikin idanunta.

"Kamar ya in sallameshi? Yanzun nan fa yazo. Kuma in sallemshi ince mashi ya tashi ya tafi kar masu gidan su ganshi ko mi? Nifa ce mashi nayi gidan aunty dita ne gaskia saidai kiyi hakuri ba jimawa zaiyi ba." Tana fadin haka ta juya sai a lokacin Batul ta lura wayarta ce hannun Kamila.

Ai batasan lokacin da tabi bayanta ba, suna tsayawa tsakiyar falon saurayin ya juyo yana kallonsu. "Bawan Allah, in rokeka? Dan girman Allah ka rufa man asiri kaji? Dan Allah kazo ka wuce, ka taimaka ma rayuwata kar masu gidan nan su iske ka a wajen nan, dan girman Allah."

Wani kalar juyowa Kamila tayi dan bata dauka Batul zata biyo bayanta ba. Dan dan zaman da sukayi ta fuskanci hakurinta da kuma tsoron rigima, bata taba tsammanin cewar zata mata wannan cin fuskar ba. "Kamar ya ya taimaka ya tafi? Wai Batul miye haka?"

Ko kallon inda take Batul batayi ba ta karasa inda yanzu Jamilu yake a tsaye yana masu kallon mamaki. "Babe, lafiya ko? Ban gane abunda ke faruwa ba." Ya furta yana kallon Batul da zuwa yanzu hawaye take share share tana kallon kofa dan gani take a koda yaushe wani zai iya shigowa cikin bangaren.

"Ba maganan Babe bane. Kaga gidan nan? Masu shi masifarsu da bala'insu yafi karfina wallahi..." Ai bata karasaba Kamila ta wani bangajeta saida ta kusa faduwa ta dafe bango ta saita kanta tana binta da kallon mamaki.

"Ni kike kokarin cima fuska Batul? To ki rubuta ki aje wallahi sai kinyi dana sanin abunda kikaman. Kuma bala'in da kike gudu sai a tabbatar ya iskeki yau dinnan ba gobe ba. Banza kawai mara mutunci." Kamila na gama fadin haka tayi wurgi da wayar Batul saman kujera taja hannun Jamilu suka nufi bakin kofar fita shi kuwa sai kokarin kallon Batul da take wani kalar kuka kirjinta kamar zai fito waje.

"Dakata mana Babe, maganar me kukeyi? Meke faruwa ne wai? Baki ganin sai kuka takeyi, ko wani abun ya faru ne?" Ya tambaya a sanyaye yana kallon Batul da take girgiza kai. Dan ko Kamila batayi maganar nan ba dama can hankalinta a tashe yake balle tayi.

Fuzgoshi Kamila tayi tana nufar kofa. Tana bude kofar ta hango Maama tana raka kawarta zuwa mota, Batul saura kiris ta fadi kasa. Da wani kalar daga murya Kamila ta furta, "Hajia! Na kama kwarto! Hajia, zo kigani!"

Da gudu Batul ta nufi bakin kofar tana kallon Kamila da idonta ya rufe ruf da tijara da kuma jan sharri. "Kamila, kwarto kuma? Kamila sharrin da zaki mani kenan? Kamila!" Da karfi take magana tana girgiza kai.

Ai Kamila bata yi shiru ba har saida suka karasa gaban Hajia da kawarta da suke kallonsu da wani mugun mamaki. "Ke dallah daka man, yi magana yanda zan fahimce ki." Hajia ce ta fada a fusace da fulatanci tana kallon Kamila dake huci.

Da yaren fulatancin wanda Batul ta fuskanci Fawad ba wai yana ganewa bane, kila shima ba dan garin bane, haka Kamila keta jero zance tana fadawa Hajia wadda yanzu haka hannayenta duka biyu suna kan kirjinta tana kallon Batul da wani kallon tsana da tuhuma.

"Me gadi! Fitar man da wannan kwarton tukunna, kuma ko kusa da gidan nan banso in kara ganinshi!" Hajia ta furta cikin harshen turanci. Cikin minti daya kattin dake gadin kofar gidan sukazo suka finciki Fawad sukayi waje dashi a wulakance, kwata kwata ma ya kasa magana sai Batul da yake kallo tana wani kalar mugun kuka mai tsuma zuciya.

"Dan Allah ka tsaya ka fada masu gaskia. Kamila karki jaman sharri, ku rufa man asiri, na shiga ukku, wayyo Allah na." Kuka Batul takeyi sosai kamar ranta zai fito daga gangar jikinta.

"Kamar ya in ja maki sharri? Duk abubuwan da nake rufa maki asiri akai? Hajia, kinga fa wayar dake hannunta, kuma na tabbatar shi ya siya mata." Kamila ta furta kanta tsaye tana kallon Batul ido cikin ido da irin kallon nan na 'na fada maki, kafin ki wulakanta ni, ni sai na wulakanta ki'.

Wayar da Kamila ke mikawa Maama Husna ta karba tana juyowa dan zuwa yanzu hayaniyar da akayi yasa dukansu sun fito. "Maama, iphone13 ce fah! Almost a million, ina wannan kafirar ta samo wannan wayar?" Ta juya tana watsawa Batul kallon kyama da tsana.

Batul babu abunda takeyi sai kuka tana kallon Kamila tana girgiza fuska. "Kamila karki jaman sharri, Kamila ki taimaka ki fada masu gaskia. Wallahi Hajia saurayinta ne yazo, aban sanshi ba, Hajia..." wani kalar mari da Maama ta saukewa Batul shi yasa tayi shiru tana kara zubar da hawaye.

"Kuji man yar iskar yarinyar nan. Dama maza kike kawo man a cikin gida? Dama karuwancinki kikeyi shiyasa kikayi ma Alhaji asiri ya maida ki can bangaren da babu wanda zaisan abunda kikeyi? Yanzu haka kila har cikin shege gareki a cikin wannan kafirar marar taki ko?"

"Hajia, wallahi tallahi..."

"To ubanwa ya siya maki wannan wayar? Haka nan dai namiji be baki wayar data kusa miliyan daya babu dalili, dan ubanki bayani zakiyi!" Hasna ce tayi magana tana dungurinta har saida tayi baya ta kusa faduwa.

"Dan Allah ku saurareni..."

"Bafa zan zauna da wannan yarinyar ba Allah ya sani! Ga kafirci, ga karuwanci ga munafunci, wallahi bazan iya ba!" Masifa Hajia takeyi kamar numfashi ya daina fita. Kowa zaginta yake ta inda suke fita ba tanan suke shiga ba. "Wannan daga gani kema shegiya ce, daga gani karuwancin da uwarki ta saba yi shine kika gada kema zakizo kiman a cikin gida? To wallahi kinyi karya."

Bude gate din da akayi ne yasa suka juya suna kallon motar har ta iso kusa da inda suke akayi parking. Khalil ne ya fito cikin motar yana mamakin ganinsu a tsaye haka. Ko inda Batul take bai kalla ba ya juya ya kalli Maama dake kallonshi da wani abu a fuskarshi.

"Khalil, zo kakai man karuwar yarinyar nan asibiti, ai mata awon ciki dana HIV da duk wani STI kana jina?" Maama ta furta tana wurga ma Batul dake durkushe a wajen tana kuka.

"Wallahi karya take mun, wallahi banyi ba."

"Me yake faruwa ne, Husna?" Khalil ya tambaya yanajin wani abu a cikin zuciyarshi. Wata kila wannan ya zama sanadin da Abba zai yarda ya sawwake wa yarinyar nan kowa ya huta.

"Hamma, ashe maza take kawowa cikin gidan nan. Kamila me aiki tasha kamata yau dai tace bazata rufa mata asiri ba, yanzun nan security suka fitar da gardin. Kaga fa ashe iphone13 ce a hannunta, ko wa yabata cikin mazan nata oho." Tunda akai maganar wayar ya juya ya kalli Batul itama shi take kallo. Sauri yayi ya dauke idonshi.

"Maama, bazaku iya bari na dan ci abinci na huta ba? Wallahi na gaji, zuwana garin kenan fah," ya fada yana dan bata fuska alamar da gaske ya gaji din.

"Uban hutawa zakayi. Allah ya kawo man dalilin rabuwa da wanan kafirar yarinyar shine zakace wai sai ka huta? Idan bazaka ba akwai drivers a gidan, ko Hasna zata iya kaisu."

"Bance bazanje ba, kiyi hakuri." Yana furta haka yayi wajen motarshi. "Duk wanda za'aje dasu su taho muje." Duk da fulatanci suke magana suke magana ita dai Batul babu abunda takeyi banda kuka. Bata fahimci abunda ake nufi ba saida Hasna ta wani hankadata ta fadi kasa warwas tana kuka mai tsuma zuciya.

"Dallah tashi mu tafi, ko so kike sai an maki dukan da shegen kafirin cikin naki zai zube tukunna?" Kasa magana Batul tayi wani sabon babin kukan takeyi tanaji dama ta tashi kawai ta fita karta kara waiwayar wadannan mutanen marasa imani da tausayi.

Wata tsawa da Maama ta buga mata yasa ba shiri ta mike da sauri har tana tuntube taje wajen motar ta shiga. Tana shiga Husna tayi maza ta matsa can gefe wai karta shafa mata kazanta. Kanta ta duke saman cinyoyinta tana wani gunjin kuka har suka isa asibitin.

Bayan an debi jininta Hasna da Husna fita sukayi wai zasu iyo ruwa sunajin kishi aka barta daga ita sai Khalil da yake latsa waya ko kallon inda take baiyi ba.

"Wallahi tallahi Hamma banyi ba. Kai ka siyo man wayar nan, amma inajin tsoro na fada waya bani. Wallahi saurayin Kamila ne, sharri kawai taja man dan nace ya tashi ya fita. Wallahi banyi ba."

Maimakon Khalil ya nuna ma yanajin abunda take furtawa sai ya kira waya. "Hello Babe," ya furta da wata kalar sanyayyar murya yana sakin wani murmushi. A take Batul taji wani abu kamar mashi ya caki zuciyarta kamar zata fashe. Dukar da kanta tayi kasa idanunta na digar hawaye.

Waya yakeyi sai lallaba Yusrah yake suna soyayya gwanin dadi Batul tana saurarensu. Duk kalma daya dazai furta ji take kamar yana diga mata wuta a cikin zuciyarta. Yana cikin waya sai ga likitan ya dawo office din yana kallonsu da wani abu a fuskarshi.

"Doctor, menene result din?" Ya tambaya bayan yacewa Yusrah yana zuwa zai kirata.

"Batada HIV ko wani STI Khalil, amma tana dauke da ciki, but bansan watan cikin nawa ba sai anyi scanning..." Da wani kalar sauri Khalil ya juyo yana kallon Batul dake kallon likita kamar idanunta zasu fado.

Mikewa tayi tsaye ta karasa a gaban teburin likatan. "Wallahi karya kake. Kaima baka jin tsoron Allah! Sharrin zaka man, wallahi banda ciki a jikina! Wallahi..."

"Kiman shiru ko?" Kalmar da Khalil ya furta kenan yana kallonta da wani kalar mixed emotions a fuskarshi. Yaji dadi dan zai iya amfani da hakan ya saketa, amma kuma wani bangare na zuciyarshi zafi yake mashi wanda baisan dalilin hakan ba.

"Bazanyi shirun ba. Idan kuna san rabuwa dani ku rabu dani, amma bazan iya zaunawa inaji ina gani kuja man sharri ba. Wallahi karya kuke ku duka! Mugaye azzalumai wanda basu tsoron Allah!" A wani kalar hirgice take magana tana nuna Khalil da yatsa.

Maganganu take zarowa tana jifansu dashi wanda saida Khalil ya sharara mata mafi kafin tayi shiru tana kallonshi da wani kalar tsananin kunci a cikin idanunta. Wallahi bata da ciki, amma tasan wannan tsarin nasu ne dan su samu su rabu da ita. Ita kuma koda zata rabu dasu bada wannan hanyar ba, Allah shine shedarta. Wallahi tasan bata da ciki!

Karshen preview chapters 😍❤️ Zaku iya samun complete littafin a kan naira 1500 while it's ongoing, daya zama fully complete zai koma 2000 insha Allah zuwa karshen August 2024.

Kuyi man message ta WhatsApp ko Telegram: 08132526951

Nagode❤️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top