11

Tunda Khalil ya fara magana takejin wani kalar mugun bugun zuciya. Kamar yanda taji ranar da suna asibiti da Nne, wanda ranar ne ta rasu. Likitoci suna saman kanta zuciyar Batul babu abunda take banda bugawa cikin tsanani tanajin wani sanyi yana ratsa jikinta. Wata kalar fargabar da bata taba ji ba takeji a ranar. Yanzu kuwa dukda a zaune take ji takeyi kamar ta koma ta kwanta dan kowacce lakka ta jikinta ta mutu.

Abba yafi minti biyar yana kallon Khalil amma ya rasa abunda zaice mashi. Shi kuwa Khalil dukar da kanshi kasa yayi yana addu'ar Allah yasa Abban ya fahimci bayaninshi dan wallahi har kasan zuciyarshi abunda yakeso kenan kuma a duk maganganun daya fada babu wanda yake karya a ciki.

"Ibrahim, da kanka kake wadannan maganganun? Ko kuwa shafar aljanu ka samu tsakanin jiya da yau?" Murya a natse Abba yake magana dan wannan kadai ya isa ya saka ka gane cewar ranshi ba karamin baci yayi ba.

Kara dukar da kanshi Khalil yayi yana dan jinjinawa. "Kayi hakuri ya yafe mani, Abba. Wallahi karshen gaskia ta nake fada maka, Abba..."

Mikewa tsaye Abba yayi yana kallonshi da wani kalar abu a cikin idonshi. "Ai da kasan abunda zakace man kenan, da tun ranar danace ka aureta ka musa man. Kaga ni sai na aureta da kaina, inma uwar taka mutuwa zatayi saidai tayi. Amma ka bani mamaki, Ibrahim, ashe dama tuncan ban isa dakai ba."

Da wani kalar yanayi Khalil ya dago ya kalli Abba wanda idanunshi har sun juya sun chanza kala tsabar wani kalar bakin cikin dayaji. Shi ba wai dan Khalil ya roki ya saki Batul bane abun ya bata mashi rai. Saboda koshi da kanshi a wasu lokutan yasan ya shiga hakkin yaron. Amma dan cin fuska da rashin mutunci kalli irin maganganun da yayi a kanta kuma tana zaune tanaji har yana daga ido ya kalleta? Be taba sanin Khalil baida mutunci ba sai yau. Kuma sai ya tabbatar ya koya mashi hankali.

"Abba ba haka..." babu tsawa babu komai Abba ya tsayar dashi.

"Ka nuna man ka cika dan zamani, Ibrahim. Kuma nagode Allah ya saka maka da alkhairi." Abba yana furta haka ya juya kan Batul data kafe bango da ido ita kanta batasan abunda take tunani ba. "Fatima..." Abba ya kira sunanta a hankali.

Juyowa tayi ta dan kalli Abba sai kuma ta sadda kanta kasa kasan. "Tashi mu tafi gida kinji?" Ya furta yana juyowa wajen Khalil da ke kallonshi baki bude. "Bani takardar magungunan da likita ya baka." Ya mika hannu yana jiran Khalil din ya miko mashi takardar.

Tashi tsaye Khalil yayi yana kallon Abba da babu idon sassauci a cikin idanunshi. "Abba dan Allah kayi hakuri zan siyo magungunan." Ya furta jikinshi har dan rawa yakeyi kadan. Dan bai tabajin tsoro da kuma shakkar Abba kamar yau ba. Sai yaji dama baiyi maganar ba dan Allah kadai yasan abunda Abba zaiyi.

"Zaka bani takardar ko kuwa sai na ci maka mutunci cikin asibitin nan, Khalil? Duk wulakancin da ka mun bai isheka ba yanzu kuma ina fada kaima kana fada ko kuwa me kake nufi?" Ya tambaya yana dan daga murya. Haka Khalil yanaji yana gani ya fiddo takardar daga aljihun shi ya mikawa Abba ita.

"Wuce muje, Fatima." Ko kallon inda Batul take tsaye Abba baiyi ba ya fice daga dakin.

A hankali Batul ta sauko daga kan gadon tanajin wani kalar zafi da nauyi da zuciyarta ta mata. Hijab dinta ta saka tukunna ta dauki ledojin da Abba yazo dasu ta nufi bakin kofa ko kallon inda yake tsaye yana kallonta batayi ba. Har ta murda murfin kofar sai kuma ta juyo tana kallonshi da rinannun idanunta.

Murya a k'ekashe take furta, "Kayi hakuri da duk abunda ya faru tun farko har zuwa yanzu. Na maka alkawari saidai idan da gawata zakayi zaman aure, amma in har ina raye zan tabbatar da ka rabu dani, insha Allah. Nagode da taimakon da kayi man." Tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin tana fitar da numfashi a hankali.

Tana da tabbacin bawai tana san Khalil bane, ko kusa da hakan ma tunanin ta baikai ba. Amma batasan dalilin dayasa maganganunshi sukayi mata wani kalar daci da nauyi a zuciya ba. Tasan ko da Abba ya baiwa Khalil dama ya saketa to tabbas Abba bazai taba barinta ta wulakanta ba, sai ya tabbatar da cewar rayuwarta ta inganta. Amma haka kawai takeji kamar ta saki komai da yake hannunta ta zura da guda duk kuwa da cewar ita kanta bama tasan inda zataje ba.

A cikin mota ta iske Abba zaune kwata kwata ma besan ta shigo ba. Saida ta zaune kanta a kasa ta kusan minti ukku amma Abba ya lula duniyar tunani kafin ya juyo ya kalleta. Baice kala ba ya tayar da motar suka fice daga asibitin. Ta madubin motar ta hango motar Khalil a bayansu. Suna ta tafiya sai can Abba yayi gyaran murya ya juyo yana kallonta.

"Fatima, kiyi hakuri kinji? Har na gaji da baki hakuri amma hakan shine kadai abunda zan iyayi, baki hakuri. Nasan kina cikin takura da damuwa mai tsanani, Fatima. Balle yanzu da Khalil shida kanshi ya bukaci na bari ya sawwake maki, karki dauka hanashin da nayi ina nufinki da cutarwa ne, Fatima, kinji? Akwai abunda nake tunani, kuma lokaci nake bawa auren nan naku idan har naga cutarwar zatayi yawa a gareki nida kaina zan umurceshi daya sawwake maki..."

Ita dai Batul kanta kasa, sai a lokacin taji wasu siraran hawaye sun fara fitowa daga cikin idanunta. "Kiyi hakuri kuma ki kara da hakuri, Fatima. Na maki alkawari bazan taba bari ki wulakanta ba. Duk inda hakkinki yake da kuma yancinki sai na tabbatar dashi a gareki. Ki yarda dani da dukkan hukuncin da zanyi a gareki, kinji?"

"Nagode Abba, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Na yarda da dukkan hukuncin da zakayi a gareni, Abba. Dan Allah ka daina bani hakuri hakanan kaji Abba." Murya na rawa haka take magana. Tunda Abba yace 'Allah ya maki albarka' bai kara furta komai ba har suka iso gidan motar Khalil tana bayansu.

Kai tsaye dakinta ta wuce ta iske an gyarashi kamar babu abunda ya faru a daren jiya. Bayi ta shiga tayi wanka saida tazo fita ne ta hango ledar jiya wadda Khalil ya kawo mata. Daukowa tayi ta fita da ita ta aje kan gado. Saida ta shirya tsaf da komai tukunna ta fiddo da wayar daya siyo mata. Iphone13 ce dan juya kwalin wayar tayi tana murmushi, koba komai tasan cewar wayar zata dauke mata kewa.

Jona wayar tayi a chaji tukunna ta fara cin abincin da Abba yakai mata asibitin. Duk iya kokarin da Batul tayi na kan cewar ta kawar da maganganun da Khalil yayi a asibiti kasawa tayi. Sai ya zamana tanajin abincin tamkar dussa takeci a cikin bakinta. Dole tasha ruwa ta koma kan gado tana zubar da hawaye a hankali. Rashin darajar yayi yawa. Amma ko dan Abba zata jure kuma ta cigaba da hakuri.

Khalil tunda yake bai taba shiga tashin hankali irin wanda ya shiga a yau ba. Tunda ya shigo gidan aka aika mashi cewar Abba yana kiranshi a falonshi. Yana zuwa ya iske Maama zaune a saman kujera taji wani irin jugum ba sai ka tambaya ba kasan tana cikin tsananin fargaba da kuma tashin hankali da damuwa. Allah kadai yasan irin abunda Abba ya mata ko kuma maganganun daya fada mata.

Yazo zai zauna saman carpet kenan Abba ya fito daga dakinshi. Jallabiya coffee brown ce a jikin Abba sai ta kara fito da farar fatarshi da kuma zallar kamar da yakeyi da Khalil. "Kar ka zauna, dan zamanka babu abunda zai amfaneni tunda har ban isa da kai ba. Bansan biyayyar munafunci ka ganni nan. Mike kanka tsaye, ai ba yanzu ka fara ba."

Wani kalar dum Khalil yaji a zuciyarshi. "Abba dan Allah..." ya fara furtawa amma daga mashi hannun da Abba yayi yasa ya rufe bakinshi bai idasa maganar shi ba.

Juyawa Abba yayi ya kalli Maama. "Me kikeyi a nan har yanzu Jamila? Na dauka kashin kanki kike ci a gidan ai. Ki tashi ki wuce ki cigaba da duk abunda kikaga dama, amma ki sani akwai lokacin da bazan cigaba da daukar duk wata sharar da zaki zubar ba. In zaki shiga taitayinki ki shiga, ba yara ba ko hanjin cikinmu daya sai in tsinka su gara in mutu."

Da mamaki Khalil yake kallon Abba sai kace wanda aka chanja haka yake abubuwa a yan kwanakin nan. Kuma duk akan wannan kodaddiyar yarinyar. Sai baisan ko asiri ta ma Abba ba amma tabbas abun yayi yawa kuma a kullun tsanar daya mata tana karuwa a cikin zuciyarshi. Bai tabajin Abba yana fadawa Maama magana haka ba sai yau. Dukda Khalil shida kanshi yasan abunda Maama tayi ya wuce gona da iri.

"Sai abu na biyu. Ibrahim, a yau ko ince a yanzu nakeso ka tattara matarka ku fice man daga gida ban yarda ku kwana a gidana yau ba." Abba yana fadin haka ya juya wajen Maama dake kallonshi da tsantar mamaki.

"Wai Alhaji wadannan abubuwan duk dan kan waccan gantalalliyar kafirar ne? Alhaji kaji tsoron Allah fah, wai kodai wani abun ne tsakaninka da ita? Tunda nace ka maida ta gidan daka daukota kace babu maganar maidata can ta dawo nan dindindin. Yanzu kuma shi Khalil bansan laifin daya maka ba amma kace shida matarshi bazasu kwana a nan ba. Bayan kasan sai bayan sati daya akace zasu wuce Abuja. Alhaji na kasa gane kanka ba, wai kodai da wani abun a kasa ne?"

Murmushin takaici Abba yayi yana jifan Khalil da wani mugun kallo. "Inma akwai wani abun ai shi Khalil din yafi kowa sani. Ko kanaso na fada mata ne yanzu? Dan na lura duk ba mutunci ne daku ba, gara na fito maku a mutum..."

Da wani kalar hanzari Khalil yake girgiza kanshi. "Dan girman Allah Abba kayi hakuri. Yanzun nan zanyiwa Yusrah magana ta shirya sai mu wuce, dan Allah Abba." Jikin Khalil har rawa yake ya nufi hanyar fita daga falon. Don a yadda ya fuskanci Abba so yake kowa ma ta shafeshi. Shi kuwa Khalil yana rage zafi saboda yasan babu wanda yasan batun aurenshi da Batul, hakan ba karamin sauki bane a wurinshi. To idan har Abba ya fasa kwan zai iya tilasta mashi ma ya tafi da ita can Abujar itama.

Saida Abba ya bari Khalil ya fita tukunna ya juyo yana kallon Maama fuska a daure. "Da sun fita daga bangarenshi inaso Batul ta koma bangarenshi da zama. Daga yanzu kuma ban yarda a kara sakata aikin da ake saka sauran yan aikin gidan ba tunda ba cikinsu take ba. Kuma daga ke har sauran yaran ban yarda wani ya kara ci mata mutunci ba a cikin gidan nan. Duk wanda yayi kuma zai hadu dani, Jamila. Kar kiyi tunanin bana nan kice zakiyi abunda kikaga dama, wallahi zakisha mamakin hukuncin da zan dauka a kanku gaba daya."

Baki sake Maama take kallonshi ko magana daya ta kasayi. "Wai nikam Alhaji anya yarinyar nan ba asiri ta maka ba? Lafiyarka kalau kuwa Alhaji? Yau na bani!" Hannu ta daura a kai tanata salati. Tsaki kawai Abba yayi ya juya ya koma dakinshi ya barta a nan.

Tunda Khalil ya fada mata cewar zasu tafi Abuja Yusrah keta murna tanajin dadi. Shi daga farko ma ya dauka zata nuna damuwa ko rashin jin dadinta amma sai yaga akasin haka, murna kawai take dan dama ita can ba wani san zaman Adamawa takeyi ba. A hanyarsu ta airport kuwa waya takeyi da wata kawarta tana fada mata yau zata dawo amma sai next week zata komo makaranta. Shidai Khalil saurarenta kawai yakeyi dan shi kadai yasan abunda ke damunshi.

Shi damuwarshi bai wuce fushin da Abba yakeyi dashi ba. Kuma har yanzu baisan wani kalar hukunci Abba zai dauka ba dan yasan bazai barshi haka nan ba. Dan dafe kanshi yayi yanaji Yusrah ta doro kanta saman kafadarshi, dan yanzu haka zaune suke cikin jirgi suna jiran a tashi. Daya sani ce ke mamaye shi, daya sani da baiyi maganar da yayi ba, amma har a ranshi yayi tunanin Abba zai fahimce shi. Ina zai saka ranshi? Kuma menene Abba yake shiryawa?

Domin samun complete littafin zaku iya man message ta Telegram a kan naira 1500 while it's ongoing. Da ya zama complete it will be 2000 naira.

You can reach out to me ta wannan number din a telegram: 08132526951

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top