10

Ko kafin zafin marukan da Maama ta sakar mata su saketa sai Batul ji tayi wasu mata su biyu sun shigo dakin kamar kawayen Maama ne dan bawai gani take sosai ba. Ta bude baki zata fara magana suka fara dukanta kamar babu gobe. Tun tana kokarin kwatar kanta har ya zama ta durkushe a kasa ta hade kanta da guiwowinta su kuma suna dukan duk inda suka samu a jikinta.

Maama na daga gefe tana kallonsu tana aikin zagin Batul da cewa har ta isa ta bata mata taro? Taja mutane sai gulma suke ana zaginsu? Dama haushinta takeji abunda ya faru ranar a kasuwa, ita kadai tasan kalar cin mutuncin da Abba ya mata a daren ranar. Dan har so yayi ya hana auren Khalil din wai da sai su duka yaran da ita Maama sun bawa Batul hakurin cin mutuncin da suka mata tukunna. Can kuma ya dawo yace za'ayi, wanda ta tabbatar Batul dince ta bashi hakuri akan hakan.

Sama sama takejin Maama na dura mata zagi tana cewa in har bita bata isa ta koreta ba to ai ta isa tasa ita da gudu gidan da kanta. In ma har tace zata zauna to wulakancin da zata rika gani a gidan ko kare bazai iya daukarsa ba. Duka sukewa Batul bana wasa ba. Tun tana da karfin yin kukan da kuma kokarin kare fuskarta har ta daina domin gaba daya jikinta ya gama mutuwa. Wannan daga gani hayar su Maama tayi sadidan kawai dan suzo su lakadawa Batul dukan tsiya wanda zaisa ita da kanta ta bar gidan ba sai wani yace ta tafi ba.

So take tayi magana ta basu hakuri akan su daina dukanta haka nan dan har ga Allah karfin jikinta ya gama karewa gashi yinin yau kaf ba wani abinci taci ba dama can ba karfin ne da ita ba. Bata da tabbacin idan abunda kunnuwanta suke ji mata gaskia ne, amma taji kamar karar motar polisawa a cikin gidan kuma cikin lokaci kankanra aka banko kofar dakin aka shigo.

"You are under arrest!" Abunda taji wani dan sanda ya furta kenan da wata kalar kakkausar murya nan take kuma taji dukan da suke mata ya tsaya cak kamar daukewar ruwan sama.

A galabaice ta dago ta kalli Abba da har kusan tuntube yake ya karaso cikin dakin. Kai tsaye taga ya wuce kofar bayin ya bude sai ga Khalil ya fito daga cikin da wani kalar yanayi dauke a fuskarshi. "Abba, me zaisa ka kira yan sanda?" Ya fada cikin sigar tashin hankali. Dan shi koda ya yiwa Abba message akan yazo dakin Batul ga abunda ke faruwa bai taba tunanin wai Abba zai iya kiran yan sanda ba.

Bacin rai ne zallah a cikin idon Abba. "Idan ban kira yan sanda ba wa zan kira, Ibrahim? Wadannan matan data samo daidai suke da ka kira yan daba suyi ma wani fashi a cikin gidanshi. Kuma kaima zanyi maganinka, wane kalar sakarcin ya hana ka fito ka ceci matarka?" Sai lokacin da Abba ya furta haka ne ya juyo yana kallon Batul da har yanzu take tsugunne a kasa kanta saman guiwowinta tana sauke wani kalar numfashi me wuya.

Har kasa Abba ya duka daidai saitin fuskarta. "Fatima, ya jikin naki? Sannu kinji? Kuma kiyi hakuri dan Allah, banma san da wane kalar baki zan fara baki hakuri ba Fatima."

Kuka kawai take tana girgiza ma Abba kai. Wani kalar masifaffen ciwon kai ne yake damunta kamar kwakwalwarta ta tsage haka takeji. Ga zuciyarta da tayi wani kalar masifaffen nauyi ta rasa ina zata saka kanta taji dadi. Tarin kunci, damuwa da bakin ciki ne sukayi mata katutu a cikin rayuwarta.

"Ko nasa a kaiki asibiti ne, Fatima?" Abba ya furta cikin murya me dauke da tsantsar damuwa da kuma bakin cikin da yake ciki.

Daga mashi kai tayi a hankali dan bataji zata iya daga koda hannunta ne dan ta bugu har kwallo suka rikayi da ita. Karfafa ne na gaske, ba karamin buguwa tayi ba a wajensu. Kuma badan tana bukatar maganin ciwon kan da yake damunta da kuma na ciwon jikin da takeji ba, tabbas tana bukatar barin gidan nan koma me zai faru saidai ya faru. Amma Allah ya sani ta gaji wallahi. Tunma ba'aje ko ina ba kenan.

Laifi ne dan wani namiji, kafirin Allah, bature yazo yana kokarin tabata da iskanci ta taka mashi burki. Ita fa budurwa ce, kuma musulma sannan ga igiyoyin aure har uku saman kanta. Shin idan bata kare mutuncin kanta ba waye zai kareta?

Mikewa Abba yayi a tsaye yana jifan Khalil da wani kalar mugun kallo. "Daukarta ka kaita asibiti. In kuma kaga dama kuna fita ka ajeta bakin titi ka wuce inda zaka. Dan na dade da sanin daga uwarku har ku duka babu mai digon imani a cikin zuciyarshi. Mugayen mutane kawai." Abba yana fadin haka ya juya ya fice daga cikin dakin ranshi a matukar bace. Daga gani kasan wajensu Maama zaije dan yan sandan tuni sun dade da wucewa.

"Bakiji abunda yace bane?" Ya tambaya yana jifanta da wani kallo me cike da zallar tsana. Ta tabbatar da zai bude ido ya gane ashe duk abunda ya faru a kwanakin baya da kuma rayuwarshi data shiga ace mashi wani kalar mummunan mafarki yayi to tabbas babu wanda zai kaishi jin dadi a rayuwarshi.

Yunkurowa tayi kamar zata tashi amma sai taji kafafunta bazasu iya daukarta ba ta koma rajab ta zauna a kasa tana sauke ajiyar zuciya. Yafi minti daya yana kallonta yana sake sake a cikin zuciyarshi kafin ya daka mata wata kalar muguwar tsawa.

"Wai bakiji abunda nace bane? Zaki tashi mu tafi ko kuwa?" Ya fada.

"Kayi hakuri bazan iya tashi bane. Kaje kawai inya tambaya zance mashi ni na fasa zuwa asibitin." Abunda ta furta kenan tanayin kasa da kanta wasu zafafan hawaye suna gangarowa zuwa kuncinta wasu nabin wasu. Ita kadai tasan yanda takeyi. Duniya gaba daya ta mata wani kalar kuncin da bazata iya bayanin abunda takeji a cikin zuciyarta ba ita kanta.

"Lallai ma yarinyar nan munafuncinki ya wuce inda nake tunani. Ko wai bakiji abunda ya fada bane. Ko ki tashi ko kuma na dora maki akan wanda suka maki gara na daukeki a sume na kaiki asibitin atleast na huce takaicina." Wani kalar kallo me cike da tsana yake binta dashi.

Dauke kanta tayi dan ita iyakar gaskiarta kenan. Bazata iya tashi ba, kuma ko be fada ba tasan baya kaunarta kuma da yanada halin kara mata wani dukan akan wanda suka mata babu abunda zai hanashi yin hakan.

Batayi aune ba taji ya jefeta da wani abu ko kafin ta dago ta duba taga menene taji kamar daga sama ya sunkuceta can a hannuwanshi kamar wata diyar roba. Kusan kaman zata kurma ihu haka taji saidai dan kawai ko kadan babu karfi a jikinta haka nan ta hakura tanaji yana tafiya a hankali har sai daya bude mota ta sakata a gidan baya kafin ya koma mazaunin direba ya shiga yaja motar suka fice daga gidan.

Da kyar ta samu ta dago sai a lokacin ta fahimci hijab dinta ce ta wurgo mata cikin daki. Wani kalar gudu yake da motar daka ganshi kasan ranshi ba a karamin bace yake ba dan kamar zai tashi sama. Koda suka iso asibitin bai jirata ko yace mata wani abu ba kawai yayi gaba ba'ayi minti goma ba sai gashi tare da wata nurse da kuma wheel chair. Nurse dince ta taimaka mata har ta zauna saman wheel chair din daga nan suka wuce ciki.

Kai tsaye ofishin likata suka wuce nan ya mata tambayoyi tana bashi ansa dan har gani batayi sosai ga jikinta ko ina ciwo kamar a cire mata rai haka takeji ko ta samu ta dan ji saukin radadin azabar. Yanda taso haka akayi dan kuwa ya bata gado akan cewar sai zuwa gobe tukunna. Tun daga ofishin likitan Khalil tunda ya biya komai kawai ya juya ya wuce bata kara ganinshi ba.

Nurse dince ta kaita dakin da aka bata ta mata komai kamar yanda likitan yace. Ta saka mata ruwan da alluran duka kafin ta juya ta fita bayan ta kashe mata wutar dakin. Dukda an kashe wutar akwai hasken waje dake shigowa cikin dakin wanda hakan yasa tana ganin komai na cikin dakin. Batul ta dade da sanin bata da gata a duniya kuma bata da wani galihu, amma hakan bai kara tabbata a cikin ranta ba sai yau.

Wani kalar marayan kuka ta saki tanaji kamar ta fasa kirjinta ta fiddo zuciyarta waje tsabar wani kalar kunci da takeji. Bacci bai dauketa ba saida ta tabbatar ta yanke shawarar da take ganin cewar itace mafi a'ala a wajenta. Sai can wajen asuba bacci yayi awon gaba da ita shima kuma cike yake da mafarkai barkatai wanda babu abunda sukayi sai kara sanyata cikin tsananin bakin ciki.

Tun wajen karfe takwas nurse din tazo ta cire mata ruwan da aka sanya dan ya kare. Jin kanta take ya daina ciwo sosai takejin dadin jikin nata. Dan da ace ta kwana gida ba tare da tasha wani magani ba Allah kadai yasan irin ciwon da zatayi. Tana nan zaune batasan madafa ba sai taji an bude kofa. Fuskar Abba data hango yasa ta dan saki ajiyar zuciya tana dukar da kanta kasa.

"Ina kwana, Abba," ta gaishe shi cikin girmamawa.

Abba bai ansata ba saida ya aje ledojin abincin dake hannunshi tukunna ya janyo kujerar me jinya har gab da gadonta yana kallonta cike da tausayi da kulawa. "Sannu Fatima, yaya jikin naki?"

"Da sauki Abba," abunda ta furta kenan tana wasa da yatsun hannunta.

"Kiyi hakuri kinji Fatima? Bansan da wane kalar baki zan fara baki hakuri ba. Inaso ki sani ya dauki mataki akan wadannan matan da Hajia tasaka suka dakeki, itama kuma bawai na kyaleta bane..."

Tun kafin yakai aya Batul ta dan katseshi cikin ruwan sanyi. "Abba ni wallahi na yafe masu. Dan Allah ka bar maganar ba sai an dauki wani mataki ba ya wuce a wajena."

Shiru kawai Abba yayi bai bata amsa ba yana dan nazari. "Sauko ga abinci kici. Ibrahim yana wajen likita domin yaji yaya lafiyar jikin naki." Daga mashi kai tayi babu musu ta fara cin abincin dan kuwa dama ba karamar yunwa takeji ba.

Tana cikin cin abincin ne Khalil ya shigo doctor na biye dashi a baya. Bayani yama Abba akan jikin nata da kuma fada mashi cewar ko yanzu zasu iya wucewa gida dan komai lafiya lau. Magunguna ya rubuta ya bawa Khalil kafin ya fita ya barsu.

Nuni Abba yama Khalil da kujerar dake dan nesa da tashi. Babu musu Khalil yaje ya zauna saidai tun kafin Abba yayi magana Khalil ya rigashi. Da ka kalli yanda yake kasa da fuska kasan yanajin shakkar yin maganar da yakeson yi.

"Abba dan Allah wata alfarma nake nema a wajenka, dan Allah Abba na rokeka kar kace Aa, ka taimaka man." Ya fada da wata kalar muryar magiya idanunshi suna dan cikowa da hawaye.

Kallon tsanaki Abba ya mishi kafin can yace, "Ina jinka, wace alfarma ce kake nema?"

Saida Khalil ya tabbatar baya kallon Abba idanunshi suna kasa tukunna ya fara magana tiryan tiryan kamar wanda yayi bitar maganganun da zaiyi. "Abba ka taimakeni ka raba auren nan, dan girman Allah. Wallahi Abba auren nan matsala ne babba nidai a rayuwata. Nasan yanzu haka kana tunanin zata fadawa Maama cewar ma..ta..ta..." sai yaji kalmar 'matata' ta mashi wani kalar sororo bazai iya dangantata da Batul ba, kwata kwata abun babu dadin ji.

"Nasan zakayi amfani da hakan wajen hukunta Maama. Nidai Abba na rokeka, tunda dai har mun ceto rayuwarta mun rabata da yan'uwanta da suke neman cutar da rayuwarta, dan Allah ni kar a ruguza man tawa rayuwar Abba. Banasanta, bana kaunarta, ko kallonta wallahi banasan yi, Abba. Kace nayi adalci a tsakaninsu, wallahi Abba bazan iya ba. Kwata kwata bata cikin tsarin matan da nakewa kallon mata balle har ace na auresu. Zamanta a matsayin matata cutar da ita kawai zaiyi ni kuma yaja mani tarin zunubi Abba, wallahi bazan iya ba. Banso na tashi ranar kiyama bangare daya na jikina a shanye. Ka ceci raina ka bani izinin sawwake mata, Abba. Muna iya taimakonta ta hanyoyi da dama ba dole sai na aureta ba. Zamu iya samar mata admission wata kasa tayi karatu, zamu iya kaita wajen sauran yanuwanta da zasu sota, akwai abubuwa da dama da zamu iya yi a gareta..."

Abba yazo zai katsetsi Khalil ya dan daga murya a hankali yana kallon fuskar Batul wadda tunda ya fara magana itama take kallonshi zuciyarta tamkar zata fito kirjinta. "Dan girman Allah Abba ka barni na sawwake mata."

Ya kuke gani? Mu tsaya da preview chapters a nan ai ko?😁🤭

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top