1
Tsugunne take daga can gefen bango ta makure ta yadda idan ba mutum ya biyo ta wajen ba kuma yana lura babu wanda zai lura akwai mutum a wajen. Dukda kasancewar yau Juma'ah, kuma masallacin cike yake makil da Al'umma, inda take ba waje bane da mutane suka fiye bi ba. Waje ne da yake sadaka da inda liman yake shiga masallaci to ko sahu ba'ayi ta wurin.
Ba kuka take ba, dan kuwa tayi me isarta har ta gaji. Idanunta sunyi jajir sun koma kamar danyen nama. Jikinta gaba daya babu karfi dan kuwa rabon da cikinta yaga abinci kusan kwana uku kenan. Saidai in ta samu ruwa ko ragowa taci. Amma abinci me sunan abinci? Ba dai ita ba saidai wata.
Tasan tunda liman yace ta jirashi a wajen to tabbas zai dawo, dan mutum ne shi me cikar kamala idan tun farko yasan bazai taimaka mata ba ta tabbatar bazai mata karya yace zaiyi ba. Jinginar da kanta tayi jikin bango tanajin yanda zafin rana yake ratsa jikinta, gashi sai zufa takeyi jikinta ya jike sharkaf da ruwan zufa.
Batasan bacci yana neman kamata ba sai lokacin da taji alamar wasu sun tsaya saman kanta. Firgigi tayi ta tashi dan ita a tunaninta su Baba Kamalu ne suka gano inda ta ruga sukazo daukarta. Zuciyarta na dukan uku uku haka ta bude ido. Ganin cewar Malam Zakariya ne tare da wata mata sanye da hijabin yan agaji na mata yasa ta saki wata kalar ajiyar zuciyar da batasan tana bukata ba.
Mikewa tayi tsaye tanaji gwiwowinta suna ansawa saboda yanda ta dade a tsugunne. Dago da nauyayyun idanunta tayi. Dan sunkuyawa tayi ta gaidasu baki daya.
"Ina yini, Malam," ta gaida shi kafin ta juya ta gaida matar itama. "Ina yini?" Dukda cewar a Kano aka haifeta kuma a nan ta taso, hakan be hana cewar da tayi Hausa a gane cewar ita din ba cikakkiyar bahausa bace.
"Lafiya lau," Malam ya amsa yana nuni da ita, "Yama kikace sunanki, yarinya?" Ya tambaya.
"Sunana Fatima amma anfi kirana da Batul ko Islam." Ta fada tana me sadda kanta kasa. Domin kuwa kaf dangin mahaifinta duk wanda zai kirata da Islam sai ya tabbatar ya tuna mata da asalinta da yadda a ganinsu wannan sunan sam be dace da ita ba.
"Masha Allah, Batul. Yanzu Hajia Hauwa zata wuce dake bangaren mata. Karki damu insha Allahu abunda muka tattauna zanyi kokari akai. Inma hakan be samu ba zamusam yanda zamuyi koda hukuma ne sai mu saka idan ma abun yafi karfinmu..." Shiru tayi ta sadda kanta kasa tana sauraren Malam Zakariya. Ita kadai tasan tsananin da take ciki da kuma cikakkiyar sanayyar cewar idan har abunda suka tattauna be faru ba to tabbas rayuwarta tazo kan gaba wajen karewa.
"Karki damu kinji? Malam yaman bayanin komai. Muje masallacin," Fadar Hajia Hauwa wanda hakan yasan Batul kallonta tana gyada kai.
So take ta kara rokan Malam Zakariya akan ya taimaka mata. Dan wallahi ita kadai tasan halin dangin mahaifinta amma sai taji nauyin yin hakan. Tunda ya tabbatar mata da zaiyi kokari tasan zaiyi din. Kuma ta mika ma Allah dukkan lamuranta tasan zai kawo mata mafita.
Sumsum tabi bayan Hajia Hauwa har suka shiga wani bangare na masallacin mata inda suke ajiye ajiyen kaya. Juyowa tayi ta kalli Batul tana murmushi kadan. Miko mata da wata zumbuleliyar hijabi tayi. "Karbi nan ki saka Fatima. Kinci abinci kuwa?"
Girgiza mata kai tayi. Wata kila Hajia Hauwa ta lura da yanayin da take ciki. Fita tayi ta shigo sai gata dauke da takeaway biyu sai robar ruwa data lemu, da alama wanda ake bayarwa sadaka ne a duk ranar Juma'ah a masallacin. Koda Hajia Hauwa ta miko mata karba tayi hannu bibbiyu tana godiya. Duka ta cinye su tas tasha ruwa da lemun ta dago tana kara yi mata godiya.
Jin an gama huduba za'a tada sallah yasa Hajia Hauwa tace mata taje tayi alwallah su shiga suyi sallah. Hakan kuwa akayi. Koda akai sujjada kuka Batul ta fashe dashi tana kara yima Allah magiya akan kar yabari su Baba Kamalu suyi galaba a kanta. Allah ya kawo mata mafita cikin gaggawa.
Bayan an kammala sallah Batul ta jinginar da kanta jikin bango tanata istigari. Dan ita kam tayi imani da Allah babu irin matsalar da istigfari baya kawar wa. Ta yadda ita din me zunubi ce, ta hanyar gafarar Allah kadai zata samu sassauci a rayuwarta.
Daga nan fa aka fara daure dauren aure. Tun tana saurara taji har ta fitar da rai zuciyarta na wani kuna. Tana tunanin yanda zasu kare da kanne da kuma yayyen mahaifinta. Tasan duk inda suke ana can ana nemanta. Kuma idan har ta bari sukayi ido hudu bata samu mafita ba tabbas sai na kabari ya fita jin dadin duniyar.
Kamar daga sama taji wata murya kamar ta santa. "Wannan kamar wannan k'abilar cousin din su Sholy ko?" Taji yarinyar ta furta.
Dukda ta daure akan karta dago taga wacece dan kuwa duk wanda zai kirata da K'abila tabbas yasan wani nata amma ji tayi ta kasa. Inda sabo yaci ace Batul ta sama da sunan K'abilar nan daya makale mata tun batasan ma'anar kalmar ba amma kuma ta kasa. Duk lokacin da aka jefeta da kalmar sai taji kamar ta daga hannu sama ta rusa ihu.
Ko kafin ta sauke numfashinta taji Hajia Hauwa tayi magana cikin kakkausan lafazi. "Haba yan mata. Ba sallah muka gama yanzu ba? Ita bakiga tayi sallar bane kuma yanzu kikasan tasbihin da takeyi? Keda ita miye banbancinku da zakice mata Kabila? Idan kin ganeta ai kinsan sunanta ko?"
A wani gatsine Jaly kawar cousin dinta Sholy ta kalleta kafin ta maida kallonta zuwa Hajia Hauwa. "To ai kabilar ce ko Mama. Ance har uwarta ta mutu ba'a taba ganin ta rufe kanta ba musuluncin dai da sunan tanayinshi ne. Itama din bakiga zubinta ba? Allah yasa ba najasa aka dauko aka kawo mana masallaci ba."
Kan kace kwabo mata cikin masallaci da masu fita da masu gyara zama anata uhm uhm ana yar murya. Batul naji wasu na cewa aita masu kwashe kwashe ana kawowa salan suyita sallah a kan najasa. Wasu kuma suce inda ma cewa akai yau ta musulunta da sauki. Wasu kuma suce wannan dai karya take ba wani alamar musulunci tattare da ita.
Duk magana daya da zasuyi ji take kamar suna zuba mata wani kalar mad'aci a daidai saitin zuciyarta. Wani kalar kunci da bakin ciki takeyi kamar ta hade zuciya ta mutu. Tanaji tun Hajia Hauwa na magana har tayi shiru ta kyale su. Duk yanda taso ta danne hawayenta kasawa tayi ta dora kanta saman gwiwowinta kawai tana wani irin kuka marar sauti ko kadan.
Wannan shi ake kira da rana zafi inuwa k'una.
Tayi nisa cikin tariyo rayuwarta taji Hajia Hauwa ta tabo hannunta. Dagowa tayi jiki sake taga tana mata wani dan guntun murmushi.
"Tashi muje kinji Fatima? Dadin abun musuluncin na Allah ne. Su din da suke ganinsu Hausawa wata kila Allah be yarda dasu ba kamar yadda ya yarda dake. Kiyi hakuri kinji?" Cikin murya tattausa tayi magana sai Batul taji wasu hawayen sun taru mata a idanu. Daga kai kawai tayi ta tashi tabi bayan Hajia Hauwa har sukaje wani office da yake can gefen masallacin.
Ganin takalman maza a bakin kofar yasa Batul taji gabanta yayi wata irin muguwar faduwa. To kodai su Baba Kamalu sun gano inda ta gudo ne? Ko Jaly ta kira Sholy ta gaya mata shine sukazo?
Har ta dan tsaya ta toge a bakin kofa amma Hajia Hauwa ta rike hannayenta ta jata suka shiga office din. Waje ne me girma ga sanyin AC yana ratsa mutum. Tunda ta shiga wajen idanunta ke kan kafafunta, kallon zoben da yake kan babban yatsanta tayi tana tuno lokacin da mahaifiyarta ta mata kyautarshi. Tun ranar data saka mata shi har yanzu bata taba cirewa ba dukda irin zagi da zargin da takesha a kanshi.
Kamar saukar aradu haka taji Malam Zakariya yana furta, "To Alhamdulillah, Fatima. Kamar yanda na miki Alkawari, Allah ya taimakemu an samu wanda ya aminci da kudirinmu. Wannan bawan Allah shida mahaifinshi sunyi jihadin ceto rayuwarta. Cikin aurarrakin da Allah ya bamu ikon daurawa a yau an daura hada naki. Dukda kasancewar bansanki ba balle danginki, na yarda da duk abunda kika sanar dani. Kuma daga nan wajen zamuje wajen ahalinki domin tabbatar masu da cewar ke din yanzu matar aure ce."
'Kedin yanzu matar aure ce...'
Wadannan kalmomi su kadai suka rika yi mata wata kalar zarya cikin ilahirin hanyoyin jininta. Kamar ta mike ta zuba da gudu haka taji. Amma sai ta runtse idonta. Daga can kasan ranta ta fara karanta 'Alhamdulillah ala kulli halin...' tun batayi da yaqinin maganar har ta farayi tanajin kalmomin suna ratsa zuciyarta har taji ta samu natsuwa.
Bata dago ba saima ta kara dukar da kanta hawaye suna mata sintiri saman fuskarta. "Nagode Malam. Allah ya saka maku da mafificin alkhairi. Yanda kuka ceci rayuwata, kuma Allah ya taimakeku. Nago..." kasa karasawa tayi ta fashe da wani kalar mugun kuka ta durgushe a kasa baki daya.
Kuka takeyi kamar ta fasa zuciyarta ta fiddo. Wani kalar kunci da bakin ciki sun mamaye ilahirin ruhinta. Tayi tunanin abubuwa da dama a rayuwarta amma bata taba tunanin wannan ba.
"Bar kuka kinji yarinya? Allah shine gatanki, ni kuma daga yanzu na zama gatanki. Insha Allahu bazaki kara zubar da hawaye ba. Share kukan kinji? Kowane bawa da irin tashi kaddarar a rayuwa, ke wannan ce taki, ki rungumeta hannu biyu ko kin samu dacewa wajen Allah, kinji?" Daya daga cikin mutanen ya furta, wanda dagaji kasan babban mutum ne me cikar kamala da haiba.
Kokari tayi ta danne hawayenta tana share wanda suke kwance kan fuskarta. "Nagode Baba. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Allah ya maka albarka me tarin yawa." Tana furta hakan saida taji kamar ta kurma ihu, dan kuwa Nne bata taba cewa Allah ya maka albarka haka kawai. Saidai tace Allah ya maka albarka me tarin yawa.
Murmushi yayi yana daga kanshi. "Amin Fatima. Sunana Alhaji Sule Barkindo. Nine mahaifin Khalil, wanda shine Allah ya rubuta zai zama mijinki a yau. Bamuzo garin Kano da shirin auren Khalil ba sai dan wata hulda ta kasuwanci data kawo mu, amma Allah ya rubuta ta hanyarmu zai tsameki daga halin da kike ciki. Kiyi hakuri kibar kuka, insha Allahu karshen kuncinki yazo, kinji?"
"Nagode Baba." Abunda kawai ta iya furtawa kenan kanta a kasa. Tunda ya furta sunan Khalil taji kamar ta dago taga yaya suffar wannan bawan Allah take. Sannan kuma da wane baki zata mashi godiya? Me zata ce mashi?
Tana nan zaune taji sun gama magana da Malam Zakariya har aka yanke shawarar a fara zuwa ofishin hisba a dauko jami'ai kuma ai masu bayani tukunna suje gidan Baba Kamalu. Hakan kuwa akayi. Ita da Hajia Hauwa suna cikin motar Malam Zakariya har suka isa gidan.
Tun daga nesa ta fara hango dangi maza da mata anyi cincirindo kofar gida. Gabanta yayi mummunar faduwa. Daurewa kawai tayi tanata karanto sunayen Allah har ta samu ta fito daga cikin motar kamar yanda Malam Zakariyya ya umurceta.
Daya daga cikin yaran gidan taji ta furta. "Laaah Baba kaga Batul!" Ko kafin ta rufe baki dama daya daga cikin samarin gida yana gab da motar, wannan irin kukan kura yayo ya tad'iye ta sai gata kasa rigib.
Kafin suyi wani kwakwaran motsi ji kake tim tim tim, dukanta kawai suke ta duk inda sukaga dama. Ashar ne ke yawo kota ina ana tambayarta gidan ubanwa taje bayan tasan yau ne daurin aurenta?!
Tun tana kokarin dago kanta tayi numfashi har abun ya gagara ga duka ta ciki ta kirji ta fuska. Kadan kadan taji karfinta yana karewa har ta ida sulelewa nan kasa taananin duhu yana mamaye idanunta.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top