Chapter 6

"Gumi ne mai zafin gaske yaci gaba da zubowa a fuskar maimoon cike da nazari take cigaba da kallon takardar inda gefe daya zuciyarta ke mata zafi cike da takaicin marin da iqbaal yayi mata

Excuse me,shine abinda ya sanya maimoon dagowa a firgice ta kalli wanda yake mata magana kamal ne tsaye jikinsa sanyaye yake kallon maimoon,shiru tayi ba tare da tace masa komaiba sai kallonsa da taci gaba dayi cike da tunanin meya kawoshi,ruwan da yake hannunsa ya mika mata wanda take da tabbacin yana da sanyi idan har tasha ko kadanne ze sanyaya mata zuciya

Girgiza kanta tayi cike da rashin son yin magana tace thank you

Sake mika mata cup din hannunsa yayi yace kiyi hakuri ki karba kisha ko kadanne naga ranki a bace yake kuma kyakkyawan mace kamarki bai kamata ace tana fushiba

Lumshe idonta tayi tace karka damu wannan ba bakon abu bane a wajen maimoon kawai ka tafi abinka

Shiru ya sake yi yace please ya marairaice kamar zeyi kuka

Ganin kamal na shirin takura mata ya sanyata karbar ruwan tasha kadan sannan ta nufi office din iqbaal cike da bacin rai da takaici ta tura kanta ta shiga ba tare da sallamaba sannan ta sake rufe kofar ta tsaya a cabin din fuskarta babu alamar tsoro sedai zafin da zuciyarta keyi mata

Ganin inuwar mutum a kansa ya sanyashi dagowa cike da tuhuma yake kallon maimoon da alama shima har yanzu ransa a bace yake,kallonta yayi a wulakance yace what?

Gyara tsayuwarta tayi tace nothing,nazone na tuna maka cewar dan adam abune mai matukar daraja da kima Sannan Allah baya farin ciki da mutumin da yake tozarta dan uwansa,menene ribarka don kayimin sharri don kawai ka tozartani a gaban mutane dayawa?ko ba komai ya kamata kasan cewa ni macece mai matukar rauni a zuciya kuma menene ribata idan nayi maka rubutu jikin kaya saboda tozarci,ka zageni ka mareni duk gaban mutane.......saurin daga mata hannu yayi hakan ya sanyata kasa cigaba da magana

Will you shut up! Idan kina tsoron abinda nayi miki meyasa zaki min rubutu ki sanya jikin kayana?saboda kawai kinaso duniya tayi min kallon wani shashasha bana bukatar jin wani zancen banza sannan ina sake warning dinki karki kuskura ki sakeyimin irin wannan kalar shashancin...i will never ever love you

Murmushi maimoon tayi tace me too baka yimin ba ko kadan ko alama balle har na sanyaka a raina saboda tsarin rayuwarka kadai abin gudune ga kowacce mace idan har tasan ciwon kanta da rayuwarta toh tabbas bazata taba yin shaawar hada zuri'ah da kaiba balle har ka zama uban yaranta

Mikewa yayi tsaye bayan ya dauki rigarsa da wayarsa ya kalleta yace cool smart girl zan gwada kadan daga cikin habits dina wanda baki sansuba sannan yayi murmushi ya ajiye mata breif case a gabanta ya fita

Turo baki tayi a zuciyarta tace Allah wadaran naka ya lalace sannan ta dauki breifcase din ta bishi,kamal ne yasha gaban iqbaal yace Mr london nifa gaskiya na kamu wannan kanwar taka nakeso

Over my dead body! Iqbaal yayi saurin fada yace Allah ya sauke wannan ta zama kanwata she is just a bodyguard,be jira kamal ya bashi amsaba yayi tafiyarsa da alama sauri yake yi

Bayan ya shiga mota maimoon ta shiga itama ta kalleshi idonta cikin nashi tace point of correction Mr london ni ba bodyguard dinka bace,i am your guardian sannan ba inayi maka aiki bane saboda kudinka ba komai ina yinsa ne saboda Allah

Kamar wasu kananun yara haka iqbaal da maimoon suka dinga arguing har suka karasa gida,bangarenta ta wuce jikinta babu wani karfi sai bacin rai a cikin zuciyarta

Wanka kawai iqbaal yayi ya fito dinning area,zaune ya tarar da kowa yana jiransa inda aka jere abinci sama da kala goma,zama yayi fuskarsa dauke da murmushi walida ce ta mike ta fara yiwa kowa serving abinci lokaci zuwa lokaci tana kallon fuskar iqbaal don ta gane shin plan dinsu yayi kuwa?sedai har yanzu babu abinda ta fuskanta na bacin rai a fuskar iqbaal

Ransa a bace ya kwanta akan hadadden king size bed dinsa sedai har yanzu haushin maimoon yake ji wanda bashi da wani dalili,mikewa yayi ya dauki wayarsa da wallet dinsa ya nufi hanyar fita daga dakin

Parking yayi a millionaires paradise wanda a yanzu shine gurin da iqbaal yafi samun nutsuwa fiye da ko ina,karar tashin kida tare da mata da maza jikinsu na gogar junansu suna rawa cike da nishadi shine abinda zaka fi fuskanta a club din,vip section ya wuce kamar yanda ya saba ya zauna kan couch baa jima ba aka kawo masa order din da yayi ordering tequila,rum da whiskey.

A gajiye iqbaal ya dawo tare da dove yarinyar daya samo daga club kenan,inda suka wuce apartment din iqbaal

Zaune suke a dinning inda kowa yake jiran iqbaal don yin breakfast,a hankali suke saukowa daga upstairs din har suka karaso dinning area fuskar iqbaal cike da murmushi yake kallon dad,dove ce tayi murmushi cikin tsingilallen kayanta wanda bashi da maraba da tsirara tace "morning fam"

Muryar dad a shaqe yace iqbaal wacece wannan?

Gyara tsayuwa iqbaal yayi yace dove ce mana dad she's my freind

Cikin takaici dad ya sake kallon dove yace yanzu saboda lalacewa wannan yarinyar ka dauko ka kawo min ita cikin gida har ka kwana tare da ita a daki?

Kallon dad iqbaal yayi cike da rashin fahimta yace dad it's normal ai.....hannu dad yasa ya kai masa dakuwa yace kaci gidanku iqbaal fita ka bani guri na dauki komai amma bazan taba daukar rayuwarka ta lalace a banza ba ya zama dole na dauki mataki babba a kanka

Gaba daya mutanen da suke gurin kowa banda mamaki da rike baki babu abinda sukeyi cike da munafurci da farin ciki

Ransa bace ya fita yayi dropping din dove bayan ya bata 500k sannan ya juya ya koma gida don shirin tafiya office,mamakin iqbaal shine meyasa har yanzu bega maimoon ba ko har yanzu tana fushi da abinda yayi mata a office ne,tsaki yayi alamar he don't care yace whatever....nidai abinda nasani bazan taba yarda yarinya tayi wasa da rayuwata ba sam and she is nothing to me

Sanye yake cikin hadaddiyar suit black colour kana gani kasan ba kudi kadanne ya siya wannan kayan ba,har ya nufi hanyar fita walida tace yaya iqbaal,a hankali ya tsaya ba tare da ya kalleta ba yace what?

Dad ne yake kiranki yanzu ta fada a takaice

Bai amsa mata ba ya nufi bangaren dad zuciyarsa cike da tuhumar to me kuma dad zeyi masa bayan fadan da ya gama yi masa dazu?a hankali ya tura kofar ya shiga cike da ladabin bogi ya tsugunna yace dad are you alright?

Kallon iqbaal dad yayi ransa a bace yace iqbaal na yanke shawarar yi maka aure nan da sati 3,a firgice iqbaal ya dago ya kalli dad cike da mamaki yace what?aure?how?hell no

Murmushi dad yayi yace ba shawararka nake nemaba iqbaal hukunci na yanke maka kawai na sanar dakai ne

Cike da rudani iqbaal yace dad stop this kinda jokes i don't like it

Iqbaal this is not a joke,ka fara shirye shirye nan da 3 weeks zaa daura maka aure kuma bana bukatar sake jin komai ka tashi ka fitar min daga daki yanzu

Jikin iqbaal sanyaye ya mike ya fita daga dakin,saurin daukar wayarsa yayi mom na daga wayar yace mom ashe dad ya dena sona shine kika turoni nigeria?cikin mamaki mom tace what kamar ya what's going on?

Shiru yayi yace wai fah kawai don jiya na kawo mace gida ta kwana a dakina shine dad yake fushi dazun ya kirani wai ze dauramin aure nan da 3 weeks what an insult?i am just 25 amma ake kiramin aure yanzu

Murmushi mom tayi saboda tun kafin iqbaal yasan zancen tuni sun gama magana da dad kuma ta amince da shawarar daya yanke ko dan samowa iqbaal mafitar rayuwarsa aure shine ze iya gyara iqbaal cikin sauki

Mom why are you silent?iqbaal ya fada a fusace jin tayi masa shiru

Mr london nasan komai saboda kafin yayi maka magana seda ya fara kirana yayi min bayani kuma nayi farinciki sosai da decision din daya yanke,inaso kayiwa mahaifinka biyayya kayiwa aurenka fatan nasara tare da matar taka ta fada a takaice

Ohh mom kinsan komai ma ko?that is good ashe kema kin dena sona to wai ma taya zan samu matar da zan aura cikin 3 weeks?ni gaskiya i am not ready for marriage don bashi da wani amfani a gurina kawai kayi aure ka haifi yara finally su fara kiranka da daddy sam i am not interested ya fada a fusace

Dariya mom tayi tace dad dinka baya bukatar ka samo wata yarinya ko wani abu daban saboda already ya samo maka yarinyar da zaka aura

Who's that bitch ya fada cike da jiran wacce zaa ce masa

Shiru mom tayi kadan tace your guardian "Maimoon" itace yarinyar data kwanta mana a rai muka zabi hadaku aure da ita....bata karasa magana ba iqbaal ya kashe waya cikin tsananin mamaki da tashin hankali ya sanya takalmansa ya nufi dakin "Maimoon"

Vote
Share
Comment

Heroine 🦋

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top