Chapter 19

"Duk da bacin ran da moon keyi da iqbaal be hanata yin shirye shirye ba kamar wata karamar yarinya take shirya komai gani takeyi kamar idan tayi wasa da damarta zata rasa komai,tasan morning flight zata bi ya sanyata kwanciya da wuri bacci mai nauyi yayi gaba da ita sedai time to time tana farkawa ba tare da tasan dalilin yin hakan ba

"Murmushi tayi a hankali ta janyo littafinta na addu'oi ta fara karantawa bayan ta sanya seat belt dinta idonta ya sauka a kyakkyawar background din airport din kasancewar window seat shine favorite din moon wow home sweet home ta fada a hankali inda take kallon sky a hankali jirgin yake tashi tana sake samun damar kallon sky daga nan ta mayar da hankalinta wajen karatun adduointa,sedai duk lokacin da ta tuno da cikin da yake jikinta wani irin takaici yana matukar kamata sam yaron da yake cikinta beyi sa'ar mahaifiba mutum mugu mazinaci kamar iqbaal be dace ace ya zama uba so soon ba

"Bata dade tana jira a airport ba mutum 2 daga cikin guards din gidan iqbaal suka karaso suka karbi traveling bag dinta inda tabi bayansu,oh shit!ta fada a hankali ganin sunyi parking a kofar gidanta,sam moon batayi niyyar sauka a gidanta ba son ranta a kaita gidansu ta karashe kwanakinta duk sanda iqbaal yazo sai ta koma gidanta amma tasan tunda aka sauketa nan toh umarnin dad ne ya zama dole tayi following rule dinsa,a gajiye ta shiga bathroom tayi wanka idonta ya sauka akan dining area wanda aka cikashi da food flask kala kala,wow ta fada a hankali tayi saurin karasawa ta fara budewa colours din abinci kala kala masu matukar birgewa tana da tabbacin daga gidansu iqbaal aka kawo wannan abincin,zama tayi taci abincin sosai da drinks natural masu matukar dadi da birgewa tayi mamakin yanda taci abincin dayawa sosai...simcard din wayarta ta cire ta sanja cikin tsananin farin ciki ta fara kiransu nimcy face time a lokaci daya gaba daya freinds din sukayi picking video call din

"Hey lovelies ta fada fuskarta cike da farin ciki

"Hey girl moon have you see yourself in mirror?maryam ta fada cikin tsokana

"Bata rai moon tayi kadan tace no any problem?

"Malama kalli yanda kikayi kyau kalli kumatunki omg i'm dead kin koma orobo..maryam ta karasa magana tana dariyar tsokana

"Tsaki moon tayi tace kanku akeji you know how i missed you ba,so yaushe zan ganku?

"Murmushi sukayi a tare sukace not that soon ooo ki gama hutawa sosai...sun dade suna waya kafin suyi sallama bayan sun gama tsokanar moon

"Tunda moon ta dawo 9ja iya kacin gidansu iqbaal da gidan aunty falila kadai taje ta gaishesu kowa kallo daya yakeyi mata ya tabbatar da tana dauke da ciki ganin yanda moon ta kara wani kyau mai masifar birgewa...yau kwanan moon 5 da dawowa 9ja sedai sam babu labarin iqbaal balle ma ya kirata yaji labarin ya ta iso

"Knocking din da akeyi kamar zaa fasa kofa yasa moon saurin farkawa daga baccin da takeyi a tsorace ta sanya cap a kanta ta sauko daga bed din ta nufi kofar cikin mamaki da tunanin shin waye yake buga kofa haka cikin tashin hankali,idonta cikin mamaki take bin iqbaal da kallo da kyar ta daga lips dinta ba tare da tasan tayi hakan ba tace is that you?

"Harara ya sauke mata bayan ya ajiye traveling bag din hannunsa a gefe yace "may be"

"Harararsa tayi cikin tsananin tsana ta juya zata koma daki sedai da sauri iqbaal ya kama hannunta yace hey sau nawa zan fada miki cewar doctor ta fada miki cewar ki dinga yin aiki kina exercise din jikinki amma sam baki da aiki sai kwanciya shiyasa nazo nayi checking dinki saboda nasan baki da cikakken hankalin da zaki kular min da abinda yake cikinki right?

"Kallonsa tayi a wulakance dariya kadan yaso kwace mata tace ohh ai bansan ma kana da wani baby a wajena ba,kaga mallam please don't disturb me ka koma ka tambayo yanda ake rainon cikin dai daga step na farko har na karshe tukunna sai ka dawo ka fadamin amma ba yanzuba da bakasan komaiba,bata jira ya sake magana ba tayi juyawarta daki tayi locking door tana mamakin shin wanne irin daliline ya dawo da iqbaal nigeria a irin wannan lokacin?

"Apartment dinsa ya wuce saboda tsananin gajiyar da yayi shima,wanka yayi bayan yaci abinci kadan ya nufi bar dinsa ya gama shan vodka anan sannan ya kwanta,lokaci zuwa lokaci yana tunanin shin menene ya dawo dashi 9ja?shin da gaskene yana missing moon?meyasa ya kasa zama shi kadai har seda yazo ya ganta?god this is super story shine kalar tunanin da iqbaal keyi wanda ya kasa sanin dalilin dawowarsa

"Yau kam moon a makare ta tashi ita kanta tayi mamakin irin dogon lokacin data dauka tana bacci sai bayan tayi wanka ta nufi kitchen direct ta dade tana tunanin abinda zata girka,chips da sausage sauce sai eggs tayi frying dinsa sosai gidan yake tashin kamshi duk da moon is not good in cooking amma atleast she's trying duk sanda tayi abinci yana bayar da aroma mai matukar kamshi da dadi,a dining ta ajiye plate din ta nufi bedroom da sauri jin karar da wayarta keyi.....murmushi yayi kadan bayan ya zauna a kan dining din sannan ya janyo plate din ya fara cin abincin cikin tsananin tsokana da jin kai,cikin sauri iqbaal ya cinye duka chips din da tea din data hada tare da danna wayarsa da alama yana enjoying karanta chats din da suke shigowa wayarsa,cikin farin ciki moon ta mike daga doguwar wayar da tayi jin su basma sunyi mata albishir yau zasuzo sosai take farin cikin ganin besties din nata,ganin iqbaal har ya gama da abincin nata yasa moon yin suman tsaye ranta a matukar bace tace how dare you?

"Sam be dago ya kalletaba sai cigaba da yayi yana danna wayarsa cikin tsokana da rainin hankali

"Plate din ta buga da karfi cikin rashin tsoro tace waye ya fada maka wannan abincin naka ne?

"Sai a lokacin iqbaal ya dago ya kalleta fuskarsa babu alamar dariya yace this is my house duk abinda yake ciki nawane got it?

"Da sauri ta girgiza kai tace hell no excluded me...got it?

"Murmushi yayi kadan wanda ya bawa kyakkyawan dimple dinsa fitowa sosai yace ohhh i got it mss 9ja abincinki yayi dadi sosai sedai karki manta it's your duty kullum ki dinga dafawa mijinki abinci me dadi kamar wannan

"Turo baki tayi kamar wata karamar yarinya tace no and never,sannan ta shige kitchen a dole ta sake dafa wani abincin taci,duk da moon ba wata gwana bace wajen aiki amma yau tayi aiki sosai wajen gyara gidanta tare da sanya perfumes da fresheners masu dadin kamshi sai data gama gyara komai sannan ta shiga kitchen shiru tayi kadan tana tunanin me zata girkawa su maryam omgieee this is the first disadvantage of being a slay queens freind ta fada a hankali...yanzu ni mezan dafa musu ta fada a hankali sannan tayi murmushi bayan ta danna wayarta tace chicken biryani of course

"Cikin sauri moon ke yin aikin komai da taimakon phone dinta ta kammala chicken biryani saboda tasan kawayenta suna matukar son indian dishes sannan ta dauki wayarta tayi musu order snacks da sauran pastries a deedee's chops and more

"Sosai iqbaal ke bacci saboda tsananin gajiyar da yayi wayarsa ne ya dameshi da kara da kyar yayi picking ganin tun dazu mom ke kiransa ya sanyashi yin magana kamar zeyi kuka yace hey mom

"Hey sleeping big head ina ka shige tun dazun ina kiranka mom ta fada a takaice

"Mom you know na gaji sosai ina bacci ne tun dazun,ya london?mom i am missing london like seriously iqbaal ya karasa magana yana hamma

"Of course kayi missing london amma bakayi missing dina ba ko?mom ta fada cikin tsokana

"Murmushi iqbaal yayi kamar tana ganinsa yace of course i missed you mom and i will see you soon

"Shiru mom tayi kadan sannan tace iqbaal inaso ne zamuyi magana yanzu but i dont know ko kanada lokaci yanxun

"Murmushi iqbaal yayi yace mom say your mind indai maganarki ce bata karewa kullum kina mayar dani karamin yaro something like hey mr london have you aet?kasha ruwa?ina kaje something blah blah mom i am not a kid fa ya karasa magana yana dariya

"Dariya mom tayi tace yau dai you guess it wrong,iqbaal inaso nayi maka magana ne akan azeezah yar gidan former senate iyayenta sun matsa min akan maganarta and ina ganin yanzu shine right time din daya kamata ace ka aureta,cikin tsananin mamaki iqbaal yace mom you mean zeezah?

"Eh ita mom ta karasa magana a takaice

"Zeezah shine sunan da iqbaal ya kara maimaitawa a hankali yake sake girgiza kansa tare da yin wani fitinannen murmushi yace mom we will talk about it later yanzun zanje gym

"Yanayin knocking dinsu maryam ya sanya moon gane sune suka karaso da gudu ta bude door cikin farin ciki sukayi hugging junansu,omg moon kalla yanda kika kara kyau wannan ai kinfi eiffel tower ma kyau ke kam you are yourself background so Masha Allah,turo baki moon tayi tace idiot zaki fara ko?

"I am so serious you look so take away madam see your skin omo skin like milk gang u dey nimcy ta karasa magana tana waqa cikin tsokana

"Murmushi tayi tace freinds like you are damn boring of course,guys i really missed you wallahi kun kalla yanda kukayi kyau wow nasan mazan abuja will suffer ooo

"Sun dade suna hira kafin moon taja hannunsu zuwa dining area suka fara cin abinci gaba dayansu cikin farin ciki suke cin abincin suna sake yabon yanda moon ta kware wajen girka biryani din so perfectly masha Allah,da sauri ta nufi gaban sink din ta fara yin amai dama moon ta saba tunda ta samu cikin nan is hardly taci abinci batayi aman ko da rabi ba,a tare suka zaro ido cikin tsokana suka fara waqa  Joromi Joromi
I want you to love me
Joromi baby
(Joromi Joro)
Kilode kilode o
Why you no dey call me ee
Kilode baby
(Kilode Joro)
Sosai su basma ke tsokanar moon inda suke ta farin ciki sosai sedai maryam da ta san halin iqbaal ita kadai ke matukar tausayin halin da moon zata shiga,bayan sun gama cin abincin sunyi sallah cikin farin ciki sosai moon ta fara fito musu da kayan tsarabarsu da sauran abubuwa sun dade don sai dare suka bar gidan moon sosai take farin ciki

"Hoton azeezah ne a jikin wayar tashi daya zubawa ido yana kallo,lokaci zuwa lokaci yana maimaita sunan zeezah yana sake juya wayar a hannunsa

AUTHORS NOTE

So here is an update finally...finally after a long time😩I know you are angry with me🥺so firstly i have to apologize,nayi mantuwa ban sanar dakuba kafin na fara exams ayi min afuwa nasan jiran labari sam babu dadi🥺please masu jajayen face dinnan dai ayi min hakuri 😂😩yanzu i am done with my exams and my wattpad is always active yay💃love you all❤️

Heroine 🦋

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top