Chapter 17

Har tasa hannu ta dauki kayan zata wuce dasu bedroom ta ajiyesu jikinta sanyaye,a hankali zuciyarta taci gaba da tuno mata tsanar iqbaal da kalar kiyayyar da iqbaal keyi mata"don't trust him anymore....don't trust him moon....he's going to ruined your life and break it into million pieces moon don't you ever trust him just because of his madness shine abinda zuciyarta ke fada mata,cikin sanyin jiki ta bar gurin da kayan suke ta nufi bedroom sedai bata dade ba taji ana knocking door,is that iqbaal?Shine abinda ta fada cikin mamaki saboda ta haddace bugun kofar iqbaal

Who's that?ta fada a hankali

Open and see shine amsar da iqbaal yake bawa moon duk lokacin data bukaci sanin waye yake yin knocking din,jikinta sanyaye ta bude door din,direct kitchenette ya nufa ya ajiye ledojin da suke hannunsa ya dauko cup da plate yayi serving abincin,fuskarsa hade ya karaso inda moon take tsaye ya rike hannunta kadan ya zaunar da ita akan daya daga cikin couch ya kalleta yace you have to eat something kinsan doctor yace zama da yunwa ze iya affecting baby din dake cikin ki and i dont like it....ya zama dole ki dinga cin abinci ya karasa magana yana tura mata plate din gabanta da cup din fresh milk

Turo baki tayi ganin yanda yayi wani kicin-kicin yana bata umarnin taci abinci kamar wani mutumin arziki,har sai daya fice daga dakin tukunna ta sauke idonta akan hadadden "french chicken casserole" wanda yake ta tashin kamshi wow i just love the aroma for sure,murmushi tayi ta ciro wayarta daga jikin chaji ta shiga snapchat cikin murmushi tayi snapping french chicken casserole tayiwa nimcy sending streak....sannan ta fara cin abincin sosai taji dadin abincin duk da ba wani me yawa zata iya ci ba amma tasan abincin yayi matukar birgeta atleast tasan zata ci ko babu yawa

French bread da french chicken casserole ta fara sosai take jin dadin abincin,notification message ne ya shigo wayarta murmushi tayi dama tana expecting reply din nimcy,snap video call ne ya shigo wayarta da sauri ta daga cikin tsokana tace hey gurlll

Hey queen of paris....you are so lucky moon darl kinsan french chicken casserole is my favorite dish of all the time,wow you know what..nifa idan nazo paris idan har banci ba gaskiya daidai yake da banzo paris ba,hey moon can you remember lokacin da akayi inviting dinmu wani french wedding a abuja,sunyi mana wannan kalar dish din shikenan nayiwa kaina promise idan nazo paris sai naci har ya isheni wow paris suna da top chef's wanda suka iya girki sosai

Murmushi moon tayi tace yes i know,so ya kike?

Turo baki kadan nimcy tayi tace ayam fine gurll(i am fine girl)but kinga yanda kika yi fresh kuwa moon,you are just glowing damn goddess moon kalleki you are the definition of beauty itself gaskiya iqbaal is so lucky

Kinga sarkin surutu wannan bakin naki baya gajiya da surutu,i have to sleep now kinsan nan it's already 1am and gobe inaso na tashi da wuri....murmushi moon tayi kadan tace guess what?gobe zanje "Parc des Buttes-Chaumont"

Omgieeeeeeeeee don't tell me babes,kinsan ance "Parc des Buttes-Chaumont"shine biggest park a paris....wow how i wish ace gobe tare zamuje wurin chan but no problem i am expecting your pictures nimcy ta karasa magana tana kokarin kashe waya

Okay see you tomorrow goodnight...moon ta fada sannan ta kashe waya ta mike ta wanke hannunta ta dauko sauran abincin ta sanya a freezer ta wuce daki bayan ta kulle ko ina ta karanta adduo'i kamar yanda ta saba sannan ta kwanta

"Karar da wayarsa yake yi ne ya tasheshi daga nannauyan baccin da yakeyi,sauke idonsa akan wall clock din da yayine ya sanyashi saurin mikewa har 9am amma be sani ba ganin number dad ya sanyashi ture dove daga jikinsa sannan yayi clearing throat dinsa cikin sanyin jiki yace dad

Iqbaal are you alright?ina ka ajiye wayanka tun dazu nake kiranta bakayi picking ba

Sorry dad i slept late yesterday shiyasa yau ban tashi da wuri ba,ya nigeria?iqbaal ya fada a takaice

Alhamdulillah mutanen paris,hope kaima kana lafiya?

Lafiya lau dad but paris is more boredom to me nafison london you know.....

Well i know shiyasa bana manta sunanka mr london......murmushi sukayi a tare sannan dad yace iqbaal mom dinka ta fadamin maimoon is pregnant and i am happy for you people's Allah yayi albarka ya sauketa lafiya,sedai ta fadamin cewar moon ta bukaci tanaso ta dawo nigeria so da nayi tunanin hanata sai naga kuma yafi dacewa zamanta kusa damu saboda idan ka tafi aiki babu wanda zai taimaka mata,so ina ganin nan da 2 days kayi kokarin samarwa maimoon ticket din nigeria kamar yanda ta bukata dad ya karasa magana cike da izzah

Shiru iqbaal yayi duk da ba wata matsala bace a gurinsa don zamansa da moon ma kamar wata takurace a wajensa sedai bai san meyasa tunda moon ta samu ciki yake jinta a zuciyarsa ba sedai sau da yawa yana tabbatarwa kansa yaron dake cikin moon iqbaal ke so ba ita kanta moon din ba.....but how?

Iqbaal kana jina kuwa?dad ya fada a takaice

Ammm sorry dad ina jinka wannan ai ba wani matsala bane insha Allah zanyi kokari na samo mata ticket nan da 2 days din but senayi kokari gaskiya kasan sunata X-mas celebrations ticket yana wahala wannan kwanakin iqbaal ya karasa magana yana kallon dove wacce tunda ta farka daga bacci ta hade rai tana jira ya gama waya taji menene yake faruwa

Alright!sena jika shine abinda dad ya fada sannan ya kashe waya bayan sunyi sallama da iqbaal dad ya kira moon ya sanar mata sosai take farin ciki kamar wata karamar yarinya....she's missing her family and her friends...especially madness dinsu

Kallon dove yayi bayan ya ajiye wayar hannunsa yace yo!are you okay?

Ture hannunsa tayi daga jikinta bata tanka mishi ba ta nufi bathroom for refreshment domin gaba dayansu tashinsu kenan a bacci

"Kamar wata yar tsana take tsaye jikin mirror wannan shine karo na farko da tayi attempting yiwa kanta makeup,wow she's looking more beautiful,tana cikin farin ciki sosai tun bayan data samu labarin zata je nigeria nan da 2 days,black turkish abaya ta sanya wacce tayi matukar fito mata da asalin kyawunta kamar balarabiya,she's tall,slim tana da idanu wanda zasuyi maka defining kyau na moon kadai ba tare da ka kalli sauran jikintaba,murmushi taci gaba dayi bayan ta dauki wayarta tayi mirror selfie's sannan ta dauki handbag dinta bayan ta saka wayarta da Atm card dinta ciki ta fita zuciyarta fess

Gidan miss haneefa ta nufa saboda duk sanda zata fita outing tafiso ta fita da miss haneefa ko sahiba angella saboda tafi jin dadin tafiya da wanda yasan gari,bayan tayi knocking da gudu angella ta bude kofar cikin farin ciki tace "vous êtes les bienvenus....tu es si belle"

"Murmushi moon tayi don yarinyar sosai take birgeta duk da ba french ta iyaba amma ta fahimci kalmar karshe da sahiba angella ta fada cikin jindadi tace "Merci mon amour"

"Cikin farin ciki itama miss haneefa ta fito cikin abaya outfit itama wanda yayi matukar dacewa da kyawunta tace "vous êtes les bienvenus miss iqbaal sayeed...asseyez-vous"

"Thank you moon ta fada sannan ta samu guri ta zauna tana yiwa sahiba angella dariya saboda ta kasa bude handbag dinta tana kokarin fito mata da waya

"que voulez-vous manger?miss haneefa ta fada a takaice tana kallon moon cikin farin ciki

"Saurin girgiza kai moon tayi tace Ahh no...soft drink is okay

"Cikin some seconds miss haneefa ta dawo hannunta rike da lemo ta ajiye gaban moon inda suka mayar da hankali ita da sahiba angella suna taking pictures,a hankali ta kalli yarinyar sosai ta shiga ranta tace i,m gonna miss you angella

"I will miss you too l'amour ta fada cikin muryarta da baya fita sosai

"Bata dade ba suka fita gaba dayansu sun dade a Parc des Buttes-Chaumont,suna yin pictures da videos ganin yanda kowa yake rayuwarsa a gurin yasa yanayin sake birgeta sosai a hankali tace life is sweet...but when everything is okayssssssssssssss...yes i mean okays not okay shine abinda moon ta fada a hankali,sai da suka ga yamma ya fara yi tukunna suka wuce Carrousel du Louvre inda moon tayi siyayya sosai ta siya kaya wanda zatayi amfani dasu idan ta koma nigeria da kuma wanda ta siyawa kawayenta da yan'uwanta tsaraba bayan siyayyar da miss haneefa da angella suka yiwa moon na perfumes,wrist watch,abaya da shoes shine abinda miss haneefa ta siyawa moon ta bata

"A gajiye ta sanya card ta bude dakin,sedai ganin dove hannunta rike da bindiga tare da wasu manya manyan maza guda 2 fuskarsu babu alamar wasa suma rike da nasu guns din sun sanya baqaqen kaya sun rufe face dinsu da mask ya sanyata mutuwar tsaye gaba daya ledojin da suke hannunta suka zube a kasa ta fara ja da baya tana fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,cikin bacin rai dove ta kalli mazan dake tsaye tace what are you waiting for?

Da sauri daya daga cikinsu ya dauki handkerchief din dake hannunsa ya shaqawa moon nan take ta fadi kasa inda suka kalli dove tayi wani fitinannen murmushi ta riketa kamar marar lafiya suka sanyata a mota suka fita da ita da sauri

"A gajiye yake don da kyar iqbaal ke daga kafarsa,be yi deciding yin knocking ba saboda baya bukatar bata lokaci musamman yau daya sha wahala wajen samowa moon ticket na komawa nigeria gobe,card ya fara lalubawa amma sam bega card dinsa na dakin ba,sam be damuba saboda yayi tunanin ko ya manta a hotel dinsu ne shi da dove,cigaba yayi da knocking babu alamar zaa bude masa kofa cikin bacin rai ya nufi reception ya samo wani card din ya bude dakin ya shiga sedai abin mamaki kayane barbaje da alama siyayya akayi ga kuma jakar moon itama a gefe komai na dakin hargitse kamar wanda akayi kokawa,cikin mamaki iqbaal ke bin komai da kallo what's this?shine abinda iqbaal ya fada cikin tuhuma sannan ya dauki jakar moon ya bude komai nata yana ciki hatta wayarta tana ciki....something most be wrong iqbaal ya fada jikinsa a matukar sanyaye,gaba daya dakin babu moon babu alamar inda ze sameta toh where is she?kallon ticket din dake hannunsa yayi ya ajiyeshi a gefe hakan yayi daidai da shigowar kiran miss hanifa

Da sauri iqbaal ya daga wayar cikin muryarsa me matukar dadi yace hey this is iqbaal sayeed where is she?shiru yayi yana sauraron daya bangaren jikinsa sanyaye yace but she's not here...there is is no sign of her....cikin matukar sanyin jiki iqbaal ya ajiye wayar jin maganar da miss haneefa ta fada masa cewar tabbas moon ta dawo dakinta don saida ta tabbatar da shigarta ma tukunna ta juya ta tafi but where is she?meyasa dakin ya zama yayi kacha kacha haka?meyasa moon zata fita da takalmi wari daya?meyasa zata fita babu wayarta?meyasa zata bar card dinta na daki a tsakiyar daki bayan tasan idan ta dawo dashi zata bude dakin?karar wayarsa ya dakatar dashi daga wannan tunanin ganin sunan dad ya sanya gabansa matukar faduwa sannan ya dauki wayar a tsorace

"Hey iqbaal....ya gajiya?nasan kayi kokari sosai yau dai tunda har ka samowa moon ticket dinta lazy son as you are.....kowa yana farin ciki sosai we are so excited to see her gaba daya gida ya fara cika da baqi sunaso suga yanda ka kula da maimoon dafatan ka shirya mata komai nata kasan mata lokacin da suke laulayi suna fama da kasala dole sai ana tayasu da wani aikin....dad ya karasa magana cikin farin ciki

Okay.....here is another update after a long time and i hope you like it

Heroine 🦋

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top