Chapter 14
Salam,Hello,Hi,Namaste,Bonjour,Good morning,Good afternoon and Good evening to my dearest superb innocent readers souls,i am so sorry for my late in update actually i dont have any specific time for typing and other writing stuffs😩i am just doing it whenever i am less busy,na shiga busy sosai wanda ya sanya dole na ajiye rubutu na tsawon 2 weeks amma Alhamdulillah i am back here we are so let's enjoy the weekend together as i promised you zanyi aiki with my energy,sweat,blood and tears to make Iqbaal become the best for you insha Allah....Allah ya dawo damu
"Wow Alhamdulillah shine abinda miss hanifa ta fada daidai lokacin da doctor din ke mikewa tana gyara rolling din abaya dinta sannan ta dauki box dinta tayiwa miss hanifa sallama ta fita
Har doctor ta karasa fita idon maimoon be fasa kallontaba cike da tsananin mamaki wanda bakinta ya kasa furta komai sai jirin da taci gaba da ji,a hankali miss hanifa ta zauna gefen maimoon cikin murmushin farin ciki miss hanifa tace "félicitation miss Iqbaal sayeed"(congratulation miss Iqbaal sayeed)
Da kyar maimoon tayi creating murmushi a face dinta tace thank you miss hanifa sai dai kana kallon face din maimoon kasan akwai damuwa sosai a fuskarta,mikewa tayi tace thank you miss hanifa i gotta go
Murmushi miss hanifa tayi tace thank you so much see you soon,a tare suka mike sai da miss hanifa da angel suka raka maimoon har gate din hotel dinda take zaune sannan suka juya cike da farin ciki, da kyar maimoon ke daga kafarta ta karasa apartment dinsu,ganin kofar bude ya sanya maimoon mamaki sosai sedai halin da take ciki yanzu bata da wani lokacin tambaya ko wani tunani saboda jirin da yake dibanta lokaci zuwa lokaci
Tura kofar tayi ta shiga sedai ganin Iqbaal kwance akan couch ya sanyata tsananin mamaki ganin yaushe rabonsa da zuwa hotel din da take?kuma menene ma dalilin zuwan nashi?
Mikewa yayi zaune wannan karon fuskar Iqbaal babu alamar wasa ko dariya sedai kana kallonsa zaka fahimci magic look dinsa wanda yake dauke da rainin hankali a cikinsa,dauke idonta tayi daga kallonsa ta mayar da hankalinta wajen kallon gabanta ta nufi bedroom sedai taku 2 kawai tayi taji Iqbaal yace heeeyyy bitch
Cak ta tsaya wanda a yanzu idan akwai sunan da maimoon ta tsana be wuce sunan da Iqbaal ke kiranta ba yanzu "bitch"
Mikewa yayi ya karasa inda take tsaye cikin isa da gadara yace kin iya wasa sosai miss 9ja don zakiyi yawon karuwanci a paris ai ba lallai sai kin dage akan cewa zaki biyoni ba kema kina da right din da zaki yi yawonki duk kasar da kikeso ba tare da kin tafi tare daniba ya karasa magana yana gyara tsayuwarsa
Kamar Iqbaal ya caka mata mashi haka maimoon taji zancensa fuskarta cike da tuhuma ta kalleshi tace ban fahimceka ba
Well,ina nufin nasan duk wani yawon iskancin da kikeyi tun zuwanki kasar nan,duk fitar da kikeyi ba tare da kin tambayeniba koda yake ban damu da ki tambayeni ba saboda ba zamana kikeyi ba zaman kanki kikeyi idan kuma har yanzu baki fahimta ba yanzu daga gidan ubanwa kike ko kina da family ne anan wanda zaki iya zuwa ki kai musu ziyara ba tare da sanin mijinkiba?
Jikinta ne yayi sanyi sai a lokacin maimoon taga rashin dacewar fitar da take yi ba tare da ta sanarwa Iqbaal ba sedai toh ina ta ganshi ma balle ta sanar masa?shine tambayar da tayiwa kanta cike da rashin sanin me bata amsa da kyar ta daga lips dinta da yayi mata nauyi tace first of all,don't you dare called me bitch again and lastly kamar yanda ka fada zaman kaina nakeyi a paris toh yana da kyau ka dena shigar min harka kamar yanda nima ban shiga harkar kaba,bata jira yayi magana ba ta wuceshi fuskarta babu alamar tsoro ta shige bedroom ta turo kofar ta fada kan gado zuciyarta na tsananin zafi kamar zata fashe ya rabb ni maimoon na shiga 3 ciki meya hadani da ciki?
Turo kofar da yayi a fusace ne ya sanyata kallon gurin da sauri tare da hadiye takaicin da ya bayyana a fuskarta taci gaba da kallonsa fuskarta babu alamar tsoro
This is a last warning kar na sake ganin kafarki ya fita daga gidan nan i am not begging you,i am ordering you kuma wallahi indai kika tsallake rule din dana sanya miki ranki zeyi mugun baci ai zuwan da kikayi paris on my behalf ne right to sai ki bari idan kin koma gida sai kici gaba da yawon iskancin naki ba anan ba stupid brat yana gama fadan haka ya fice daga dakin da alama gaba daya ma ya fita daga hotel din
Binshi tayi da kallo cikin tsoro ta kalli kanta a mirror a hankali tace ya Allah see this innocent maimoon bani da kowa sai kai Allah kasan ni ba mazinaciya bace ba Ya Allah ya sanya mafarki nakeyi wannan abun ba gaskiya bane....cikin kuka maimoon ke cigaba da sambatu da kyar ta mike ta daura alwala sannan tayi sallah hakan ya nuna agogo 9:30pm sai a lokacin ta fara jin yunwa sannan ta tuna rabon da taci abinci tun safe don ko abincin da taci gidan miss hanifa amayar dashi tayi
Palour ta fito tana kokarin karasawa inda zatayi warming abinci ta hango abinci ajiye gaban couch din da Iqbaal ya kwanta dazu,karasawa tayi ta bude food warmer din taga catfish ne anyi farfesunsa sai french bread da zafinsa,murmushi tayi cikin farin ciki ta zauna ta fara cin abincin ba tare da tasan ma shin abincin na waye ba,sai da taji cikinta ya koshi sosai tukunna tace Alhamdulillah bayan ta goge hannunta da tissue sannan ta mike ta nufi sink ta wanke hannunta ta goge da hand towel sannan tasa hand sanitizer lol corona virus is real
Fridge ta bude ta dauko watermelon juice me sanyi ta sha,sedai tana gama sha ta fara amai sai data amayar da abinda ke cikinta tsaf tukunna,kamar zata mutu saboda tsananin ciwon ciki da ciwon kai ga damuwa wacce itace jigon ciwon gaba daya,ya salam tabbas amai da kasala yana daya daga cikin signs and symptoms na pregnancy duk babu wanda bata yi ciki toh amma taya mutum zeyi ciki shi daya?hell no wannan ma zancen banzane hakan bazai taba faruwa ba fashewa tayi da kuka kamar karamar yarinya cikin kukan taji aman ya sake taso mata da gudu ta nufi sink taci gaba da yin aman bayan ta gama ta kashe famfo din jikinta sanyaye ta juyo jin motsi a bayanta ya sata firgita kadan ganin Iqbaal tsaye yana kallonta cike da rashin fahimta ya sanyata sake rikicewa kana kallonta zaka fahimci tsoro da rashin gaskiya a fuskarta,kamar zeyi magana kuma sai ya fasa ya juya ya dauki wayarsa daya manta sannan ya fita ba tare da yace mata komai ba,itama ajiyar zuciya tayi tace thank god sannan ta koma kan couch ta kwanta cikin rashin karfin jiki,firgigit ta mike da sauri ta dauko wayarta ta bude mobile data ta shiga safari ta fara browsing a google "how to do abortion ta rubuta tuni google ya fara bata mafitar hanyoyin da zata zubar da ciki a saukake sedai kowanne ta karanta daga karshe sai anyi warning it's injurious to health sannan yana da risk a rayuwa zata iya rasa ranta cikin lokaci kankani idan tayi kokarin zubar da ciki,tsaki tayi ta jefarda wayar ganin har yanzu bata samu wata mafitaba
Mikewa tayi ta kashe hasken dake palour din ta nufi bedroom shima ta kashe ta bar dim light bayan tayi addu'oi ta kwanta sedai har yanzu bacci ya kasa zuwar mata,kamar a mafarkin take jin motsi a palour cikin tsoro ta sake shigewa blanket gabanta na matukar faduwa,Iqbaal ne ya turo kofar ya shiga sannan ya kunna haske ya tsaya dai-dai saitin gadon da maimoon ke kwance ya dora hannunsa a wuyanta sosai yaji zafi shi kansa zazzabin nata yayi bala'in bashi tsoro wannan shine karo na farko da yarinyar ta bashi tausayi,da kyar take jan numfashi saboda zafin zazzabib dake jikinta
Jikin closet ya nufa ya dauko hijab ya sanya mata sannan ya dauketa kamar karamar yarinya a hannunsa ya nufi palour da ita,cikin mamaki da tsoro take kokarin sauka daga hannunsa sedai ya riketa sosai muryarta na rawa tace meye haka?wai ina zaka kaini?drop me please....stop it mr london
Sake riketa yayi fuskarsa babu alamar wasa ko dogon bayani yace baki san baki da lafiya ba kenan ko?ko har yanzun kina cuta bakinki be mutuba?toh palour zan kaiki ga doctor chan ze dubaki......bata jira ya karasa magana ba ta fincike jikinta daga jikinsa cike da tsoro tace ni lafiya ta kalau ka sakeni inda a zuciyarta tace tab hauka nakeyi zan yarda a gwadani gabanka ace inada ciki,ai kafin ma kasan halin da ake ciki na rabu da wannan cikin,bata karasa tunaniba ya janyo hannunta yace banason gardama and you know it be jira ta sake cewa komai ba ya janyo hannunta ya fito da ita palour din duk da fincikewar da takeyi be hana Iqbaal sake riketa sosai ba ya zaunar da ita gaban doctor din fuskar likitan a sake yace "merci"
Finally here is an update yay!!!!nagode kwarai da cikiyan da kuka dingayi,text message,phone call,whatsapp call,whatsapp message,mutanena na telegram hahaha i really missed you my lovely nana khadii (miss hamdan charming prince)tana kular min daku sannan duk wanda be fara karanta littafin hamdan ba wanda marubuciya nana khadii ke rubutawa toh lallai rayuwansa yana cikin kwale kwale,don kuwa hamdan yayan Iqbaal ne lol....see you next time yanzu dai an dawo bakin aiki💃bazaku sake neman Iqbaal ku rasa ba
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top