Chapter 10

"Hargitse gurin bikin yake sosai banda rawa da ruwan kudi babu abinda akeyi,manya manyan artist aka gayyata gurin kamarsu olamide,omah lay,joeboy,ado gwanja da ali jita gaba daya banda ihu da nishadi babu abinda akeyi a gurin cike da farin ciki banda abinci da kayan ciye -ciye fa kowa ke ci son ransa a gurin ya Rabb this is the world renowned wedding that i have ever seen

Maryam kin gani ko dama na fada miki ba zuwa zeyi ba ya Allah yanzu ya zanyi maryam?maimoon ta karasa magana idonta na shirin zubar da hawaye

Shhhhh! dont cry maimoon waye ya fada miki kyakkyawar mace tana kuka ranar aurenta?kinga karki damu nasan me zan fada idan aka tambaya ki saki ranki banaso kowa ya fuskanci wani abu a gurin nan thank god su falmata basu fahimci abinda akeyi ba hankalinsu yana wajen rawa dasu nimcyluv iyayen gulma

"Muna bukatar ganin ango da amarya a tsakiyar filin nan"ango da amarya please "shine abinda MC ke fadi wanda ba wannan ne karonsa na farko da yake faman cikiyar ango da amarya ba tun shigowar maimoon ake neman ango da amarya se dai ace masa ango yana nan shigowa amma yanzu har karfe 9:30pm ango bai shigoba

Aunty falila ce ta karaso fuskarta babu alamar walwala ta tsaya gaban maimoon da maryam cikeda tuhuma tace maimoon wai ya har yanzu Iqbaal be karaso bane?mutane sai tambaya suke yi ai ya kamata ace yanzu ya dade da zuwa kinga kirashi a waya ki fada masa yayi sauri ya karaso fah

Ammmm Aunty ai tun dazu Iqbaal ya kira maimoon yace ta fada muku kuyi hakuri bazai samu damar zuwa dinner dinnan ba wani babban uzuri ya taso masa kuma dole shi zeyi aikin yanzu haka yana office yana karasa aikin maryam ta fada tana satar kallon Aunty falila don ganin reaction dinta

What?wannan wacce irin maganar banzace haka?aiki har ranar auren mutum baze huta ba sai kace kanshi aka fara aikin office,yanzu ke tun dazu ya fada miki baze zoba shine baki fada mana ba mu sallami mutane don banga amfanin taron ba Aunty falila ta fada cike da bacin rai sannan ta bar gurin

Kallon maryam maimoon tayi tace Alhamdulillah maryam god save me Aunty falila bata fahimci komaiba

A gajiye kowa ya koma gida saboda gajiyar rawa banda hirar artist babu abinda yammatan keyi cike da farin ciki,a gurguje maimoon ta sake wanka ta fito sanye cikin farin lace sai alkyabba yellow wacce tayi matukar yiwa maimoon kyau kamar sarauniyar kyawawa

Malamai kuyi sauri motoci suna waje suna jira ke kuma maimoon kizo muje kawun niger yana jiranki,hannun maimoon ta rike har suka karasa guest room inda kawun niger ke zaune cikin kayansa na sarauta yana jiran maimoon

Kawu ina wuni?ta fada sanda take tsugunawa  a gabansa

Lafiya lau maimoon kuma ina yi miki fatan alkhairi a rayuwarki ta aurenki da zakiyi,inaso ki sani cewa shi aure bautar ubangiji ce sannan duk abinda yake da nasara baza ka taba samunsa cikin sauki ba dole sai ka fuskanci kalubale sosai kafin nasara,nasan ke mai biyayya ce inaso ki kara akan wacce kike da ita,sannan ki sani yanzu kin shiga wani section ne na rayuwarki domin yanzu zaki zauna a karkashin ikon wanine,ki zama mai hakuri da juriya sannan ki zama mai dauke kai kar ki zamo mai yawan korafi idan anyi miki abu saboda korafi yana zubar da mutunci kiyi wa mijinki biyayya ki zamo mai rike sirrin mijinki karki yarda ki dinga fadar sirrin mijinki ga yan uwanki ko kawayenki....maimoon bamu da ishashen lokaci amma idan kikayi amfani da shawarar da na baki insha Allah zakiji dadin rayuwar zaman aurenki kije Allah yayi miki albarka,Allah ya jikan iyayenki naso ace suna raye wannan ranar tazo senafi kowa farin ciki ya karasa magana yana kuka

Tuni fuskar maimoon ta wanke da hawaye kamar ruwan sama,da kyar Aunty falila ta janye maimoon daga jikin kawun niger wanda ya zamo shine kanin mahaifin maimoon,motoci sama da 20 aka turo daga gidansu Iqbaal na daukar amarya aka wuce kai amarya maimoon gidan angonta Iqbaal

Wow masha Allah,oh my god!wow....wow shine kawai abinda mutane ke fada wasu kuma suna Ayiriririri ayiiriyiri bayan anyi parking motoci a kofar hadadden gidan maimoon dake millionaires street,hadadden mansion wanda fasalta kyawunsa da tsaruwarsa ze dauki tsawon lokaci,police sama da 5 ne tsaye a bakin gate rike da guns suke bawa gidan cikakkiyar kulawa

Ya ilahi!maimoon you are the most luckiest person wlhi Nimcyluv ta fada tana kallon maimoon cike da tsokana

Aini wallahi idan nice aka kawo gidannan wlhi babu abinda ze fito dani waje har karshen rayuwata falmata ta fada tana sake daga kanta tana kallon tsananin kyau da tsaruwar mansion din

Sosai kowa yake yaba kyawun gidan inka cire maimoon wacce fuskarta ke rufe da alkyabba,a babban katafaren bedroom dinta aka ajiyeta a gefen gadonta,tuni yammatan suka mike suka fara pictures da videos saboda yanda background din gidan maimoon ya hadu sosai

Malamai ku tashi mu wuce idan kuma anan zaku kwana kuma toh,Aunty falila ta fada cikin tsokana,Haba Aunty ai wlhi da ana kwana babu abinda ze hanamu kwana saboda wannan gidan kwana cikinsa kawai ze sanya maka peace of mind mubeena ta fada cikin tsokana

Maryam ce ta kallesu tace girls 11:30pm dai tayi kunga mu da ba mazane garemu ba kuzo mu wuce kar mu jawa kanmu fada a gida,dariya sukayi suka ce wlhi kuwa sannan sukayi sallama da maimoon kowa ya watse ya barta zaune bakin gado

Bayan kamar 20 minutes da fitarsu maimoon ta mike ta cire alkyabbar da ke jikinta saboda ta fara damunta hasalima bata taba sanya alkyabba ba sai yau,toilet ta nufa bayan ta bude kofa baki bude maimoon tace oh my god!ya ilahi what a nice place ta karasa magana tana kallon bathroom din da yayi matukar tsaruwa,watsa ruwa tayi ta daura alwala sannan ta fito ta gabatar da sallolinta na nafila da nemawa kanta zaman lafiya tare da mijinta,pink night gown ta sanya sannan ta koma gefen gadon kamar wata marainiya ta zauna zuciyarta cike da tunani kala-kala

12:30am shine abinda agogon dakin ya nuna,har sha biyu da rabi amma Iqbaal be zoba,mikewa tayi ta nufi inda fridge yake ta bude wow!ya rabb cike yake da kayan ciye ciye hannu tasa ta dauko fresh milk sai cookies ta ajiye sannan ta nufi kitchen don dauko cup da plate,idonta ne ya sauka a kan jerin food flask din da aka ajiye akan dinning table din dake kusa da kitchen,a hankali ta karasa ta fara bude flasks din fried rice,white rice,chicken pepper soup,farfesun kayan ciki,farfesun naman rago,farfesun hanta,soyayyan dawisu duk sune ajiye mom tasa akayi,zama tayi ta fara cin abincin sosai yayi dadi saboda tsananin yunwar da take ji sai da taci dayawa kafin ta mike ta sanya sauran a fridge sannan ta koma dakinta bayan tayi addu'oi bacci mai dadi yayi gaba da ita saboda tun da aka fara shirin biki maimoon ba wani baccin kirki takeyi ba

"Thank you babe,dove ta fada sanda take mikewa tsaye gaba dayansu a bige suke musamman su john,chris da frank wanda sukazo daga london don zuwa bikin Iqbaal,karfe 3 su Iqbaal sukayi parking a kofar katafaren gidansa inda gaba dayansu suka wuce apartment din Iqbaal wanda yake da dakuna 6,kowa daban ya kwanta banda Iqbaal da dove da suka kwana daki daya kamar wasu gawa haka kowa yake bacci saboda tsananin buguwar da sukayi

"Ganin har karfe 6 yasa maimoon saurin dirowa daga kan gadon saboda makarar da tayi ta daura alwala ta gabatar da sallar asuba,komawa bacci tayi bayan tayi wanka,sai karfe 9 ta farka jin cikinta na juyawa saboda yunwar da take ji,a gajiye ta zira slippers dinta ta nufi hanyar kitchen,cin birki tayi ta tsaya cike da tsananin rudewa da rikicewa ganin Iqbaal da mace sanye cikin kayan bacci suna girki a kitchen cike da soyayya,kallonta yayi bayan sun hada ido ya sakar mata wani fitinannen murmushi wanda ta kasa gane na soyayya ne ko kuma na kiyayya ne ko kuma na rainin hankali ne?jikinta sanyaye ta juya ta koma daki duk da bata wani damuba saboda itama ba sonshi takeyi ba sedai ko babu komai darajar auren da sukayi be kamata ya kawo mace har cikin gidaba ya kwana tare da ita

Wayar hannunta ce ta fara kara ganin number mom ya sanyata saurin dagawa cike da ladabi kamar tana ganinta tace mom ina kwana?

Lafiya lau moon ya kwanan rashin sabo?

Lafiya lau mom Alhamdulillah

Yawwa ina fatan dai baki wahalar da kanki ba kinyi girki saboda yanzu gashinan an taho kawo muku abincin breakfast mom ta karasa magana cike fa kaunar maimoon

Cike da kunya maimoon tace toh mom angode Allah ya kara arziki

Turo kofar da akayine ya sanya maimoon saurin kallon kofar,Iqbaal ne hannunsa rike da tray ya ajiye gabanta murmushi yayi na rainin hankali a wulakanci sannan yace welcome to prison.......

Vote
Share
Comment

Baalmoon or baaldove?😂

Heroine 🦋

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top