Chapter 1
London UK
Cikin fushi ya sauka daga floor din rawar bayan ya jefar da glass cup din daya shanye giyar dake hannunsa sannan ya fito da wayar dake aljihunsa saboda karar kiran wayar da ake masa ya fara damunsa,kallon screen din wayar yayi yaga har 30 missed calls cikin fushi yace shit..shit mom what the hell are you doing?over 20 missed calls iqbaal ya fada cikin fushi
Mr london whats up?frank ya fada cikin mamaki ganin yanda lokaci daya iqbaal ya sauka daga inda suke rawa
Murmushi iqbaal yayi yace mom is calling bayan ya nuna musu yawan missed call din dake wayarsa a tare suka dinga yi masa dariya cikin matukar mamaki suna fadin OMG over 20 missed calls,ganin su frank basu da niyyar dena yi masa dariya yasa iqbaal yin tsaki yace you guys are so annoying,i gotta go,catch ya later sannan ya juya ya fita daga babban club din
A gajiya ya tura kofa ya shiga babban parlour din da sauri mom ta taso cikin fada tace iqbaal what the hell are you doing?ina kaje tun dazu ina kiran wayarka yafi sau 30 amma baka daga min wayaba kafi kowa sanin gobe by 8am flight dinka ze tashi zuwa nigeria amma babu abinda ka shirya wai iqbaal yaushe zaka zama mutum kamar kowane wanda yasan ciwon kansa da damuwar kansa?mom ta karasa magana zafafe cikin fushi
Bushewa yayi da dariya sannan lokaci daya ya hade ransa yace shut up mom,why are you always treating me like a kid?i told you morethan several times that i am not a kid,cikin fushi ya zaro wayarsa daga aljihu ya nuna mata tarin missed calls din dake wayar yace what is this?taya zaki zauna kiyi ta kirana waya almost 30 missed calls haba this is very annoying i dont like it at all kinsan irin dariyar da freinds dina suka yimin kuwa ganin wannan missed calls din naki,this is a last warning mom don't try it again ya karasa magana yana kallonta
Murmushi mom tayi saboda inda sabo ta saba ji da ganin irin wannan kalar shirmen haukan gurin iqbaal sam besan wanda ke sonsaba kuma besan wanda baya sonsa ba ko cikin abokanansa sau dayawa shiyasa ake cutar iqbaal saboda sam damuwar wani tafi damunsa fiye da damuwarsa shiyasa shirmensa har ya dena damunta sam,kallonsa tayi cikin takaici tace idan ka gama yimin fadan ka samu guri zauna
A tare suka samu guri suka zauna cikin tausayi mom tace iqbaal kamar yanda naketa yi maka nasiha kusan wata 2 kenan yau akan cewar ka kula da kanka da rayuwarka iqbaal a duniyar nan kowa shi yake kula da kansa sai Allah daya haliccemu kuma muke rayuwa cikin tsarewarsa don Allah na rokeka iqbaal ka kula da maganganun da nake fada maka cewar nigeria ba london bace there is alot of differences and challenges ya zama dole ka nutsu kayi amfani da maganar da nake fada maka,gidan da zakaje iqbaal babu wanda yake kaunarka sai mahaifinka kawai kowa burinsa ka mutu ka bar duniyar ma saboda su samu gadon mahaifinka tunda kai kadaine dansa dole sai ka kula iqbaal ka ajiye duk wani shirme ka kula da rayuwarka saboda rayuwarka yana cikin risk you have to be very careful and trust no one
Murmushi iqbaal yayi yace mom naji but wai taya zaace mutanen nan basa sona?they are all my siblings sai stepmoms dina sai kuma uncle ta yaya zaace family dinka basa sonka wai mom?
Dariya mom tayi tace iqbaal bazaka gane komaiba kawai kayi amfani da maganar dana fada maka
Murmushi yayi alamar he don't care yace cool but mom i am going to miss you ya karasa magana kamar zeyi kuka
Itama kallonsa tayi cike da tausayi tace i will missed you too mr london ta fada cike da soyayyar yaron nata
Nigeria-Sayeed mansion
Gaba daya gidan banda shirye shirye babu abinda akeyi masu aiki fiye da 10 ne suke gyare gyare a cikin gidan don tarbar Mr london(iqbaal)shi kansa Alhaji sayeed banda farin ciki babu abinda yakeyi kansancewar yaronsa tilo wanda yafi so fiye da komai a duniya zai dawo gareshi bayan shekara 20 rabon da ya sake sanya iqbaal a idonsa tun yana shekara 4 a duniya bayan sun rabu da hajiya labiba mahaifiyar iqbaal ta nisanta da kowa ta koma london daga ita sai iqbaal saboda ganin yanda kishiyoyinta da matar kanin mijinta ke kawowa iqbaal hari ganin sun kasheshi ya bar duniyar gaba daya saboda bakin cikin shi kadaine yaron Alhaji sayeed tun bayan shekara 4 da haifar iqbaal Alhaji sayeed ya shiga damuwa ganin be sake samun yaroba nan aka duba lafiyarsa bayan bincike aka tabbatar masa mahaifarsa ta samu matsala bazai sake samun haihuwa ba nan suka shiga damuwa shi da sauran matansa wanda ya auro daga baya bayan hajiya labiba,ganin yanda Alhaji sayeed ke nunawa iqbaal kauna da soyayya ya sanya matansa tsanar iqbaal da mahaifiyarsa har seda suka suka shirya mata sharri Alhaji ya saketa tun daga nan ta koma london da zama ita da iqbaal sai yanzu da iqbaal ya kammala masters dinsa ze dawo gida wajen mahaifinsa don cigaba da rayuwa
Balkissa wai bazaki tashi daga wannan banzan baccin nan ba cewar walida,tsaki balkissa tayi tace walida kinada problem wlhi me kikeso in tashi nayi miki kuma?dariya walida tayi tace tashi zakiyi mana ki tayamu shirye shiryen dawowar Mr london ko baki da labarin gobe zai dawo kuma ance morning flight ze biyo
Tsaki balkissa tayi tace so what?nifa tun kafin na ganshi ma na tsaneshi wlhi
To dama waye yake sonshi?saboda nasan zaa sameshi da shegen fadin rai he will definitely be arrogant walida ta karasa magana tana mikewa tsaye tace nifa wlh takaicina daya da banzo a matsayin yar dad ba amma all is well tunda albarkacin iyayenmu gamu zaune cikin the most dream family ever wai ni abinda nake tunani ma ko ya kamannin iqbaal din suke oho
Ganin har karfe 6:30 iqbaal be fitoba kuma bataji alamar motsin shirye shiryen sa ba yasa mom zuwa dakinsa don tasan halin Mr london,cikin tsananin mamaki mom ke kallon parlour din iqbaal kafin ma takai ga shiga dakin kwalaben giyane jere wasu duk an zubar sai iqbaal kwance akan kujera yana ta bacci ko takalmin kafarsa be cireba
Ya salam iqbaal mezan gani?mom tafada cikin tsananin fushi sannan ta fara jijjigashi tana tashinsa,da kyar ya bude idonsa cikin maye yace mom what's wrong?
Iqbaal you drunk,bayan kasan nan da 1 hour zakayi tafiya kuma kafi kowa sanin it's illegal mutum ya hau jirgi a bige?iqbaal baka jin magana sam bansan wanne irin mutum ne kai ba iqbaal,shirme yaci gaba da yi mata cikin maye ba tare da yasan inda kansa yake ba haka dole mom ta koma dakinta cikin bacin rai yanzu da wanne bakin zata bude tacewa Alhaji sayeed cewar yau iqbaal bazai samu damar zuwaba ya salam tasan babu kalar shirye shiryen da baayiba don tarbar iqbaal amma yanzu ya bata musu komai
Hajiya laila,hajiya ramlat sai Adda fatu sune jere a palour din kamar wasu kishiyoyi dama kishiyoyinne inka cire adda fatu itace matar Alhaji jalal kanin alhaji sayeed su kuma hajia laila da hajiya ramlat wanda sune matan alhaji sayeed kowaccensu ta dauko yar riko walida da balkissa
What?cikin fushi suka mike tsaye hajiya laila tace bangane baze samu damar zuwa yau ba?wannan wanne irin abune haka duk wahalar da mukasha a banza kenan tun jiya muna tsaye bamu zaunaba muna faman aiki abinci yafi kala 30 da kanmu muka zauna mukayi saboda yaron nan amma yanzu kace mana baze samu damar zuwaba alhaji
Gyara kafarsa yayi daga kan wheel chair din da yake zaune yace yanzu mahaifiyarsa ta kirani take fadamin baze samu damar zuwa yau ba sai gobe bansan meye daliliba
Amma ai kowanne dalili ai bazai hana asan dashiba tun jiya sai a sanar damu kawai dai yana sane yayi haka saboda ganin yanda ake nuna masa soyayya yasa yake ganin kowa kamar sa'ansa hajiya ramlat ta karasa magana a fusace
Murmushi Alhaji sayeed yayi yace wannan ba wani abun damuwa bane,iqbaal yana da ikon da zeyi abinda yakeso saboda ina sonsa fiye da komai a rayuwata komai na gidannan mallakin iqbaal ne saboda haka ba abin damuwa bane don anyi asarar wani abu akan iqbaal
A tare su hajiya laila suka kalli juna sannan suka tabe baki sukayi shiru cike da sake tsanar iqbaal a ransu
Parlour ta fito ta zauna ranta na matukar kuna cikin takaici tace iqbaal bazaka taba iya kula da kanka ba ya zama dole in samo maka wanda zai taimaki rayuwarka murmushi tayi a hankali tace "Maimoon" ke kadai zaki fahimceni
Authors note
Littafin iqbaal ya dade cikin raina sai dai yanzune lokacin daya dace na kawo muku shi,kuma insha Allah zanyi amfani da karfina,jinina da gumi na wajen kawo muku labarin kamar yanda ya dace the only thing i need is your support sannan comments dinku is urgently needed ina bukatar shi kamar yunwan cikina saboda insan views dinku akan labarin
Vote
Share
Comment
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top