INTRODUCTION
_DANDANO DAGA LITTAFIN_
*𝐈𝐁𝐍 𝐅𝐀𝐑𝐇𝐎𝐎𝐍*
𝘉𝘠
𝙽𝙴𝙴𝚂𝙷𝙰𝚁.𝙹𝙰𝚈
Kallon sa take cike da tausayi, kwallan daya zubo mata saman kunci ta share tana jin gaba daya karfinta ya fara gazawa, abun masarautar kara yawa yake ba raguwa ba wannan wace irin qaddara ce ta afko mata cikin rayuwa, ko a iya zaman gidan su da tayi kawai yaci ace ta gama karantar rayuwar duniyar nan sai dai kash! Ko wace rana ko wace safiya da kalar sauyin da yake zuwa wala'alla na farin ciki ko aka sin haka. Wace irin curkudaddiyar rayuwa ce qaddara zata kuma bude mata a wannan matakin.
Tabbas ita kaddara zananniayar abuce da tun kafin a haifi dan adam aka rubuta masa kalar tasa kaddarar sai dai ita tana mamakin irin tata qaddarar, kullum Kara samun hakse take game da abubuwa da yawa dake faruwa a fadin duniya.
Ta san ita din ba kowa bace kuma ba komai bace kawai qaddara ce ta hada ta dashi Wanda hakan yana nufin kuma bude sabon babi na bigirin rayuwar ta, sai dai tana addu'a da kuma fatan komai yazo mata cikin sauki.
A iya zaman da tayi cikin gidan ba tare da kowa yasan matsayin ta ba ta karanci kusan rabi da kwatar halayyar mutanen masarautar dake cike da makirci kala kala.
Numfashi ta fesar tana mikewa daga zaunen da take a bakin gadon da yake kwance ta karasa bakin window tana fesar da wani irin huci mai zafi. Tabbas ya kamata ta kawo karshen komai a wannan karon, sai dai baza ta iya ita kadai ba dole sai da taimako to amma tana tsoron plan dinta ya lalace dole ne ta samu wani bayan mahaifiyar sa ta Kara neman shawara da kuma haske, bata da Wanda tayi trusting a duniyar kamar yar uwarta sai dai matsalar da take ciki a gidan mijin ta ke hanata kusantar zuwa gidan tun ba yanzu ba, dole zata nemi mafita ta kubutar da bayin Allah da basuji ba basu gani ba.............
Anya kuwa hakarta zata cimma ruwa?
Wace irin curkudaddiyar rayuwa ce qaddara ta kuma gefo ta ciki?
Find out in IBN FARHOON
STARTING RANAR EID
LIONESS 👑
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top