1
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
*𝐈𝐁𝐍 𝐅𝐀𝐑𝐇𝐎𝐎𝐍*
𝘉𝘠
𝙽𝙴𝙴𝚂𝙷𝙰𝚁.𝙹𝙰𝚈
*Ya Allah ka bani damar rubuta abunda zai amfani al'umma gaba ɗaya, yanda na fara Allah ya nuna min na gama lapiya*
#beginning
__________________________________
*GWANDU EMIRATE*
Babbar masarautace mai cike da iko da kuma zallar mulki gami da wata irin cikakkiyar izza, tun kakan ni da suka shude a baya, masarauta ce wacca ta ginu bisa tsarin adalci da kuma wani salon mulki mai cike da zallar qasaita da kuma uwa uba kwarjini da haiba.
Marasauta ce wacce take cike da girman qasa da fadin yanki,girmanta kawai abun mamaki ne, tana daya daga cikin masarautun da ake ji dasu bama a iya Nigeria ba har Africa gaba daya. Masarautar gwandu masarauta ce da zaka iya kiranta Kai tsaye da gari guda, tana dauke da sassa daban daban ta kowane bangare kama daga bayi, barori, kuyangi, jakadai, Waziri, galadima, hakimi, da kuma iyayen gayya wato mai martaba sarki Abdussalam Jalaludden gwandu.
Mai martaba sarki Abdussalam Jalaludden Gwandu shine sarki na goma sha daya a masarautar Gwandu ya gaji wannan sarautar ne a gurin kakan sa na hudu, sarki Jalaludden Abdul-qadir Gwanda shine mahaifin sa sannan kuma bayan mutuwar sa sarauta ta dawo kan dansa sarkin yanzu wato Addussalam, shima sarki Jalaludden ya gaji sarautar ne a gurin nasa mahaifin sarki Abdul-qadir Shamsudden Gwandu, Wanda shima ya gaji sarautar ne daga gurin nasa mahaifin sarki Shamsudden Abdullahi, shima dai a gurin mahaifinsa Abdullahi ya karbi sarauta Wanda daga kanshi ne sarautar ta dawo hannun zuri'ar sa.
Asalin sarautar ta gidan Sarki Adamu Mu'azzam Dan Ali ne mutuwar sa ce tasa sarauta ta koma hannun sarki Abdullahi kasan cewar bashi da yaro namiji gaba daya mata Allah ya azirta shi dasu wannan dalilin ne yasa sarauta ta koma hannun dan Kawunsa, toh daga nan ne sarauta ta dawo ga Abdullahi Wanda hakan ba karamin haifar da fitina tayi ba.
Mulkin sarki Adam Mu'azzam mulke ne daya ginu bisa zalunci da rashin adalci da bayi da mutanen gari suka samu daga gurin azzalumin sarkin nasu na wancen zamani, shi yasa da sarauta ta koma kan adalin sarki sarki Abdullahi bayi sukayi farin ciki bayan fara mulkinsa, sosae aka samu sauyin abubuwa da yawa ciki kiwa harda rashin galihu da banzantar da makarantar da 'ya'yan bayi da sauran mutane gari keyi acikin masarauta acewar sa su bayine dan haka wahala ce kawai ta dace da su bawai neman ilima ba, sai kuma asibiti da itama ta zama tamkar makabarta a gurin hadiman masarautar wanda hakan yayi sanadin rasa rayuka da aka dinga samu a cikin masarautar, ga ciwo ga rashin abinci sai azabar aiki da bayi keyi kamar saboda shi ka dai aka hallice su.
Sosae canjin mulkin yayi wa mutanen masarautar da kuma na gari baki daya dadi dan yanzu alhmdulillah suna samun adalci, ilimi na addini Dana boko duk da a wancan zamanin maza kawai aka yarda suyi karatu Banda mata sai dai hakan bai damesu ba tunda dama mata zaman gida aka sansu dashi, asibiti ma ta inganta da magunguna kala kala ga sauyi na gine gine da aka samu sosae Wanda hakan ya Kara asassa sassa daban daban na cikin masarautar.
•••_____________________________•••
Sarki Abdussalam Jalaludden Gwandu sarki ne mai izza, qasaita, adalci da kuma uwa uba kwarjini da cikar haiba, sarki ne da gaba daya mutanen jihar kebbi da kewayenta ke alfahari dashi saboda adalcin.
Matan sa uku kuma gaba daya kafin sarauta ta koma Kansa ya aure su, Gimbiya Zuwaira itace matar sa ta farko tana da yara uku kafin auren Gimbiya Zeenatu. Saudat itace ta farko sai Habeebullah sai Siddiqa.
Gimbiya Zeenatu kuwa bayan auren ta sai da ta kusa shekara biyar kafin Allah ya bata haihuwa Wanda hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba, ganin taja dogon zango ko batan wata bata taba yi ba, sosae Abdussalam ya dinga kwantar mata da hankali a wancen lokacin ganin yanda tabi ta damu ita kuwa ba komai ya Kara daga mata hankali ba sai ganin Zuwaira ta kuma samun ciki ita kuma shiru, tayi yawon neman magani har ta gaji, bayan wata tara kuwa Zuwaira ta kuma haifo santalelen yaro mai kama da Abdussalam sak wanda yaci suna Anwar, wannan abun ba karim dadi ya mata ba sosae take alfarahi da ta kuma samun wani magajin.
Wannan haihuwa itace ta fara zaman mabudin fada sakanin Zuwaira da Zeenatu dan sosae Zuwaira ta fara yaba ma Zeenatu habaici da gorin haihuwa tun tana hakuri har takai da fara ramawa.
Cikin amincin Allah anwar nada wata hudu Zeenatu ta samu ciki murna da farin ciki gurin ta da danginta ba'a magana haka ma Abdussalam yayi farin ciki sosae da jin wannan daddan labari, bayan wata tara ta haifo danta mai kyau dashi sai dai ko awa hudu baiyi ba Allah ya dauki ran abunsa. Zeenatu tayi kukar kamar ba gobe damuwar data sanyawa kanta ce tayi sanadiyyar hawan jini kamata, Abdussalam ma yaji mutuwar sosae cikin ransa da ruhinsa yana matukar so da kaunar Zeenatu ta haihu ko dan damuwar data sanya kanta.
A kwana a tashi ba wuya gurin Allah sai ga Zeenatu da ciki bayan wata uku kuma sai ga Zuwaira da ciki, sosae kowa ke tattalin cikin sa har na Zeenatu ya Kai watan haihuwa ta haifo yarta mai kyau da ita a lokacin cikin Zuwaira na wata shida. Ranar suna jaririya taci suna Azima.
Haka Zuwaira wata tara na rufuwa ta haifo yarta wacca aka saka ma suna Umm khulthum. Toh daga kanta ne haihuwa ta tsayawa Zuwaira sai Zeenatu ta dauka.
Bayan Azima ta kuma haifar yan biyu Umaima da Unaisa sai Sadiya da Hauwa, tana da cikin Zainab ne a lokacin Abdussalam na da mukamin minister of finance kuma a lokacin ne ya fara shirin Kara aure, sosae matan sa suka daga hankalin su har suka kasa dannewa sai da suka tare su da maganar sae dae abunda Allah ya riga da ya rubuta ba'a iya canza sha, bayan wata uku kuwa sai ga amarya mai suna Aisha, doguwar macece mai cikar haiba da kwarjini fara ce sai dai ba can ba amma tana da masifar kyau Wanda yana daya daga cikin abunda ke Kara jan hankalin Abdussalam, gata masha Allah akwai diri.
Tun daga lokacin da Aisha ta shigo gidan kishi ya karu sosae su ziwaira suka dauke ta kishiya ba abokiyar zama ba kullum cikin habaici da bakar magana, kasancewar ta mai sanyin hali yasa ko daga Kai bata yi ta kallesu kuma tana bama kowa girmansa a cikin su, Sanin da sukayi cewa ita din ba kowa bace kuma ba yar kowa ba yasa abun nasu ya Kara yawa musamman gori da suka dakko yanzu, duk Wanda abun shi ya tashi a cikin su to kan Aisha yake karewa duk da abun na damunta amma bata taba nunawa ko a fuska ba ballanta har mijin su ko wani nata ya gane. Watan ta uku kawai cikin gidan amma ta gama karantar halin kowa.
*A'isha* ta kasance 'ya ta hudu a gidan su baban su malam Shu'aibu babban malamin addini ne da yake wa musulunci hidima, ba mai Kudi bane sae dae yana da rufin asiri dae dae gwargwado, matan sa biyu maman su Aisha Atine itace ta farko a gidan dan haka ita ke da yara manya, sai matar sa ta biyu Wasila suna kiran ta da inna, a gidan malam shu'aibu kishi ake mai cike da ilimi, ba hayani ba fada sannan ya'yan su kansu a hade yake baza ka taba jin cecekuce ba agidan tsakanin iyaye ko ya'ya sannan malam na kokarin yin adalici a tsakanin matansa.
Hakan yasa Aisha ta dan sha wahala a gurin abokan zaman ta ita ba haka ta taso ta ga akeyi a gidan su ba idan ba fada ma akayi ba bazaka ce matan babansu kishiyoyi bane saboda yanda suke zaman lpy.
Zainab na da wata biyar Aisha ta samu ciki, sosae Abdussalam yayi farin ciki da wannan labarin har ya kasa boyewa yinin ranar da ka kallesa zaka gane yana cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa, a bangaren matan sa kuwa ba wacca wannan abu yayiwa dadi musamman Zeenatu tsoron ta daya kar Aisha ta haifi namiji sosae tsoro ya shige ta a wannan lokacin Zuwaira kuwa ita ba wannan bane ya dame ta yanda Abdussalam ya nuna farin cikin sa ne abun ya tsaya mata a rai.
Zeenatu kuwa ganin tunani ba shi bane mafita yasa ta Kira aminiyar ta ta shaida mata halin da ake ciki ita kuwa Hasna'u ganin hankalin kawarta ya tashi ya saka ta bata shawara zuwa gurin malam dan a canza mata abunda ke cikin ta idan namiji ne ya koma mace, bada jimawa ba suka shirya suka tafi, tashi daya malamin ya shaida masu da macece ba namiji ba hakan ya kwantar da hankalin Zeenatu sosae acewar ta bata ga dalilin da zai saka tabar Aisha ta haifo namiji ba ko Zuwaira dan ta haihune kafin ta shigo da ba abunda zai saka tabarta ta haifi magaji.
Aisha kuwa sosae ta dage da addu'ar neman tsari daga sharrin mai sharri bata wasa da alwala da azkar dinta a hannu daya kuma tana rainon cikin ta har ya shiga watan haihuwa, cikin ta na da wata tara da sati biyu Abdussalam ya dauke ta ya maida ta gida sosae hakan ya sosa ransu zuwaira musamman Zeenatu da kwana biyu haka kawai taji a jikin ta Aisha namiji zata haifa ga mafarki da take ta yawan yi ta so ace a cikin gidan Aisha zata haihu dan ta ganewa idon ta ta kuma San matakin dauka da wuri.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top