Թɑցҽ 15

❄️❄️❄️❄️❄️  
    *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
      ❄️❄️❄️❄️❄️

         *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

       *WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

       *ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________

                              💥
    
     *Թɑցҽ 1⃣5⃣*

Misalin karfe biyar ta asuba alokacin tuni har an soma kiraye-kirayen assalatu,Faruq ya mike,mai martaba ma tuni shima ya farka,don yama riga Faruq din farkawa.

    "Abbana harka farka?toya jikin naka?" acewar Faruq.Kai kawai ya daga masa alamun da sauki,gashi babu damar tashiwa don gabatar da sallah,dama Faruq din yaketa jira ya tashi yayi masa alwala,tunda ya kwanta rashin lafiya Faruq ko kuma Haj.Babba ko kuwa Najmiy sune ke masa alwala idan yaso sai yayi sallar acikin xuciyarsa.Mai martaba Mk Bahago kenan akwai son ibada.

   Yanxu ma haka Faruq dinne ya shiga bathroom ya soma dauro alwalarsa,kana ya debi wani ruwan acikin buta sannan ya dauki wani bawo mara girma sosai,yaje ya daurawa Abbansa alwala,ahankali yaketa bi dashi harya kammala.Mai martaba ya shiga gabatar da sallarsa acikin xuciyarsa ayayin da Faruq kuma ya shimfida dadduma don sauke nasa faralin.

   Bayan ya kammala ya juyo yana duban Mai martaba,lazimi yaga yakeyi da hannunsa mai lafiyar.ahankali yace"Abba mai martaba bara naje na shirya donna samu na isa da wuri."
Binsa kawai yayi da ido harya bacewa ganinsa.

    Misalin shidda saura Faruq ya gama shirinsa tsaf cikin kananan kaya wanda sukayi matukar karbar jikinsa,kaya kala daya kurum ya zuba acikin laptop bag dinsa irin na school bag dinnan,kana ya ratayoshi,ya fito tsab dashi kuwa,komawa turakar mai martaba yayi ah inda ya tarar da Haj.Babba dasu Najmiy har sun fito sallamarsa.(Idan zaku tuna awani page nace tunda mai martaba ya kwanta rashin lafiya Faruq ya tare awurinsa,toh shine ita kuma Najmiy ta koma kwana tare da Hidaya sabida tsoron kwana take ita kadai).

     "Faruq har an fito?"acewar Haj.babba.

"Eh Hajiyata gwara na daka sammako donna samu na gama abinda yakaini yau dinnan,gobe kuma na juyo idan har naci nasara kenan."

   "Insha Allah zama aci nasara... " acewar Haj.Babba,ya russuna ya gaida ita da kyau,bayan sun gama gaisawar,Najmiy da Hidaya suma suka russuna suka gaidashi,ya amsa musu cikin sakin fuska.Can ya nufi inda mai martaba yake zaune asaman gado,yayi matashi da kansa akan wani pillow.Zuba masa idanuwa yayi tun kanma ya karaso gareshi.

     Tsugunnawa yayi tare da kamo hannunsa mai lafiyar,ya shiga dan murzasu kana yace"Abbana barka da safiya,ya karfin jikin naka?" ya fadi hakan tare da sakar masa murmushin karfin hali,shima mai martaban sakar masa murmushin yayi gami da daga masa kai alamun amsawarsa kenan.

Sannu ahankali wasu hawaye masu dumi suka sakko saman kuncin Faruq,da rawar murya yace"Abbana don Allah ka sanya min albarqarka acikin wannan tafiyar da zanyi bawai donna so bane,a'ah sai don kawai ya zamar min dole na fita naje na samo maka maganin lalurar nan taka,idan har naci nasara toh kuwa insha Allahu zan komo gobe Abbana,Abba bazan dawo ba har sai.......  "

   "Kai Faruq meye haka?so kake ne ka  tada masa hankali kuma?" acewar Haj.Babba cikin hargowa.Ai da sauri ya shanye sauran maganar tasa don shi baima san ya sake layi haka ba sai datayi saurin ankarar dashi.Shi kuwa mai martaba tsura masa ido yayi cike da rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa,dake Faruq din yace masa wani gidan redio ne suke nemansa ah garin lagos da gaggawa(ku tuna shi din dan jarida ne),yanxu kuma yana ce masa wai zaije samo masa maganin lalurarsa,shiyasa ya rud'e.

   Faruq ya lura da tsananin mamakin dake shimfid'e saman fuskarsa don haka murmusawa yayi yace"Abba mai martaba don Allah karka daga hankalinka ba wani abin bane kawai alheri ne ke ƙirana,nidai kawai albarqarka nake nema kafin na tafi... "

   Ahankali ya zare hannunsa dake sarke cikin na Faruq din,ya dora hannun asaman kansa,yadan bubbuga kan alamun ya sanya masa albarqan kenan.

"Nagode Abbana." Faruq ya fada da murmushi sannan ya nufi Haj.Babba itama ta sanya masa albarqa da kuma yi masa fatar alheri.

   Agurguje suka fito suka masa rakiya zuwa wurin mota,Haj.Babba na kara jaddada masa kan ya rike addu'a abaki kuma Allah yasa yayi nasara.

   Babu bata lokaci direba yaja motar suka bar gidan sai *'N.S.T.A GARAGE MINNA'*, sam bayason xuwa amotar gida shiyasa ya zabi xuwa amotar gwamnati.Acikin motar ne ya fito da system dinsa daga cikin jaka,ya shiga sarrafata cike da kwarewa,so yake yayi booking hotel kafin ya isa don bayason abata masa lokaci idan yakai, wani hotel ne yaga ya bashi shaawa don haka babu bata lokaci ya shiga booking *'GRANDBEE SUITES HOTEl IKEJAH,LAGOS'*.

   Adaya bangaren kuma yayi connecting wayarsa da Bluetooth speaker din dake kunnensa,kana yayi dialing layin Spanzy ya sanar dashi cewa yana kan hanyarsa ta xuwa gareji ne don haka idan wani abin ya shige masa duhu toh zai nemeshi kuma karya kuskura ya sanarwa su Hayat da tafiyarsa.Spanzy yace masa tuntuni ma ya sauya layi donsu.

    Isarsu garejin yayi daidai da gama abinda yakeyi,dake akwai network mai karfi shiyasa nan da nan ya gama harma yayi musu transfer din kudi ayayin da su kuma suka aiko masa da room number.Bai wani sha wahala ba ya samu ya siye ticket,bakwai saura bus dinsu ta tashi.Sai da direba yaga tashiwarsu kafin ya tada mota ya tafi.

___________________________________

        _*°•IKEJAH,LAGOS STATE•°*_

   Hayat da Roughcoin kuwa tunda garin Allah ya waye suga shiga gari,suka shiga tallar motarsu suna nemar wanda zai siyeta,don Sam yanzu basu wani samun kasuwa kamar da,gashi duk wani kudaden hannunsu sun gama karewa,kuma adaren jiya Hayat yayi mafarki da mahaifinsa yana rokansa kan ya dawo gida,tofa shine hankalinsa ya daga,da safe ya labartawa Roughcoin mafarkin nasa,kuma yace shifa washeqari zai koma gida abinsa,sosai yayi nadamar irin wannan rayuwar daya jefa kansa hadda kukanshi,shima Roughcoin bawai ya saba da irin wannan rayuwar babun bane,bai saba da rayuwar buga buga ba amma kawai don Hayat yake kokartawa,gasu da result dinsu mai kyau amma sun kasa samun aikin kwarai ta gwamnati,toh da Hayat ya kawo masa wannan zancen,ai da sauri shima yace ya gaji zai koma gida gaban iyayensa amma yau su fita suje su siyar da wannan bus din tasu idan yaso su biya basussukan da ake binsu,sauran kudin kuma su samu na komawa gida.

   Wannan karon Spanzy bai nemi Hayat ya gaya masa cewa ai mahaifinsa na kwance babu lafiya ba,don shima abinna Hayat ya soma bashi haushi,yace shifa koman iskancinsa bazai iya guduwa yabar gaban iyayensa kamar yadda Hayat yayi ba,ya biyewa wani katon Arne suka lula wata uwa duniya.Akansu ya sauya layi don kada suma sake samunshi.Ai kuwa idan sun nemeshi basa samunshi,Hayat ya daina samun duk wani information na gidansu,watannin mahaifinsa biyar kwance babu lafiya amma duk bashi da masaniya akan hakan.

     *****

  Toh! awannan ranar har karfe biyu na rana babu kanta,basu sami mai siyar bus din ba,ga wani irin yunwar dake addabarsu,gashi basu da ko sisi,akarshe yanke shawarar xuwa gidan wani abinci sukai inda anan ne suke cin bashi akodayaushe idan basu da kudi,idan sun samu kuma sai sukai daga baya dake sun riga sun zama customer,toh dayake kasuwarsu ta kwanan nan sai ahankali,ba wani samun kudin suke sosai ba,shiyasa matar ta dena basu abinci akan bashi,acewarta akwai kudaden da take binsu sosai akasa,don haka sai sun biya wannan kafin ta basu wani.Sun kwana biyu basa xuwa amma dake yau basu da wani option shiyasa sukaje.

   Matar tana ganinsu tayi wani irin Zabura daga inda take zaune,da karfinta tace"Badman,Roughcoin you again in my shop?hope say no be food issue bring u here again?I hope say na my money u bring?" ta rike kunnenta daya tana ja don susan cewa da gaske take.

    Roughcoin yace"Madam Becky pls help us jus for today,we promise to bring all ur money if we sell our bus today.... "

      "Madam pls.... " Hayat ya fadi hakan kamar zai saki kuka,hannunsa daya rike da cikinsa wanda ke masa ciwo sosai don yunwa,dake komai yau basu saka aciki ba idan ka cire ruwa.Toh dayake Allah yayi madam Becky mace mai tausayi,sai ta amince zata basu amma wannan karon idan har kudinta ya dade basu kawo ba toh kuwa police ne zai rabasu don tabbas tasan inda suke zaune sai dai idan ba guduwa ne sukai daga nan ba.Babu bata lokaci kowa ya fadi abinda yakeso yaci ita kuma tayi serving nasu.Hayat ne ya soma gamawa,yacewa Roughcoin bari yaje yayi sallar azuhur amasallacin dake kusa kafin ya gama.Akullum idan sukazo cin abinci anan,idan har lokacin sallah ne tofa sai Hayat yaje masallaci kafin yaci ko kuma bayan yaci,kuma duk madam Becky na lure dashi da hakan.bayan wucewarsa ta dubi Roughcoin wanda sai kai loma yake bakinsa tace"Rough diz ur frnd bad buh him no dey play with prayer at all... ".

   Dariya sosai Roughcoin yayi kana yace"Kinsan Waye shi?he's the son of the Niger state emir...... "

      "What????" ta fada with a suprised face.
         "Son of the Niger state emir?then wetin bring him into diz useless life?"

Roughcoin ya gajerta mata labarin Hayatudden Bahago.

   Cike da tausayi tace"Eyya I pity the guy,Roughcoin kai ba abokin kirki bane wallahi,gamuwarka da Yesu Sam bazaiyi kyau ba,how I wish him no follow ur advice at all,Rough biko let the child go back home pls,eya his mum died becuz of him.... " tuni hawaye ya soma shatato mata saman kunci na tausayinsa.Ana haka nefa sai ga Hayat ya dawo alokacin Roughcoin ya kammala cin abincinsa.Hayat yace masa ya tashi su tafi su kokarta su siyar da bus din sannan suzo su biyata kudinta don shifa ya rantse gobe goben nan zai koma gida.

   Da sauri madam Becky tace"No! Leave the money,wallahi nina yafe harga Allah... " ta fada cikin hausarta da baya fita sosai.

    Da mamaki Hayat yace"Because of wat ma?"

Cike da tausayinsa tace"Nothing! Just go back home my child cuz diz life dosnt fit you at all,accept ur destiny and go back to your family cuz they nid you,go go goooo my child..... "

    Wani uban kuka ya subuce mata,da gudu ta shige cikin shagonta gudun kada ta tara musu jama'a.Hayat kuwa duk jikinsa ne yayi sanyi qalau da maganganunta,atake anan ya gano cewa Roughcoin ne ya bata labarinsa.Da sauri ya sanya 'yar yatsa ya dauke hawayen daya dan zubo masa.ahankali yace"Abraham let's go.... " yayi gaba abinsa don sosai maganganunta sukayi tasiri akansa,ya kudura aransa cewa koda kuwa zai kwana yana bara ne toh kuwa zaiyi don insha Allahu gobe garin minna yayi.

  

  _*weldon мadaм вecĸy ĸeмa ĸιn тaĸa rawa awannan page dιn,jιnjιna agareĸι*_

_*ιna laвarιn prιnce ғarυq?*_ мυ вιѕнι🏃*_

     *тaĸυ ce*

     *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*

   

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top