Page 26-30

❄️❄️❄️❄️❄️  
    *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
      ❄️❄️❄️❄️❄️

         *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

       *WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

       *ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
___________________________________
                     💥

_*dα чαwαnku ѕun mαntα αвíndα nα ruвutα αkαrѕhєn pαgє 22,cєwα nαчí вαrí mu вíncíkσ wαní вαngαrєn wαndα ѕhímα pαrt σf lαвαrín nє wαtσ  'kαuчєn tєwí,lαвαrín вαíwαr αllαh αíѕhαtu fulαní*_

        *Թɑցҽ 26-30*

Zaman da Fulani tayi acikin gidan mai unguwa Mal.Muhammadu,zama ne na matsi da kuma takura wanda take fuskanta daga wajen matansa biyu *'MARIYA'* da kuma *'UWALE'* ,afarko farko fita daga harkarta sukai amma yadda suka ga mijinsu keta rawar kafa akanta da kuma cikinta yasa suka tashi tsaye,Mariya dama akwai biye-biyen bokaye,toh anan ne ta samu ta kama Malam ahannu,ya zamana sai abinda tace yakeyi,ya koma ya tsani Fulani wanda har takai ma ko ganinta baya son yi,amma wani abin ikon Allah ya kasa korarta daga gidan.Fulani ta zamar musu baiwa,duk wani aikatau kamawa daga zuwa debo ruwa arafi,wanke-wanke,wanki,girki da dai sauransu babu wanda batayi,ko kadan basa tausayin tutsetsen cikin jikinta,da wuya kaga Fulani ta kwanta tana hutawa sai dai in dare ne.

    Kullum cikin kuka take da kuma addu'ar Allah ya karkato da hankalin Malam ya maidata gaban iyayenta ta rokesu gafara,so da yawa takan tsareshi da maganar komawarta amma abu daya yake cewa"Babu inda zaki,zamanki daram agidannan,idan har kuwa kika ga kin bar nan gidan,toh sai dai in Mariya ce ta bukaci hakan...."

        Last time data sake masa maganar har dukanta saida yayi,su Mariya nata mata dariyar mugunta,toh tun asannan bata sake tunkarensa da batun ba.Farar mace kyakkyawa amma wahala da kuma kuncin rayuwa ya sanya ta koma baƙa,baƙin ma irin na wahalan nan.Takai tsawon kwana biyu tana nakuda agida,tana ta roƙonsu Mariya"Don Allah Yayah ku taimakeni zan mutu....." amma babu wanda ya kulata,haka ma Malam koda ya dawo yaga halin da take ciki sai ta bashi tausayi sosai,har zai nufi inda take kwance tana murƙususu,sai gani yayi Mariya ta doka masa tsawa tare da nuna masa hanyar dakinta"Ina zaka? Maza yi nan..."

    Rokonta ya soma yi"Haba Mariya nakuda fa take ki bari akira unguwanzuma karta mutu mana agida....."

Bud'ar bakinta sai cewa tayi"Toh ta mutun mana sai meh?akanta za'a fara?ko kuwa akanta ne za'a kare?inma ta mutu iyakacin mu haƙa rami acikin gida mu binne shegiya koko ya kikace ta hannun dama?"

   Uwale ta saki sowa tace"Ai kuwa Yayah maganarki dutse ce,mu ina ruwanmu da mutuwarta?wallahi malam ni wani sa'in kana bani mamaki yadda kake rawar kafa akan yarinyar nan,kodai karuwarkace kake boye mana?wato mu bama haihuwa shiyasa kaje kayiwa wata ciki awaje ka kawo mana mu mu raineta,toh wallhi da sakel babu taimakon da za'a mata saidai ta mutu anan,maganin mazinaci kenan....."

 

    _*"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...."*_  shine kalmar da Malam da kuma Fulani keta nanatawa,Malam bai iya cewa komai ba yasa kai ya fita tare da furta"Aishatu Allah ya saukeki lafiya..."

Fulani sam bata ganin laifinsu don aganinta haqqin mijinta ne ke bibiyarta,komai dake faruwa da ita bata ganin laifin kowa face nata.Su Mariya na ganin ya fice suka nufi inda Fulani ke zaune,kai wasu dai basu da imani ko kadan,basu tausayawa halin da take ciki ba suka shiga jibgarta kamar Allah ya aikosu,tun tana ihu har ta galabaita ta kasa,can tayi wani dogon nishi,sai ga yarinya ta fad'o kan tabarma tana canyara ihu.
   

      Basu damu da jinin daya rufe jikin yarinyar ba suka dan bubbuge kumatunta,jin motsin shigowa cikin gidan yasa duk suka ruga aguje xuwa dakunansu.Uwani ce ta jiyo iface-iface yayi yawa shiyasa ta shigo,tana ganin Fulani da kuma 'yar dake gabanta tana tsala ihu,ta murmusa tace"Allahu Akbar Fulani ashe haihuwarce ta iso da yamman nan?haba shiyasa nake ta jiyo ihunki ashe kina nan kina fama ne,sannu kinji inasu Mariyar suke ne?"

   Kuka Fulani ta sakar mata tace"Uwani kedai kawai taimaka ki tsaftacemu....."

Jikin Uwani yayi sanyi qalau,jikin nata ne ya bata cewa watakila su Mariyar basu taimaka mata ba,suna kallonta tana ta fama harta haihu da kanta babu taimakonsu,afusace ta nufi dakin Mariya ta daga labulen dakin,can ta hango Mariya zaune saman gado tana karkad'e kafafuwanta tare da yin tagumi.

     "Ke!Mariya amma wallahi anyi girman burodi anan,ban taba sanin cewa ke din marasa imani da tausayi bace sai yau,haba haba azatona ko baki hada komai da Fulani ba ai tamkar kanwa take agareki,amma don rashin kirki kuna kallo tasha wahala wajen nakuda,kuna kallonta tana murkususu amma babu wacce tayi tunanin taimaka mata,wa'iyazubillah! kai duniya ina zaki damu?Allah ya kyauta...."

  Ta share hawayenta kana ta nufi dakin Uwale itama ta zazzaga mata ruwan bala'i,toh duk cikinsu babu wacce ta tanka dake ita kanta Uwanin ba tayar baya bace amma kam akwai kirki.

     Uwani ta tsaftace mai jego da kuma 'yarta,sai dai kuma wani abin mamaki da suka lura dashi shine,yoyo Fulani take yi,ma'ana cutar yoyon fitsari ya kamata,sabida tsawon lokacin data dauka tana nakuda ba'a damu akaita wajen mai karbar haihuwa ba,ah kuma kankantar shekarunta shine dalilin daya sanya ta kamu da cutar yoyon fitsari wato fistula.

Fulani taci kuka harta gode Allah sanda taga jarabawar da Allah ya sake saukarwa akanta duk kuma haqqin miji dana iyaye ne.Tun daga ranar su Mariya da kuma Malam suka kara tsanarta,su Mariya suka zuga malam kan yaje har gidansu Uwani yayi mata tatas don sunga nema take ta taimaki Fulani kuma su abinda basa so kenan.Ai kuwa yaje din,ya sameta da agaban mijinta ya mata tatas kuma yaje karta kara takowa gidansu. uwani akwai xuciya toh shiyasa tun aranar ta dauwa kanta alqawarin ba ita ba gidan Malam Muhammadu amma akasan xuciyarta tausayin fulani take sosai.

   Wannan lalurar data sami Fulani ya sanya su Mariya da Uwale daina bata ayyunkansu tayi,acewarsu baza su iya cin kazantarta ba don ba dama ta giftasu sai suyi ta toshe toshen hanci suna mata iskanci,kai hatta mallam ma shi karan kansa idan ta matso kusa dashi hantararta yake.Dalilin hakan ya sanya tunda ta haihu ta kuma sami wannan lalurar sai ta rage fitowa tsakar gida sai idan ta kama dole,kullum tana cikin dakin da 'yar 3days baby dinta data shiga sahun wannan kuncin rayuwar,suyi kuka tare,suyi bacci tare,basu da mai tausayinsu ko daya balle har su samu wata lallashi.Gashi bata samun wata kulawa kamar yadda akewa mai jego,komai ita kewa kanta,idan tana neman wani abin sai ta aiki almajiri gidansu Uwani ta sammata,abincin ma da k'yar take samu taci sau d'aya arana daya,shi ma din sai idan su Uwale sunci sun rage suke kawo mata,suna bata wannan ne don acewarsu wai bazasu so ta mutu ace su suka kasheta ba.

    *WANNAN KENAN*

  Makircin su Mariya ya wuce yadda kuke tsammani,don tasa mijin nasu sukai agaba suna zugashi akan ya kori Fulani daga garin don wannan lalurar tata ta janyo yanzu sam mutane basa son rab'ansu,k'awayensu ma wai duk sun gujesu.

   Mariya ta k'arashe da"Wallahi Mallam gwara kasan nayi da ita don wallahi wannan mayyar yarinyar ta gama janyo mana bak'in jini acikin k'auyen nan..... "

  "Mallam ina ganin Kawai mu koreta kada ta sanya wannan lalurar tata ta shafemu ko kuma wani acikin kauyen nan ya kwasa don nasha jin ana cewa irin lalurar nan tata gadon maita ce.... " Uwale ta k'arashe maganarta tana taunar cingam,ta turo dankwalin kanta gaba irin ture gaka tsiyar nan.

      Malam yace"Dama so nake da zarar Allah ya sauketa lafiya tabar min gida...." ya tashi ya fice afusace xuwa dakin Fulani.Su Mariya na ganin fitarsa suka chafe hannu suna masu murna na ganin ayau plan dinsu yayi aiki.

     ***
"Mallam Muhammadu don girman Allah karka min hakan,ka taimakeni ka maidani gaban iyayena kamar yadda ka dakkoni afarko,idan ka koreni ina kakeson naje don ba sanin hanyar garinmu nayi ba....." ta karashe zancenta tana kuka.

    Axuciye mal.yace"Aishatu ki shiga duniya ina ganin kawai shine mafita,don ko kin koma gida bana tunanin iyayenki zasu kalleki balle sukai ga yafe miki,kuma ni wallahi na gaji da zama dake,matana ma basu qaunar su budi ido su ganki acikin gidan nan,nan haka yanxun nan ba gobe ba ki tashi ki dauki shegiyar 'yarki kubar min gida....."

    Cikin kuka tace"Malam ka dena shegenta min 'ya don 'yata 'yar halak ce,ta hanyar raya sunnar ma'aiki na sameta....."

Ya soma toshe-toshen hanci yace"Koma dai miye kedai kika sani,karki sake na sake shigowa na sameki anan,na baki nan da mintuna goma kibar min gida....." ya juya ya fice daga dakin.

   Ita kuwa Fulani kuka ta sakar tana mai nadamar abinta ta aikata watanni goma da suka shud'e wanda ta tabbatar haqqi ne ke bibiyarta.

       "Wayyo Allahna ta ina zan fara?ina na dosa acikin yammacin nan?" shine abinda ta fada tare da aza hannayenta asaman kanta alamun ta shiga ukunta........

     *

Misalin biyar ta yamma jirginsu Mai martaba Umar faruq Bahago ya dira ah birnin tarayya wato Abuja,su waziri wato Mal.Jabiru ne suka je taryosa da zuga-zugan motoci,suka kamo hanyar minna......

   *Kash! Low batri*

   *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ*


    

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top