54
️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
*°PAGE 54°*
*NOT EDITED❌*
---------Shidda saura yaran Capt.Sumayyah sukayi dropping nasu ah kafcecen gidanta wanda tsaya fassara muku haduwarsa k'auyenci ne,an narka uwar dukiya wajen tsara wannan gidan,duk kudinka idan har ka shigo gidan capt.Sumayyah saika raina naka don har sake baki sai kayi,zaka koma ne tamk'ar wani bak'auye.
Sauke kafafuwanta ak'asa yayi daidai da isowar wani d'an karamin k'yakkyawan yaro wanda bazai haura shekaru goma sha hudu ba aduniya.Rungumeta yayi tamk'ar zai yadda ita yana mai farin cikin ganinta.
"sweet mom I rilli missed you.." Ya fad'a cike da qaunar uwar tasa.
Ita kuwa cewa tayi"Amaan ashe wai bana hanaka wasa idan magrib ta kawo kai ba?kasan halina wlh zanyi ceasing din kwallon nan..."
Dad'a kankameta yayi yace"Mom kiyi haquri karkiyi ceasing wallahi bazan sake ba."
Tace"Idan ka sake fa?"
"ki sanya akonata kuma kisani tsallen kwado.." Ya fadi hakan with full seriousness ah sa'ilin daya cikata.Sosai Fulani ke dariyar maganarsa hadda kwalla.sai alokacin ya lura da ita.Da mamaki ya maida kallonsa kan uwar yace"Mom who is she? I've nvr seen her before..."
Saida ta soma tafiya ta bashi amsa da"She's our fam...."
Da mamaki yasha gabanta yace"Mom our family kikace fa?amma ni koda wasa ban tab'a ganin wani yazo nan gidan da sunan danginmu ne shi ba..."
Wani uban tsawa ta doka masa"Amaan allow me have some rest pls!!haba ka cika surutu da yawa,maza jeka sallami tarin gayyar abokanka daka gayyato min cikin gida and allow the visitor feel at home.."
Axuciye ya soma takawa don barin wajen ayayin da yake aikawa Fulani kallon banza,babu zato babu tsammani sai kawai suka ji ya saki siririn tsaki yayi gaba da sauri.
*"Amaannnn!!!!!"*.....
Uwar ta kira sunansa da k'arfi,cak!ya tsaya wuri guda ba tare daya waigo ba,ta sake cewa"Come back here!wat was dat hissing for?ita kayiwa koni?dakai fa nake magana?
Hawaye fal acikin idanuwansa ya juyo ahankali ya furta"Sorry mom it was meant for her not you..."
"Amaan rashin kunya kakeson ka koya right?toh wallahi ba'a cikin gidana ba don sanya Yara zanyi su maka daurin gaske sannan su maka dukan tsiya,this should be ur last time da har zan kawo bako gidan nan ka wulaqantasa kana jina ko?"
Cike da nadama yace"Am sorry mom baran kuma ba..."
Tace "Good! oya get down on ur kneels and tell her sorry! kace mata kiyi haquri Anty Aisha bazan sake miki tsaki ko wani rashin kunyar ba..."
Babu b'ata lokaci yabi umarninta,ita kuwa Fulani murmushi kurum tayi tare da jin wani zazzafar qaunar captain Sumayyah na dad'a ratsa duk wani gaba na jikinta.ashe dama ana samun masu kudi kamarta wa'enda basu bari ya'yansu su lalace ba don so?lallai kam capt.ta had'a komai da akeso.Ita azatonta ma data ce mata tana da d'a ta aza ko zato zo taga shibgegen saurayi ne ashe dai dan kwaila ne wanda ko tsaranta be kai ba (lol muje dai zuwa).
Daki mai k'yau da tsari shi aka baiwa Fulani amatsayin mallakinta,tsananin mamaki da kuma farin ciki ya hanata yiwa capt.godia yadda ya kamata don gani ma take kamar mafarki takeyi,itace yau zata kwanta kan tattausan katifa ba irin na gidan Mal.Muhammadu ba wacce take kamar na bodin bera ma har sun gwagura sun gaji,daga karshe daukeshi tayi takai waje sannan ta shimfid'a tabarma,yau gata ga tattausar katifa asama irin sakko mu gaisa dinnan,ga Ac,ga bathroom mai tsafta da kamshi,kai komai da komai da duk wani d'an gayu zai buqata dakin ya tara.
Capt.ce ta lek'o dakin tace"Idan kin gama santin daki saiki shiga wanka ki fito kiyi sallah,daga nan ki fito muna jiranki ah dinning?
"Diyenin?mey hakan ke nufi kuma?ta ayyana aranta,kamar Capt.tasan tunanin da take kenan don haka awasance tace"'yar k'auye ina nufin bayan ki gama ki samemu wajen cin abinci afalo..." Tayi gaba tana 'yar dariya don ta lura kamar Fulanin bata yi boko ba.Ita kanta sai data ji kunya don har runtse idanuwa tayi,da sauri tayi bathroom ayayin data furta ahankali"Insha Allah mama saina baki mamaki yadda nan gaba zan fiku jin wannan yaren naku."
"swey mor" ta sake furtawa,dariya ta d'an saki tace"Kai dallah ba haka yake fad'a ba ban iya ba..." Ta b'ata rai sosai,wai ita fa adole so take tace 'Sweet mom' kamar yadda Amaan ke k'iran uwarsa.
Yarinyace ta fad'o mata arai,ko yanxu awani halin take ciki?shin Yallabai sun koma gareta ko yaya?sannan kuma ya Yallaban ya qare da dangin nasa?
"Yah!Salam Yallabai don Allah ka yafe min..." ta fad'a tana mai share hawayenta,can ta sake furta"Anya yarinya na k'yauta miki kuwa?"
Ta fad'i hakan tana mai danne kukanta.
***
Abuwa budurwace wacce bazata haura shekaru ashirin da biyar ba,da ita da Mama sameera dattijuwa 'yar shekaru hamsin da dori ne ke kula da b'angaren jira-jirai agidan marayu.Bayan ta gama lallashin baby Hibbah har tayi bacci,ahankali ta kwantar da ita acikin gadonsu na yara tare da gyara mata lullubi.Waje ta nufa can backyard inda tasan babu wanda zaizo inda take,da sauri ta latso wani layi,bugu daya biyu aka dauka.
Daga daya b'angaren akace"Abuwa yadai?ta samu ne?"
Da sauri Abuwa tace"Haj.Baraka an samu irin yarinyar da kikeso kuma sosai zaki samu kudi da ita amma matsalar jinjirace don yau ne satinta daya da haihuwa,dazun nan aka kawo mana ita gidan marayu...."
Da sauri wacce aka k'ira da haj.baraka ta katseta"Badai tana k'yau ba?"
Abuwa tace"K'yan ma kamar ita tayi kanta,yarinya kamar ki wanke hannu kafin ki tab'ata..."
Dariya Haj.Barakah tayi tace"madallah an gama,ai ina da mai kula da yara wanda zaiyi ta training nasu har su girma,ita kuma wannan tunda kince jinjira ce toh zanyi kokari na samo mata wanda zai dunga kula da ita har girmanta sannan asanyata cikin training group ta soma daukar lectures,don haka zanyi adopting nata..."
Baki Abuwa ta bud'e tace"Kut! wane ke Haj.Baraka ai wannan yarinyar bazata yiwu adopting ba saidai saceta don wani ne ya kawota ya narka uban kudi yace kuma kar ah bari kowa yayi adopting dinta,nidai idan kin shirya xuwa takwas kimin waya sai mu hadu ta gaban Habee's restaurant na mika miki ita..."
"Toya zancen kudin?nawa zan baki?"
Dariyar jindadi Abuwa tayi jin anzo gun,tace"Aini kinsan nace miki agidan marayun Nima na tashi ko?"
"haka kikace min..." Acewar Haj.Barakah
Ta cigaba"Toh meh zai hana ki daukeni amatsayin wacce zata dunga kula da jinjirar?Kinga saiki dunga biyana koya kikace?"
Dan Jim! Haj.Barakah tayi kan tace"kina ganin babu wata matsala?don kinsan ranar da muka soma haduwa dake na gaya miki cewa ah porthacourt nake harkana inda babu ruwan wani da wani,don haka idan har kinsan babu wata matsala toh ki shirya xuwa takwas saimu hadu inda kikace keda yarinyar..."
Da sauri tace"Wallahi babu wata matsala hajiya ki yadda dani.."
"anya Abuwa kin tabbata don gaskia banason na shiga cikin wata matsala..."ta sake jaddada mata.
" Babu ki yadda dani... " ta sake tabbatarwa.
Ajiyar xuciya Haj.Barakah ta saukar kana tace"Toh shikenan sai kinga kirana anjiman,juz be getting ready for me,sannan kibi komai asannu kuma ah ilimance har ki samu ki fito..."
"Toh hajiya saina jiki..." sukayi sallama,da sauri ta koma ciki tana waige-waige.
Haj.Barakah tsohuwar 'yar bariki ce wacce take xaune ah porthacourt,takan bi garuruwa ta nemi wayayyeyun 'yan mata ta basu aiki na sato mata kananun yara wa'enda basu da gata wa'enda kuma basu fi shekaru goma ba,bayan sun kawo mata sai ta sallamesu da makud'en kudad'e kana tayi gaba da yaran xuwa porthacourt, tana da masu hora yaran wa'enda ke dorasu kan turba Mara k'yau har yaran su dauki karatun da aka koya musu,da yarinya ta zamo expert sai asoma aikata tana karuwanci har kasashen ketare don ta kawo mata kudi,atakaice dai muna iya cewa Haj.Barakah tana kasuwanci ne da 'ya'ya mata.(wa'iyazubillahi).
Toh bata taba karban yarinya jinjira ba sai akan *'HIBBATULLAH'* ne zata soma,ita da Abuwa had'ewa sukayi awani waje inda anan ne sukayi exchanging contacts har Abuwan tace mata idan har ta samu sarari zata sato mata yarinya kyakkyawa,toh ita babu wanda wacce tayi kalar irin Hajiyar ta mata bayanin tanaso sai Hibbar,don Hibbah jinjira ce k'yakkyawa na bugawa ajarida.
Duk abinnan da Haj.Barakah takeyi ba'a tab'a kamata ba,amma ni kam Hafnan nace muje zuwa asannu dubu zai cika.
***
Bayan sun kammala cin abinci Amaan ya mik'e zai bar wajen don shi Allah ya gani jininsa bai hadu dana wannan sabuwar bak'uwar antin tasa ba.
Da sauri Capt.ta dakatar dashi "Amaan get back and sit...."
Sannu ahankali ya komo ya zauna.
Clearing throat tayi kana ta soma jawabinta ga Amaan"Amaan kamar yadda na fad'a maka tun farko wannan family dinmu ce na kawota nan gidan ta zauna,so henceforth she will be staying with us,don haka inason ka dauketa tamk'ar yar'uwarka da kuka fito ciki daya da ita,inason ka bata girmanta da kuma darajata amatsayinta na wacce take gaba dakai,Amaan dede da rana daya banison naji ance ko kuma na gani da idona kana wulaqanta Aisha don zanyi mugun sab'a maka ne,akarshe inason muyi zaman lafiya duka,Amaan my durling am I cleared? "
Murmushi yayi kana yace"Yes!mom insha Allahu baza kiyi kuka dani ba I promise.."
Cike da jindadi tace"Good.."
Juyawa tayi ga Aisha wacce idanuwanta ke kansu tace"Aisha da fatar kema bazaki bani matsala ba?"
Da sauri tace"Mama insha Allahu Nima nayi alqawari baza'a sami kowacce matsala daga gareni ba,zamu zauna lafiya qalau da yardan ubangiji..."
Dariya Amaan ya fashe da sosai yace"Meye kuma mama?call her mom..."
Uwar ma dariya tayi da shirmensa tace"Ina ruwanka da yadda take kirana?ina ce duk abu daya dai yake nufi?"
Yace"Nooo! 'Yan gayu ne ke cewa mom ayayin da villagers ke cewa mama..." Ya sake fashewa da dariya yace"So she's a typical villager...."
Tsawa capt.ta doka masa tace"Amaan kasan dai yanxu na gama gargadinka amma kana kokarin k'arya doka ko?wat u did is disrespectful karka kuma"
"Okay am sorry mum..."
Ita kuwa Fulani halin yaron birgeta yakeyi kawai,dan kwaila dashi amma ya iya barkwanci,duk da cewa batasan bayanin da yayiwa uwar ba amma tasan magana ce ya tsoka mata.
"Villaja..." Ta ayyana aranta.
Ta sake fad'i aranta"Asannu zan baka mamaki ne dan kwaila...."
Capt. Tace"Oya maza kowa yaje ya kwanta ya huta,don gobe wkends banda aiki don haka zamu fita outing duka...."
Amaan knows what the outing means don haka yace"Yes!yes!! tomorrow is another wkend happy me,mom don Allah ki sauya min kayan wadrope..." Ya marairaice murya.
Harara ta jefa masa tace"Last two weeks na canza maka shine har sun isheka?toh baka isa ba..."
"Mom plsssss,Small Anty don Allah kisanya baki...."
Capt ta dubi Aysha tace"Aisha tashi kije ki kwanta abinki kinji?"
Ta mik'e tana murmushi tayi ciki ta barsu don bacci take ji dama.Haka dai sukayi ta dragging,dakyar ta yadda zata canza masa don Amaan akwai naci sosai.
***
Abuwa ta gama planning komai don haka tana ganin shigar mama sameerah wanka ta dauki Hibbah tayi mata goyon gaske, cikin dabarunta da kuma basirar da Allah ya bata ta samu ta fice daga gidan marayun.
Bayan ta shiga adaidaita sahu tayi picking call din Haj.Barakah wacce take ta damunta da kira,tace"Haj.muna hanya mun kusa....."
_Tofa!hibbanmu ta shiga mugun hannu,Allah ya tseratar mana da ke_
_Ku muje zuwa sabida wannan shine mafarin rayuwar Hibbah_
*#Intelligent_Writer's #*
*#Hibbatullah#*
*#Official_Hafnancy#*
**
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top