53
️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
*°PAGE 53•
_*°Wannan page din naku ne Janaf Novella ngd kwarai da gaske da yadda kuke nuna qaunarku kan wannan littafin°*_
*NOT EDITED❌*
Awanninsu Mai martaba goma sha daya da mintuna talatin asararin samaniya kan su iso garin Mumbai.ah agogonmu na Nigeria misalin biyar saura suka isa ayayin da kuma agogon India ya nuna tara na dare suka isa sabida India is 4hours,30mins ahead of Nigeria.Dama already Dr.Bature ya aika da motarsa k'irar 'Rolls-Royce Phantom'
Acikin 20mins kacal suka iso Hiranandani hospital Mumbai.Ana ida parking ah harabar asibitin,mai martaba da amininsa mai girma gwamna Alh.Aminu Abbas sukayi hanzarin fitowa babu b'ata lokaci suka soma tattaki xuwa ward din da Aryaan yake,kai kace ko matching parade suke tsabar sauri.
Sannu ahankali mai martaba ya murda k'ofar dakin ayayin da xuciyarsa ta cika da farin cikin son ido biyu da d'an nasa.Fes! idanuwansa suka sauka kan gayyar mutanen dake dakin wa'enda suka saka Aryaan ah tsakiya,iyalen Dr.Bature ne dashi karan kansa Dr.Baturen sai kuma masu yiwa Gimbiya Najmiy hidima.Kallonsa ya tsayar kan Aryaan wanda Umman tasa ke zaune agabansa tana bashi ruwan shayi da kuma Rogan gosh abaki.Aryaan duk yabi ya rame tamk'ar mai ciwon sickler,idanuwa sun rage girma ba kamar bulb eyes din da aka sanshi dasu ba,Allah sarki ciwo kenan mai sauya halittar dan'adam.
Gabaki daya hankalin mutan dakin ya koma ga wa'enda suka shigo,cike da farin ciki Dr.Bature ya mike yana fadin"A'ah mutumina barka da isowa ya hanya?"
Mai martaba bai iya bashi amsa ba don gabaki daya hankalinsa naga Aryaan ne.Aryaan din shima Abbin nasa yake kallo,can ya saki kara tare da mikewa tsaye ya ture kofin shayin dake hannun uwar yana fadin"Abbiiiiiiii......"
Cikin k'aryewar murya mai martaba shima ya furta"Aryaan my son!ashe zaka mike?wallahi ada mun cire rai akan tashiwarka,sai gashi Allah ya karbi koke-kokenmu ya sanya ka tashi,come to me my son,maza zo gareni naji dumin jikin d'ana......"
Da gudu ya isa gareshi ya rungumeshi,alokaci gud'a suka fashe da kuka mai tsuma xuciya,babu wanda baiji tausayinsu ba acikin dakin.
Can Aryaan ya cikashi ya soma dube-duben bayan ubansa kamar dai yana neman wani abin,
Mai girma Gwamna Aminu yace"Son come to me...."
Da gudu ya isa ya rungumeshi,can ya cikashi ya dubi uban yace"Abbii ina uncle yake?
Yana nufin Hayat.
Murmushi uban yayi tare da duk'awa daidai tsawonsa yace"Uncle dinka mun barosa agida sabida jama'a amma bari na kirawo maka shi awaya kuyi magana kaji?
"Abbi yi maza ka kirashi nayi kewarsa,rannan yace idan na kara girma zai siya min keke,toh kaga ai na qara girman ko?
Murmusawa akai da shirmensa don da'ace yasan yakai shekara guda da dori kwance rai ahannun Allah toh kuwa da beyi wannan maganar ba.
Bayan Hayat ya daga wayar yace" Assalamu alaykum Yayah har kun isa?ina d'an nawa yake?bani shi naji muryarsa.
Alokaci gud'a ya jerowa Mai Martaba wadan nan tambayoyin,
Mai martaba yace"Gaya nan yana jinka...."
Aryaan ya wafce wayar tare da kange wayar akunne yace"Uncle ni nayi fushi dakai shine kaki zuwa ka ganni ko?
Ajiyar xuciya Hayat ya saukar kana yace"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! d'ana ashe dai Allah zai nuna mana tashiwarka?Allah abin godia,kayi haquri son idan kuka dawo zamuyi magana kaji ko?
Sun dad'e suna magana awaya,da kyar aka kwace wayar ahannun Aryaan don Dr.Bature ne keson sake duba jikin nasa.
Dr.Bature yace"Kai dai na rasa wacce irin soyayyace take tsakaninku da wannan uncle din naka..."
Bayan an duddu bashi Dr.Bature ya tabbatar musu da cewa lallai Aryaan ya warke,yanxu haka komansa normal yake,acikin wannan daren suka dunguma sai gidan Dr.Bature don washeqari sukeson su komo Nigeria tunda ance yanxu Aryaan normal yake.
¶¶¶
Washeqari qarfe goma na safe tayiwa su Captain Sumayyah ah headquarter don anan ne aka kaisu prosper,tun adaren jiya da suka ji azaba tayi yawa babu shiri suka fad'i wanda sukewa aiki,ai babu b'ata lokaci acikin tsohon daren nan akaje aka taso Alh.Ibrahim Nabalaska agaba don sanannan dan kasuwa ne,babu wanda ya tab'a lafiyar jikinsa an barshi ne har sai captain Sumayyah tazo don ita din ce daidai dashi,sai zazzare idanuwa yake tayi tamk'ar wanda beda masaniyar wannan al'amarin.
Yana ganin shigowar Captain Sumayyah saida 'yan hanjin cikinsa ya kada don yana da labarin yadda bata daukar shits.Bayan Su corporal Aliyu sun gama yi mata bayani,cike da tsana take bin Alh.Nabalaska da kallo kan ta soma zagayeshi,shi kuwa wani mugun tsoronta ne ya tsirgu cikin xuciyarsa Wanda har hakan yasa jikinsa ya dauki rawar mazari.Can Capt.Sumayyah ta zagayo ta ganbanshi tana huci,wani uban tsawa ta doka masa tace"Don Allah dubarshi kamar dai mutumin kirki alhalin koren maciji akarkashin koren ciyawa kenan ake gani anan,mutum na gab da rami bazai nemi kusanci da ubangijinsa ba a'ah sai dai neman abinda zai kaishi gidan wuta,toh dan bantan ubanka tashi ga yarinyar nan na kawo maka ita da kaina tashi maza ka fille mata kan,sannan kuma ka cire mata mamunan nata tunda abinda kake so kenan shiyasa ka sanya asatota,ko baka ji abinda na fad'a bane?ka tashi nace...."
Bata damu da tsufansa ba don hukunci ya zama dole kokai waye kuwa,ta saukar masa da wani wawan mari,tuni ya saki fitsari tsugunne anan tare da fashewa da kuka.
Ta shiga nannad'e hannun rigar kakinta tace"Ai baka ma soma kuka ba tukun don mutuwa zakayi.."
Waro idanuwa yayi jin ta ambaci mutuwa,ganin yanayinsa yasa ta sake cewa"Yes!ka jini dakyau cewa nayi mutuwa zakayi,dan babban bura uba ashe dai kana tsoron mutuwa shine kai kake kashe bayin Allah akan neman abin duniya?ashe rai tana da dadi kake rab'a mutane kamarka da ita ta k'arfi da yaji,cikin azab'a da kuma rad'ad'i?ai wallahi babu sassauci ko ka gayan mutane nawa ka halak'a ko kuma na soma aikina....."
Haquri ya shiga bata akan ko nawa sukeso ta fad'a masa zai basu don kawai akashe maganar basai ankaisu headquarter na Abuja ba inda anan ne za'a zartar musu da hukunci.Ita kuma arayuwarta abinda ta tsana kenan wato cin hanci,ta tsani duk wani mai karban cin hanci.ai kuwa batayi wata-wata ba ta daukeshi da wani mahaukacin mari aqaro na biyu,axuciye ta soma magana"Don iyayenka dubar ni dakyau kaga na maka kalar irin mutanen dake karbar cin hanci ne?ko kuwa an gaya maka cewa ina yunwar kudi ne?ko kuma dai mantuwa kayi da wacce take tsaye agabanka *'CAPTAIN SUMAYYAH ABBAS'*?"
Miko mata wani kakkauran rodi Corporal Aliyu yayi,da Sauri ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu tace"Dakata corporal ai wannan laifinsa ya girmi hukunci da rodi,sakamakon tayin cin hancin da yai min zai shiga dakin kankara na 1hr kana amaidashi dakin shock for 30mins,that will serve as a welcome program to him and a sound warning, maza nace ku daukeshi....."
Da Sauri suka isa gareshi yana kuka tare da rokanta kan ta yafe masa amma ina Capt.Sumayyah bata canza 'A' dinta.bayan sun fita dashi ta dubi su prosper wa'enda keta rawar dari tace"Ku kuma an kulle chappy naku anan sai kuma nacan babbar headquarter..." Ta fad'a tana mai murmushin mugunta.
Juyowa tayi ga Fulani wacce itama tsananin tsoronta ne ya rufeta,murmushi captain tayi tare da shafa kan Fulani tace"Don't worry baby babu abinda zan miki okay?yanxu muje eatery muyi break kinga bamu karya bafa.."
Bata jira ta cewarta ba ta makala shades nata kana tajah hannun Fulanin suka fice,yaranta na ganinta suka taso zasu bita tace"Don't worry I can take care of myself... "
Komai na Captain Sumayyah na birge Fulani ta rasa meyasa?kuma akwai tambayoyi cike fal aranta wanda takeson yi mata amma sai nan gaba idan suka sami nutsuwa.Nima Hafnan nace ai kema Fulani akwai tambayoyi masu dama wanda ita kanta Captain Sumayyar keson miki.
*•Ah gurjuje pls•*
Atakaice dai sai misalin hudu saura komai ya kankama,Captain Sumayyah sun had'a duk wani bayanan da za'a buqata acan babbar hedikwata Abuja,yanxu haka sunyi pushing case din Alh.Ibrahim Nabalaska da kuma yaransa can inda anan ne za'a zartar musu da hukunci.
Ah gurguje Captain Sumayyah ta had'a yanata yanata suka baro Kaduna xuwa Abuja inda nan ne ainahin location nata,straight ofishin *'general major Alkali Muhammad Nafi'u'* ta nufa Wanda shine oga kwata-kwata.
Cire Shades dinta tayi don bashi girmansa,bayan sun gaisa yayi mata tayin Zama idanuwansa kyam akan Fulani wacce ta kame jikinta,ganin taki zama yasa Capt.Jawota ta mata rad'a akunne"Wai ba nace ki saki jikinki ba ko kuwa so kike na tub'eki na zaneki?
Da sauri ta girgiza kai alamun a'ah,ta sami waje ta zauna.
General yayi clearing throat nasa yace"Captain haqiqa bansan wacce irin kalma ce ta dace nayi amfani da ita wajen gode miki ba don ba karamin kokari kike yiwa al'umma ba,Allah ne dai kawai zai biyaki,yanxu wannan itace yarinyar da aka sato?"
"yes sir itace...."
Duban Fulani yayi yace"Ke yarinya daga ina ne suka satoki?"
Wiki-wiki tayi da ido ta dubi Capt. Kan ta fashe da kuka mai tsuma xuciya,arud'e general yace"A'ah Captain Sumayyah wat's going on?daga tambaya kuma sai kuka?ko sunci nasarar yi mata wani abin ne?
Tsawa Capt ta doka mata"Shut! the hell up! Wallahi Aysha karki bani haushi anan if not zan zaneki dakyau,don't allow me repeat myself again for the very last time am warning you,haba ke komai kuka kuka?shin kukan ne zaiyi maganin matsalarki?mtswwww.."
"Mama kiyi hquri bazan sake ba..." ta fad'a tana mai kokarin danne kukanta,sanyi Capt.taji aranta don sosai take qaunar yadda yarinyar ke darajata.
Capt. tayiwa General bayanin Fulani,akarshe ta duka gwiwa har kasa tace"Don Allah Sir na rokeka abarta awurina nadan lokaci tunda kaji tace bazata iya tuna komai agame da ita ba Wanda hakan ke nuni da cewar tabbas dama can tana cikin wata babbar matsalar ce kafin asatota,aganina da kuma tunanina watakika aikin sihiri ne ke dawainiya da ita,sir pls juz grant my request kaga ban tab'a rokan wata alfarman awajenka ba...."
Saukar da ajiyar xuciya yayi kana yace"Naji amma sai kin amince zaki aureni...."
Da sauri tace"Zanyi tunani akan hakan sir!.."
Murmushin jindadi yayi ganin atleast ayau Capt Sumayyah tadan tabuka abin kirki kuma duk akan case din Fulani,don sau da yawa tasha turning down din marriage request nasa.Ya dauwa kansa alqawarin zai taimaki Fulani muddin ya samu ya auri Capt Sumayyah.
Ita kuwa Fulani tsananin mamaki ne ya cikata,ashe dama Capt.Sumayyah bata da aure?toh ina ta sami danta da take ikrarin tana dashi wato *'AMAAN'*?kodai shege ne?
Da sauri xuciyarta ta kwabeta akan karta soma mummunan zargi akanta.
Kafin su wuce saida Capt Sumayyah ta tursasa su prosper kan su gaya mata inda suka sato Fulani,bata bari Fulani ta sani ba alokacin da taje tambayarsu.sukace mata daga garin minna ne suka sato ta.Jin sunan garin ya sanya numfashinta soma yin sama da kasa don arayuwarta bata qaunar abinda zai sake maidata garin Minna,(ko miye dalili?).
Gidanta dake Asokoro road suka nufa.
****
Duk yadda Yarima Hayat yaso Jabir ya gaya masa gaskiyar magana agame da Aisha Fulani da 'yarta abin ya faskara don Jabir kafewa yayi akan shi besan komai akai ba,don makirci har kuka Hayat saida yayi masa yana dad'a rokansa hadda bashi makud'en kudad'e amma fir! waziri Jabir yace besan komai ba,akarshe ma tashiwarsa yayi yabar masa dakin.Cike da jin haushinsa Hayat ya nemi Awwal ya gaya masa yadda sukai kuma ya karawa Awwal wasu kudad'en yace ya saka idanuwa kan Jabir,ya kasance duk ina Jabir din zashi ya dunga bin bayansa ah b'oye har agano inda suka b'oye matar.
_Tofa!ko wacece wannan captain Sumayyar?_
_mudai je zuwa_
*#Intelligent_writer's #*
*#Hibbatullah#*
*#Official_Hafnancy#*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top